Showing 36001 words to 39000 words out of 153964 words

Chapter 13 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3787

yaja motar ya tafi wajen aikinsa.

A parking lot na makarantar yayi parking sannan ya fito, yabi ta cikin jerin d'aliban ya shiga ciki.

Abinda ya faru a wannan ranar, shi yayi sanadin guntule alak'arsa da Fadeelah, alak'ar data faru ta kuma k'are cikin abinda bai wuce wata guda ba, a tunaninsa kuma ya rabu da ita kenan har abada, don hatta ziyararsa gidan Mami ta ragu sosai wanda hakan ya sanya Aunty Miryamah cikin farin ciki da tunanin yayi mata biyayya ne yabi shawarta... Sai dai daga ita har shi basu san cewa wata k'addarar bata ma fara ba!

***

*BAYAN WATA DAYA.*

"Na zata a rana ta k'arshe baza ki saka ni jiranki ba."

Muryar Adam ta fad'a a hankali sanda yake jingine jikin motarsa a harabar parking lot na wani k'aton amusement park (wajen shak'atawa) dake gabansu.

Bata san da wani irin yanayi mai dad'i ya tashi a yau ba wanda ya saka shi saka wata doguwar jacket ta cotton mai tsananin kyau kalar ruwan toka mai haske, gashinsa kansa a barbaje sannan yanayin fuskarsa a nutse, haka kurum sai taji kamar wani b'angare na zuciyarta itama ya samu nutsuwa da kallonsa.

A yau shine rana ta k'arshe da zasu k'are lesson d'insu, zasu kammala topic na ashirin da biyu a jerin wad'annan topic din daya fara bata da cewar ta haddace. Abubuwa da yawa sun faru a cikin tsukin lokacin wanda muhimmi shine Daddy ya samu aiki a wani Babban asibiti dake Nigeria a birnin Abuja kuma suna ta shirye-shiyen tafiya ta kowanne b'angare.

Burin Mami ya cika don a yanzu kusan kullum sai sunyi waya da 'yan uwanta na gida akan shirin tafiyar, ta fahimci ba ita kad'ai ba dukkan 'yan uwanta irin murnarta suke yi don ita kad'ai ce take nesa dasu, don ma iyayenta duk sun rasu ne sai kishiyar mamanta ce kad'ai ta rage musu.

Jarabawar da taci burin yi don ta samu ta tsallake ajin gaba a yanzu ba zata tab'a yinta ba, sai dai karatunta da Adam wani babban nasara ne da baza ta tab'a manta shi ba a rayuwarta, ya bata alkhairin gane lissafi ta hanyoyi kala-kala da take ganin in za'a tara mutane dubu baza su iya ba sai an sami guda d'aya irinsa.

Shi yasa a yanzu take mutuk'ar ganin girma da kuma darajarsa, gashi kuma sunyi sabon da ta dad'e da ajiye dukkan wata gadarar da take masa a gefe, sannan yadda yake nuna sha'awarsa ga son sanin abubuwa game da addininta yasa ta rage kusan kashi saba'in na tsanarsa a cikin ranta, sauran talatin d'in yana jingine da cewar shi d'in ba musulmi bane har a lokacin.

"Kayi hakuri sai da nayi bayani a gida na fito that's why." Ta amsa a hankali.

Ya ciji gefen lebbensa kad'an sannan ya gyada kansa.

"You should'nt have done this, da baka wahalar da kanka ba, ba dole ne sai mun bi dukkan abinda na rubuta ba."

Ta fad'a tana nuna k'ofar shiga wajen, a jerin hobbies d'inta data rubuta harda zuwa irin parks d'in nan masu wadatar fili da bishiyu, wanda sanyin iskar wajen kan sa mutum ya manta da matsaloli da yawa na rayuwarsa.

Bata tab'a tunanin cewa kamar yadda suka bi dukkan abinda ta rubuta shima zasu zo kansa ba musamman ganin shine na k'arshe a jerin, sai a yau da ya same ta a makaranta ya bata ticket d'in wajen da cewar a can zasu yi lesson d'insu na k'arshe da misalin k'arfe hudu.

Sannan bata tab'a tunanin cewa Mami zata barta ba shi yasa ma bata tambaya da wuri ba, sai da ta nemi numbersa a wayarta ta rasa sannan ta yanke shawarar tambayar tunda babu ta hanyar da zata gaya masa cewar ba zata iya zuwa ba.

Dalilin makarar ta kenan don da alama hankalin Mami gabad'aya ya tattara wajen shirye-shiryen komawarsu Nigeria, shi yasa har ta iya barinta ta fito.

Lokacin da suka yi nisa a karatunsu daga cikin park d'in inda suka sami waje mara yawan mutane, Fadeelah ta kasa daure kanta wajen kallon fuskar Adam, wadda tayi tsananin kyau da wani fresh a lumshin yammar, dogon gashin idonsa daya kwanta akan na k'asa ya k'ara fito da cikar zatinsa, ance wai wanda yake ba musulmi ba a fuskarsa ake ganin cewa babu alamun rahma, amma ba don kar tayi sab'o ba, zata iya cewa a yanzu da ta san kammanin Adam sosai, zata iya kwatanta yanayinsa dana masu tsantsar Imani ma, a share zancen rashin musuluncin gefe.

Wani lokacin zai d'ago ya kalleta idan yaji shirun nata yayi yawa, bata san me yasa ba, haka kawai taji wani gefen zuciyarta na tunanin cewa daga yau shikenan karatu tsakaninta dashi ya k'are, watakila kuma ba zata sake ganinsa ba kenan, tunda akalar rayuwarta zata koma wani b'angaren daban, can tushenta gida Nigeria, inda sanadin komai ya fara daga nan!

"Ciwonki yayi sauki yanzu?"

Muryarsa ta tambaya a hankali lokacin da suka gama karatun dake shirin dasa aya a mu'amalarsu.

Da mamaki ta juyo ta kalle shi domin tun bayan ranar daya fad'a mata ya san wani abu game da ciwonta, bai sake sako zancen hakan ba sai a? yanzu. Tunaninta ya gangara kan yadda ta soke zancen zuwanta asibiti itama a tsawon lokacin nan, tun sanda suka fara karatun ta wad'annan hanyoyin taji bata da bukatar ganin wani likita, zamanta dashi yasa ta koyi cewa ba sai mutum ya dogara da likita ba sannan zai iya samun sauki a ciwonsa, akwai hanyoyin da kai da kanka zaka nemowa kanka waraka. Dr. Florence ta dawo har sunyi kiranta sun gaji bata tab'a reporting apointment d'inta ba.

Al'amarin Al'ameen na kwanakin baya ne kawai ya saka ta cikin damuwar da taji tana buk'atar shawar wani, amma shima ta daure zuciyarta a tallafi kanta da kanta, tunda a lokacin da ta sanya shi cikin rayuwarta bata nemi shawarar kowa ba.

"Akwai abinda nake son in fad'a maka."

Ta fad'a ganin wannan ce damar da ya kamata tayi masa sallama.

"... watak'ila ba zaka ji dad'i ba amma ba yadda zanyi ne... a cikin watan nan zamu koma k'asarmu, don haka jarabawar da muke ta wannan tanadin don ita ba zan sami damar yi ba."

Kamar yadda mutum zai ji idan guduma ta fad'o masa a tsakar kai ba tare da zato ba, haka Adam yaji saukar maganarta amma sai ya b'oye ta hanyar tankwashe k'afarsa akan dardumar da suke zaune sannan ya lumshe idanunsa a hankali.

"Kina tunanin ba zan ji dad'i ba?"

Idanunta na kan yatsunta ta d'aga kai.

"Na sani babu dad'i ace duk abin nan da muke yi babu amfaninsa..."

"Amfaninsa yana tare dake har abada leelah kuma na koya miki karatun nan bane don kici jarabawar makarantar kawai ba, na koya miki ne don kici jarabawar Maths a koina cikin fadin duniya."

Ta d'ago ta kalle shi sannan ta gyad'a kanta a hankali.

"Nagode, ka taimake ni sosai ina fatan kaima Allah ya taimake ka ta hanyar data fi kowacce."

Sai ya mik'e tsaye rike da jakarsa, yayi murmushi kad'an wanda ya k'ara wa fuskarsa kyau, ya riga ya san me take nufi don haka yace.

"Kar ki damu in har addininki gaskiya ne wata rana zan shigo cikinsa, kuma watakila mu sake had'uwa in nuna miki hakan."

"Allah yasa hakan, ina fatan zuwa lokacin kuma ka koyo harda yadda ake fad'in sunana."

Ta fad'a tana tattara sauran papers d'in ta zura a tata jakar sannan ta mik'e, murmushinsa ya k'aru kafin ya sake cewa.

"Insha Allah."

Hakan ya sata murmushi itama sanda ta mik'e tsaye rungume da jakarta a k'irjinta, yadda kalmar ta fito a nannad'e cikin accent d'insa na turawa yasa ta murmushin.

"It's been nice knowing you, ina miki fatan alkhairi leelah Allah ya maida ku k'asarku lafiya."

Haka da wuri? har zasu yi sallama?

Zuciyarta ta tambaya amma kwakwalwarta tayi saurin ture hakan, to me kuma zasu tsaya suce, komai tsakaninta dashi a yau yazo k'arshe, karatun cikin wata guda ya zama sanadin bud'e abubuwa da yawa a wannan rayuwar tata, wanda muhimmai a ciki sune fargawa da lamarin Al'ameen tun kafin abubuwa su cakud'e mata da kuma yin hankalin cewa bai kamata ka d'orawa mutumin dake nesa da kai wanda baka fahimci halinsa ba tsana mai yawa, don daga baya zaka zo kana dana sanin hakan ne.

Tunaninta ya katse sanda ya mik'o mata zara-zaran yatsunsa na dama alamar su gaisa, sai ta janye nata ta b'oye shi a bayanta.

"Babu kyau gaisawa da maza a addini na."

"Ohh, I'm sorry."

Ya fad'a game da d'auke nasa hannun. Lokacin da suka fita harabar parking d'in, ya juyo ya kalle ta sannan ya tambayi abinda yake tambaya kullum bayan gama karatun nasu.

"Zan iya kai ki gida?"

Ta girgiza kanta a hankali, ba zata k'are mu'amalarta dashi da abinda tun farko bata fara ba.

"Idan na fita..."

"... zan sami mota."

Ya k'arashe mata abinda take fad'a kullum, sai ta d'aga masa kai kawai da murmushi a fuskarta.

"Allah sada mu da alkhairinsa."

Wannan kalmar itace ta dasa aya guda a mu'amalarta da mutumin da take wa kallon muguwar tsana ada, a yanzu kuma take masa kallon wanda yayi mata taimakon da ba zata sake samun irinsa ba, zuciyarta ta bashi wani matsayin da har take ganin zata yi kewarsa a cikin ranta.

Adam ya lumshe idonsa kad'an yana hangen tafiyarta, yaso ya tambayeta k'asar da zasu koma amma sai yaga babu amfanin da hakan zaiyi masa, da kowanne taku da take yi, gani yake kamar tana warware wannan zaren da yake tunanin ya had'a k'addararta ne da tasa a waje d'aya.

A yanzu komai zai cigaba da tafiyar masa, ya kammala aikin da Mr. Hawkins ya sanya shi, don haka dole ne shima ya cika alkawarinsa ta hanyar d'auko masa file d'in farko da Malamin phisics na makarantar ya fara cikewa sanda yazo kamar yadda suka yi yarjejeniya, tunda Mr. Hawkins shine ke da iko akan d'akin da ake ajiye bayanan malamai.

Da bayanan cikin file d'in zaiyi amfani ya kammala abinda ya kaishi makarantar, dasu zaiyi amfani ya fito da dukkan wata shaida daya tattara da zata nuna cewar malamin physics na makarantar, David Peters?shine dai mutumin da ake zargi da kisan wata yarinya a garin Alaska shekara biyu da suka wuce!

A yanzu komai zai cigaba da tafiya kan tsarinsa kenan, zai koma bakin aikinsa sannan zai samu hutun da ya nema a baya wanda dashi ne zaiyi amfani ya gyara rayuwarsa, ya nemo asalinsa ya fita daga wannan rayuwar ta bogi da yake ciki. Komai zai tafi masa daidai da yardar ubangijinsa.

Komai!

Ya k'ara jaddadawa kansa sanda ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga.

Sai dai abu d'aya ne bai tabbatar dashi a cikin komai d'in ba... yaushe kwakwalwarsa zata goge hoton idanun Fadeelah daga cikin kansa? tunda a tunaninsa shi da ita sunyi hannun riga a yanzu, k'addarar data had'a ta raba su. Sai dai abinda bai sani ba shine...

... wata k'addarar bata ma fara ba!

?%O??%

_Me ya faru tsakanin Al'ameen da Fadeelah a wannan ranar da yaje makarantarsu?_

_Wace k'addarar ce ke shirin jan akalar labarin bayan shekara guda?_

_Wai ina mutanen Ikara ne? 'yan uwan Bintun mu me hatsari?_

_Ina Maryam 'yar uwar Bintu? ko kuma ince Mairo?_

_Kuna tunanin akwai dalilin shigowar wad'annan lauyoyin biyu cikin rayuwar Fadeelah?_

*Waye ya hango cewa yanzu zamu fara warware zaren labarin?*=??

*BAYAN NA MUTU!*

?AYSHA SHAFI'EE

*12*

*(&_&)*

*BAYAN SHEKARA GUDA*

*ABUJA, NIGERIA.*

Asiya ta ware atamfar dake hannunta daga tsaye a gaban mudubi, kalar peach ce, k'asanta kuma yana da ado irin na leshi.

"Kai! gaskiya atamfar nan tana had'u wallahi, Zainab ta iya fito da anko... Rahma kalle ta fa a bud'e."

Cewar Fatima wadda fitowarta kenan daga band'aki bayan ta d'auro alwala. Rahma dake kan gado tana danna waya ta juyo da kanta.

"Kai-kai, ke anya ba zan siya ba kuwa?"

"Wallahi mu siya.." Fatiman ta amsa 15k sai mu canja kala kawai tunda ba bikin zamu je ba."

Asiya ta kalli Rahma tace.

"Amma kuwa da anyi mara zuciya, a kwace muku saurayin sannan kiyi ankon bikinsa."

Rahma ta tab'e bakinta.

"Ke wallahi Nanah ita ba damuwa tayi ba, don yanzu ma tana da wanda suka tattaka shi a hannu,?kar kiyi mamaki ma ya gaiyace ta kuma taje."

Fatima ta k'araso daga k'ofar toilet d'in ta d'auki dardumar sallah sannan tace.

"Haba ko bata son shi fa da ciwo abin sai taji ba dad'i ko yaya ne, zata daure ne a gaban ku kawai."

"Baki gama sanin duniyancin Nanah bane wallahi, dama shi ya nace mata amma tun farko ya san tafi k'arfinsa."

Asiya ta juyo fuskarta da alamun mamaki kafin tace.

"Deelah kin san Nanah k'awar Rahma?"

Tayi tambayar tana kallon can gefe k'asan window inda FADEELAH ke zaune ta baje tarin littattafai a gabanta, da alama karatu tayi ta gama don a yanzu hannunta dake rik'e da pencil d'in da ta gama zana graph akai zane yake yi, irin zanen da mutum kanyi a lokacin da yayi nisa cikin tunani.

Kiran sunanta da Asiyan tayi ne ya katse dogon tunaninta, da d'an sauri ta d'ago da fuskarta wadda cikin shekara d'aya ga wanda ya santa a baya, yanzu zai hango alamun girma a idanunta da kuma kyawunta da ya sake fitowa, kamar an k'ara fik'e wasu abubuwan ne na fuskar tata.

"Me kika ce?"

Ta tambaya a hankali tana kallonta ta cikin siririn medicated glass d'in idonta.

"Kin san wata Nanah k'awar Rahma?"

"Eh, kamar na tab'a ganinta sau d'aya."

"To kinga ankon bikin saurayinta ne wannan, wai shine Rahma take tunanin yi."

Kafin Fadeelah tayi magana Rahma ta mik'e zaune tace.

"Wai sai cewa kuke saurayinta, mutumin da har ya gama bilinbituwarsa akanta bata taba bari yaje gidansu ba."

Fatima ta karb'e da saurinta.

"Amma dai ai saurayinta ne, tunda taci kudinsa kamar ba gobe, kuma ko ke nan kinci kud'insa ba ita ba."

"To wannan ne zai nuna tana sonsa, kawai dai yazo ya bata rabonta da Allah yayi zai fito daga hannunsa ne."

"Kin san Allah.." cewar Asiya. "... zan iya rantse miki Nanah ta so shi don watarana na had'u da ita a Stream (Asibiti) tace min shi akayi wa aiki taje duba shi, kuma kin san Nanah in bata son mutum ko mutuwa yayi sai taga dama zata ce Allah ya jikanshi."

"Kai k'arshen zance kawai bari in nemo muku ita kuji daga bakinta.."

Rahma ta fad'a tana danna wayarta, yayin da Fatima ta cigaba da zancen tana fad'awa Asiya, Fadeelah daga gefe kawai murmushi take tana kallonsu, bai kai minti d'aya ba Rahma ta nuno musu screen d'in wayarta data hau kan video call na whatapp, hoton fuskar Nanah wadda da alama daga bacci ta tashi ya nuna tar! akai.

"'Yar iska bacci ma take yi." cewar Asiya.

Ta cikin speaker wayar muryata ta fito.

"Yo me yafi raina Asee."

Fatima ta taho da sallaya a hannunta tace.

"Nanah bikin Umar za'ayi next two weeks."

Ta d'an had'e fuska kad'an.

"Wanne?"

Rahma ta zuro kanta.

"Dalla Umar fa sky."

"Ohh shege ya turo min katin last week nace Allah ya sanya alkhairi, kun san amaryar ne?"

"K'awar Asiya ce." Fatima ta amsa.

"Haba! kice zaku sha biki kenan, a watse a barta da gaiyar tsiya."

Asiya tace.

"Wannan dai kishi ne Nanah, don kin san mun yi miki kwace."

Ta cikin wayar ta d'an zare idonta alamun mamaki sannan taja tsaki.

"Wannan kwarangwal d'in zan wa kishi, to Allah na tuba in ana zancen maza ma wannan ai supplementary list zai zo, ko ita k'awar taki ba don kud'insa ba ba abinda zai sa ta kai kanta wannan wahalar."

Suka kyalkyale da dariya kafin Asiya ta sake fad'in.

"In dai har da gaske bakya kishi ga ankon bikin nan kiyi."

Ta d'ago mata atamfar daga kan cinyarta.

"Tayi kyau kuwa ba laifi, sannan kar ki damu kanki shine ma zai yi min... anjiman nan zan kira shi ince ya kawo min anko, ke nan gidan ma zance yazo wallahi dani dake zamu je mu karbo a wajensa."

"Yawwa Nanah!" cewar Rahma.

"Kice ke da k'awayenki ne ya kawo hud'u har da Fadeelah."

"Biyar ma zance besty, baza'a rasa wani mai son ba, ko a k'arawa Asee ta had'a biyu, in tana ganin kishin wannan abin zanyi."

Suka sake kyalkyalewa da dariya, sanda Fadeelah ta maida idonta kan zanen da hannunta ke yi. Sak! idanunta suka gano mata wad'annan lumsassun idanun irin na Adam akan paper ta, abinda take zanawa dama kenan? wane irin tunani ta tafi haka?

Sai ta lalubo cleaner da sauri ta gurje shi daga kan paper, amma duk da haka shatinsa bai tafi ba saboda yadda ta danna fensirin ya shiga ciki. Ya Allah! wai yaushe tunanin Adam zai barta ta runtsa ne? shekara guda fa? me ya sami kwakwalwarta ne.

Sai ta mik'e ta wuce su Asiya dake cigaba da zancensu ta nufi corridor d'in da zai kaita k'asa da niyyar zuwa kitchen ta d'auko ruwa.

A tsawon shekara guda da dawowarsu Nigeria kuma cikin 'yan uwan Mami, har yanzu ta kasa sabawa da hirar 'yan matan wadanda suke 'yayan yayyen Mami, saboda duk sanda suka had'u kafin tayi magana d'aya su sunyi biyar, ga salon magana kala-kala a bakinsu da kuma yadda suke mu'amalarsu na harkar k'awaye, biki da samari duk bak'on abu ne a wajenta, wani abu da bata tab'a fuskanta ba a sabuwar rayuwarta.

Shi yasa a duk ranakun k'arshen mako ko kuma juma'a irin wannan da suke zuwa Family house d'in a had'u gabad'aya, sai dai tayi ta sauraren su, in ta gaji kuma ta d'auko aikinta na makaranta tayi, duk da cewar suna iya kokarinsu wajen sako ta cikin harkokinsu amma ta kasa sabawa har yanzu.

Yanzun da take cikin wata irin nutsuwa fiye da duk lokacin daya wuce na baya, lakacin da suke rayuwa cikin k'asar turawa don ta yarda da karin maganar da Mami ke fad'a a kullum 'Kowa ya bar gida, gida ya barshi.' babu ta yadda zaka hada rayuwa a cikin mutane masu irin jinsi da kuma yarenka da mutanen da komai nasu daban ne da naka, ko da kuwa akwai alak'a wajen addini, dole ne ka jika a gefe a yanayin mu'amala yadda suke tafi da rayuwarsu.

A yanzu ba k'aramin k'okarin Mami take gani ba, yadda ta iya barin wannan rayuwar da tarin 'yan uwanta ta koma inda bata da kowa sai 'yanuwan miji wanda suma a cikinsu kusan kowa yarensa daban, ta tabbata in ba aure ba babu abinda zai saka mata wannan juriyar.

Hatta ciwonta yayi sauki yanzu, don kusan a kodayaushe suna da abin yi, al'amarin 'yan uwa da struggles na Nigeria yasa babu ranar banza da zata zo babu wani abin yi, ba kamar a America ba da komai gashi nan cikin sauki. Sai dai kuma kowannensu na mutuk'ar jin dadin hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login