Showing 126001 words to 129000 words out of 153964 words

Chapter 43 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3782

gama rantsar da ita. Sanin halinta da yadda ya sami amsa daga wajenta a jiya yasa kai tsaye ya tambaye ta.

"Me kika sani game da shari'ar nan?"

Anna ta girgiza kai tana kallonsa.

"Ni babu abinda na sani game da shari'ar nan, babu wanda yake fad'a min me ake ciki, na gaya maka hakan tun ranar da ka tambayeni, ko ka manta ne d'an bature?"

Da yawan mazauna wajen suka murmusa jin sunan da ta kira shi, Adam ya girgiza kansa muryarsa a hankali yace.

"Ban manta ba na sake tambayarki ne kawai ko kin samu wani abin."

"Ban san komai ba..." Tana magana tana yin alama da hannayenta.

".... iya hirar Sule da mahaifiyarsa da na gaya maka tun wancan lokacin ita kawai na sani."

"Ko zaki iya yiwa kotu bayani kamar yadda kika yi min?"

Ta d'aga kanta.

"Me zai hana? Ai dole ne ma in fad'a."

Sai ta juya ta kalli Alkalin.

"Zan fad'a maka komai yanzun nan kotu, shekaru 'yan kad'an da suka wuce kafin Hajiya ta rasu ku fara wannan shari'ar, Yaya Danjuma ya bani wani d'aki a jikin katangar b'angarensu Sule, to ina nan zaune a ciki kullum, sai wani gefe na d'akin ya rufta har ina iya lek'o d'akin mahaifiyar Sule daga nan, kuma kullum ina jin zancenta dana 'ya'yanta.

Amma zancen dana fi ji shine in Sule ya shigo wajenta sai tayi ta masa fad'a tana cewa ya zama bawa a Babban gida, yana ganin kowa yana da abinyi amma shi yana zaune kawai ya kasa magana a basu gadonsu suma su sami kud'i, shi kuma yace mata ai ba zai iya bijirewa umarnin Hajiya ba, kullum-kullum suke ta yin wannan zancen har Hajiya tazo ta mutu..."

Sai ta had'e tafukan hannayenta biyu ta kwanta akansu alamun bacci. Adam ya juyo daga wajenta ya kalli Alkali yace.

"Ya mai girma mai shari'ah, Tun a farko munji daga shaida ta biyu cewa mahaifin Sule ya rasu amma Hajiya ta hana a raba musu gado kuma saboda irin biyayyar da yake mata baice komai. Idan muka yi la'akari da wannan bayanin zamu ga cewa bayan anyi hakan mahaifiyarsa ta shiga tursasa shi cewa bai kamata ya yarda da hakan ba."

Yana gama fad'in haka ya juya wajen Kutama ya bashi izinin nasa tambayoyi, amma ga mamakin kowa sai ya girgiza kansa kawai alamun bashi da tambaya akanta.

Ya yarda cewa a wannan gab'ar, babu wani abu da kokarinsa zai canja, Adam ya riga ya tunkari shari'ar baki d'ayanta ba tare da wani kewaye-kewaye ba irin nasa kuma yana baiyana komai ne a ainihin gaskiyarsa, don haka kudirin daya dauka a baya nana ganin ya toshe duk wata hanyar samun nasararsu ba zai tab'a tabbata ba, a yanzu haka ma shi ba ta wannan shari'ar yake ba, tunaninsa hange kawai yake na yadda zai kare tauraruwarsa daga dusashewa.

Adam ya d'anyi shiru sanda ya lura da rubutun da Alkalin yake yi, bai sake cewa komai ba har ya sai da ya k'arasa ya d'ago ya kalle shi sannan yayi magana.

"Ina neman kotu ta bani damar kiran shaidata ta k'arshe."

Babu shiri Kutama ya had'iye yawu cikin mak'ogwaronsa yayin da Alkalin ya zare gilashinsa ya kare masa kallo daga inda yake zaune.

"Shaida ta k'arshe? kana nufin daga wannan shaidar ka rufe shari'ar daga b'angarenka?"

Adam ya gyad'a kai gami da lumshe ido.

"Haka nake nufi ya mai shari'ah."

Sai ya maida gilashinsa sannan ya ware hannunsa a iska.

"Kotu ta baka dama."

Ya amsa hakan ta hanyar cewa.

"Zanso in kira Sulaiman Muhammad Idris a matsayin shaida ta ta k'arshe."

Babu b'ata lokaci kuwa aka shigo da Sulaiman wanda kowa yafi sani da SULE cikin wajen, biye dashi d'ansanda d'aya ne wanda ke nuna cewa a hannun hukuma yake, idanunsa sunyi zuru-zuru alamun tashin hankalin k'arara a cikinsu, kuma kamar yadda idanun suke haka ma muryarsa ke fita sanda ake rantsar dashi.

"Ina so ka yiwa kotu bayanin abinda ya faru bayan rasuwar mahaifinka."

Wannan itace tambayar da Adam yayi masa bayan ya gama amsa dukkan wasu tambayoyin da suka shaida matsayinsa a cikin zuri'ar da kuma irin alak'arsa da Hajiya Balaraba.

Sai ya kawar da kansa ga barin kallon 'yan Babban gida, tun daga ranar da mahaifiyarsa ta fad'i ta mutu yake jiran wannan ranar, ya riga ya san zata zo kamar yadda yake kwana da sanin cewa ranar mutuwarsa zata zo.

Shi yasa a baya ranar da aka fara bud'e shari'ar nan, da kyar ya yarda ya tsaya a matsayin shaidar Kutama, don sai da Kawu Danjuma yasa baki tukunna sannan ya yarda yazo, tun a lokacin gani yake kamar daya bud'e baki zai fad'i gaskiyar komai ne, amma sai talalarsa ta k'aru.. Ubangiji ya k'ara masa lokaci Adam bai zarge shi ba a sannan.

Amma a yanzu daya riga ya gama nemawa k'annensa mafita, ya yarda komai yazo k'arshe, shi yasa lokacin da 'yan sanda suka zo tafiya dashi baiyi musu ba yabi su, kuma baiyi wani musun ba a lokacin da Adam ya tsare shi da tambayoyin da kullum suke haskawa a cikin mafarkinsa. Ya bashi amsa tiryan-tiryan kamar yadda yake maimaitawa a yanzu.

"Hajiya ta hana a raba gado bayan mahaifinmu ya rasu, saboda bashi da wani kud'i ajiyayye sai gidaje kawai guda biyu wad'anda 'yan haya ke ciki, saboda haka tace baza a sayar da muhalli ba sai dai a cigaba da karb'ar kud'in hayar kawai wanda shi kuma ba wani abu ne mai yawa ba kasancewar tun farko mahaifinmu bai d'auki gidajen da muhimmanci ba yafi maida hankali kan sana'arsa. Bayan wani lokaci sai kud'ad'en dake hanunmu suka k'are ni kuma ba wata sana'a nake yi ba gashi auren k'anwata dake bina ya taso kuma babu wani tallafi da muke samu, saboda haka mahaifiyata ta matsa cewa dole ne mu samarwa kanmu mafita ba zai yiwu muyi ta zama a haka ba.

Babu irin bayanin da banyi mata ba akan girman abinda take son mu aikata amma ta tursasa ni cewa idan muka kawar da Hajiya daga duniya komai zai bud'e mana don in babu ita, ba wanda ya isa yayi magana akan gidajen muna da damar sayar da abinmu.

Ita ta tsara komai da cewar mu saka mata guba a abinci ta yadda baza a zarge mu ba, sai dai a zargi wanda ke da alhaki da abincin, babu yadda na na iya, dole na yarda da ita kuma na bada shawarar mu d'orawa Bintu hakan tunda ita ke kula da abincin safen Hajiya kuma kowa ya riga ya san yadda Hajiya bata sonta, sai ayi tunanin ta kashe ta ne saboda hakan.

Ko kad'an bamu san shirin Habiba na son kashe Hajiya itama a wannan ranar ba, don haka ban san cewa ba Bintu ce tayi kokon ba kamar yadda ta fad'a, abinda na sani kawai shine a wannan safiyar na sami filas d'in Hajiya wanda na san ana zuba mata koko a ciki, na zuba garin gubar da mahaifiyata ta bani yadda in an zuba kokon zai had'e da ita sannan naje na sami Bintu wadda ke wanki a lokacin..."

Duk wannan bayanin da yake yi, idanun Fadeelah na sunkuye tana kallon teburin gabanta, sai da yazo daidai nan sannan ta d'ago ta kalle shi, take komai na wajen ya janye daga idanunta lokaci ya d'auke ta daga cikin kotun zuwa wani zamani can baya.

"Ke!"

Wata k'atuwar murya a gefe ta janyo ta daga cikin tunaninta, ta zabura da sauri sanda atamfar rigar da take wankewa ta sub'uce cikin bokitin kafin ta d'aga idonta akan siffarsa, Yaya Sule.!

Wani mutum guda d'aya da baya tab'a barin tayi yini guda a rayuwarta ba tare da hargitsi ba, a lokuta da yawa da tunaninta ke tafiya rubutun wasik'ar jaki, tasha hasko cewa rayuwarta a cikin gidan zata fi sauk'i in har zai matsa wani wajen, don shi ba mutum ne mai yawan fita ba, saboda haka kusan kullum yana gefen Hajiya yana k'ara b'antare ragowar rusashshiyar alak'ar dake tsakaninsu.

"Me kike yi anan?"

Ya tambaya yana kallon bokitin dake gabanta.

Me? na zata kana zaune a wajen lokacin da Hajiya ta jefo min tarin kayan wankinta da sanyin safiyar da ba kowa ya gama tashi ba taje inje in wanke.

Taso ace zata iya gaya masa hakan ba tare da ta jawowa kanta wani abun ba.

"Kayan Hajiya nake wankewa." Ba yadda ta iya, ta amsa a hankali.

"Toh tana jiran kokonta in kin gama."

Ashe wannan lokacin shine MAFARIN HARGITSIN RAYUWARTA! ashe sai da ya riga ya gama zuba gubar sannan yazo ya same ta, ashe daga ita har Habiba dake nata shirin sun fad'a tarkonsa ne cikin rashin sani... Sai ta janye idonta hankali ta maida k'asa, wata kwalla mai d'umi ta taru a cikinsu, karo na farko taji kuka na shirin kwace mata a cikin kotun...

Ashe ba tsakaninta da Hajiya kawai Sule ya rusa a baya ba, rayuwarta gabad'aya ya ture daga tubali, ya barta tana reto a gefe, wani reto mai ciwo da wuya... Idonta ya dinga hasko mata duk irin wuyar da ta sha tunda daga lokacin da tayi hatsarin nan ta farka kwakwalwarta a mace, kowanne k'alubale data fuskanta BAYAN TA MUTU.... duk akan wannan gaskiyar da bata fi tsakanin minti biyar a fad'e ta ba!

Sai ta kasa rik'e kukan da take dannewa a k'irjinta, kawai ta kifa kanta akan teburin gabanta sannan sautinsa ya shiga fita cikin siririyar muryarta da wani irin amo mai k'arfi, kuka ne irin wanda bata tab'a yi ba a wannan sabuwar rayuwar tata, kuka ne da Bintu kawai ta sanshi ba Fadeelah ba... Kuka ne irin wanda Bintu kawai ta tab'a yinsa a wasu keb'abb'un lokuta...

Sanda aka nemi Mairo aka rasa...

Sanda Innarta ta rasu...

Sanda Babanta ya rasu...

Da sanda aka raba ta da Inna Saratu!

Kuka ne dake fitowa tun daga k'asan zuciyarta, tana iya jin yadda k'arfinsa ke jijjiga kowanne k'ashi na jikinta tamkar zasu b'alle su rabu da junansu, tana iya jin yadda jijiyoyin jikinta ke nannad'ewa kamar ana k'ulle su... Sannan tana iya jin yadda bangwayen kotun ke amsawa da sautinsa tamkar zata iya zama silar tsagewarsu!

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

40

(&_&)

Zaune akan kujerarsa, Alk'ali yace.

"Bayan dukkan bayanai da kuma hujjoji da kotu taji daga kowanne b'angare, Kotu ta yanke hukunci cewa yarinyar da ake zargi bata da laifi, haka ma duk sauran wad'anda ake zargi daga baya sakamakon gano ainihin wanda ke bayan kisan Hajiya Balaraba, sannan kuma kotu ta yankewa Sule wanda aka samu da laifin kisan hukuncin d'aurin rai da rai tare da aiki mai tsanani a gidan yari. Da wannan hukuncin kuma, kotu ta kawo k'arshen shari'ar da Iyalan Malam Idris Musa suka shigar watanni biyu da suka wuce."

Adam ya rufe file d'in gabansa a lokacin da wajen ya rud'e da hayaniya bayan tashin Alk'alin.

Ya mik'e tsaye shima jikinsa babu kwari, *It's over!* komai ya k'are... Ubangiji ya amsa addu'arsa ya kawo k'arshen shari'ar nan a yau, Fadeelah zata cigaba da rayuwarta sannan zumuncin Babban gida kuma zai gyaru!

Kawu Ibrahim yace dashi.

"Ban san ta yaya zan gode maka ba Adamu, ban san me ma ya kamata ince ba."

"Nima ban cancanci godiya ba Baba, nayi abinda ya dace ne kawai." Ya fad'a a hankali kamar mai rad'a.

Sai yasa hannu ya rik'o kafad'unsa duka biyun yace.

"Ina alfahari da kai Adamu, ina alfahari da kai irin alfaharin da mahaifinka ya mutu yana burin samu, A yau ka shigo cikinmu ka tabbatar masa da mafarkinsa, kayi abinda ba wanda zai tab'a irinsa, ba a wajenmu kad'ai ba Adamu, wallahi duniya kaf zata shaida cewa kai tauraro ne daban a cikin taura..."

Bai k'arasa ba Adam ya rungume shi kawai, don shi kansa a wannan lokacin ji yake tsakaninsa da magana akwai tazara mai nisa.

Alh. Ahmad, marik'in Fadeelah yace dashi.

"Kayi aiki mai kyau Adam, kayi namijin k'okarin da ba kowa ne zai iya shi ba, mun gode kwarai da gaske kuma na tabbata wannan case d'in zai jawo maka muhimmiyar d'aukaka a Nigeria, you did a brilliant job!"

Sauran mutanen Babban gida suka yanyame shi da murnar Allah ya sanya alkhairi da kuma jinjina ga k'ok'arinsa. Sa'id ya mik'o masa hannu suka gaisa sannan yace.

"Ba sai ka gaya min komai ba, na riga naga dukkan abinda na dad'e ina jiran amsarsu daga wajenka yau. Kayi k'ok'ari sosai yaya, Allah ya k'ara k'arfin basira."

Bayan mazan, mata ma birjik suka yi ta taruwa a gabansa da irin tasu murnar, ba 'yan Babban gidan kad'ai ba, har da mutanen waje na Ikaran da kuma jama'ar gari wad'anda suka zo kallo, sai dai duk a cikinsu wadda yafi rik'ewa itace marik'iyar Fadeelah, matar Alh. Ahmad.

Da hawaye a kowanne idonta ta kamo hannunsa d'aya da duka nata biyun, ta dinga jero masa wasu tarin addu'o'i da bai tab'a samun irinsu ba a rayuwarsa, don addu'o'i ne irin na uwa kuma bahaushiya wadda bai tab'a samu ba.

Har yaje kwanciya a wannan ranar bayan tarin hayaniya da kuma cike-cike na rufe case d'in kafin a baza shi ga Media, abu biyu ne basu gushe daga ransa ba, farko addu'o'in matar da yaji kowa na kira da Mami Saffiya, sannan kuma kamar koyaushe a rayuwarsa... Idanun Fadeelah, sanda ta tafi ta rungume yayarta da yaji ana kira da Mairo bayan awanni hud'u da gama shari'ar kafin a kammala komai kotun ta sallameta, Mairon ce farkon wadda ta fara zuwa ta rungume sanda ta fito wajen tarin jama'ar dake jiranta, yana iya tuna yadda dukkan jikinsu ke jijjigawa da wani irin kuka da yafi k'arfin a kira shi da na murna, kuka ne da su kad'ai kawai suka san abinda suke fitarwa daga cikinsa.

Fitarwa. Kalmar ta d'auki hankalinsa, ya lumshe idonsa kad'an sannan ya k'ara lumewa cikin filon dake k'asan kansa, fatansa a lokacin shine Fadeelah ta gama fitar da dukkan wani bak'in ciki yau cikin kukan da ta sha, kukan da ya hana shi samun magana ma da ita, don ba zai so ace ta cigaba da wahalar da kanta da irin wannan kukan ba... Ta cigaba da wahalar da idanunta!

Ya rufe idanunsa a hankali tare da hoton nata a cikinsu sanda azababbiyar gajiyar dake nukurkusar sa taci galaba akan kowanne b'angare na jikinsa.

Sai a lokacin ya fahimci abinda Sa'id yaji lokacin da suka dawo daga Mimbiri, don sai a sannan ya shiga biyan bashin kowacce gwagwarmaya da yayi tun sanda ya karb'i shari'ar Fadeelah. Burinsa a wannan lokacin bai wuce ace ya samu kamar kwanaki uku ba abinda yake sai bacci ba.

Sai dai me? Washegari ya tashi da abubuwa guda biyu, farko wani irin matsanancin zazzab'i mai zafi daya rufe shi, na biyu kuma labarin rasuwar SADIYA daga Babban gida!

***

Sadiya ta rasu ne a dalilin hatsarin mota data samu a hanyarta ta komawa Abuja tsakanin garin Zariya da Kaduna, cikin matsanancin gudun da mai motarsu keyi yaci karo da wani mai irin nasa gudun ya bangaje shi, abin da ya haddasa motar ta shiga wul-wuli kenan akan titi tana wullar da mutanen dake cikinta, Sadiya ta booth ta fito kanta ya bugu da kwaltar titi ya tsage ta mutu a take, kuma har aka kawo ta gida bayan su Kawu Yahya da aka kira ta wayarta sunje sun d'auko gawarta, akayi mata wanka da sutura, jini bai bar zuba daga kan nata ba, haka akayi mata sallah aka kaita kabarinta.

Ba wai alhinin rashin Sadiya ne ya girgiza 'yan Babban gida ba, a'a yanayin mutuwarta ne da basu kad'ai ba hatta jama'a da yawa daga cikin Ikaran basu tab'a gani ba, don da farko ma da aka kawo ta rasa mai yi mata wanka aka yi, saboda yadda kowa ya tsorata da ganin gawarta kai a rabe, sai daga baya aka samu su Kawu Ibrahim da Kawu Nazifi da kuma limamin unguwarsu suka yi mata wankan sannan aka sallace ta.

Don haka babu laifi a jajantawa Sadiya kuma anyi zaman makoki na gaske, don ko Fadeelah wadda tun bayan sallamarta take b'angaren Kawu Ibrahim tare da Mairo, ta ture komai ta jawo wannan dangantakar ta cewa ko ba komai Sadiya k'anwar mahaifinta ce, Dangin ta ce ta hanyar da baza a rasa irin jininta a nata jikin ba, saboda haka ta bud'e zuciyarta tayi mata addu'a da fatan Allah yayi mata rahma.

A yau ake sadakar uku don haka gidan ya cika fiye da koyaushe, kusan kowanne b'angare da mutane ana karb'ar gaisuwa, suma suna zaune a falon Aunty Hassanah tare da wasu daga cikin danginta. Ta juya kanta gefe kad'an inda Aunty saratu da Mami Saffiya ke zaune waje d'aya, duniyarta guda biyu had'e a waje d'aya!

Mami ta koma Abuja tun washegarin ranar da aka sallameta daga kotu, amma yau ta sake biyo jirgi ita da Faruk suka zo addu'ar ukun wadda daga ita za'a share makoki... A tsakaninta da Aunty Saratu bata san soyayyar wa zata fifita sama da ta d'aya ba.

Aunty saratu ta sota tsakani da Allah kuma ta kula da ita tun a lokacin da mahaifiyarta take raye, sannan bayan ta rasa jigon iyaye duka biyun, ta kula da ita har bayan sanda aka raba su, sanda take zaune a gaban Hajiya, wani lokaci da ya zama a duniya kaf! itace kad'ai wadda zata gani taji dad'i.... Ga Mami Safiyya kuma, wadda ta tsince ta rana tsaka ta hanyar dangin karere, amma tun daga wannan lokacin bata tab'a banbanta ta da 'yayan cikinta ba, tana yi mata soyayya ne irin wadda Allah yake halattawa uwa ga d'anta.

Kuma cikin wani ikon na Allah sai su biyun suka had'a kansu tun sanda suka had'u a zama na k'arshe a kotu, to mai hali iri d'aya ne ya had'u da d'anuwansa. Ta lumshe idanunta a hankali sanda muryar Mami wadda ke waya ta shiga kunnenta.

"To ai ban gane bane Abdullahi, wai fingerprint d'in Samiran ne yak'i hawa?"

Bata san sanda ta dakatar da duk wani tunani ba ta tsaida hankalinta akanta.

"To me yasa tun jiyan baka d'auke ta daga islamiyya ba kuje a sake yi mata?"

Ta sake tambaya tana k'okarin nemo wani abu cikin jakar gabanta, jin haka sai Fadeelah ta juyar kanta d'aya b'agaren d'akin, ta sauke ganinta akan mutanen dake zaune sannan zuciyarta ta shiga bugawa da sauri.

Tsawon wani lokaci Mami ta dad'e da daina yi mata zancen Al'ameen, amma shekaranjiya bayan sun dawo gida, sanda ta samu kad'aicewa da Kawu Ibrahim ya gaya mata cewa su Daddy sun zo masa da zancen an fasa aurenta da Al'ameen saboda mahaifiyarsa ta zab'a masa wata a can zai aura. Kwata-kwata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login