Showing 60001 words to 63000 words out of 153964 words

Chapter 21 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3780

cikin wajen nan, tun d'azu suka fita, gashi kuma tace kayan na amfanin gobe ne."

Ya cije lebbensa kad'an alamun tunani.

"Kawai muje wajen, duk motar da zata koma can gidan sai a saka kayan a ciki."

Da hakan suka sami wani direba daya d'ebo wasu mata daga can gidan bikin suka kwashe kayan gabad'aya aka saka a motar tasa.

"Gobe zan koma fa."

Al'ameen ya fad'a sanda ya mik'o mata fakitin wasu cokala na k'arshe a cikin kayan, ba don ta riga ta mik'o hannunta ba, watakila daya sake su ne a k'asa saboda yadda maganar ta shammace ta.

"Zaka koma ina?" Tambayar ta fito kai tsaye ba tare da tantancewa ba.

Sai yayi murmushi kad'an, hannunsa akan murfin booth d'in dake bud'e.

"Garinmu mana, ko kin manta d'azun nan ma ki gama min gorin na saka kayanku."

Mamaki bai barta ba, ta had'e hannayenta sosai ta rik'e cokulan.

"Amma nayi tunanin Mami tace sai bayan bikin tukunna."

"Flight d'ina na yamma ne, saboda haka zan sami d'aurin auren da safe, ai shine k'arshen bikin koh?"

Saboda shirme sai ta girgiza kanta tace.

"Akwai kai amar..." Kan ta k'arasa ta hango shirmen nata saboda haka tayi saurin had'e zancen da cewa.

"Mami ta sani kuma?"

"Ina zan saka Mami a wannan lamarin, Daddy ne kawai ya sani amma ita sai goben tukunna idan taga babu yadda za'ayi kinga sai in tsira."

"To amma me yayi zafi haka? Saurin me kake yi?"

Ya d'anyi shiru wannan karon kafin yace.

"Mamina ta matsa in koma can d'in ma, beside ai ban ma yi sauri ba in kin duba kwanakin dana k'ara bayan gama aikina, sannan hutuna ma ya kusa k'arewa."

Zuciyarta tayi tsalle sannan ta hantsila a lokaci d'aya jin sunan Aunty Miryamah daya kira, itafa ta riga tabi shawarar Fatima ta cire ta kwata-kwata daga kanta a yanzu,shi yasa take iya yin komai ba tare da fargaba ba.

A idonta ta hasko da za'a iya nuna haska mata duk abinda ya faru tsakaninta da Al'ameen a cikin d'an lokacin nan, ta tabbata ba abinda zai hanata kashe ta sannan ta had'a ta binne ta tare da duk wata shaidar kisan!

Ta had'i yawu ya zarce makogwaronta wajen kokarin b'oye damuwarta sannan a hankali tace.

"Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya kiyaye hanya."

Shikenan fa! Komai ya kai k'arshe, shirmen da zuciyarta ta d'ora ta akai har ta janyo Fatima cikin wautar tata duk ya k'are a yau, duniya ta koya mata wani b'angare na hankali, ta fahimci ba'a kodayaushe ne Allah ke azurta mutum da dama har sau biyu ba dole ne ka girbi abinda ka shuka a wasu lokutan. Al'ameen ya riga ya barta kamar yadda wannan shekara d'ayan ta horar da ita, babu kuma wata dabararta da zata dawo dashi.

"Kin tuna ranar dana fara ganinki?"

Muryarsa ta katse ta daga ramin tunanin data rufta, ta d'aga ido ta kalle shi hannunsa d'aya na rik'e da murfin booth d'in yana kokarin rufe shi, sai itama kwakwalwarta ta tuna da ranar, a can Washington sanda suka rako su da kaya ranar dawowarsu garin na farko.

Har ya sunkuyo da hannunsa ya karb'i ledojin data rik'o sannan ya wannan muryar tasa mai d'auke da maganad'isun data ratsa ko'ina a jikinta ta fara janta gare shi.

"Kusan shekara d'aya da rabi kenan yanzu, gashi zamu sake rabuwa a daidai jikin mota, don na san ba lallai ne gobe in ganki ba, Allah kad'ai ya san sai kuma yaushe k'addara zata sake had'a mu."

Baza ta tab'a bari yaga rauninta ba, saboda haka ta tsaida fuskarta sosai sannan ta d'anyi murmushi.

"Hakane, ina fatan Allah ya sake had'a mu cikin alkhairi."

"Ameeeen." Yaja kalmar wajen amsawa.

Kuma da kalmar da jan, da muryarsa dama wannan lokacin su suka dasa aya mai kauri kan shirmammiyar hanyar da take ganin ta fara nasara da ita wajen dawo da wannan damar da ta riga ta tankwabe a baya.

?%O??%

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

20

(&_&)

Kwana nawa mutum ke d'auka ne wajen saita kwakwalwa da zuciyarsa ta dawo daidai game da wani abu daya rasa?

Watakila babu wani takaimaiman lokaci, ya danganta da iya yadda mutum ya d'auki wannan abun da muhimmanci kawai. Shi yasa a kullum Fadeelah ta tashi da wannan nauyin zuciyar da kuma kumburin idon da ta fitar da kwalla d'aya ko biyu cikin dare, sai ta tsaya a gaban mudubi ta tambayi kanta sunan wanda take yaudara?

Don in ba yaudarar kai ba ta yaya za'a ce har tsawon sati biyu da tafiyar Al'ameen wai ta kasa cire damuwarsa akanta? Farko,?banda kyautatawa tafi kowa sanin babu wani abu kuma daya faru tsakaninsu, na biyu ko a? rabuwarta dashi na farko bata damu kanta sosai haka ba, na uku, su kansu 'yan gidan dake da dangantakar jini dashi sun gama kewarsa sun shiga harkokinsu, sai ita karan kad'a miya kawai wadda ta riga ta gama shuka masa rashin kyautatawarta a can farko.

Ta jawo tawul daga cikin wata drawer da suke jera su ta fad'a band'aki a wata safiyar da ta gama irin wannan nazarin, ko Fatima data taimaka mata wajen 'yan dabarunta ta riga ta dad'e da gaya mata cewa tayi hakuri kawai Al'ameen babu abinda yake ji game da ita tunda har ya iya tsallake k'asar da tsawon sati biyu bai ko nemeta a waya ba.

Tayi wankan had'e da wanke gashinta sannan ta fito d'aure tawul d'in a jikinta da wani kuma k'arami akanta. Safiya ce irin ta asabar da kowa ke gida sannan bata da lectures,?don haka bata damu da fita can falo da wuri ba ta shiga shirinta a tsanake, sanda take binciken neman wani man kwakwa a cikin kayanta ne hannunta ya d'ago wata 'yar mitsitsiyar purse a can k'asa da tayi ajiyar id card d'in ADAM a ciki.

Da sauri tasa yatsunta ta sake tura ta can cikin drawer sannan ta danne ta da wasu tarin littattafai, Tun lokacin da ta yarda zata biyewa Fatima su gwada sa'arta kan Al'ameen ne ta d'auki wannan matakin, ta tattara duk k'ok'arinta ta tura azababben tunanin Adam dake cinyeta a kullum can baya cikin kanta, tayi wa kanta nisa da duk abinda zai dinga tuna mata dashi don ta san cewa zuciyarta ba zata tab'a tsayawa waje d'aya ba in har zata cigaba da tunanin bad'ini akan zahirinta.

Ta yarda cewa Adam ya riga yayi mata nisan da bai kamata tayi ta tauye kanta tana k'arewa a tunaninsa ba, tunda hakan ba zai amfane ta da komai ba saima dakushe wasu abubuwan a rayuwarta, don Allah ya sani duk sanda take tunaninsa, wani irin abu ne ke tsagawa cikin b'argo da ruhinta ya kuma tab'o har cikin zuciyarta.

Ta rufe idonta a hankali tana jin makamancin hakan na shirin ratsata.

"Aunty deelah, wani irin wanka kika yi wai? Tun d'azu nake shigowa baki fito ba."

Muryar Iman ta fad'a kuma ta katse ta sanda ta murd'o k'ofar d'akin ta shigo. Ta juyo ta kalle ta.

"Har da wanke kai nayi, me ya faru? Mami ta fita ne?" Don ta san ba zai wuce abinci take nema ba.

"A'ah bak'i akayi Mami tace in kira ki kizo gaishe su, 'yanuwan su ya Al'ameen ne kuma harda Daddynsu a ciki, baki ga kayayyakin daya kawo min ba daga Haneefa."

Sai idanunta suka zare a lokaci d'aya,? 'yanuwan Al'ameen kuma? Daga ina haka a safiyar da ko azahar bata k'arasa ba?

"Iman me suka zo yi? Me ya faru?"

Da mamakin rashin fahinta itama ta tambayeta.

"Gaishe da Daddy fa suka zo yi, ko kina tunanin wani abu ne ya faru?"

Kafin ta amsa ta kara cewa.

"To ni dai naga suna ta fara'a, in ma mutuwa ce bana tunanin ita akayi."

Sai itama tambayar da tayi ta bata dariya, ta juya kawai ta cigaba da shirinta, Al'ameen d'anuwansu ne fa, me yasa don DANGINSA sun zo zata yi tunanin wani abin?

Sai dai me, bata je koina a shirin ba,? Mami ta bud'e kofar d'akin ta shigo fuskarta d'auke da wani abu kamar fara'a kamar kuma mamaki sannan ta sallami Iman kai tsaye daga d'akin ta samu gefen gado ta zauna.

"Ai na san ma Iman ta riga ta gaya miki bak'in da muka yi ko?"

"Eh tace wai Daddyn Al'ameen ne da 'yanuwansa suka zo."

Tayi zaton Mamin zata fad'i wani abu game da mamakin zuwansu itama amma sai maganar data biyo baya ta zama akasin hakan.

"Fadeelah yaushe kuka shirya kanku ne ke da Al'ameen?"

Cak! Ta tsaya daga k'okarin zufe zip d'in rigarta da take yi a lokacin ta juyo ta kalleta.

"Shiryawa? Wace irin shiryawa kuma Mami?"

"Abinda nake tambayarki kenan don Mahaifinsa da 'yanuwansa da suka zo yanzu, aurenki suka zo nema masa!"

***

Maganar ta dake shi!

Amma sai ya d'aure bai katse shi ba,? ya cigaba da kallonsa cikin nutsuwa yana saurarar bayanin da ya riga ya gama shiryawa fuskantarsa.

"Saboda me zaka bar aiki? Don me yasa saboda zaka yi tafiya kayi resigning?"

Shugaban nasu ya fad'a cikin kumfar baki yana kallonsa.

A hankali Adam ya kifta idanunsa, ya bud'e su sannan ya bashi amsa.

"Saboda in na tafi ba zan dawo."

"And for what reason ba zaka dawo ba? Me zaka tafi kaje kayi a wannan banzar k'asar?"

Kalmar ta sake dukansa, ya cije gefen lebb'ensa kad'an kawai ya cigaba da kallonsa.

"To idan baka sani ba gwara kaji yanzu,?ba'a ajiye aiki alhali ka sawa mutane hannu akan alkawarin case d'insu, dole ne ka koma ka k'arasa duk wasu ayyukanka da jama'a tukunna sannan ka dawo muyi wannan maganar."

Ya k'arasa yana turo masa file d'in dake d'auke da wasikar barin aikin da ya kawo masa. Adam baice komai ba sai da ya mik'e zaune sosai sannan yasa dogwayen yatsunsa biyu ya maida masa da file din gabansa.

"Na riga na gama aikina da kowa Mr. Shawn, na rufe kowanne case dana fara kuma bansa hannu akan kowanne sabo ba, don haka gani na dawo mu cigaba da maganar barin aikina."

Sai mamaki ya kama shi kwarai,?don wannan b'angaren na Adam sabo ne da bai taba gani ba, a da komai yace masa baya tsallake yinsa koda kuwa abun nan yana da matsala, amma yanzu har zai k'i bin maganarsa ba tare da tantama ba? Lallai ko me zaije yi Nigeria nan yana da muhimmaci a wajenshi. Sai ya sauke murya k'asa kad'an yace.

"Ka saurareni da kyau Adam, kai yaro ne yanzu kake tasowa baka san duniyar nan ba, sannan ubangiji ya baka damar kwarewa a aikinka,?kayi amfani da damarka ka cigaba da samun d'aukakar daka fara mana,? baka gani ne... Suna, Kud'i, Daraja, Fice, D'aukaka... Gasu nan yanzu a hannunka sai yadda kaga dama zaka yi dasu, me muke nema a duniyar ne bayan wad'annan?"

Tsaf! Adam ya nazarci maganganunsa kuma ya fahimci inda suka dosa.

Saboda haka ya sake komawa ya jingina kansa a kujerar da yake zaune sannan wannan malalaciyar muryar tasa ta shiga magana a hankali.

"Ka san me yasa na zabi aikin lauya Mr. Shawn?"

Baiyi tambayar don amsa ba saboda haka kai tsaye ya cigaba.

"Shekaru gama sha biyar da suka wace,?wata yarinya 'yar shekara sha shida ta samu sab'ani da iyayenta a wani dare har ta gudu ta bar gidan, basu k'ara ganinta a raye ba bayan nan.

Sai bayan kwanaki uku aka sami gawarta yashe a bayan wani gini, an d'aure wuyanta da hannunta da kuma k'afafunta da wata igiyar karfe,? sannan anyi mata fyad'e kafin a shake wuyanta da irin wannan igiyar har ta mutu.

Da wannan igiyar police suka lalubo yayan wani abokina bayan kwana biyu cewar shi ya kasheta, nida abokina mun san bashi bane, domin munga sanda wani ya haura d'akinsa ya d'auki wannan igiyar k'arfen da yake amfani da ita wajen had'a kayan k'arafansa.

Amma ba wanda ya yarda damu a lokacin saboda bamu kai munzalin a karb'i shaidarmu ba kuma dukkan wasu hujjoji su nuna shi a matsayin mai laifi, don har wajen da aka kashe yarinyar yaje a ranar da ake tunanin ta mutun, saboda haka babu wani b'ata lokaci aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kuma aka kashe shin.

Tun a wannan lokacin zuciyata ta bani cewar babu adalci a shari'ar,? don haka na shiga d'an karamin bincikena har bayan shekara biyu na samo amsar komai."

Ya mik'e zaune sosai yana kallonsa sannan yace.

"Ka san me na samo?"

Bai bashi amsa ba kamar d'azu,? amma idanunsa sun shaida son sanin amsar.

Adam ya sanya d'an manuninsa na hagu ya share gefen siririn hancinsa,? hakan ya tafi da 'yar guntuwar gyaran muryar da yayi sannan ya cigaba.

"Yana tare da wata k'ungiya ne ta sirri da suke yin garkuwa da mutane don a basu kud'i, sai yayi niyyar fita bayan ya gama nazarin abinda suke yi ba daidai bane, suka yi masa dukkan gargad'in cewa ba zai iya barinsu ba amma bai saurare su ba ya bi shawarar zuciyarsa ya fita d'in, shi yasa suka yi masa wannan k'azafin da ita yarinya da suka kama bisa kukure sanda suke targeting 'yar wani shahararren mai kud'i."

Office d'in ya d'auki shiru na wani lokaci, a cikin lokacin kuma zuciyar shugaban na tarawa da d'ebewa ne kan wace irin kwakwalwa ce da Adam? Kafin ya amsa muryarsa ta cigaba zuwa k'arashen daya fahimci ya riga ya gano shi.

"Kamar haka kake shirin yi Mr Shawn, zaka iya yin komai a yanzu don tsaida ni, don ka riga kasa hannu a wasu ayyukan da sunana kuma baza ka iya maida musu da kud'insu ba, shi yasa kake shirin yin amfani da wad'annan cases d'in ka mik'a su can sama, saboda su saka a hani ni barin aiki da cewar ban kammala ayyukan da akayi yarjejeniya dani ba..."

Ya sake yin shiru kad'an.

"Ina tabbatar maka wannan hanyar ba mai b'ullewa bace, don in har kayi,??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? cikin ruwan sanyi zanbi in nusar dasu cewa ni bani da masaniyar hakan, kaine mai laifin karb'ar cases da?sunan mutum d'aya kawai alhali ga sauran lauyoyi nan birjik da basu da ayyuka kamar ni a ma'aikatar.

Sannan in duk da haka kana tantamar saka hannun, zan iya cewa ka barshi don bana son in takura ka da kaina, amma zan iya biyowa kuma ta hanyar da ba zata yi maka dad'i ba, shi yasa naga watak'ila zai fi kyau ace mun rufe komai iya mu biyu anan kawai ba tare dana uku ba, balle har a samu d'aruruwa kuma su biyo baya."

Wani ruwa ya zarce makogwaron shugaban, kwarai! Ya san wannan kad'an da aikinsa ne, don ba tun yau ba ya fahimci kwakwalwar Adam daban take a al'amarin bincike, shi yasa baya son rasa shi ko kad'an, don a yanzu mafi yawan mutane harda manya kuwa suna kawo cases d'insu wajensu ne don shi kawai. Ba sai an wani lissafa ba, yanzu ya riga yafi kowanne lauya kawo musu hanyar samun kudi, don har sai da wani babban judge a kwanakin baya ya sara masa da cewar ko mutum kisa yayi, ya binne kansa daga shi har gawar daya kashe, sai dai in ba'a saka Adam a lamarin ba, amma tsaf! zai tono shi har ma da makamin da yayi kisan.

Ba yadda ya iya haka ya jawo file d'in nan ya shiga saka hannunsa a duk inda ya dace, da kowanne sa hannu kuma yana hango irin asarar dake jiransa nan gaba kad'an. A lokacin da ya kai ta k'arshe ne idonsa ya kai kan sunan Adam da ya samu canji akan wanda ya sani, Surname d'insa na 'Steve' ya juya zuwa kalamai biyu.

ADAM AHMAD MUHAMMAD.

Da tsananin mamaki ya d'ago ya kalle shi, yace.

"Wane irin wasa ne kuma wannan? Ya akayi sunanka ya canja?"

Maimakon ya amsa, sai ya mik'o hannunsa ya janyo wata paper a k'asan file din ya nuno masa.

"Ba wasa bane Mr. Shawn ga shaida nan, nabi dukkan wani tsari na canja sunana zuwa irn na addinin da kuka sanya ni nuna k'iyayyarsa a zamana na makarantar nan."

"Amma ta yaya? Saboda me zaka yi hakan?"

Bai bashi amsa ba, sai ya nuna masa paper kawai alamar ya cigaba babu ruwansa da sanin dalilin hakan.

Don banda iyayensa na bogi baya jin duk duniya akwai wanda zai tattauna labarinsa dashi, suma kuma d'in don ya zama dole yayi musu sallama ne su san cewa in ya tafi ba zai dawo ba. Abinda suka fada a baya gaskiya ne,? ko ba komai sun kyautata rayuwarsa sun raine shi ta hanya mai kyau har ya zama wani a yau.

Don haka ba zai tab'a yanke alak'arsa dasu ba, duk da ya lura a yanzu su d'in sun riga sun hakura sun sallama shi.

Ya fita daga office d'in da dukkan wani farin ciki na ganin tsarinsa na tafiya daidai, ya riga ya gama tsara komai yayi booking jirgi, nan da sati d'aya kawai! Zai bar k'asar America bari na har abada zuwa Nigeria inda zai binciko DANGIN mahaifinsa, karo na farko a duniya da zai samu wanda zai kalla yace d'anuwa ne a wajensa na jini!

Ya lumshe idanunsa a hankali sanda idanun Fadeelah suka haska cikin nasa, kamar suma suna taya shi murnar wannan nasarar da yake shirin samu ne, kuma ba abin mamaki bane hakan, don tare suke shiga duk wani tudu su fad'o, suna d'aya daga cikin abinda ke kwantar da hankalinsa duk sanda wani abu ya cakud'e masa.

Ta dad'e da yi masa nisa, amma kamar tana tare dashi ne a kullum!

***

LARABA, TA BAWA RANAR SA'A!

Bayan tafiyar awanni goma sha uku da kimanin mintuna arba'in da Takwas daga k'asar America,?Adam Ahmad Muhammad ya sauka a babban birnin Abuja na Nigeria.

A wannan ranar ne kuma, cikin wata unguwa ta garin Abujan, Daddy ya dawo daga garin Kano wajen dangin mahaifiyarsa,?kuma a ranar ya buga waya can k'asar America ya shaida cewa sun amince da auren Al'ameen ga Fadeelah.

A dai cikin wannan ranar ne kuma, wani magidanci a cikin garin Abujan ya d'auki mota shi kad'ai zuwa wani k'auye mai suna 'Talfa' dake tsakanin Abuja da kuma Kaduna, ya ajiye motarsa a gefen hanya sannan yabi da k'afa ya zagaya zuwa kushewar mutanen k'auyen.

Sau d'aya ya taba zuwa wajen,?amma tsayin shekarun basu sa idanunsa sun kasa gane kabarin da yake nema ba, cikin mintuna 'yan kad'an kuwa ya hak'e gefensa ya ciro layar mutum-mutumin daya tab'a binnewa da hannunsa a wani dare!

A dai larabar kuma, wata mata daga cikin k'awayen Aunty Hadiza yayar Mami Safiyya, tayi wata sabuwar 'yar aiki fil! daga garin IKARA.

?%O??%


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

21

(&_&)

I K A R A

"Wai da gaske ne Sadiya aikatau ta tafi?"

Ladi, k'awa ga Zainab matar Rabi'u d'aya daga cikin 'ya'yan BABBAN GIDA ta tambaya lokacin da ta shigo sashen Zainab d'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login