Showing 51001 words to 54000 words out of 153964 words

Chapter 18 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3772

ya riga ya sani cewa ta bar k'asar tare da 'yan gidansu, kuma kamar wancan karon bai tambayi sunan k'asar ba, don baiga amfanin hakan ba.

"Wannan ba rayuwarka bace Adam.."

Muryar dattijon nan ta katse tunaninsa, bai sani ba ko tun d'azu yake magana don in yana irin wannan tunanin baya fahimtar komai dake gabansa.

"...bamu zauna da kai tsawon shekarun nan don ka girma ka zama haka ba,? ko bamu haife ka ba ak'alla mun raineka ta hanyar da zaka bamu girman da muke..."

"Steve! An kawo maka sak'o."

Muryar matar dake amsa sunan mahaifiyarsa ta kira daga can bakin kofar falon gidan,?hakan yasa Adam ya bud'e idonsa a hankali ya kalle shi.

"Na san cewa akwai abinda kake tsarawa a cikin kanka, dole duk wannan abinda kake yi yana da dalili,? na sanka..."

"Steve! Yana buk'atar sa hannunka."

Muryarta ta sake katse shi, sai yaja guntun tsaki kafin ya mik'e ya nufi cikin falon,?daga inda Adam ke zaune,? yana hangota tsaye cikin shigar riga da wando dogon gashinta na reto a kowanne gefen kafad'unta yayin da mutumin daya kawo sak'on ke tsaye daga waje cikin uniform dinsa rik'e da wani k'aton kwali.

Kafin yayi wani tunani wayarsa da ta fad'i can k'asan wasu takrdu ta shiga ruri alamun shigowar kira, ya mik'a hannunsa ya d'auko ta, number sabuwar sakatariyar da aka bashi kwanan nan ce ta nuna akan screen d'in, saboda haka babu tantama ya amsa don ya san zancen aiki ne... Sai dai abinda ta fad'a ya zama sab'anin tunaninsa.

"Yallab'ai na samu kira d'azu daga wata ma'aikatar kula da tsofaffi ta garin Leicestar a k'asar England, wai suna nemanka ne akan wani abu mai muhimmanci suna son in basu number wayarka ko adireshin email."

Ya rufe idonsa kad'an ya bud'e,? ya san zancen ba zai wuce na yazo ya karbi ragowar dukiyar Magareth da suke ta naci ba,? kamar yace mata ta rabu dasu sai kuma kalmar 'abu mai muhimmanci' ta d'auki hankalinsa,? saboda haka a gajarce yace.

"Ki tura musu da adireshin email d'in."

Ya rabu da layin da yake kiransu tun a da,?in suka san na yanzu zasu takura masa ne akan abinda ba zai taba zuwa ya karba ba,?tunda a baya yayi musu bayani amma sun kasa yarda cewa shi ba d'anuwanta bane hasali ma bai tab'aganinta ba ko a hoto.

Mintuna kad'an bayan hakan, shigowar sabon sak'o ya nuna akan computer da yake aiki da ita, ya riga ya san ko daga ina ne saboda haka bai bi ta kansa ba sai bayan awanni biyu daya kammala had'a evidence d'in da yake kan yi.

Ilai kuwa yana dubawa yaga wata doguwar wasik'a ce daga can gidan kula da tsofaffin. A hankali ya koma baya kan kujerarsa sannan ya shiga jan idanunsa kan rubutun.

Dear Mr. Steve

Bayan binciken da muka shafe muna yi akanka na tsawon shekara guda,? mun yarda cewa baka da alak'a da Magareth Whitford, kuma mun gode da baka karb'i dukiyarta ba.

Sannan muna farin cikin sanar da kai cewa abinda ka dad'e kana nema ya samu a yanzu, mun san cewa duk duk sanda ka kira waya kana neman Magareth ne da zummar son sanin wani abu game da iyayenka, to a farkon watan da ya wuce ne d'aya daga cikin ma'aikatanmu ta binciko wata tsohuwar wasika a cikin kayan marigayiyar, wadda aka buga ta da sunanka tun shekaru goma da suka wuce.

Muna fatan cewa zaka sami amsar da kake nema a cikin wasik'ar, don haka tana nan a wajenmu cikin kyakkyawar ajiya,?duk sanda ka sami dama kazo ka karb'a.

Sa hannu,

Gidan kula da tsofaffi na garin leicester, k'asar Ingila.

?%O??%

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

*18

Assalamu Alaikum, ina gaishe ku sosai tare da fatan alkhairi.

Daga wannan zuwa update na gaba zamu saurari labarin Adam ne. So yake yi ku san asalinsa kafin ya sake dannowa cikin shafukanku a karo na biyu.

Shi yasa zamu d'an dakata da b'angaren Fadeelah da Al'ameen na d'an lokaci kafin mu sake waiwayarsu.

Kar ku manta tattare da kowanne labari na duniyar nan akwai kunci da kuma tarin fad'i-tashi, don haka a labarin Adam ma wad'annan abubuwan baza su b'ace ba.

(&_&)

Karfe biyu da rabi na ranar litinin,? jirgin 'virgin america' ya dira a harabar babban filin saukar jirage na garin leicester dake k'asar Ingila,? kamar kowacce rana, wajen cike yake da mutane da kuma d'imbin ma'aikatan dake ta zirga-zirga a kowanne b'angare, sannan ga jirage a zube wanda da alama wasu basu dad'e da sauka ba yayin da wasu kuma ke shirin tashi.

Ta cikin jerin fasinjojin da suka fara biyo matattakalar saukar jirgin, Adam ya sanyo k'afarsa sanye cikin wani dogon takalmin Boot kalar ruwan k'asa, gashin kansa a taje cikin wani style mai kyau, sannan idonsa na b'oye cikin bak'in gilashi.

Ya tsaya daga inda yake ya kalli yanayin garin da kuma hada-hadar mutane, murmushi ya b'alle a bakinsa, wani murmushi mai zurfi daya manta yaushe rabon da yayi irinsa sai a yanzu da komai na kewayensa ke nuna masa cewar ya iso inda zai gyara rayuwarsa.

Yanayin fuskarsa yayi kyau cikin siririn hasken ranar daya b'ullo ta tsakanin hazon daya mamaye garin bakid'aya, yana sanye cikin wata doguwar coat k'irar kamfanin 'London fog' rik'e da 'yar karamar jaka a hannunsa.

"Idan zaka iya matsawa kad'an zamu wuce."

Muryar wani dattijo daga bayansa ta fad'a, sai a lokacin ya tuna akwai mutanen dake tsaye a bayansa zasu fito, cikin nutsuwa ya biyo jikin matattakalar ya sauka a k'asar garin dake rik'e da sirrinsa tsawon shekaru.

Bayan ya karbi 'yar k'aramar jakar daya sanyo kayansa a ciki, ya fita waje inda ya hayi taxi zuwa hotel d'in da yayi booking d'aki tun kafin zuwansa,? babu wani b'ata lokaci ya karb'i muk'ullin daki na d'ari biyu da uku (203) ya shiga, komai a tsare yake k'al kamar kowanne hotel, bai b'ata lokaci ba ya fad'a band'aki yayi wanka sannan ya shirya cikin wasu kaya kalar ruwan k'asa, a samansu ya dora doguwar jacket mai kyau data zarce har k'asan gwiwarsa.

K'ararrawar d'akin ta amsa sanda yake taje kansa a gaban wani dogon mudubi, d'aya daga cikin masu aikin hotel d'in ne d'auke da wani faranti mai cike da tarin cima kala-kala, a layi d'aya ya gaya masa cewa shi bai nemi abinci ba, amma sai ya shaida masa cewa wannan kyauta ce daga garesu kamar yadda suke yiwa duk wani sabon bak'o, ba yadda ya iya haka ya bud'e masa k'ofar ya shigo ya ajiye, bai ko bi ta kan abincin ba ya juya ya cigaba da shirinsa, abinda yake gabansa a yanzu yafi k'arfin cimar kwanaki biyu ma.

Lokacin daya fita harabar hotel d'in,? agogon 'Brew Watches' dake d'aure a tsintsiyar hannunsa ya shaida masa cewa k'arfe hud'u da rabi ne na ranar, babu wahalar taxi a wajen don haka take ya samu mai motar daya nunawa address d'in hannunsa suka nufi inda zuciyarsa ta dad'e tana mafarkin zuwa tsawon shekaru biyu... Gidan kula da tsofaffi na garin leicestar!

Sanda suka isa wajen, mai?motar ya wuce doguwar harabar wajen mai cike da bishiyu da kwantacciyar ciyawa har zuwa daidai barandar shiga cikin ginin take, wani security ya k'araso da sauri ya bud'e masa k'ofar ya fito.

"Barka da zuwa yallab'ai."

Da alama hakan wata hanyar girmama bak'insu ce,?ya amsa masa da murmushi kafin ya juya ya sallami mai taxin.

Yadda yake tunanin da hasashen wajen, haka kuwa ciki ya kasance, d'an banbancin kad'an ne da nasa tunanin.

Cike da d'oki yabi gajeren layin mutanen dake ganin receiptionist d'in wajen, idonsa na kan yadda take karb'ar kowanne mutum da murmushi iri d'aya kafin ta bashi damar ganin wanda yazo ya nema, ya matsa gaban desk d'in nata sanda matar gabansa ta kauce.

"Barkanka da zuwa gidan kula da tsofaffi da masu rauni na garin Leicester, wajen wa kazo?"

Sai yaji guntun murmushi ya sauka a kumatunsa jin muryar matar da ya saba ji a waya, yau gashi a gabanta IDO DA IDO.

"Barkanki da aiki, sunana Adam steve..."

"Ohh Adam!" Ta katse shi da k'arin wani murmushin a fuskarta,?Da alama yawan wayar da ya dinga damunsu dashi a shekarun baya baisa sun manta da sunansa ba.

"Barka da zuwa Mr. Steve, fatan ka iso lafiya?"

"Lafiya kalau."

"Naji dad'in haduwa da kai a zahiri,? sannan ina maka ta'aziyyar mutuwar Magareth."

Ya gyad'a kansa sau d'aya. "Nagode."

"Tun jiya muke saka ran ganinka, gashi yau Manager baya nan, da kun gaisa."

Ya sake gyad'a kansa a hankali da wani murmushin sannan yace.

"Ba komai, ina fatan abinda nazo karb'a yana nan."

"Kwarai kuwa, minti d'aya ka zauna a can wajen yanzu za'a kawo maka."

Ta fad'a tana nuna masa wajen wasu kujeru dake can gefe, ya k'arasa ya zauna a bayan inda wata tsohuwa ke zaune tare da 'yarta da jikanta da suka kawo mata ziyara.

Watakila suna amfani da agogo mai kad'awa ne a jikinsu, don baya jin minti d'ayan ta wuce sanda wata ma'aikaciyar ta iso wajensa tallafe da bayanin asalin wanzuwarsa a duniya.

"Barka da zuwa Mr. Steve, munji dadi zuwa da kanka da kayi ba sak'o ba,? sannan muna k'ara gode maka akan kare dukiyar Magareth da kayi baka karb'a ba."

Ta fad'a da fad'ed'en murmushi a fuskarta irin wanda suke yiwa dukkan bak'insu kafin ta mik'o masa wani tsohon envelop mai girma, da sauri ya d'ago da hannunsa ya karb'a, tudu da kaurinsa ya shaida masa cewa koma meye a ciki to yana da d'imbin yawa ba kad'an ba. A hankali ya shiga juya shi cikin hannunsa,? babu b'angare ko guda d'aya da aka zana digo balle sunansa kamar yadda suka fad'a a cikin wasik'ar da suka aiko masa...

... d'aya daga cikin ma'aikatanmu ta binciko wata tsohuwar wasika a cikin kayan marigayiya Magareth, wadda aka buga ta da sunanka tun shekaru goma da suka wuce.

Sai ya d'ago ya kalleta yace.

"Nayi zaton kun ce wasik'ar tana d'auke da sunana, amma yanzu banga inda aka rubuta a jiki ba?"

Har a lokacin da murmushin a fuskarta tace.

"Wannan wasik'ar ita ta bamu amsar da muka shafe tsawon shekara guda muna neman akan 'yan'uwan Magareth mr. Steve, ita kuma ta tabbatar mana cewa kai ba jininta bane kamar yadda ka fad'a a baya, Magareth bata sanka ba bama ta tab'a ganinka ba amma ta rubuta wasik'ar ne da sunanka, sunanka na asali data sani ba wanda kake amfani dashi yanzu ba, in ka karanta zaka fahimci komai."

Kamar ya sake tambayarta wani abu yaga meye amfanin hakan alhali ga amsar komai yanzu a hannunsa saboda haka ya karb'i takardun d'aya hannunta yayi signing akai kamar yadda tace, sannan yayi musu sallama ya fita, abu da'ya daya zauna a kansa shine itama ya san muryarta kamar yadda ya gane ta receiptionist d'in farko.

****

Bayan ya koma masaukinsa, ya kashe wayoyinsa baki d'aya, ya rufe tagogin d'akin bakid'aya, ya rufe k'ofa ya kange kansa da duk wani abu da zai katse shi sannan ya b'are ebvelop d'in ya zaro doguwar wasik'ar da tayi kusan tsawon wani d'an adam din.

Kwanan watan dake rubuce a farko ya shaida masa cewa an rubuta wasik'ar ne kusan shekara goma da wasu watanni baya. A hankali idanunsa suka shiga bin rubutun da aka yi shi da zubi irin na typewriter d'aya bayan d'aya.

*_~_*

Ban sani ba ko wasik'ar nan zata tab'a isa gareka d'an Maria, don ganina da kai na k'arshe a cikin jinin haihuwar da Mahaifiyarka ta mutu ta barka ne, watakila bayan rabuwarmu kaima ka mutu a wannan daren, watakila kuma ka rayu ka zama mai kishin kai kamar mahaifinka har ka lalubo inda zan ajiye maka wannan wasik'ar a doron k'asa.

Naso ace baki da baki zan shaida maka labarin iyayenka don ba komai ne zai saku cikin wannan gajeriyar wasik'ar ba, amma a kullum tsufa dad'a cinye ni yake gashi ban san lokacin da zan yi nasarar nemoka ba, kuma bana son in mutu ban cika alkawarin dana d'aukarwa mahaifiyarka a daren da zata bar duniya cewa in har ni da kai munyi tsawon rai zan gaya maka asalinka ba,?zan fad'a maka asalin mahaifinka don kaje ka nemi 'yanuwanka kar ka k'are rayuwarka a garari kamar yadda dukkaninmu muka yi.

Ba sai mun je da nisa ba d'an Maria... Yak'i! Shine mafarin samar da halittarka a duniya.

SHEKARAR 1987

A wannan lokacin, ni da mahaifiyarka muna d'aya daga cikin k'ananan ma'aikata masu goge-goge a sansanin sojojin dake yak'i da wata k'asa akan iyakar America.

Maria k'awata ce da muka taso tare a gidan marayu, kamar ni itama ta tsinci kanta a can ne bayan yak'in daya faru a yankinmu aka kashe danginmu bakid'aya. Saboda yawan da ire-irenmu suka yi, sai aka dinga d'ibanmu zuwa wajaje da dama inda ake neman k'ananun ma'aikata, sanadin haka ni da mahaifiyarka muka tsinci kanmu a yankin sojoji inda muke aikin dafa musu abinci da duk wani aiki daya kama k'ark'ashin gadin wasu sojojin mata.

Rayuwa wannan yankin rayuwa ce mai cike da k'unci da kuma tashin hankali,?duk da cewa ba'a dab da makwantar sojin muke ba,?amma a kullum ba abinda ke tashi a wajen sai k'arar fitar harsashi da kuma tashin bamabai, rana ta farko da aka kaimu kusan kurumcewa muka yi, bama iya magana da junamu sai daga baya muka koyi magana da ihu kamar yadda kowa a wajen yake, ba wani abu ne daban ba a kullum ka samu labarin mutuwar wani, koda kuwa a cikin mu ne 'yan aiki, harsashi kan iya tashi goron zabi ya sameka a koina sannan za'a iya jefo bom d'in da zai tashi waje guda a lokaci d'aya.

Ba ranar da zata fito ta fad'i ba'a binne gawa wajen ba, har sai da ta kai saboda k'arancin waje sai an tara gawarwaki da yawa sannan a binne su a rami d'aya, kuma kamar yadda ake k'aro sojojin a kodayaushe haka muma 'yan aikin ake k'aro mu da zarar adadin yayi k'asa. Tun zuwanmu wajen babu abinda muke yi sai aiki, aiki irin wanda lokacin magana da na kusa da kai ma babu shi,?gashi kusan kullum ruwa ake yi amma ba ga mu 'yan aikin ba hatta sojojin nan duk k'arfin ruwa baya tsaida al'amura.

Bamu dad'e a wajen ba muka fahimci cewa kusan rabin sojojin wajen da wanda ake k'arowa?asalinsu ba 'yan k'asar america bane,?wasu sojojin haya ne daga wasu k'asashen, wasu kuma masu laifi ne daga gidan yari irin wanda aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai,?daga baya aka basu zabin shiga aikin sojan ko kuma su k'are rayuwarsu a d'aure.

A cikin irin wad'annan fursunonin Mahaifinka yake, Sunansa?AHMAD,? musulmi ne, dan wata k'asa mai suna NIGERIA. Bamu san laifin da yayi yazo nan ba,?amma kowa a wajen ya sanshi akan mutum mara magana da hayaniya wanda koda yak'i ya tsagaita a wasu ranakun, baya tab'a sakin jikinsa kamar yadda sauran su kanyi, abu na farko daya fara jan ra'ayin Maria akansa kenan.

Hanya guda d'aya da muke ganin sojojin nan shine,?a ranakun da yaki yayi sauki suka dawo nan cikin sansanin su ci abinci, mu kuma zamu je mu kwashe kwanukansu mu wanke, sai dai?hakan ba sosai yake faruwa ba don wani lokacin sai a fi k'arfin kwanaki arba'in babu irin wannan ranar,?amma duk da k'arancin hakan Maria ta fara lura da Ahmad a irin wannan lokacin. Sai tace dani.

"Gashi can yau ma zaune, ba tare da kowa ba."

Tun ina biye mata muna yin hirarsa lokaci-lokaci, har na fahimci abin nata yayi yawa na rabu da ita. Amma Maria bata daina ba, ta cigaba da bibiyar al'amuran Ahmad har ya kai duk sanda aka samu irin wannan ranar in zamu je kwashe kwanuka, da wuri zata fita don ta riga kowa d'auke na gabansa, ta wannan hanyar ya fara lura da ita har suka karya dokar da ake jaddada mana a kullum cewar kar mu yadda wata alak'a ta had'a mu da sojojin, don bana mantawa bamu fi wata d'aya da zuwanmu wajen ba aka kashe wani soja tare da wata 'yar aiki da ya yiwa fyad'e, basu ko duba cewa babu laifinta a ciki ba aka harbeta da harsashi d'aya a zuciya kamar yadda aka yiwa sojan.

Maria tana da hikimar zance,? watakila maganar harshenta ce yasa ta ja hankalin Ahmad har ya san sunanta, don a watarana mun je don kwashe kwanukan, sai ya taso ya tsaya a gabanmu ya miko mata nasa kwanon kuma ya kirata da mai sunan 'yan garinsu, watakila ba don na janye hannunta mun bar wajen ba, tun a wannan lokacin k'addara zata datse komai tsakaninsu ba tare da an samar da kai ba.

Na san cewa Maria kyakkyawa ce 'yar k'abilar mutanen turkiya, amma a wannan halin da muke ciki kullum jage-jage ban san abinda yaja ra'ayin Ahmad ya fara sonta ba, Na fahimci hakan ne ta yadda duk ranar da aka samu sauk'in yak'i, Maria ke cika da mutuk'ar d'okin tafiya kwasar kwanuka don kawai ta ganshi, sannan idan mun je shi kuma baya tab'a iya janye idonsa daga kanta har mu gama komai mu tafi, na dad'a tabbatar da abinda ke tsakaninsu ne ranar da Maria ta sulale da duhun Asuba ta bar aikin da muke yi ta fita ta baya, ana kwara matsanancin ruwa wannan lokacin saboda haka mamakin abinda zata yi yasa nabi bayanta.

Daga can nesa na hangeta tsaye ita dashi, sunyi kusa da juna sosai sannan ya rik'e hannayenta duka biyu kamar yana mata sallama don a lokacin koina ya cika da k'arar takun sojojin dake ta fita suna tafiya gab'ar yak'in. Nabi duk wasu hanyoyi da na sani don in nusar da ita ta daina shiga al'amarin Ahmad amma bata fahimce ni ba Saboda a wannan komawar da suka yi ne yak'i ya rincab'e,?aka kashe mutanen cikinsu masu d'imbin yawa, ya zamana? kullum cikin dawo da gawarwaki ake ana binnewa, wasu ma ance a can ake barinsu kawai.

A lokacin Maria ta daina bacci ta daina komai, kullum idonta na kan 'yar k'aramar tagar dake kallon hanyar da ake shigo da gawarwakin, tun ban damu ba har nima nazo na fara fatan dawowarsa, don daga yadda naga yanayin k'awata a wannan lokacin na tabbata zata iya kashe kanta a duk ranar da aka shigo da gawar Ahmad.

?%O??%


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

17

(&_&)

Fatanmu mu duka ya karb'u a ranar da yak'in ya tsagaita, duk da anyi musu mummunar ta'asa amma sun taho da murnar cewa abinda suka yiwa wad'ancan yafi nasu muni,? don har mu 'yan aiki a wannan ranar munyi farin ciki. Ahmad ya dawo shima, a cikin cincirindon sojojin dake dawowa a wahalce kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login