Showing 69001 words to 72000 words out of 153964 words

Chapter 24 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3803

island na kitchen d'in ya cika wajen, d'aure yake cikin kujerarsa ta yara amma yana ta mik'a hannu yana k'okarin tab'o plate d'in yayarsa Afra dake zaune a? gefensa tana ta kanannad'e indomie d'inta cikin fork maimakon ci.

"Mommy Muhd zai zubar min."

Yarinyar ta fad'a cikin shagwab'a tana ture yala-yalan kitson kalabarta daga fuska, sai dai mahaifiyar tasu bata ko juyo ba balle ta nuna alamun taji me tace, cigaba da juya miyarta kawai take yi a hankali idanunta na tsaye kyam akan taswirar siffarta dake nunawa a jikin murfin gas d'in.

Watak'ila ruhinta yayi nisa ya bar doron duniya ma a lokacin, don tunani take yi mai zurfi, irin tunanin da tsawon shekaru bata tab'a yin irinsa ba, bai tab'a zuwa kanta ba don a kwakwalwarta kaf babu muhallin irinsa, Tun bayan lokacin da idanunta suka gano mata k'anwarta Bintu a wajen bikin nan, bata sake tunawa da ita ba sai a yanzu, a yanzun da take jin ba iya tunanin k'anwar tata ba ma, abubuwa ne da yawa ke ta taruwa suna kwancewa a cikin kanta, kamar a da an k'ulle su ne can wani wuri guda, sai yanzu suka sami 'yancinsu na fitowa.

A hankali taji hannu ya ziro ta gefen k'ugunta ya kashe wutar gas d'in dake shirin k'one miyar, sannan ya zuro kansa cikin wuyanta ya rad'a a cikin kunnenta.

"Tunanin me kike yi?"

Mairo ta rufe idanunta a hankali sannan ta kwance hannayensa daya nad'e a jikinta ta juyo ta kalle shi, ta kalli fuskar da tun a kwanaki biyu ta canja mata zuwa wani iri duk da cewa kammaninsa basu canja ba don shine dai mijinta, wannan Sadiq d'in da take so fiye da komai a rayuwarta, wanda har ta baro gida saboda shi, d'an kyakkyawan bafulatanin nan da tun gani na farko da tayi masa a bakin rijiyar da suke zuwa d'ebo ruwa taji zuciyarta ta fad'a duniyarsa. To me yasa a yanzu take ganinsa wani iri?

"Me ya same ki?" Ya tambaya hankalinsa kwance yana maida wani dogon gashinta daya fito cikin hular kanta.

Ta san yana yin hakan ne saboda miyar bayanta dake bud'e, yana son gashi amma baya sonsa a harkar abinci. Sai ta zame hannayenta daga cikin nasa daya rik'e sannan ta kalle shi sosai.

"Bibty akwai maganar da nake son na fad'a maka wadda ni kaina ban tabbatar da ita ba."

Watakila ba'a idanunta kad'ai ba, har a wajen wasu ma fuskarsa zata nuna cewa hankalinsa a kwance yake,? amma daga shi sai ubangijinsa suka san irin rud'ani da kuma tashin hankalin da yake ciki tun dawowarsa daga k'auyen 'Talfa'.

Ya san cewa a baya ya shigo da Maryam cikin rayuwarsa ne saboda burinsa da yake son cimma, amma tun kafin ma ya kammala samun burin nasa kyautatawarta a gareshi tasa ya kamu da son ta, bayan samun burin nasa kuma sai ya yarda cewa rayuwarsa baza ta tab'a tafiya daidai ba in har babu ita, ta riga ta zama kamar wani b'angare na jikinsa da ba zai iya yankewa ya yar ba, saboda haka sai ya ajiye komai shima ya biyewa wannan hasashen da shi da ita suka d'ora iyayensa cewa bata da DANGI, sai iya wata mata kad'ai daya kaita wajenta bayan sun gudo daga garinsu, inda yasa iyayensa suka nema masa aurenta a gurinta.

Hankalinsa a kwance yake da hakan tsawon shekaru, amma daga lokacin da tazo haihuwar d'ansu na biyu tasha wata irin wahala kamar zata mutu, daga wannan lokacin nadamar abinda yayi mata ta fara kama shi,? don kusan kwananta biyu cikin matsananciyar nak'uda kafin ta iya haihuwa saboda likitocin sunce gwara ta haihu da kanta, a sannan ne kuma daya duba yaga wata yayar mahaifiyarsa ce kad'ai tare da ita a asibitin sai tausayinta ya kamashi, ya ayyano da mutuwa zata yi kenan haka zata tafi babu kowa nata a kusa, saboda yasa an hana ta tuna duk wasu DANGINTA a duniya.

Nadamar abinda yayi ta fara kama shi har zuwa ranar da suka tsaya wajen bikin nan yaga alamun kwalla a idanunta, tunaninsa ya bashi cewa watakila taga wani ne data sani a baya kuma ta kasa gaya masa saboda ya riga yasa an k'ulle kwakwalwarta daga son tuna 'yanuwanta.

Amma a yanzu ya shiryawa komai, ya shirya masa da dukkan dauriya da kuma k'arfin hali, zai amsa tambayoyinta ya kuma karb'i laifinsa hannu biyu... abu d'aya da har yanzu bai shirya masa ba shine rabuwarsa da ita.

"Daddyn Afra ranar da muka tsaya a wajen bikin nan bayan mun dawo daga park..."

"Mommy Muhd ya zubar."

Muryar Afra ta katse ta sanda k'arar plate d'in abincinta ya tarwatse a k'asa.

Shikenan! Sadiq ya ayyana a ransa sanda ta janye idanunta daga nasa ta tafi wajen yaran, daga yanzu komai zai fara, zai fara girbar k'addarar abinda ya shuka. Yana kallonta ta kwashe abincin ta zuba a shara sannan ta bud'e k'asan fridge inda ba sanyi sosai ta d'auko madarar kwali, ta zubawa Afra a kofi sannan ta zubawa Muhd a feedersa mai straw, ta bawa kowannensu sannan ta sake dawowa ta d'ora idanunta akan nasa.

"Bibty ka tuna ranar? Har na juya ka tambayeni me nake kallo?"

Bata bari ya amsa ba ta cigaba.

"Wata na gani kamar k'anwata Bintu ta can Ikara kuma tun daga lokacin sai na kasa mantawa da ita, kullum sai na tuna fuskarta don na tabbata ita d'in na gani."

Tirk'ashi! Gabad'aya abin yazo kenan,? wato k'anwarta ma ta gani ba wai wani na nesa ba, k'anwarta da ya san ita kad'ai take da ita a duniya, to amma ta yaya hakan ta kasance? Aikatau ne ya kawo ta Abuja ko me? Don zai iya tuna yarinyar k'arama ce sosai a wancan lokacin da yake zuwa Ikara, don samun Maryam kawai!

"Ka tuna ta?" Muryarta ta katse tunaninsa, sai ya kamo duka hannayenta biyu ya matso da ita gabansa sosai.

"Ta yaya zan manta 'yaruwarki Sweetum, na gane Bintu sosai."

Ta shiga motsi da yatsun nata cikin hannunsa a hankali.

"Ban san ina zamu same ta yanzu ba,? amma da gaske ina son ganinta Daddy, jikina yana bani cewa bayan duk wad'annan shekarun 'yanuwana zasu manta da komai."

Da gaske ne yaje Talfa, da gaske ne ya tone kabarin nan kuma da gaske ne ya k'ona layar mutum-mutumin data zama silar arzikinsa, in ba haka ba tsawon shekarun nan yaushe Maryam ta tab'a zancen 'yanuwanta, yaushe ma ta iya tuna su balle har tayi tunanin komawarta wajensu? Sai dai godiyarsa d'aya a lokacin shine bata yi tunanin ya akayi ta manta su a baya ba, ya akayi shima bai tab'a yi mata zancensu ba sannan ya akayi ma har ta iya gudowa daga gare su... Don wad'annan tambayoyin su zasu canja akalar rayuwarsa.

"Kin shirya a yanzu kina son komawa wajensu kenan?"

Yayi tambayar ne da ma'ana biyu,? farko in har da gaske ta shirya tunkarar k'alubalen da daga ita har shi zasu fuskanta, sannan na biyu don ya maida abun kamar itace a baya bata neme su ba.

Ta d'aga kanta a hankali.

"Na shirya Daddy, ina ganin lokaci yayi da zan neme su... Ko don su Afra."

Ya gyad'a kansa a hankali shima sannan ya fad'i abinda ya shirya masa?tun farkon bayaninta.

"Kije ki shirya yanzu mu fara da neman Bintunki Maryam."

Idanunta suka zare a lokaci guda.

"Yanzu? Yau?"

"Ko zamu bari sai gobe?"

Sai ta saki hannunsa sannan ta shiga girgiza kai.

"Da gaske kake?"

"Da gaske nake, kije ki shirya."

"To amma ina zamu ganta? ranar ma.."

"Ssshhh..."

Ya matso a lokaci d'aya ya d'ora yatsansa akan lebb'enta.

"Kar kice komai, kije ki shirya mu fara gwadawa."

Mamaki ya kusa had'iye ta inda take a tsaye, anya daidai komai yake faruwa kuwa? Ta yaya zai yarda da ita a lokaci d'aya haka? Ta bud'e baki kamar zata sake yin magana kuma sai ta fasa ta d'auki Muhammad da sauri tayi hanyar d'aki da niyyar shiryawar tun kafin ma ya canja shawara. Ya bi bayanta da kallo tare da godewa Allah data fasa maganar data yi niyya, don ya san in har godiya zata yi masa,? daga baya zata zo tayi dana sanin hakan fiye da tunaninta.

****

"Alhaji kace ranar shida ga wata ko?"

Habibu, mai kula da harkar wajen biki ya fad'a yana fitowa daga wani d'aki mai cike da takardu a cikin office d'insa.

"Kwarai ranar shida ga wata ne."

Sadiq ya amsa daga kan kujerar tsallaken teburin da yake zaune.

"To ai ba'a ma tafi da nisa ba, shi yasa da nayi tunanin sai mun duba sannan ka dawo, amma wata biyu ai record d'in yana kusa."

Ya karaso ya zauna akan kujerarsa sannan ya d'ora yatsansa d'aya kan wani layi a cikin littafin.

"Gashi nan bikin wata Aseeyah akayi daga yamma har zuwa Magariba."

"Washe gari fa?" Ya tambaya kai tsaye.

"Bikin wata Aminah Salihu Mu'azzam."

Kwarai! Itace 'yar shugabansu a office da aka gaiyace shi suka zo bayan fitar da suka yi a ranar akace ba ranar ne bikin ba.

"Ranar bikin Aseeyan, an samu wad'anda suke zuwa neman bikin Amina?"

Habibu ya danyi murmushi sannan yace.

"Yallab'ai ai ni harkata ta masu zuwa neman hayar wajen ne da kuma biya kud'i, wannan sai dai a kira securities din wajen su zasu san wannan."

"A'a barshi kawai, yanzu zaka iya bani address din wadanda suka nemi hayar wajen?"

"Na bikin Aminan?" Habibu ya tambaya.

"A'a na ita Aseeya d'in."

"Eh to yallab'ai, ai ka san irin wannan abin ne da d'an matsala, kazo ka bada bayanin mutum kuma wani abu ya faru ace..."

"Kaga..." Sadiq ya tsaida shi.

"Babu wani abu da zai faru, bayani kawai nake nema daga wajensu ba wani abu ba, ko kaga nayi maka kama da wanda zai aikata wani abu mara kyau ne?"

Fatan Sadiq a lokacin, Habibu ya amsa da 'Eh' don da gaske ne shi mai aikata abu mara kyau d'in ne, banbancin kawai,? a bad'ini ba zahiri ba.

"Shikenan to, Allah ya kare bari na samo takarda na rubata maka address d'in matar da ta karbi hayar wajen."

Sanda Sadiq ya tashi fita daga office d'in, ya ajiye masa rafa na takardun 'yan d'ari biyu sababbi.

"Bibty address d'in waye wannan?"

Mairo ta tambaya sanda ya fita ya same ta tsaye a jikin motar daya barta a cikinta, da alama ta kasa zaman ciki ne saboda d'okin dawowarsa.

"Mutanen dacsuka karbi hayar wajen."

Sai ta d'ago ta kalle shi da wani sabon mamakin a fuskarta.

"Me address d'in zaiyi mana?"

Bai amsa ba Muhd ya fara kuka daga cikin motar saboda haka ta bud'e ta d'auko shi, a take shima ya matso ya karb'e shi ya shiga jijijiga shi.

"Ina jin kwarewa yayi,? shi yasa bana son tsotson hannunsa, ta fada tana shafa bayansa sanda yake jijjiga shin.

Daga can gefensu wata budurwa na zaune a cikin mota tana jiran yayanta ta hango su, a lokaci d'aya taji zuciyarta ta murmushe da sha'awarsu, taji dama itace Mairo da wannan kyakkyawan mijin da kuma kyawawan yaran don tana iya hango Afra dake dukan glass na windon motar alamun tana son fitowa, gani take Mairo ta gama samun sa'ar duniya, bata san cewa itace take cikin sa'a ba da take cikin DANGINTA, da mahaifiyarta bata mutu da bak'in cikinta ba, da bata kasance matar mutum dake rayuwa cikin haramun ba, da kuma bata had'a zuri'a da wanda yake cutar da ita tsawon lokaci ba.

D'an Adam baya taba kallon wani yace 'yayi sa'a',? kowanne mutum da irin damuwarsa a duniya.

****

<ض?

K'amshi k'amshi yana tashi... 'Yan mata zamu je kamun amarya!



<ص?

Wak'ar dake ta tashi a wajen kenan yayin da mutane suka dabaibaye rumfar zaman amarya da ake gudanar da kamun amarya Fadeelah.

Sadiya dake gefe taja tsaki a k'asan ranta, ita tun d'azu taso ganin amaryar,? amma wadda ta d'aukarwa kayan nan ta hana ta fon suna zuwa k'ofar d'akin ta juyo ta karb'i kayan sannan ta sallameta, yanzu kuma an shigo da ita fuska a rufe wai sai anyi kamun za'a yaye tukunna.

"Wannan fa duk shirme ne walkahi ba haka ake ainihin Kamu ba, a garinmu ranar kamu amarya ko kwalli bata sawa balle tayi kwalliya."

Wata a gefen Sadiya ta fad'a a inda suke zaune,? daga can gefen filin ne inda kusan tawagar 'yan aiki ne da kuma wasu 'yanuwan masu gidan na k'auye da basu da wayewa sosai.

"Ai kin san abin al'ada-al'ada ne, mu a namu b'angaren ruwan turare ma ake wanke amaryar dashi."

Cewar wata kuma a gefe. Wata daga can hausarta cakud'e da yare tace.

"Mu namu duk wanda yazo kudi zai je ya dank'a a hannun amaryar kafin ma ya nemi wurin zama."

Suka kyalkyale da dariya, wata tace.

"Ashe duk amarya kud'i take yi da bikinta."

"Ko kad'an ake bata kuwa ai ta tara."

Haka suka yi tayi Sadiya na jinsu bata ko ce uffan ba, don ita tunaninta na can wajen hangen abinci da kuma son ganin amaryar, tana son ta tashi amma ta san da hajiyarta ta ganta zata dank'a mata wannan fitinannen d'an nata,? a cikin ranta ta kudirce cewa duk randa ta kori mahaifiyarsa daga gidan shi zai fi kowa shan azabarta kamar yadda ta bauta masa fiye da kowa.

"Yawwa kinga zo ki taya ni dan Allah."

Muryar wannan yarinyar data taya d'aukan kaya d'azu ta yafito ta daga gefe,?Fatima take ko wa? Da saurinta kuwa ta mik'e tayi wajenta don daman neman hanyar tashi daga wajen take. Buhu ne na jakunkuna masu d'auke kayan amfani kitchen dama na gida kala-kala a ciki.

Lallai kud'i na inda suke! Ta ayyana hakan a ranta sanda ta hango rayuwarta ta Ikara shekara da shekaru,?musamman a gidan mijin ta na biyu data sha mutuk'ar wahala. Amma ba komai ita zata yi abinda yafi haka ma ranar da ta tashi aurar da 'yar da zasu haifa da Alhajin hajiyarta da take shirin aura.

Can gefen rumfar amaryar yarinyar tasa ta ajiye buhun,?ashe da sauran wasu ma don sai da suka koma ta d'ebo kai uku banda wasu ma da suka taya ta d'ebowar.

Mutane sun ragu sosai a rumfar saboda haka sanda ta ajiye na k'arshe ta juyo ne idonta ya hango mata abinda take nema tun farkon zuwanta wajen... Cikin rumfar amaryar da mutane suka ragu a yanzu sannan amaryar dake zaune fuskarta shab'e-shab'e da hawaye.

Yadda tsawa ke fad'owa kan wani abu walau tsirrai ko dutse ta tarwatsa shi ya tashi daga kammanninsa, haka Sadiya taji a lokacin da kammanin fuskarta suka juya take cikin tsananin mamaki da rud'ewa sanda fuskar amaryar ta haska cikin idonta, ba wai don tsananin kyan da tayi ba ko don darajar fararen kayan jikinta da ta san sunfi kadarar data mallaka gaba d'aya a Ikara... A'a sai don tsaf idanun nata sula gane mata kammanin d'iyar d'anuwanta marigayi, d'iyar da ta kashe mahaifiyarta har lahira kuma ta gudo!

Bintunsu dai a matsayin amarya!

BINTUN IKARA!

***

"Kana tunanin zamu iya samun wani abu ne a wajenta?"

Mairo ta tambaya sanda suka shawo kan kwanar adireshin dake hannunta.

"Sweetum kince sanda kika ganta ankon bikin ne a jikinta,? kinga kenan dole tana da kusanci dasu masu bikin,?? in ma basu gane ta ba ko a hotunansu za'a iya samunta."

"Haka ne." Ta fad'a tana damk'e takardar a hannunta sannan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. A hankali Sadiq ya ziro hannunsa ya d'ora akan nata.

"Komai zai tafi daidai Insha Allah Maryam."

Da sauri ta kyallo fararen idanunta ta kalle shi, a zamansu kaf! inda tana rik'ewa zata iya kirga adadin sanda daya kira sunanta kuma dukkansu a lokuta masu mutuk'ar muhimmanci ne, saboda haka maimakon taji sauki? sai hakan ya k'ara nauyin ajiyar zuciyar tata, ta maida kanta jikin glass ta langwab'ar a hankali yayin da tayar ta cigaba da motsawa.

Minti biyar kawai ya isar dasu gida mai lamba d'ari uku da ashirin kamar yadda yake rubuce a hannunsu, sai dai me? K'ofar gidan cike take da motoci da kuma mutane sannan ga kid'a na tashi daga cikin gidan.

"Bibty biki suke yi." Bakinta ya furta a hankali tana kallon gate d'in gidan.

"To ko zamu koma gobe ma da...?"

Ta katse shi ta hanyar girgiza kanta.

"Inaga wannan lokacin shine daidai, in har zata je wancan bikin, wannan ma baza ta kasa zuwa ba..."

Ta juyo daga kallon gate d'in ta kalke shi.

"...zan iya ganinta ba tare dana tambayi kowa ba."

Har yanzu hannunsa tana rik'e da hannunta ya d'aga mata kai.

"Haka ne sweetum, kina shiga zaki ganta insha Allah."

Sai ta juya ta kalli su Afra dake kwance a bayan motar sunyi bacci, kafin tayi magana ya riga ta.

"Kije kawai, har ki dawo na san baza su tashi ba."

Yana iya jin yadda hannunta ke rawa kafin ta zarw shi daga cikin nasa sannan ta bud'e k'ofar motar ta fita,? fitar ta dake gaya masa cewa zamansa da ita ya fara tangard'a kenan,? don bai san me zai faru ba in har ta k'arasa fahimtar abinda yayi mata.

***

Sadiya ta kafe idanunta kan Bintun da take kallo babu ko k'akk'autawa, gani take kamar an sa sanda ne an ture duk sauran mutanen dake tururuwa a rumfar, fuskar dai Bintun dake ta dallarawa cikin hasken camera kawai take iya gani yayin da mamaki ke rarakarta inda take tsaye.

Me zai kawo Bintu nan? Ta yaya ta canja rayuwa ta samu duk wad'annan DANGIN? Har zata yi aure cikinsu? Ta yaya suka karb'eta? Su san ko ita wacece? Su san me tayi? Ita ta manta da nata dangin kenan? Ta manta dasu? Ta zata tayi nisan da har baza su iya ganinta ba?

"Lalle yarinya k'arshen shirinki yazo, ana yi miki bikin barin duniya ne."

Ta furta a hankali sanda ta juyawa rumfar baya sannan ta zaro wata 'yar qurqurar wayarta da niyyar kiran wad'anda zasu datse wannan al'amarin ba tare da b'ata lokaci ba.

Tayo gaba a hankali don samun wajen da zata iya jin kiranta sosai ba tare da karar kid'an dake tashi ba. Tazo daf! da hanyar gate d'in ne ta bangaji wata mace don yadda idanunta suka rufe da zumud'i da kuna rud'ani yasa bata ko ganin gabanta.

"Dan Allah yi hakuri." Muryar matar ta fad'a sai dai bata ko bi ta kanta ba tayi gaba da niyyar wucewa.

Cak! K'afafunta suka tsaya sanda muryar tace.

"Aunty Sadiya!!!!"

Sai da sunan ya fito sannan ta fahimci rawa muryar keyi, da sauri ta juyo don ta san kaf! garin Abuja ba wanda ya santa da Aunty Sadiya,? wannan lak'abi ne da 'ya'yan yayye da k'annenta ke kiranta dashi a can Ikara.

Fuskar Mairo ce ta hau k'aru akan ta Bintu da ta cika tunaninta, Mairo wadda ta gudu da saurayi tsawon shekarun da suka dad'e da goge ta cikin lissafinsu a Babban gida.

Mairo dai yayar Bintu!

Mairo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login