Showing 78001 words to 81000 words out of 153964 words

Chapter 27 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3800

Habiba ta gyara muryarta tace.

"Salame yanzu duk ba wannan ba, kin san Allah jikina yana bani wannan yaron d'an gidan Ahmadun nan da yazo zasu ce ya karb'ar musu shari'ar tunda shima lauyan ne, kuma daga ganin k'irarsa wannan ba mutunci zaiyi ba ya rayu cikin turawa, tsorona Allah-tsorona Annabi Salame d'an nan zai iya gano abinda muka shirya."

"Habi ko shi maye ne bana jin zai iya gano komai a lamarin nan, tunda ko a wancan lokacin kowa ya yarda babu hannunki a ciki, sannan ba mahalukin daya ganta sanda ta shiga b'angarenki karb'ar kokon, k'arewa ma tsohon da ya samo mana gubar ya bar garin nan, watakila ma ya mutu can inda ya tafi. To saboda Allah gaya min me wani zai iya ganowa anan?"

"Rigakafi yafi magani dai, Ni yanzu kiran dana yi miki k'auyen Kaduna zaki raka ni gobe, can wajen bokan daya fara yi min aiki akan Malam (mijinta) mu samu ko yaya ne a hallaka yarinyar nan tun yanzu a can asibitin da take ba tare da wani zargi ya d'arsu akanmu ba."

"Kin yarda da aikinsa ne? Naga ko shekara ba'a rufa ba wancan karon Malam ya daina baki kudin ribar gonarsa."

"Salame harkar nan fa sa'a ce kawai, naga gashi yanzu ina gaya miki aikin na Niger d'in ma ya fara rawa, da mun take ta kawai shikenan!"

Da wannan zancen washegari Habiba da Salame suka buga sammako kan hanyar Kaduna ba tare da wani mahaluki ya san da fitarsu ba.

***

A B U J A.

A hankali duhun dake cikin idonta ya yaye, haske tar! Ya maye gurbinsa tare kuma da shigowar muryoyi, sai tayi saurin maida idon nata ta runtse sakamakon shigowar hasken da sara har cikin kanta, bayan wani lokaci kad'an ta sake bud'e su.

Wata iska mai sanyi ta zarce har cikin k'irjinta, hakan ya harba wani tsini mai zafi kirjin nata, ta kasa banbance zafin rashin jin iska na tsawon lokaci ne ko kuma zafin ciwon da take ciki ne. Hoton d'akin mai rawa ya shaidawa kwakwalwarta cewa a asibiti take, asibitin dai da ta farkavwancan karon ta ganta a cikinsa, sai dai wancan d'akin da kuma wannan da banbanci, tun yaushe aka kawota nan kenan? Tsawon wane lokaci aka d'suka daga waccan farkawar tata zuwa wannan? Ba zata iya tuna sanda ta bar haiyacinta ba, abu na k'arshe da zata iya tunawa shine Mami ta fad'a mata 'yanuwata suka kawo 'yan sandan da ta gani suna gadinsu wancan karon, daga nan tunaninta ya hargitse, abubuwa game da rayuwarta ta baya suka shi dawowa cikin kanta, kwakwalwarta na dawo mata da su daki-daki cikin kanta tare da wani irin matsanancin ciwo dake shaida kwancewar duk wani k'ulli na mantuwa cikin kanta.

Tun a baya, likitanta ta America, Dr. Florence ta riga ta shaida mata cewa kwakwalwarta ta fara taka matakin warkewa wato 'Retrival stage' matakin dake nufin duk sanda taci karo da wani abu daya danganci rayuwarta ta baya, kwakwalwarta zata yi reacting akansa ta hanyar jin ciwo ko kuma ta saka ma ta fita daga haiyacinta.

Ganin 'yaruwarta Mairo da tayi da kuma Sadiya a baya, shi ya hargitsa kwakwalwarta da ciwon daya haddasa sumanta a wancan lokacin, amma a yanzu da Mami ta shaida mata abinda ya zamto sanadiyyar faruwar abubuwa da yawa na rabin rayuwarta sai komai ya sake hargitse mata da wani irin ciwo da kuma rud'ad'i, ciwo irin wanda ke shaida cewa alamu ne na warkewar duk wani sauran duhu dake cikin kwakwalwar tata, don ji take kamar dukkan azabar duniya aka tattaro aka saka cikin kanta.

Komai na rayuwarta ta baya ya dawo tar cikin idanunta, tun daga yarintar ta da zata iya tunawa har zuwa kan duk wani hargitsi daya faru akanta, tana iya tuna komai kamar a sannan suke faruwa, komai ya had'a tun daga farko har k'arshe, lokacin da tayi wata tafiya mai nisa a cikin duhun titunan dake bayanta, jikinta na rawa ta cikin cukurkudadden hijabinta.

Da sanda gari ya waye ta isa tasha ta hau motar Kano, da sanda motar ta gama cika suka fita daga tashar suka hau kan titi, da sanda bayan tafiya mai nisa motar tasu ta tarwatse a tsakiyar titi... k'arshen rayuwarta ta farko kenan!

BAYAN TA MUTU kuma, sai ta tsinci kanta a asibiti inda bayan Nurses d'in da suka zo kansu ita da sauran mutanen motar dake kwance cikin jini, ita aka sallame ba tare da wani dubawa ba sai don ganin ko kwarzane babu a jikinta.

A sannan ne kuma ta fahimci cewa ba ita ce ta mutu a wancan lokacin ba, kwakwalwarta ce! Kwakwalwarta ta mutu don ta fita daga asibitin nan ne babu ilimin sanin wacece ita kanta balle koda mutum d'aya a duniya, sai sanin yanayin mu'amala na rayuwar al'umma kawai!

Abinda ya rik'e ta tsawon kwanaki tana walagigi a cikin garin Kano kenan ba tare da ta san inda ta nufa ba.

Ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba, ruwan sama yasha yi mata d'anbanzan duka tsakar dare saboda rashin ko da wajen fakewa ne ma balle makwanci, hakanan ba sau d'aya ba sau biyu ba tasha yini ta kuma kwana da yunwa sakamakon rashin sanin hanyar da zata nemi abinci.

A yadda idanunta ke nuna mata watakila tayi kusan wata guda a hakan don tana iya tuna lokuta da yawa da take cikin mawuyacin hali kafin wata k'addarar tazo ta gifta.

Daddy ya kad'eta a mota lokacin da ya d'auko hajiyarsa zai kaita asibiti check-up na ciwon zuciyarta, daga nan suka d'auketa zuwa asibitin da suka nufa, inda anan ne bayan d'inmbin gwaje-gwaje da tambayoyi aka tabbatar musu cewa kwakwalwarta ta bugu da wani abu ne kuma ta manta dukkan rayuwarta ta baya, abinda ya sanya tausayinta a zuciyar hajiyar Daddy kenan ta yanke shawarar d'aukarta ta rik'e ta a wajenta, wanda ba'a yi hakan ba sai da yardar hukuma da kuma cike-cike wajen 'yan sanda sannan ta koma wajenta da zama.

A cikin shekara guda, tayi rayuwa da Hajiyar Daddy cikin dad'i da aminci, duk da cewa rabin lokacin ta shafe shi ne a asibiti da taimakon wata ma'aikaciyar hajiyan mai suna Ladi, inda suka yi ta zaryar ciwonta da yake yawan tashi a sannan, amma a d'an lokacin nan ta kyautata zamanta da hajiyar iya iyawarta ta yadda lokacin da ciwon zuciyarta ya tashi har ta kai an kira Daddy dake can America, wasiyyar da ta fito ta k'arshe daga bakinta shine ta dank'a amanar cigaban kulawarta a hannun Daddyn.

Allah ya sani taji mutuwar Hajiyar har cikin k'ok'on ranta a lokacin, amma haka ta daure ta zauna tare da 'yanuwanta akayi ta karb'ar gaisuwa har ta kan taya bada hakuri ma ga wasu masu kukan, sannan ta k'arar da dukkan kud'in hannunta wajen siyan abin sadaka tana sawa a rabawa yara da cewa su yiwa Hajiyarta addu'a, ai kuwa haka a kullum kofar gidan nan ke rud'ewa da muryoyin yara suna.

"Allah ya jik'an Hajiya."

A wajensu wasa suka maida abin, suna yi kamar wak'a don a basu abin sadakar, amma ita da kowanne muryar yaro tana yarda cewa addu'ar na tafiya har al'arshin ubangiji, don ance addu'ar yaro ba juyayyiya bace wurin ubangiji, don shi mai wankakkiyar zuciya ne da bashi da koda d'igo na zunubi.

Bayan an share makoki ne kuma komai ya canja, aka barta gidan daga ita sai lami don iyalan Daddyn ma a lokacin sai suka tattara suka tafi can Abuja wajen danginsu.

Bayan Daddy, ita da Ladi sunfi kowa sabawa da Hajiyar a lokacin, saboda haka sai kewa da alhinin rashin suka yi sallama wa rayuwarsu, gidan yayi musu fadi haka ma komai na rayuwar, sai dai har gwara ladin don ita sai ta shafe yini? guda a d'aki tana kukan da bata yi tare da mutane ba, wani lokacin ma har sallah ta wuce ta. Gani take kamar itama k'arshen tata rayuwar ne ke gangarowa tunda babu sauran mai taimakonta, k'ark'arin zamansu a gidan ba zai wuce na wata guda ba, don Ladi har ta fara shirin komawa garinsu kuma babu alamun a dangin hajiyar wani na da niyyar rik'eta, tunda ita d'in ai ba hakkinsu bace.

Wannan yawan tunani da damuwar su suka haddasa mata wani sabon ciwon, kwakwalwarta kuma ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kasa karb'ar shi ta d'ora akan na da, saboda haka sai komai ya sake shafe tunaninta a karo na biyu, ta manta komai ta manta kowa... ba hajiyar ba, ba 'yanuwanta ba, ba Ladin da kullum suke tare ba balle kuma d'an Hajiyar Daddy.

Saboda haka sanda Daddyn ya tashi komawa tare da ita bisa umarnin mahaifinsa, da kyar ta yarda ta bishi can Abuja inda akayi fafutukar sama mata visa sannan suka d'unguma har da matarsa wadda ta karb'eta hannun biyu da kuma 'ya'yansu.

Shekara guda a bak'uwar duniya tare kuma da bak'in mutane kafin ta iya sakin jikinta ta karb'i rayuwar da k'addara ta bata, sai dai har a lokacin bata iya tuna Hajiyar Daddy sosai balle kuma rayuwarta ta baya, ta maida hankalinta kawai ga rayuwa cikin su Mami ta kuma saba dasu, a haka har Daddy ya samo mata malamin lesson a gida, bayan watanni shida tayi jarabawar makarantarsu Faruq kuma ta shiga, makarantar da ta hadu da k'awayenta biyu da kuma Adam, mutum guda d'aya daya kasa barin zuciyarta tsawon wannan lokacin.

Daga nan kuma wata k'addarar ta kawo Al'ameen cikin gwagwarmayar rayuwa da kuma ciwonta, zuciyarta ta bashi dama har suka yi sabon da ko a rayuwarta ta baya bata yi da wani namiji ba. K'addara ta raba su kuma wata k'addarar ta dawo dashi har a yanzu da aure ke shirin shiga tsakaninsu!

Ta tuna komai kuma ta tuna kowa, yanzu abinda ya rage shine ta tashi ta fuskanci k'addarar da ta gujewa tun a farkon lokaci, k'addarar data haddasa faruwar d'inbin abubuwa a rayuwarta, don a yanzu ta banbanta da wannan 'yar k'aramar yarinyar data baro Babban gida cike da tsoron mutanen cikinsa, Tayi wayo kuma duniya ta koya mata cewar rauni baya cikin hanyar nasara.

Dole ne ta tashi don ta fuskanci wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya, idan har sun rufe idonsu daga kawaicin DANGANTAKAR dake tsakaninsu, to itama zata yakice cewa sune wannan DANGIN da tsawon shekaru take masifar son tuna su da komawa cikinsu, ta jawo sanin cewa sune dangin da suka yi sanadiyyar hargitsewar rayuwarta, sune sanadin ciwon data sha wahalarsa kuma sune wad'anda har Innarta ta koma ga ubangiji da bak'in cikinsu a ranta!

Daga yanzu ta tashi daga wannan Fadeelan mai sauk'in kai da rauni, ta koma Bintun ta ta asali, mai dakakkiyar zuciyar da har ta iya barin gida a k'ananun shekaru.

Habiba! Ina Habiba take ne?

"Ina ga kamar ta farka, idanunta na shirin bud'ewa."

Muryar wani akanta data tabbatar likita ne ya fad'a.

Sai tayi murmushi kad'an sannan ta bud'e idanun nata bakid'aya. Ba zata k'ara asarar lokaci ba wajen komawa IKARA!

***

Adam ya bud'e k'ofar office d'insa a hankali sannan ya zare muk'ullin ya shiga ciki. A kwanaki biyu kawai da bai zo aiki ba har kan table d'inshi yayi kura don bai bada spare key wanda za'a dinga shiga ana gyara masa ba, ya yarda cewa office musamman nasa, waje ne dake buk'atar sirri.

Ya ajiye jakar daya shigo da ita sannan yayi amfanin da wayar cikin office din ya kira can reception kan a turo masa mai shara.

Ya matsa ya karkad'e wata kujera dake can jikin k'aton windon office d'in sannan ya zuge labulen jikinsa haske ya shigo ciki, akwai d'an k'aramin tebur na d'ora k'afa a wajen saboda haka ya d'ora labtop d'insa akai sannan ya zauna, ya shiga bin duk bayanan da ya rubuta game da abinda su Kawu yahya suka gaya masa kwanaki biyu da suka wuce.

Ya fahimci komai kuma ya gano hanyar da zai bi komai, zaiyi amfani ne da mutane kawai har ya kai ga? evidence d'in da zasu fito da komai d'in, don bayan wad'annan shekarun baya jin kai tsaye zai samu ko tsinke ne da ya danganci lamarin.

Sai dai abu d'aya da bai fahimta ba shine a yadda yaga tsari da kuma had'in kai na Babban gida me yasa zasu kasa yafewa 'yar d'anuwansu wannan laifin? Shi lauya ne ya san muhimmanci da kuma ciwon laifin kisa musamman ace na mahaifiyarsu, ya san kuma ko da d'anuwan nasu ne zasu iya k'in yafe masa suce sai an hukunta shi, amma yarinya k'arama irin haka? Shekaru ashirin da biyu? Me zai sa suk'i yafe mata? Sun kuwa san cewa kashe ta za'ayi in har komai ya tabbata?

Dole ne ma ya sake tuntunb'ar Sa'id, ya fahimci akwai wani abu dashi da Kawu Ibrahim basu gama baiyana masa ba game da Babban gida.

K'ofar Office d'in ta bud'e, wani abokin aikinsa ne ya shigo maimakon mai sharar da yake jira.

"So yau kaga damar shigowa kenan?"

Nasir ya fad'a da murmushi sanda ya k'araso ciki, shima murmushin yayi masa sannan cikin tattausar muryarsa yace.

"Wallahi Nasir, hayaniyar case d'in can ya wahalar dani, shi yasa na nemi hutun kwana biyu wanda da kyar ma aka bani."

Nasir ya nemi waje ya zauna.

"Ai dole ne a baka da kyar, mutane irinku hutunsu kad'an ne Adam, ko jiya na shiga office d'in Haro naga an kawo wani case suna requesting d'inka."

Ya girgiza kansa a hankali.

"Da kamar wuya in karb'a, don ina da wani case din yanzu."

"Anan ne?" Nasir ya tambaya.

Ya sake girgiza kansa.

"Na waje ne, ko kuma ince na gida ne... Daga Family na ne."

"Allah ya taimaka, thou na san ma zaka yi nailing d'insa."

Kafin ya amsa, had'addiyar wayarsa daya nemo a daren jiya ta shiga vibrating a gefen labtop d'insa. Kawu Ibrahim ne saboda haka ya gyara zamansa kad'an sannan ya amsa.

"Kunyi magana dasu Yahyan?"

Kawu Ibrahim d'in ya tambaya bayan 'yar gajeriyar gaisuwar daya bada dama suka yi.

"Eh, Baba sunyi min bayanin komai, munje asibitin ma har sau biyu amma bamu ga yarinyar ba, ance ta shiga cikin d'an k'aramin coma ne, sai dai su marik'an nata muka gani."

"Yawwa, tunda ka fahimci komai yanzu so nake in tambaye ka zaka iya yi min wata alfarma?"

Bai san kalmar alfarmar ba, amma fahimci ma'anarta, ya fahimci yana rok'onsa yayi masa wani abu ne don haka kai tsaye yace.

"Insha Allah Baba, ka fad'i ko meye."

Baya fatan Allah ya kawo ranar da zaiyi koda musu dashi ne kan wani abun balle kuma bijirewa.

"Adamu so nake yi ka juya akan case d'in yarinyar nan, maimakon lauyan masu shigar da k'ara, so nake ka koma lauyan da zai kare ta!"

Adam ya had'iye wani abu da bai san menene ba cikin mak'ogwaronsa, a yanzu ya k'ara tabbatarwa kansa akwai wani abu game da rayuwar yarinyar nan!

***

Al'ameen ya shak'i iska a hankali lokacin da yake kallon waje ta tagar motar da Kamaal ke tuk'awa, zuciyarsa tarawa take da kuma d'ebewa, ya san baiyi amfani da tunaninsa ba ko kad'an wajen tursasa mahaifinsa su b'oyewa wa Maminsa zancen aurensa da Fadeelah.

Gashi a yanzu komai ya cakud'e lokaci na shirin k'ure masa, don ranar da Mami ta sanya na aurensa da Hamida a can na k'ara gabatowa alhali bai cimma komai anan ba. Shi yasa ya kasa d'aukan wayar da tayi ta masa jiya, me zai ce mata? Zaman makokin ne ba'a gama ba alhali mahaifinsa ya koma tuntuni?

Allah kad'ai ya san damuwar da take ciki yanzu na rashin ji daga gareshi, ya maida kansa ya jingina a saman kujerar yana kallon saman motar.

"Wai me kake tunani ne?"

Kamaal ya tambaye shi cikin harshen turanci.

"Abubuwa da yawa." Ya amsa a tak'aice.

"Yau zamu karb'i license d'in nan, sannan na gaya maka shari'ar nan mai sauk'i ce, zamu samu duk evidence d'inmu tunda yarinyar ta aikata ne kafin ta kai shekaru...?"

"Bata aikata ba Kamaal, ni na san Fadeelah bata yi kisan nan ba."

"Sorry, ina nufin suna zarginta da kisan ne a lokacin da shekarunta basu kai sha takwas ba, to komai zai zo mana da sauk'i. Meye sauran damuwarka?"

"Mami." Ya furta sunan tare da furzar da iska daga bakinsa.

"Ban tab'a mata k'arya ba sai yanzu, gani nake ban kyauta ba, na zalunceta, na zalunci duk k'ok'arinta akaina Kamaal."

Kamaal baice komai ba yayi shiru kawai ya cigaba da tuk'insa, don ya san baza'a rufa awa d'aya ba zai zo kuma yana gaya masa cewa zai iya bijirewa kowa akan Fadeelah.

Zuwa can wayar Kamaal d'in tayi k'ara?akan dashboard, ya mik'a hannu ya d'auka sannan ya kara ta a kunne sa. Magana d'aya yayi Al'ameen ya fahimci daga can wajen da suke neman license ne, don haka ya juyo ya kalle shi sanda ya ajiye kiran.

"Meye?" Kamaal ya tambaya.

"Dan Allah kar ka raina min hankali Kamaal, just say it!"

Sai yayi murmushi kawai sannan ya juya fuskarsa ya mayar titi.

"An samu license d'in Al'ameen, daga yanzu zaka iya shiga kowacce kotu a Nigeria ka kare Fadeelah."

Maimakon yaji farinciki kamar yadda ya dad'e yana zumud'in hakan, sai yaji yawu ya wuce kwat! cikin mak'ogwaronsa. Ya juyar da kansa a hankali ya mayar kan tagar gefensa, me ya same shi ne wai yau? Meke shirin faruwa dashi.

"Al'ameen." Kamal ya kira sunansa da muryar dake nuna mamaki.

"Muyi sauri Kamal, tunda mun samu license d'in ya kamata in had'u da lawyer wad'ancan 'yanuwan nata, Daddy yace jiya ma sun shiga asibitin nama nan."

Daga haka bai k'ara cewa komai ba, kuma akayi sa'a Kamaal din ma bai sake magana ba wanda hakan yayi masa dad'i don ya fi so a barshi da hargitsin cikin kansa kawai.

Sai dai hakan bai d'ore ba, don wayarsa dake kan cinyarsa ce ta shiga k'ara tana nuna wata sabuwar number ce ta k'asar waje, bai yi tunani sau biyu ba yasa hannu ya danna button d'in amsawa.

Magana d'aya ya gane mai maganar, wani kawunsa ne d'anuwan Maminsa, ma'ana daga dangin su Daddy na can washington kenan, ya gaishe shi cikin girmamawa da kuma taraddadin abinda zai biyo baya.

"Al'ameen tun jiya Maminka nata kira baka d'auka ba. Lafiya dai koh?"

Wane zab'i yake dashi banda k'arya? Saboda haka kai tsaye yace.

"Bana kusa ne amma insha Allah zan kira ta yanzun nan."

"A'ah kar ka kira ta ma, don baza ta iya d'auka ba. Dama mahaifinka ne yake ta rashin lafiya tun jiyan aka kaishi asibiti, yau da safe kuma Allah yayi masa rasuwa, sai dai hakuri Al'ameen mu kuma bishi da Addu'a, ka nemi koda jirgin yawo ne in zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login