Showing 3001 words to 6000 words out of 153964 words

Chapter 2 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3765

d'auka.

Ni kuma fa? ina k'ulle a wani d'aki na b'angaren gidan yayin da zaman makokin ya cigaba da gudana a can b'angaren Hajiya, sai dai kafin a k'ulle ni su Yaya Salisu sunyi min d'an banzan dukan da yasa na fita daga haiyacina, kuma a cikin tarin jama'ar gidan kaf! ba wanda yayi yunk'urin cetona in banda tururuwar 'yan kallon da aka samu wand'anda ke k'ara masu dukan.

Kawu Ibrahim, wan Babana shi kad'ai da ya shigo gidan ya taimakeni, ya rik'e bulalar daga hannun Yaya Salisu sannan ya waska masa mari tare da fad'an cewa bai san bashi da hankali ba sai a lokacin.

Daga nan ya ja ni zuwa b'angaren Babban d'an Hajiya wato Kawu D'anjuma, anan ne na kula cewa gidan ya fara cika da d'imbin mutanen dake tunkud'owa don tabbatar da labarin da yaje musu, ta cikinsu na hango Gwaggo Lami kuma kamar kowa a wajen idanunta cike suke da tsana, wata irin tsana fiye da wadda na saba gani a wajenta tun tasowata.

Sanda muka shiga b'angaren sai Kawu Ibrahim yace in tsaya daga gefe shi kuma ya shiga cikin k'aton d'akin da nake hango maza fal a ciki, na fahimci yawancinsu manyan gidan ne sai kuma wasu 'yan uwa na kusa. Daga inda nake tsaye jikina na d'agawar kuka, ina jiyo muryar Kawu Danjuma yana fad'in wad'anda zasu yiwa gawar wanka in an dawo da ita daga asibiti.

Bayan wani lokaci mai tsawo sai na jiyo muryar Kawu Ibrahim tayi magana ban san me yace ba ko me akace masa, amma lokacin daya fito sai kusan idanun kowa ya biyo bayansa suna kallona, jikina ya shiga b'ari sosai, saboda kallon da kowannensu ke min, kallo ne kamar na tabbacin cewa ni na kashe mahaifiyarsu... zan iya rantsewa naga hakan k'arara.

Daga nan Kawu Ibrahim ya kaini zuwa can b'agarensa ya k'ulle ni a cikin wani d'aki na yaransa k'anana, Ba kowa a gidan don duk wani mahaluki yana b'angaren Hajiya a lokacin.

"Komai zai daidaita insha Allah Bintu, ki zauna anan kafin in dawo."

Ya fad'a kafin ya tafi, ina iya jin sanda ya k'ulle kofar d'akin sannan ya fita. Sai kawai na sulale k'asa naci kuka mai d'imbin yawa har saida hawayen suka k'afe suka daina fitowa sai ajiyar zuciya kawai, sannan kuma wani zazzab'i mai zafi ya rufe ni.

Bayan wani lokaci na kifa kaina a jikin bango tunani da yawa na yawo cikin kaina, nayi-nayi in gano dalilin da yasa Aunty Habiba ta d'ora min wannan mummunan laifin amma na kasa, don kawai ta b'ata rayuwata ne ko kuwa wani abu ya faru tsakaninta da hajiya? duka biyun zai iya zama daidai amma na k'arshen yafi d'aukar hankalina... saboda rashin shirin dake tsakaninsu, amma duk da haka na kasa tunanin wane irin abu ne zai faru tsakaninsu da zai kai Aunty Habiba ga kashe Hajiya? Kashe surukarta? kuma ta binne ni a cikin laifin!

Tsawon zamana a gidan, nayi k'okarin binne komai na karb'i rayuwa a yadda yazo min saboda bani da zab'i, amma abinda ya faru yau ya bud'e dukkan ramukan cikin zuciyata, rushin dake binne ya sake ruruwa ya kama da wuta, kuma ina iya jin yadda yake k'one duk wani sauran fatana daya rage.

Me yasa rayuwata take cike da k'alubale ne?

Me yasa kowa ya tsane ni?

Ta yaya zan iya rayuwa mai kyau a yanzu?

Ya Rabbi!

Na san a duk duniya babu wanda zai yarda dani a wannan al'amarin irin Aunty Saratu, ita kad'aice na san zata iya tsayawa a gaban ko waye ta bada shaidar da zata wanke ni, sai dai a yanzu tayi min nisan da ganinta zai min wuya, don watanni shida baya tayi aure a can jihar Kaduna.

Ba zan iya da wannnan halin ba ya Allah ka taimakeni!...? zuciyata tayi ta nanata hakan kamar istigfari.

Tsawon lokaci ina kwance a cikin d'akin nan ina kallon k'ofar dake k'ulle, na san cewa bada dad'ewa ba Kawu Ibrahim zai dawo da bayanin da aka tattauna na yadda k'arshen rayuwata zai kasance, saboda haka na cigaba da jira ina kuma k'okarin kar bacci ya d'auke ni saboda zazzab'in dake jikina.

Kwakwalwata nata juya yadda zamana yanzu a gidan zai kasance, don duk fad'in garin bani da wajen zuwa in ba Babban gida ba, amma a yanzu rayuwa da mutanen da suka tsaneni tare kuma da abinda ya faru yau zai zama kamar yadda yaro ke hango jahannama ne.

Tunaninnika da yawa suka cika kaina amma duk da haka bacci b'arawo ya tsame ni daga cikin koginsu!

_______

03:15 AM

"Lokacin da aka kai gawar Hajiya asibiti, likitocin sunk'i tab'ata sai da shaidar 'yan sanda shi yasa ba yadda aka iya dole abin ya kai gaban hukuma, saboda haka Kawu Danjuma yace in gaya muku keda Habiba, 'yan sandan zasu zo gobe su tafi daku."

Ina zaune gaban Kawu Ibrahim a lokacin da yake fad'in hakan, ya dawo ne ya tashe ni da tsakar dare yake gaya min labarin da na kasa fahimta, don sai da ya kai k'arshen zancensa sannan naji ma'anar kowacce kalma na bi ta kan fatata tana isa cikin kwakwalwata.

Za'a kaini ofishin 'yan sanda gobe!

Kalaman suka yita maimaitawa a kaina amma suka gagara nutsewa, abin da mamaki, kamar mafarki... wai ni za'a kai ofishin 'yan sanda gobe? me yasa rayuwata take cike da masifa ne?

Subahanallahi! wani yankin zuciyata yayi saurin kwab'ata.

"Kar kisa damuwa a ranki, ba wani babban abu bane, kawai za'ayi muku wasu 'yan tambayoyi ne shikenan."

Ya fad'a don kwantar da hankalina, amma kalaman suka tafi can bayan kaina suka yi matsugunni, ban yi girman da zan iya tsallakewa maganarsa ba, amma rayuwa ta koya min wayon da na san meye matsayin zuwa ofishin 'yan sanda a matsayin wanda ake zargi da kisa, kamar a shafe mutum ne da gishiri sannan a jefa shi cikin kejin mayunwatan kuraye!

"Na san baki yi wannan abin ba Bintu, sai dai abinda ya d'aure mun kai shine yadda kika ce Habiba ce ta dama kokon Hajiya da safen, na san Habiba tsawon lokacin da aka auro ta gidan nan, bata tab'a damuwa da harkar mutane ta wannan fannin koda 'ya'yanta ne kuwa."

A lokacin da Mamana take gab'ar mutuwa kuma ina rik'e da hannunta, akwai wani irin bugu da zuciyata keyi, a lokacin da Kawu Yahya yazo sanar damu rasuwar Baba, irin wannan bugun zuciyar yana nan, a lokacin dana had'a ido da Hajiya ranar da na dawo gidan nan, ba abinda ya canja game da bugun zuciyar.

Sannan a yanzu ma da Kawu Ibrahim mutum d'aya da nake samu sassauci a gurinsa ya fad'i wannan maganar, irin wannan bugun zuciyar dai na sake ji, bugun zuciyar da kullum ke gaya min cewa wani shafi na k'addarar rayuwata ya bud'e.

Idona ya sake cika da kwalla, amma meye amfanin kukan? bayan tun safe nake yinsa kuma babu abinda ya canja?

"Ina son ki gaya min gaskiyar abinda kika sani Bintu, ta haka ne kad'ai zan samu kwarin gwiwar cigaba da taimakonki, kuma idan akwai wani abun ma ki yarda dani ba wanda zan gayawa."

Kun san ma'anar kalamansa? Bai yarda dani ba kawai, don lokacin da na d'aga ido na kalle shi, zargi ya haska sosai cikin nasa idon.

"Wallahil azeem Kawu, na san darajar?rai kuma na san laifin kisa, ba zan tab'a iya cutar da hajiya ba kome take min kuwa, ina sonta a matsayin kakata da kuma mutum mafi kusanci da nake dashi na b'angaren Baba, na san hukuncin kashe mutum wallahi Kawu ba zan tab'a iya kashe ta ba, wannan tunanin ma bai tab'a zuwa kaina na...."

A lokacin kukan da nake rik'ewa ya fito cikin 'yancinsa.

"Ya isa, ya isa, nima na san baza ki iya ba Bintu, kiyi shiru komai zai daidaita insha Allah."

Ya fad'a a hankali kamar bai yarda da abinda yace d'in ba.

"Wani yaro Abdul ?yazo nemanki d'azu amma Kawu Bashir yace kar a bar kowa ya ganki."

Ya fad'a bayan wani lokaci, Sai naji k'arar wani abu ya tarwatse a k'irjina daya fad'i sunan mutumin da ya shigo cikin rayuwata ya karb'e ni da dukkan tabona, ta yaya zan iya kallonsa a yanzu da wannan sabon tabon da ba zai goge ba. Na san a lokacin Kawu Ibrahim zai so sanin waye Abdul da kuma alak'a ta dashi, amma ba hakan ne mafi amfani a sannan ba.

"Kici wannan na san ba abinda kika ci tun safe."

Ya fad'a yana mik'o min wani faranti a rufe, sai a sannan nima na tuna banci komai d'in ba tun safe, na zame murfin a hankali sanda hoton wata damammiyar shinkafa da na san ta wajen zaman makokin ce ya fito.

"Nagode."

Na fad'a a hankali ina jan farantin kan cinyata.

"Zanyi dukkan k'ok'arina in taimake ki insha Allah."

Ya sake fad'a kafin ya bar d'akin, sai dai wannan karon bai k'ulle k'ofar ba, ina jin maganganunsa shi Aunty Hassana a k'ofar kafin su tafi.

Wata kwalla mai d'umi ta fad'a cikin abincin, Ba zan tab'a bari rayuwata ta gintule iya nan ba, saboda zuwa ofishin 'yan sandan nan baya tab'a nufin dawowata, ba wanda zai tab'a yarda Aunty Habiba tana da hannu a lamarin nan, dalilan da suke nuna ni sunfi tasiri.

Kuma dole ne inyi wani abin, dole inyi dukkan iyawata don in fita daga wannan hargitsin, na cigaba da cusa abincin cikin bakina yayin da kwakwalwata ke bincike cikin kaina, neman mafita nake yi ko ta wace hanya kuwa.

A lokacin dana kai lomar k'arshe bakina, a lokacin wani tunanin ya dirar min, na damk'e farantin a hannuna zuciyata na maimaita shi, kuma da kowanne maimaici sai naji ina kara yarda dashi, Haka za'ayi kawai!

Na ajiye farantin da sauri sannan na lalubo k'arshen atamfata, na kwance d'aurin kud'in da nake tarawa tsawon watanni na sake k'irga su, sannan na mayar na k'ulle.

Na d'auki curkudadden hijabina da muka sha duka tare na saka sannan na nufi k'ofa, na tura ta a hankali amma k'arar net din ta cika tsakar gidan, sai da na tabbatar ba wanda yaji sannan na zura k'afa na fita. Iska mai sanyi ta busa kan fatata sanda na fita daga b'angaren, tunda gidan a rarrabe yake waje-waje ba wanda ke damuwa da rufe b'angarensa in dai an rufe k'ofar can waje.

K'afata ba ko takalmi na dinga wuce tabarmi da aka jingine da kuma butocin da akayi amfani dasu da rana, babu kowa kuma ba karar komai sai ta kukan gyare. Nayi ta tafiya a hankali har sanda na iso babban zauren dake rik'e da k'ofar fita, an sanya sakata a tsakaninsa.

Na tsirawa sakatar ido da zuciyata mai zurfi!

Fita daga gidan yana nufin guduwa kenan, guduwa kuma zai tabbatar musu da rashin gaskiyata, zai sa kowa ya yarda cewa da gaske ni mai laifi ce, amma ban damu ba yanzu, ban damu da abinda mutane zasu yi tunani akaina ba, abinda na sani kawai shine rayuwata ba zata rushe a haka ba, dole ne in tafi in samo wajen da zan cigaba da ginata!

Nasa hannuna na bud'e sakatar sannan na taka waje, taku daya kawai ya fitar dani daga cikin Babban gida, kantangarsa ta tsaya a bayana, sai naji na shak'i wata iska mai dad'i kamar ada ina rik'e da numfashina ne, na gyara fuskar hijabina sannan na nufi cikin duhun.

Ko'ina yayi shiru da fad'i, duhun daren da nake tsoro a da ya zama mai haske cikin idona a yanzu, na riga nasa zuciyata a abinda nayi niyya kuma ba abinda zai hanani. Burina shine inyi nisa da babban gida, inyi nisa da duk wanda ya san ni, inje wani wajen da mutane baza su lura dani ba, wajen da damuwar kowa ke kan rayuwarsa ba ta wani ba, zan iya rayuwa cikin duniya amma banda nan.

Tunani da yawa ya cika kaina akan wajen da zanje kafin fitowar rana wani tunanin yace in samu waje in b'oye amma na ture shi, wani?zai iya fitowa ya ganni duk da cewa guduwa shine abu na k'arshe da kowa ke ganin zanyi.

Abinda yafi kawai shine in tafi wajen da zuciyata ke hank'oro, saboda haka na cigaba da mik'ar titin yayin da kukan karnuka ya cika kunnuwana.

______

06:20 AM.

Na sunkuyar da kaina a jikin tagar motar sanda direban ya tada injinta tayoyin suka shiga motsawa.

"Allah ya kaimu lafiya." kwandastan motar ya fad'a yana rufe k'ofar, muryoyi da yawa suka amsa da Ameen.

"Allah ya kiyaye oga!" wani mai talla ya fad'a yaana d'agowa direban hannu.

"Allah ya kaiku KANO lafiya."? maigadin tashar motocin Ikara ya fad'a yana dukan bayan motar, naji zuciyata ta buga tare da k'arar.

Na sunkuyar da kaina lokacin da muka hau titi gudun hangen idon sani, na tuna lokacin dana iso cikin tashar bayan tafiyar kusan awa biyu a k'afa mai cike da 'yar b'uya duk sanda naji motsin wani abun, na hango Hamza daga cikin tashar wani abokin Yaya Sani, hakan yasa nayi saurin b'uya a k'asan wani karyayyen tebur. A lokacin tashar ba mutane sosai saboda haka anan nayi ta zama har sai da wajen ya cika da hayaniya.

"Kano! Kano!!" Wani mutumi nata ihu sanda na fito.

"K'anwata Kano zaki je? taho nan, motocin suna can."? Ya fad'a sanda ya k'arasowa wajena, ba tare da musu ba nabi bayansa, don bani da tunanin inda zanje, abinda nake nema kawai taya ce da zata gangara dani na bar cikin garin Ikara.

"Subhaanal-lathee sakhkhara lanaa haathaa..."

Na jiyo muryar wata mata a gefe na tana biyawa 'yarta yayin da yarinyar ke maimaitawa cikin gwarancinta.

"....wa 'innaa'ilaa Rabbinaa lamunqaliboon." Tawa zuciyar ta k'arashe sanda na hango shafin hisnul muslim d'ina.

A take kuma tunani na ya gangara kan kayana dake d'akin Hajiya, Ya salam! kwata-kwata na manta da zancensu sai yanzu, ta yaya zan iya rayuwa da kaya d'aya kawai... sai na tuna ma ai ba ko takalmi a k'afata saboda haka na ajiye wannan tunanin a gefe, Kaya ba sune abinda ya kamata ya dame ni yanzu ba.

Na juya fuskata jikin tagar, ina kallon yadda hoton waje ke sulalewa cikin gudun motar, korayen bishiyu, k'auyuka da kuma digon mutane na yawo cikin safiyar. Naji zuciyata na washewa da kowanne hoto dana kalla, dukkan tsoro da damuwata suka dinga bajewa da kowanne motsi da tayar motar ke yi.

Bayan awa d'aya da rabi, zuciyata nata yawo cikin gajemaren tunani, na tsinci muryar wani yana k'orafi game da gyaran hanya da kuma bin titi d'aya.

A wannan lokacin kuma naso da dukkan fatana direban nan bai juyo yayi magana ba.

Motar ta tarwatse, k'arfin shigowar gingimarin dake d'auke da itace ya haddasa wata k'ara kamar ta tashin bam, k'ofofin motor suka yage daga jikin bodin, gaba wajen zaman direba ya fita ta taga, injin motar ma yayi tsalle wani wajen. Ka'ra mai yawa ta cika iska, yadda k'arfe ke had'uwa da d'an uwansa, yadda k'arfe ke datsa bishiyoyin gefe da kuma yadda karfe ke k'onewa.

_______

FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.

BAYAN NA MUTU..!

?AYSHA SHAFI'EE

(&_&)

01

BAYAN SHEKARU BIYAR!

WASHINGTON, AMERICA.

"Zaki iya tuna me kika gani bayan hakan?"

"Zan iya..."

Fadeelah ta amsa a hankali tana rufe idanunta, hotunan mafarkin da tayi a daren jiya ya haska tar cikin ganinsu.

"Ina gudu, a cikin wani daji mai yawan bishiyu, ganyen bishiyun suna da siffar fuskoki munana, bana iya jin me suke cewa amma suna ta ihu akaina... bana iya gani sosai amma na cigaba da gudun zuwa wajen wani abu, zuwa cikin duhun dake gabana, ban san me..."

Sai ta tsaya a da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????idai nan, kalaman suka gutsire a iska.

"All through the way, a voice was shouting 'kin kashe ta!"

"A cikin gudun na tsinci wata murya na fad'in 'kin kashe ta!"

"Me abinda kika fad'a na k'arshe yake nufi?"

Dr. Gilbert ya tambaya cikin harshen turanci yana kallonta.

Hakan yana nufin na kashe ta, nayi kisa a cikin wata rayuwar da ban santa ba, na kashe wata a can d'aya duniyar da idona ke nuna min, wata da ban san wacece ba.

A cikin kanta tayi wannan tunanin yayin da Dr. Gilbert ya cigaba da kallonta yana jiran amsa. "Miss Malik?"

"Me? Oh yi hak'uri, hakan na nufin kamar in gudu kenan."

Tayi k'arya cikin harshen turancin da suke magana, Dr. Gibert likitanta ne tsawon shekara guda, wanda ke bata tallafin warkar da ciwon kwakwalwarta, (Psyiotherapist.)

Saboda haka bata tab'a b'oye masa wani abu da ya shafi ciwon nata, amma abinda ta gani jiya a mafarkinta wani abu ne da bata tunanin akwai mahalukin da zata iya shaidawa, babu wanda zata iya tunkara tace mafarkanta na kwanan nan suna nuna mata ita mai kisa ce a wata rayuwar!

Tana iya jin yadda idanunsa ke nazarinta kafin yace.

"Wancan mafarkin da kika yi shima wani abu ne ya biyo ki koh?"

"Yes, wannan karon kuma muryoyi ne, Dr. Gilbert ban san ya zan maka bayani ba amma ina ganin abin k'aruwa yake, a baya ina dad'ewa kafin mafarkin yazo sai dai na zahiri kawai, amma wannan shine kusan na sha biyar fa a wata d'aya."

"Well, bari mu gwada wasu tambayoyi toh." Ya fad'a yana ajiye biron hannunsa akan k'aton littafin dake gabansa.

Sai ta kwantar da kanta kad'an a jikin kujerar da take zaune, wata kujera mai taushi da dad'i, kamar yadda komai na ofishin yake mai kyau, don shi kansa ginin a wani waje yake da zuwansa kad'ai zai sa maka nutsuwa.

"Tunda aka fara hayaniyar nan game da addininku, kin fuskanci wani k'alubale?"

Ta girgiza kanta.

"In banda kallon da mutane ke bina dashi duk sanda na fita, ban fuskanci komai ba."

"Wani na kusa dake fa?"

Ta d'an had'iye yawu kafin ta amsa wannan.

"Wancan satin an kori Mami Saffiya daga aiki akan tace baza ta daina zuwa da hijaab d'inta ba."

"A lokacin kin saka abin a ranki sosai?"

"Zuwa kwana biyu ne kawai na damu, amma yanzu Alhmdlilah mun manta shi, ya wuce kuma tana neman wani aikin."

Ya rubuta wani dogon layi cikin littafin kafin ya sake d'agowa ya kalle ta.

"Yaushe kika yi bacci jiya?"

"Ban tabbatar ba amma zai kai kusan sha d'aya da rabi."

"Me kika yi kafin ki kwanta?"

"Na k'arasa wani zane dana fara ne."

"Har yanzu kina gidan yayanki?"

"Eh."

"Akwai wani abu... ina nufin kina d'an takura ko yaya ne da hakan?"

Da sauri ta sake girgiza kanta.

"No, I'm Okay."

"Kina da matsala a makaranta?"

"A'ah na fara sabawa da komai, sai dai karatun kawai da yake min yawa."

"Fassara min kalmar 'yawa'"

"Yawa sosai, da sai in kai dare ina assignment."

"Kina ciwon kai?"

"Wani lokacin."

"Kina shan magani?"

"Sosai, yadda wata rana ma zan tashi cikin dare ne in sha."

"Kina--"

Wasu tambayoyin da yawa akan makaranta kafin ya fad'i abinda tayi hasashensa.

"Daga yadda na fahimta Miss Malik, yawan mafarkan yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login