Showing 48001 words to 51000 words out of 153964 words

Chapter 17 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3785

yin harkokinsa kamar ba komai, alhali damuwar na rarake ruhinsa ne ta ciki a hankali, sannan ya koyi yadda ake hak'uri da abu ma, alhali abun nan mai mutuqar muhimmanci ne.

So yake kamar yadda shekara guda ta horar da zuciyarsa, a yanzu ma ya cire ta a ransa, ya k'arasa abinda ya kawo shi sannan ya tafi, tafiya mai nisan da zata k'ara datse duk wata hanya ma da zata had'o kalmar 'ita' a rayuwarsa, ya samu yin harkoki kala-kala, aikinsa ya bunk'asa, yayi abubuwa, yaci nasararsu, sannan ya samu cigaba a rayuwarsa...

...amma gani yake kamar komai ba zai yiwu ba, kamar bashi da kuzarin da zai cim musu, duk akan yawan ganin Fadeelah yanzu da yake yi, shi yasa tun farko bai bawa kansa tabbacin in zai iya cigaba da bin umarnin mahaifyarsa akanta ba.

"Zazzabi ne kawai da matsanancin ciwon kai ke damunta, amma ba wani abu bane, tasha wad'annan magungunan na kwana uku, idan baiyi sauki ba sai kuje asibiti ayi mata wani check up d'in."

Likitan da Ibrahim (abokin aikin daya hadu dashi anan) ya turo ya fada yana miko masa takardar da yayi rubutu akai bayan fitowarsu daga cikin gidan.

"Okay, amma babu wani abu game da ciwonta dana gaya maka?"

"Gaskiya ni a dubawata ban gani ba, duk da cewa iya b'angarena kawai na bata maganin, amma dai in tasha magungunan ba'a sami yadda ake so ba, sai dai a nemi wani likitan da yake kwararre a b'angaren kwakwalwa."

"To shikenan Doctor, Nagode sosai!"

Ya fad'a da murmushi sanda ya karbi takardar maganin. Ya raka shi har mota yana k'ara yi masa godiya kafin ya kalli takardar daya bashi, wajen magaunguna hudu ne a jiki, watakila Mami zata sha daga da ita kafin ta yarda tasha, watakila kuma idan ta fahimci cewa ba ciwon nata bane zazzabi ne kawai ya sameta ita da kanta ta yarda ta karb'a.

Maimakon ya koma cikin gidan sai ya d'auki mota kawai ya juya ya fita, ya soke duk wasu abubuwan da zaiyi a lokacin ya fita neman maganin Fadeelah, a ciki harda cin abincinsa da tun jiya bai sa komai a cikinsa ba bayan ruwa, da kuma Hamida dake jiran wayarsa, rashin lafiyar Fadeelah tabi ta ruguza komai banda abu d'aya, abu d'aya da ba zai iya tsallake shi ba!

"Barka da war haka Abbu."

Ya fad'a cikin tsantsar girmamawa lokacin da aka amsa wayar daga d'aya b'arin, yana shirin shan wani round-about ne a lokacin wanda zai kaishi hanyar chemist d'in da aka kwatanta masa. Daga can cikin wayar muryar wani dattijo mai cike da kamala ta amsa.

"Barkanmu dai Al'ameen kana lafiya? ya aikin naku?"

"Alhmdlilah Abbu, aiki mun kusa gamawa, na kira jiya kafin jirginku ya taso amma ban same ka ba."

"Lokacin na cire layina na can ne, d'azu kuma naga kiranka amma shima a lokacin Maminku nata kiciniyar tarbata da girkinta mai dadi."

Murmurshi ya sub'uce a kumatunsa jin hakan, tun yana taro ya san mahaifinsa wani irin mutum ne mai saukin kai da yawa, hakan ne ya bawa?Aunty Miryamah damar rike kusan ragamar gidan bakid'aya, saboda kusan sai abinda tace yake yi, har kuwa zuwa yanzu.

Watakila kuma da yana da iyaye da 'yanuwa da wani abin yayi sauki, amma bashi da d'anuwa na jini ko guda d'aya, iyayensa sun mutu kuma sauran 'yanuwan duk na nesa ne dake rarrabe a garuruwa da dama, a da su kan ziyarce su lokaci-lokaci sai dai duk a cikin k'annensa ma shine mai iya tuna su sosai, don haihuwar Mami wata iri ce, bayan shi sai da ta shafe shekaru goma sha d'aya sannan ta haifi Fatima, daga nan Aysha da Haneefa suka biyo bayan shekaru bibbiyu, Saboda haka yafi su wayo a abubuwa da yawa.

Fatansa d'aya ne a yanzu, Mahaifinsa yayi amfani wannan damar ta ritaya daya samu wajen dawo da ragamar gidansa hannunsa, ya zama shine mai iko da komai ba sai abinda Maminsu tace ba..

"Yaushe kuke saka ran dawowa?"

Muryar cikin wayar ta katse tunaninsa.

"Babu rana amma dai kusan mun gama komai, So tahowar ba zata yi nisa ba."

"Allah ya taimaka kuma Allah ya kaimu, akwai zancen da zamu yi da kai in ka dawo."

"Insha Allah Abbu, nima zan taho da nawa."

Yaji alamun murmushinsa kafin yace.

"Ga Maminka nan ma ta shigo."

Al'ameen ne kuke magana? bani shi dama tun jiya bamu gaisa ba.

Tayi maganar tun daga nesa, a hankali yayi sallama da mahaifin nasa kafin ta karb'a.

"Al'ameen kana ne ina haka?"

Muryarta ta amsa daga cikin wayar. Ya kalli kowanne gefe daga kan junction d'in da yake tsaye sannan yace.

"Na d'an fita ne, bana gida."

"Yayi, dama ban fiye son yawan zamanka a gidan ba, d'azu munyi waya da Hamida tace kace mata kun kusa tahowa ko?"

Ya cije gefen lebb'ensa kad'an, shi bai sani ba idan Hamida d'aukar maganarsa take daga baya ta kunnawa mata.

"Hakane Mami, jiya na sha'afa ne ban gaya miki ba."

"Ya kamata ai, mu muna nan muna ta shirye-shirye so nake daka dawo ayi bikin a gama kowa ya samu nutsuwa."

"Bikin wa?"

Ya tambaya yana zare ido sanda ya tsaya a daidai harabar wasu gine-ginen kantinan.

"Bikin ka da Hamida mana akwai wani ne? su zahra ma duk sun gama shirinsu, abinda ya rage kawai ka dawo kayi naka shirin sannan ka sanar da abokanka."

"Abbu ya san da zancen?" Kai tsaye bakinsa ya tambaya.

"Yaushe ma ya dawo garin, zamu yi maganar dai dashi."

"Mami dan girman Allah ki ajiye komai sai na dawo tukunna, ai ba lokaci ne zai k'ure ba."

"Ai na san haka zaka ce dama, shi yasa tun farko ban fad'a maka ba sai da muka kusan gama komai tukunna, har yaushe zan zauna jiranka Al'ameen? tsawon shekara guda fa kenan dana had'aka da yarinyar nan, kuma ka san ta gama karatunta da komai, zama zamu yi tayi rana jiran k'ailularka?"

Ya tamke bakinsa cike da hasala.

"Shikenan to Mami, zan kira ki anjima akwai abinda zanyi yanzu."

Bai ko jira amsarta ba ya katse wayar, fatansa d'aya tunda Mahaifinsa na kusa yaji duk abinda ta fada, ya fara d'aukan mataki kafin ya yanke nasa hukuncin.

A cikin k'asan ransa ya ayyana cewa watakila lokaci yayi da zata daina juya su gabad'aya.

Bayan ya koma gida, Mami yaso ya dank'awa maganin hannu da hannu don ta tabbatar da cewar ta sha, amma sai tsautsayi ya had'a shi da Fadeelan a tsakiyar kitchen?d'in da ya biyo ta cikinsa.

Tana sanye da wata doguwar riga da ta d'an kama jikinta kad'an wanda hakan ya fito da irin ramar data zabge ta a kwana biyun da ta takura kanta take tunanin ciwonta ne ya tashi ba wani abun daban ba.

Bai san me take yi ba amma ta juya baya yafe da d'ankwalin kayan akanta, yayi gyaran murya had'e da sallama sai dai bata juyo ba ta amsa, saboda haka ya k'araso ya ajiye farar ledar magungunan a daidai gefen hannayenta.

Ta juyo a hankali ta kalli ledar sannan shi d'in da idanunta dake sanye da medicated glass, A cikin 'yan sakanni kawai abu guda d'aya tak! ya faru, ta samu amsar abinda take nema a cikin kanta tun bayan zuwan Al'ameen Nigeria, ta fahimci cewa a wannan shekara d'ayan da take ganin ta cire zancensa a zuciyarta, ba abinda ya ragu sai ma kewarsa da ta dad'a yi, wadda a baya take ture ta da tarin abubuwa, amma a yanzu ganinsa ya sabunta komai.

Shi yasa take jin ba dad'i yadda baya kulata a farko take kuma damuwa da son sanin abubuwansa.

"Watakila likitan ya gaya miki zazzab'i ne kawai ke damunki, in zaki taimaki kanki ga magani nan kisha."

Abinda ya fad'a kenan kawai kafin ya juya ya nufi hanyar k'ofa, a yadda yayi maganar baiyi tsammanin amsarta ba shi yasa ya juya ya tafi, zuciyarta ta gaya mata cewa in har bata ce komai ba kuwa to ba k'aramin rashin kyautatawa bace, saboda haka ta saki cokalin tean da take had'awa ta juya da sauri tabi bayansa.

"D'an tsaya..."

Har ya sanya rabin jikinsa a waje sanda ta fad'i haka, sai ya juyo a hankali ya kalleta, hasken fitilar kitchen d'in ya haska mata wannan kyakyawar fuskar tasa mai cike da kwarjini, sai taji k'afafunta sunyi rauni kamar taliyar data dafu da yawa.

"Nagode."

Kalmar ta fito kai tsaye ba tare da wani shakku ba, yayi shiru kamar hakan ya bashi mamaki kafin ya gyad'a kansa a hankali sannan yace.

"Sai da safe."

Ta koma ta jingina da durowar dake bayanta sanda ya bar kitchen d'in, bayan fitarsa tare da likitan d'azu ba irin tunanin da bai faru a cikin kanta ba, ta fassara maganganun daya gaya mata ta hanyoyi da dama akanta, ta gane cewa da gaske ne abinda ya fad'a ta dad'e tana cutar da kanta ta hanyoyi da dama bayan ma rashin lafiyarta.

Kamar Al'amarinta dashi, ta sani cewa hadisi ne guda daga manzon Allah cewa zuciya tana son wanda yake kyautata mata, amma ita take ta kokarin karyata hakan akanta, Al'ameen mai tausayinta ne da kuma kyautata mata tun farkon had'uwarsu, shi yasa zuciyarta ta yarda dashi a iya d'an wannan lokacin har ta saba dashi amma tazo ta karyata kanta a gabansa da dimbin mutane cewa bata sonsa kuma ba zata tab'a sonsa ba, ta cutar da kanta tsawon wannan lokacin, watakila ma shi yafi ta cutuwar.

A hankali ta juya ta koma wajen ledar magungunan nan, ta kai hannunta ta bud'e ciki, sanyi ne da ita kalau na rab'ar A.c motarsa da bai gama hucewa ba, sai taji sanyin ya shiga har jikinta kamar yana gaya mata wani abu da ta kasa fahimta, kuma bata kai ga fahimtar ba k'ofar kitchen d'in ta hanyar falo ta bud'e, muryar Zahra ta kwararo ciki.

"Aunty deelah kizo inji Daddy."

A hanyarta ta zuwa falo ta ayyana a ranta cewa lokaci yayi da ya kamata ta canja, ta samu wanda zata dinga raba damuwarta dashi.

****

BAYAN KWANA BIYU.

"Fadeelah son Al'ameen kike."

Zuciyarta ta fad'i ta rugurguje jin haka, da sauri ta d'ago da idonta ta kalli Fatiman dake zaune a gabanta, A duniyarta kaf! banda Mami, Fatima kawai zuciyarta ta zab'a don gayawa sirrinta.

Shi yasa a yau da suka zo gidan daga kasuwa bayan sayayyar kayan bikin Aseeyah, zuciyarta tata ta kasa hakuri sai da ta jata can k'uryar d'akin Mami ta?shaida mata komai da yake faruwa tsakaninta da Al'ameen tun farko.

"Kin riga kin sani kema kawai dai kin k'i barin kanki ki fahimta ne saboda tsoron da kika sa na mahaifiyarsa, ki lura sosai ki gani a wancan lokacin da kika saba dashi sanda kuna America, kin manta ne kwata-kwata da zancen mahaifiyar tasa kin ture ta a cikin kanki, amma daga lokacin da ya fad'a miki yana sonki kika dawo da komai kika datse alak'arku."

Ta girgiza kanta sannan ta k'aryata abinda ta gama lissafawa a ranta.

"Wannan hasashenki ne kawai Fatima, amma ni bana tunanin ina son Al'ameen, kawai dai ina ganin kyautatawarsa ne game dasu Mami da kuma yadda yake damuwa da al'amarina."

"Ai ba tunani kike ba Fadeelah, d'an balaraben nan ya dad'e da tafiya da zuciyarki, ki bud'e idonki sosai ki gani me yasa kike yawan tunaninsa?"

Ya salam! yawan tunani shine so? To in haka ne Adam fa? ta tambayi kanta, a kwanakin baya ma ai tafi damuwa da tunanin Adam, zuwan Al'ameen ne kawai ya rage shi, kamar ta gaya mata zancen Adam d'in sai kuma ta fasa, zata rikita tane kamar yadda tata kwakwalwar itama take a rikice yanzu.

Fatima dake kallonta ta d'auki shirunta a matsayin nazari.

"Kin yarda kina sonshi Fadeelah?"

Sai ta d'ago daga mutsikka 'yan yatsunta ta kalle ta.

"Ko na yarda babu amfanin hakan ai, na fad'a miki na riga na gaya masa cewa bana sonsa kuma ba zan tab'a sonsa ba sannan a cikin mutane fa?"

Fatima tayi murmushi ta kamo hannunta d'aya sannan tace.

"Kuma sai aka gaya miki shi ya yarda? yaya ma kike tunanin zai yarda? In ya yarda me yasa bayan zuwansa kuma zai cigaba da kula dake?"

"Ba fa kula ni yake ba, tunda yazo ko gaisawa ba mayi, kawai dai ranar da bani da lafiya ne muka yi magana daga nan kuma muke gaisawa."

"Ba dai kuna gaisawa ba, saka ranki a ruwan sanyi, ni zan gaya miki hanyar da zaki bi yanzu ki tattaro hankalinsa kanki gabad'aya, yadda ko ita mahaifiyar tasa sai ya manta da lamarinta."

Mamaki ya kama Fadeelah ta zare ido tana kallonta.

"Anya Fatima Psiotherapy kuwa kike karantawa a makaranta?"

"Ke bar wannan zancen, yanzu bari mu fara tsara yadda zamu rik'e d'an bak'on balarabenku."

Gefen zuciyarta na farko yayi na'am da hakan, yayin da d'aya gefen ke gaya mata cewar in har ta amince da neman soyayyar Al'ameen, Adam fa? meye matsayin tunaninsa a ranta?

Adam fa?

Ta sake maimatawa kanta a ranar lokacin da tazo kwanciya.

***

A D A M

Wani farin dattijo dake zaune daga tsallaken teburin ya kalle shi cike da tsananin damuwa da kulawa yace.

"Ya kamata ka gaya mana sauran kwanakin da suka rage maka a duniya don mu fara shirin jana'izarka."

Ya tsaya cak! da rubutun da yake yi sannan ya d'ago ya kalle shi.

"Dama mutum yana sanin ranar da zai mutu ne?"

Ya tambaya da muryarsa mai fitowa kamar auduga saboda taushi.

"Abinda nake son in tambaye ka kenan, don naga kamar kai ka tsara taka mutuwar."

Ya tsuke baki kad'an sannan ya ajiye biron hannusa.

"Har yaushe zamu daina zancen nan ne wai?"

"Har zuwa lokacin da zaka ajiye komai, ka hak'ura ka dawo rayuwarka ta baya."

Sai ya koma da baya ya kwanta a kujerar da yake zaune yayin da dattijon ya cigaba da biya abinda shi dashi suka riga suka haddace.

"A shekara guda kawai ka fita daga haiyacinka, kammanninka sun canja,? ka daina komai banda aiki, awa ashirin da hud'u kullum cikin rubuce-rubuce kake, mu kanmu mun daina samun lokacinka, in ba yanzu da za'ayi gyara aka koro ka daga offfice d'inka ba ka gaya min yaushe rabon daka zauna a gida irin wannan lokacin?"

Adam yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya tura duka hannayensa cikin lallausan gashin kansa, yatsun suka nutse a ciki kafin ya lumshe idonsa.

"Abinda kake yi ko kad'an babu daidai a cikinsa, na san cewa munyi maka laifi mun b'oye abinda ya shafi rayuwarka, amma bai kamata ace ka dauki wannan hanyar ba, ka daina walwala da nishadi gabad'aya, bama ka da hanyar yin tunda ka rabu da abokanka tun farkon fara aikinka, ka d'auki damuwa ka d'orawa kanka akan abinda bai zama tashin hankali ba sannan ka hana mu sanin halin da kake ciki,? kana cutar damu kana cutar da kanka akan abinda ya riga ya wuce."

Abinda ya riga ya wuce! haka suke gani, shi yasa a kodayaushe suke binsa da maganganun da baza su tab'a tasiri akansa, sun manta cewa idan ya saita zuciyarsa akan abu guda to duk duniya babu wanda ya isa ya canja masa shi sai k'addara.

Kamar yadda a yanzu k'addarar ta canja masa tsari da kuma tanadinsa gabad'aya, ta tankwab'e guntuwar hanyar da yayi tanadin gyara rayuwarsa da ita,?ba zai taba manta ranar nan da hakan ya faru ba.

Bayan ya kammala case d'in malamin nan ne ya samu damar hutu na shekara guda kamar yadda shugabansu yayi masa alkawari, saboda haka ya gama duk wasu shirye-shiryensa ya sayi tikitin tafiya k'asar Ingila wajen Magareth don samun amsoshin da ya dade yana mafarki game da mahaifansa na asali, bai ko shaidawa iyayensa na nan ba yace dasu ne kawai zaiyi tafiya, kuma duk raunin alak'arsu a lokacin basu zargi komai ba don a lokacin suna ta kan kokarin yadda zasu wanke kansu ne a wajensa.

Ya shirya ya kuma tsara komai sannan zuciyarsa ma ta riga shi tashi? zuwa can, mafarkinsa da tunaninsa gabad'aya a lokacin ya koma na yadda yake hasko kansa a gaban Magareth kawai tana shaida masa komai dalla-dalla game da iyayensa na asali, sai dai ana gobe tashin jirginsa ne komai d'in ya rushe,?wata mata mai zak'in murya ta kira shi da nambar wayar gidan tsofaffin inda Magareth d'in take, ta shaida masa cewa tsohuwar ta mutu a safiyar ranar, don haka ya taimaka yazo jana'izarta sannan ya karb'i ragowar dukiyarta da suke d'iba wajen kula da ita, don suna ganin shi kad'ai ne d'anuwanta.

Kamar yadda kofin tangaran zai fad'o daga sama ya daki dandaryar siminti ya tarwatse haka tunani da kuma zuciyarsa suka yi a ranar nan, yaji komai ya tsaya masa cak! Sannan komai yayi masa nisan da ba zai iya tattaro b'antarorinsu ya had'a waje d'aya ba, Uwar wahalar da yasha a shekarun baya tsakaninsa da gidan marayun da iyayensa suka karb'oshi da kuma ma'aikatu da asibitoci kafin ya iya samo sunan Magareth a matsayin wadda ta san ainihin mahaifiyarsa ta dinga nunawa tar cikin idonsa, ashe duk wannan fafutukar yayi tane kan abinda ba za??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i masa amfani ba.

Duniyarsa ta hargitse,?kamar yadda ta yaro k'arami keyi a lokacin da ya siyo alawar da ya dad'e yana mafarki bayan lasa d'aya kawai ta fad'a cikin kwatami! Tsawon wata guda a gida, ba irin k'okari da nacin da iyayensa basu yi ba amma ya daina komai, sai a rana d'aya kawai ya tashi koma office, ya soke hutunsa sannan ya karbi tarin ayyuka yasa hannu akai, wani abu da ya dad'a janyo masa k'iyayya daga masu adawa dashi a wajen aiki kenan, sannan kuma abinda ya dad'a janyo d'aukakar sunansa a wajen manyansu dama mutanen cikin gari da a da basu sanshi ba, yayi suna a garin washington da kewayensa, hatta makarantar da yayi aikin b'ad da kama sai da suka shirya masa taro na jinjina da kyaututtuka na yadda ya zauna cikinsu a matsayin d'alibi mai tashe ba tare da ko mutum d'aya ya san ainihin shi waye ba.

A hankali ya k'ara yin baya da kansa ya kwanta a kujerar, a wannan ranar Allah kad'ai ya san sau nawa yaga idon leelah ya masa gizo a cikin tarin d'aliban, idonta da ya riga ya zama wani b'angare na rayuwarsa a yanzu don tare dashi ya shiga cikin duk wata gwagwarmaya kuma ya fito, duk irin d'imbin aikin dake gabansa,? k'aryane a kowacce rana yazo kwanciya bai ga giftawarsu a nasa idon ba.

A ranar da akayi taron ya nemi k'awayenta kamar kwabon daya rasa amma matsalar shine ya manta sunayensu kuma bai san ta yaya zai banbance su cikin tarin d'aliban dake ta washe masa baki suna son d'aukan hoto dashi ba, Mr. Hawkins kawai ya tambaya shima kuma ya gaya masa abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login