Showing 114001 words to 117000 words out of 153964 words

Chapter 39 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3801

wak'ar da yake ji cikin earpiece d'insa, idonsa ya kai kan cajin dake kan wayar, bai ko kai kwata ba, gashi man dake cikin motar tasu ya kusa k'arewa, na cikin boot ma ragowarsa bashi da yawa.

Tun da gari ya waye fatansa shine su sami mutumin nan a yau su koma cikin gari, tsawon kwanaki hud'u kenan rabonsa da sevice d'in waya, ba don yana caji a motar ba ma da wayar ta dad'e da mutuwa. Allah ya sani bai tab'a ganin k'untataccen waje irin k'auyen na Mimbiri ba, tun daga 'yar banzar wahalar da suka sha a daji?yaji ya tsani garin, don sunfi k'arfin awanni biyu cikin daji suna karo da dutsuna da kuma busassun shukoki kafin su iso cikinsa, har sai da ya fara tunanin matashin da suka d'auko daga can wani k'auye k'arya yake musu bai san garin ba.

Tun a wancan lokacin kuma ya yarda cewa da gaske ne idan Adam yasa kansa yin abu, to ba k'aramin dalili za'a samu ba da zai canja ra'ayinsa, kwata-kwata bai d'auka da gaske zasu taho har wannan k'auyen neman tsohon da ya bashi labarin ya gani a wajen Habiba ana i-gobe rasuwar Hajiya ba.

Tausayin ganin yadda yake ta fafutuka akan shari'ar ne da kuma ita Bintun da yake hangen za'a datsewa rayuwa yasa ya fad'a masa cewa yaga shigar tsohon wajenta amma ba wai don yana tunanin hakan zaiyi amfani ba, ga mamakinsa kawai sai Adam d'in ya nuna zak'uwarsa wajen k'arin yi masa tambayoyi.

Ya gaya masa iya abinda ya sani cewa ya san tsohon ne kawai ta hanyar wani abokinsa dake siyan magungunan gargajiya a hannunsa...ga k'arin mamakinsa, sai cewa yayi wai ya had'a kayansa zasu yi tafiya. Washegari suka nufi Ikara, yayi sallama dasu Kawu Ibrahim akan zaije bincike ne kuma shi zai raka shi, daga nan suka tafi wajen abokin nasa daya bashi labari, acan yake gaya musu cewa tsohon ya dad'e da barin ikara kuma asalinsa d'an wani kauye ne wai shi Mimbiri a can gaba da birnin tarayya.

Kaduna suka fara tsayawa, inda mamaki ya sake cinye shi ganin yana ta bin wani adireshi a cikin wayarsa har kofar gidan tsohuwar matar mahaifin Bintu, Saratu.

A hanya hira kala-kala ba wadda basu yi ba harda ta shari'ar da ake ciki, amma bai fad'a masa inda zasu ba ko yadda akayi ya samo gidan Saratun.

Bayan sun baro Kaduna, hanyar Abuja a mik'e suka d'auka bayan sun cika motarsu taf! da kuma wasu manyan jarkuna a boot d'in motar da man fetur, a cikin Abujan suka tsaya wani bakery suka siyo tarin kayan cimar fulawa mara saurin lalacewa da fruits da katan-katan na ruwa da lemo kamar masu barin garin.

Tunda suka wuto Abujan kuma suke faman tsayawa k'auyuka-k'auyuka tambayar K'auyen Mimbiri, sai dai tun daga k'auye na biyu da suka yi tambaya aka nuna musu wata hanya data d'auke daga kan titi zuwa cikin daji, tun farko an gaya musu dama k'auyen a ciki yake, sai dai suna isa k'auyen farko a hanyar suka zata shine, ai kuwa mutumin da suka fara tambaya ya shaida musu cewa ai ko rabi na hanyarsa basu kai ba, shi yana can ciki.

Da jagorancin kwatancensa, suka k'ara luluk'awa cikin dajin, kuma tun suna tafiya suna ganin d'aid'akun mutane har ya zama sai sunyi tafiya mai nisa kafin su sake ganin wani k'auyen, kuma daga kowanne k'auye sai ayi ta sake luluk'a su ciki da cewar K'auyen na Mimbirin na gaba, tun suna tafiya service d'in wayarsu na iya kawowa har ya d'auke bakid'aya sannan k'asan motarsu duk yabi ya karkarce saboda yadda suke taka duwatsu da busassun shukoki.

Kwana, d'aya, biyu, har uku, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su sai ko in zasu k'ara mai a motar ko kuma d'aya zai karb'i tuki. Allah ya sani sun wahala kamar a zamanin DA don wani lokacin sai su yini kafin su isa inda za ga mutane su sami ruwa su wanke jiki su canja kayan jikinsu, tun yana k'orafi har ya gaji ya daina don ko kad'an Adam bai damu da wahalar da suke sha ba ko kwazazzababbiyar hanyar da suke bi wadda duk ta karce fenti da kuma k'asan motarsu tsaf!

Sai a rana ta uku sannan suka isa wani k'auye mai suna? 'Sauna' inda suka sami?jagorancin wani matashi jamilu, suka d'auko shi a bayan motarsu yana musu kwatancen hanya wanda haka sai da suka shafe awanni biyu suna tafiya daga inda suka d'auko shi kafin su isa, amma zai iya rantsewa Adam ko gezau baiyi na alamun nuna gajiya ba, tuk'i kawai yake yana bin umarnin matashin nan daya bararraje yana shak'ar sanyin A.C motar.

Bayan sun iso kuma mutanen garin suka maida su tamkar wasu Dodanni, kowa yaki kula su, kowa yak'i yarda dasu har guduwa yara suke in sun gansu, ba yadda matashin nan baiyi ba don ya fahimtar da wan mahaifinsa dake k'auyen cewa ba cutar dasu zasu yi ba, amma fintinkau kowa yak'i fahimtarsu sai da kyar aka sami k'ungiyar wasu dattijai suka turo wakili daga cikinsu cewa in suna son magana dasu sai da su jira Maigarinsu ya dawo daga gaisuwar jana'iza da yaje wani k'auye.

Haka suka kwana a cikin mota babu mahalukin daya kula su, abin ya bashi mamaki mutuk'a yaga kamar sun koma wani zamani ne dake can baya da wanda suke ciki, Amma Adam bai yi mamakin ba, don cewa yayi duba da yanayin yadda rayuwarsu take, in sun kore su ma basu yi laifi ba.

Ya kalli lokaci bayan ya dawo daga wannan dogon tunanin, k'arfe goma da rabi na safiya! Adam ya tafi dubawa ko Maigarin nasu ya dawo, shi kuma ya zauna gadin motarsu, ya juya bayan motar ya d'ebo dabino da kwakwa da kuma cake, ya had'a dabino da kwakwar yana ci, wak'ar iRobot na tashi a kunnensa.

Kwankwan-kwan!?Gilashin gefensa yayi k'ara bayan wani lokaci, da sauri ya zare earpiece d'in ya bud'e k'ofar motar ya fito.

"An aiko mu ne mu tafi da kai, yace ka rufe motar ka biyo mu."

D'aya daga cikin mutane biyun dake tsaye a gansa ya fad'a.

"Shi wa?" Kai tsaye ya tambaya.

"Wanda kuka zo tare dashi, yana can a fadar Maigari."

"Kuka ce baya nan."

"Ya dawo d'azu da asubar fari."

Sa'id ya d'an kallesu su duka biyun, zuciyarsa na son gasgata zancen, yana son d'ebe zargin wani abu a ransa, ganin haka yasa wanda yayi maganar nan ya zura hannunsa a aljihu ya zaro?wani agogo ya mik'o masa.

"Yace mu baka wannan."

Ya mik'a hannu ya karba, agogon dake d'aure a hannun Adam ne, ya sake d'agowa ya kalli mutanen, yaga dai babu alamar rashin gaskiya a fuskokinsu amma duk da haka bai yarda dasu ba, sai ya gyad'a kai sannan ya zura agogon cikin aljuhun wandonsa, ya juya ya bud'e motar, ya kashe ta, ya rufe glasses, sannan ya zare muk'ullin, har zai fito wani tunanin ya gifta cikin kansa don haka ya bud'e drawer jikin dashboard, ya zaro wata 'yar k'aramar wuk'a da Adam ke yanka apple da ita ya zura a aljihunsa.

Sai dai bai hango komai da zai iya yi da wuk'ar ba, don fatansa shine zuciyarsa tayi kuskure akansu...

****


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

37

(&_&)

Koda minti d'aya, bai tab'a mance k'irgar saura awa nawa kafin rana ta fad'i ba, bai tab'a kuskuren saura kwanaki nawa ya rage zuwa sanda za'a sake zaman shari'ar ba, zuciyarsa tana bugawa ne kamar da sautin motsawar sakanni kawai, D'aya.. Biyu... Uku... Hud'u... Biyar... A haka har a kai kowacce sittin d'in dake nuna minti guda ta ragu a lokacin da ya riga yayi tanadinsu.

Adam ya d'an gyara tsayuwarsa idanunsa k'ir! akan k'ofar gidan da Maigarin yasa aka rako shi da kyar, bai ko damu da yadda k'ofar gidan da kewayenta ta d'ad'e da rashin mutane ba, ko da dandazon yaran da suka taru daga can nesa a kowanne b'angare suna hangensa, ko giftawar kawunan matan dake lek'ensa ta saman 'yan katangar gidajen su, ko kuma d'irka-d'irkan matasan da Maigarin yasa suka rako shi har k'ofar gidan tsohon da suka biyo kwatancen nemansa tun daga Ikara... Fatansa kawai ya samu abinda yazo nema ya kuma ganshi ya d'auki hanyar juyawa.

Tana can tana jiransa, tasa dukkan fatanta akansa, tana fatan Allah zai amsa addu'ointa ta hanyarsa, kamar yadda su Kawu Ibrahim da 'yan uwanta ma ke da yak'ini akansa...

Don haka dole ne yabi duk wata hanya da zata sa fatansu ya karb'u, duk wata hanya kuma da zata tabbatar da abinda
abokin karawarsa ke tsoron faruwarsa, wato samun nasararsa!

A daidai wannan lokacin Jamilu, matashin da suka d'auko a hanya kuma yake taya su fafutukar mutanen su saurare su ya fito daga cikin gidan da yake kallo, yayi saurin gyara tsayuwarsa cike da zumud'in jin abinda zai fito daga bakinsa.

"Sunce ka shiga."

Ya gyad'a kansa, alamun ya fahimta sannan yabi bayan jamilun, wad'annan matasan ma suka dafa musu baya.

Soron farko na gidan bashi da rufi in ka d'auke yalolon buhun da aka rufe k'ofa dashi kawai, na biyu kuma dogo ne mai cike da duhu saboda irin dakakkiyar azarar da akayi masa rufi da ita, daga nan sai faffad'an tsakar gida irin na kowanne gida mai iyali na k'auye... Jerin d'akuna masu baranda daga kowanne b'angare sannan k'atuwar bishiya a tsakiyar filin.

Sai dai kuma ba irin yadda gidan ya kamata ya kasance bane, don babu ko irin kajin dake kiwo a tsakar gida balle kuma mutane, k'ofar kowanne d'aki a rufe take bam! wasu ma da alama garin sauri har da labule aka had'a aka gark'ame tare, sai a lokacin yaji zuciyarsa ta fara mamakin irin tsaurin halin mutanen kamar yadda Sa'id ke fad'a.

Sa'id. Ambaton sunansa yasa ya tuna abinda ya faru d'azu a fadar Maigari.

Malam Salisu bashi da halin fitowa ya iya ganinka a yanzu, don haka zamu barka ka ganshi amma da sharad'i.

Mai garin ya fad'a bayan gwagwarmayar da aka sha kafin su iya gane hausar sa.

Ance mana ku biyu kuka zo, don haka zamu rik'e d'anuwanka har sai ka gama da Malam Salisu lafiya, sannan mu fito maka dashi.

Ya tuna yadda babu wani dogon tunani ya amince da hakan kuma har ya bada agogon hannunsa don aje a taho da Sa'id d'in, Anya kuwa baiyi kuskure ba?

"Yana cikin d'akin nan..."

"Ku, ku jira mu anan ko?" Jamil ya juya ga wad'annan matasan dake bin bayansu, kamar basu so ba amma dai suka ja suka tsaya a k'ofar d'akin. Adam ya zare k'afafunsa daga cikin takalmansa a hankali sannan ya sunkuya ya zura kai cikin 'yar k'aramar k'ofar d'akin.

Babu duhu a ciki kamar yadda yake tunani, sai rashin isashshiyar iska da hakan ya fallasa tsamin dattin d'akin, sai dai ba wannan ne ya tsayar dashi a k'ofar ba, sai ganin tarin mutane fal zaune a cikin d'akin, yabi fuskarsu da kallo d'aya bayan d'aya kafin ya tsaya akan d'an tsohon dake kishingid'e a tsakiyarsu, anan ya sami amsarsa ta farko kafin wadda yazo nema. Wad'annan mutanen 'ya'ya da kuma 'yan uwan tsohon ne, sun zo kare shi ne saboda yazo yi masa magana.

Karo na farko tun bayan wani lokaci yaji murmushi na shirin kub'uce masa, yanzu fisabilillahi zai nik'o gari ne daga can wata duniya yazo har nan don ya cutar da wannan d'an tsohon?

"Bismillah..." Jamilu ya nuna masa wajen zama, ba musu ya zauna ya tankwashe k'afafunsa akan daud'ad'iyar tabarmar.

"Maigari ya shaida mana wai kazo ne don kayi wa mahaifinmu wasu tambayoyi."

D'aya daga cikin mutanen ya fad'a. Adam ya had'iye wani guntun yawu a bakinsa sannan yayi gyaran murya a hankali, ta ina zai fara? Ta yaya zai cewa mutanen nan shi lauya ne kuma tambaya yazo yi masa game da shari'ar kisa?

"Da gaske ne daga can Ikaran kake?" Wani ya sake tambaya yana k'are masa kallo.

Ya san abinda ma'anar tambayar ke nufi, baiyi kama da mutanen da suka sani a Ikara ba don haka yayi saurin tarar tunaninsu.

"Mahaifina d'an Ikara ne, amma ba'a can na tashi ba, kuma ba'a can nake ba yanzu haka."

Wani da fuskarsa ke nuna manyanta ya ya gyad'a kai sannan yace.

"Tambayar me kazo yi masa?"

Abin yaso ya d'aurewa Adam kai? Shi tsohon baya magana ne? In su zasu yi masa maganar to ta yaya zai sami amsoshinsa? Sai ya juya ya kalli mai tambayar yace.

"In baza ku damu ba zan iya magana dashi?"

Har mutumin ya bud'e baki zai ce wani abu tsohon nan ya d'ago hannu ya dakatar dashi.

"Kar ka damu Sama'ila ai duk kuna zaune babu wani abu..." ya juyo ga Adam.

"Samari, zancen Habiba ne ke tafe da kai?"

Dammmm! Wani abu ya buga a cikin kan Adam, idanunsa suka zare a lokaci d'aya, kamar yadda idanun 'ya'yansa ma suka cika da mamaki suna kallonsa.

"Ta yaya ka sani?"

K'arin mamakinsa, sai tsohon yayi murmushi yace.

"Na san kai ba bahaushe bane d'an nan, da watak'ila ka san karin maganar dake cewa 'Alhaki kwikwiyo ne, dole ne yabi mai shi, irin wannan ranar na dad'e ina gujewa Habiba."

Adam ya gyara zamansa a hankali, kafin tsohon ya sake tambaya.

"Kai waye a wajen Habiba? Ban tab'a ganinka ba."

"Ni d'an k'anin mijinta ne, ba'a garin nake ba har ka tafi shi yasa bamu tab'a had'uwa ba."

Tsohon ya sake gyad'a kansa sannan yace.

"Ni na san shari'ar nan baza ta tab'a mutuwa ba sai anyi ta, an samu yarinyar da ta gudu ne?"

Adam ya gyad'a kansa.

"Eh ta dawo."

Tsohon ya girgiza kansa.

"Daga Habiba har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin."

Da sauri Adam ya tare shi.

".. Ban gane abinda kake nufi ba."

Tsohon ya juyo ya kalle shi sosai.

"Ko waye ya turo ka kaje ka gaya masa ba Habiba ce ta kashe Hajiya Balaraba ba."

Adam ya had'iye yawu shima yana kallonsa sannan yace.

"Zan iya sanin abinda yasa kace hakan?"

Kafin ya amsa, ya juya ga d'ansa dake gefe ya fad'i wani abu da Adam bai ji ba, d'an ya mik'e da sauri ya kama kafad'unsa, ya mik'ar dashi zaune sosai sannan ya koma ya zauna.

"Ita Habibar da ta turo ka wajena na tabbata ta gaya maka sana'ata a Ikara kafin kazo nan, don haka na saba da ita ne ta hanyar yawan siyan magungunan gargajiya da take yi a wajena.

Ana gobe za'a yi wannan rasuwar, tazo wajena da bayanin abinda kake nema yanzu, tace tana neman taimakona da in sayar mata da sassak'en wata bishiya da yake kamar guba idan mutum yaci shi, da farko bata shaida min me zata yi dashi ba sai da na matsa mata taga da gaske ba zan bata ba har sai naji dalilinta tukunna, sannan ta gaya min cewa ta yanke shawara ne kawai zata kawar da Hajiyar daga duniya don ta samu damar mik'e k'afa a gaba tayi komai yadda take so babu mai hana ta.

Ba tun a ranar ba Habiba ta saba sakin jiki ta fad'a min duk sirrinta saboda ina biye mata a dukkan ra'ayoyinta.. saboda haka na san duk irin matsalar dake tsakaninta da Hajiyar. Ta gaya min a lokacin cewa taje wajen malamai da yawa, amma dukkanin ayyukan da akayi mata babu wanda yaci akan hajiyar, don haka k'awarta ta gaya mata in har ta samu wannan sassak'en tasa mata a abin ci ko sha, to nan take zata mutu.

Sai dai a wannan ranar, ban biyewa mata kamar yadda na saba ba, na gargad'e ta da cewa abinda take shirin yi mai girma ne, kisa ba k'aramin abu bane da zata yi ya wuce kamar sauran shirinta, amma duk iya k'ok'arin da nayi wajen ganar da ita, bata saurare ni ba ta ajiye min mak'udan kud'in da basu tab'a shiga tsakanina da ita ba tace lallai in bata.

Ganin kar in rasa kud'in a wannan lokacin yasa na amsa mata sannan nayi mata alk'awarin kawo mata sassak'en har gida, washegari kuwa na sami wani sassak'en da bashi da tasiri ko kad'an naje na kai mata a matsayin wanda take nema, saboda har a lokacin zuciyata bata bani cewar in sa hannu a kisan mutum ba."

Adam ya gyad'a kai a hankali sanda tsohon ya kawo nan, bai sani ba ko a duk duniya kaf akwai sunan abinda ke faruwa a cikin kansa a lokacin, don bashi da wani kokwanto tsohon gaskiya yake fad'a, ya yarda da maganganunsa irin yardar da zai iya tsayawa a gaban ko waye ya tabbatar da hakan, amma ta yaya wannan al'amarin ya faru? In har ba Habiba ce ta kashe Hajiya ba to waye? A lokaci guda kwakwalwarsa ta shiga hasko fuskokin 'yan Babban gida d'aya bayan d'aya, kamar a sannan za'a nuna masa wanda yake nema.

"Zaka iya yi min dukkan tambayoyin da kake so yanzu."

Muryar tsohon ta katse shi, ya maido da idonsa kansa, sai a sannan ya lura cewa ashe bai ma yi masa tambaya ko guda d'aya ba amma ya sami fiye da rabin amsoshin da yake nema.

"Me yasa duk ka gaya min wannan zancen kai tsaye?" Ya yanke shawarar fara yi masa tambayar da ko 'ya'yansa dake zaune zaso sani.

Tsohon ya k'ara yin murmushi kamar mutumin dake cike da raha sannan ya kai hannunsa ya yaye bargon da ya lullub'e inda k'afafunsa suke, sai dai me? Wajen fayau yake babu k'afafun, balle cinyoyi, sai alamarsu kawai daga can k'ugunsa wanda ke nuna alamun yankewa akayi. Adam ya d'ago daga kallon wajen ya kalle shi.

"Naga ishara mai tarin yawa daga Allah d'an nan, baka labarin halin da na shiga da irin wahalar dana sha kafin in iya k'arasowa nan abu ne mai tsaho, don haka ba kai ba, ko waye a yanzu yazo neman wani bayani daga wajena, wallahi zan gaya masa abinda na sani komai munin irin rawar dana taka a ciki kuwa."

Kamar yadda sama-sama suke gane abinda yake fad'a, shima ba kasafai Adam ke gane kowacce kalma ta cikin hausar sa ba, amma yana iya fahimtar abinda yake nufi, don haka ya gyad'a kansa a hankali kafin ya sake yin wata tambayar.

"Idan har abubuwan da ka gaya min duka gaskiya ne to waye yayi kisan kenan? Tunda labari ya dad'e da fita cewar Hajiyar ta mutu ne sanadiyar gubar data ci."

Sai da ya maida bargon ya rufe jikinsa sannan yace.

"Wanda ya taki zance akan zance ya kuma taki sa'a akan sa'a."

Adam bai fahimta ba, kuma fuskarsa ta nuna alamun hakan.

"Ina nufin wanda ya san duk abubuwan da Habiba ke k'ullawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login