Showing 45001 words to 48000 words out of 153964 words

Chapter 16 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3774

da take gani a idanunsu duk sanda suka je gidan Hajiya Amarya.

Ta tauna samosan hannunta a hankali sanda hayaniyar gidan ta k'ara rud'ewa sakamakon wata dank'areriyar sark'ar gold da aka gano a cikin d'an kit d'in kayan lefen.

Sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ta mik'e ta koma kusa da jakarta, ta zaro Id card d'in Adam, ta kalli wad'annan lumsassun idanun nasa da suke kama da yana d'aukanta a hoto ne duk sanda ya kalleta, da murmushinsa dake maqalewa a gefen lebb'ensa d'aya, da kwantaccen gashinsa daya taho har ya rufe gefen idonsa, taji kamar ta mik'a hannu ta ture gashin ta kalli idon nasa sosai, idon tayi kewa tsawon shekara guda da d'oriya.

Don a yanzu ta riga ta gama lissafawa cewa kewar Adam take, shi yasa ta kasa cire shi daga ranta tsawon wannan lokacin, shi yasa komai k'ank'antar abu yake tuna mata dashi, shi yasa a ranar data rasa magazine d'in nan ranta ya sosu. Kuma ba irin binciken da bata yi a internet ba, don ganin cewa Id card d'in nan ko na bogi ne amma license number jiki da komai baiyi kama da wanda aka kirkira ba, hasalima sunan ma'aikatar dake jiki akwai bayaninta a shafin yanar gizo, abu d'aya da bata samu ba shine sunayen ma'aikatansu don ta tabbatar in harda gaske Adam lauya ne.

Saboda har yanzu kwakwalwarta bata yarda ba, a tunaninta me zai kawo shi makarantarsu tsawon wannan lokacin in har yana da aikin yi, me zaisa ma ya b'ata lokacinsa akanta? Ta duba har cikin social media amma bata ci karo da suma d'aya ma mai shigen nasa ba.

Ita dai a yanzu bata san wane hali zuciyarta take ba, domin bayan tunanin Adam akwai al'amarin Al'ameen cakud'e fal a ranta, har ga Allah a yanzu bata jin dad'in yanayin mu'amalarsu, ta san abinda tayi masa shi ya jawo komai, amma hakan ya zama dolenta ne a lokacin, don ko ita kanta bata gama sanin kanta ba, ba zai yiwu ta biye masa su fara alak'ar da zata ruguza komai ciki kuwa har da zumuncinsu Mami ba.

Sai dai duk da haka, taso ace ak'alla yanzu bayan wucewar komai da shekara guda ko gaisuwa ce na shiga tsakaninsu amma tun zuwansa gidan bata ma ganinsa sosai, kuma a iya d'an lokacin da take ganinsa yana tare da Mami ne ko Daddy suna magana don haka babu wata kofa da ko gaisawar zata shigo.

Wani lokacin sai taji kamar ta tambayi Mami game dashi amma tsoron kar ta d'ago wani abun daga b'angarenta yasa take jan bakinta tayi shiru, don ba wai shi take kewa ba, A'ah wannan lokacin data saba dashi, hirarsu, sunayen da yake lak'aba mata, dariyar da yake yawan saka ta... ko kuma a dunk'ule ace yadda mu'amalarsu take ma gabadaya.

Ta yarda cewa a yanzu matsalarta guda biyu ce, Al'ameen da Adam.

Zahiri da bad'ini!

***

"Ina kewarka sosai, yaushe zaka dawo?"

Muryar Hamida ta fad'a ta cikin wayar dake kare a kunnensa.

"Ban sani ba gaskiya amma dai mun kusa gamawa."

Al'ameen ya amsa sanda yake jera files d'in daya gama aiki dasu a ranar cikin wata chess drawer ta office d'in.

Hamida 'yar k'awar Maminsa ce wadda take son cusa kanta cikin rayuwarsa tare da taimakon mahaifiyarta da kuma ita Mamin, suna fatan zasu iya sawa ya fad'a cikin tarkonta da wannan kissa da hilar tata, shima kuma fatansa kenan... so yake ta d'auke hankalin nasa, ta janye shi ya fad'a cikin duniyarta, sai dai hakan ya gagara duk kuwa irin kokarinsa da nata.

"Na maka text da safe baka duba bane?"

"Ban fiye duba sak'onnin wayata ba shi yasa ban gani ba, amma tunda kin turo d'in ya shigo kenan, zan duba."

Lokaci ya riga ya shud'e da sanda yake damuwa da shigowar sak'o wayarsa.

"Ya wuce ma ai, nayi maka Barka da safiya ne kawai. Yanzu ka bani labarin Nigeria, na san kayi bak'i ko? don ance ranarsu tana da zafi."

Ya rufe idonsa a hankali, hirar ce baya buk'ata a lokacin.

"Kin san me? zan kira ki anjima na koma gida,yanzu ina wani aiki ne."

"Sure King, ayi aiki lafiya sai na jika."

Har ga Allah yasha mamakin tsananin hakuri irin na Hamida, don a yadda mu'amalarsu take yaci ace tun a baya ta sallami kanta, amma irin hak'urin da take yi dashi yasa shima yake d'an bata girma, matsalarsa daya da ita shine duk abinda ya faru tsakaninsu, hira wannan, to kalma bayan kalma kuwa sai ta gayawa mahaifiyarsa.

Ya bar cikin temporary office d'in da aka basu anan cikin garin Abuja da misalin k'arfe uku da'yan mintuna, sun riga sun kusa kammala komai na aikin daya kawo su saboda haka abinda suke yi yanzu bashi da yawa, ba kamar kwanaki ba da sai su kai har goman dare a waje. Da fitarsa d'an tsohon maigadin wajen ya taso da 'yar torchlight d'insa yana fad'in.

"Yallab'ai an fito, sannu da aiki... Allah ya kaika gida lafiya, Allah ya huta gajiya."

Bai fiye fahimtar zancensa gabad'aya ba amma idonsa ya kai kan torchlight d'in hannunsa, mamaki ya kamashi na tunanin me yake da fitila da rana tsaka haka, ba tare da ya tambaye shi ba ya kalli k'ofar d'akin daya taso, a d'an wani lungu yake saboda haka cikin d'akin dind'im yake duk da hasken ranar daya wadata ko'ina, ba haske ba taga sannan k'ofar ma ta karye sai kara ta da akayi. Cikin gurb'atacciyar hausarsa mai had'e da larabci da turanci yace.

"Babu haske a d'akin ka?"

Baba tsoho ya kalli k'ofar d'akin nasa sannan yace.

"Yallab'ai da yake ginin ba fuskar rana yake kallo ba kuma tun watan jiya da kwan ya mutu ne ban sake samun faragar ajiye kud'insa ba wallahi, amma ga wannan ai ina siyan batir duk sati."

Ya fad'a yana kad'a torchlight d'insa. Al'ameen bai gane duka zancen ba ya dai fahimci cewar babu d'in ne saboda haka ba tare da wani tunani ba ya zura hannunsa a aljihu ya zaro kusan rabin kud'in dake ciki ya dank'a masa.

Mamaki ya daskarar da Baba tsoho a tsaye a wajen, ya kalli kud'in sannan ya d'ago yace.

"Yallab'ai wani abu za'a siyo?"

"A'ah ka sayi fitila."

A hankali ya saki baki kawai yana kallonsa, shi mamakinsa da farko ai na me za'a siyo masa da yawa haka ne, amma ace wai shi aka bawa duk wannan kud'in? Bakinsa ya k'ulle, ya gagara cewa komai har sanda ya Al'ameen d'in ya shiga motarsa ya ja ya bar gurin, sai yabi fitilar motar da kallon mamaki kawai... ya san cewa ya bashi kud'in nan ne don yayi gyaran d'akin da zai kwana, amma ya ayyana a ransa cewa daga ranar ya bar gadi, zai je ya nemi wata sana'ar da zata rik'e shi da iyalansa fiye da sana'ar gadi.

Al'ameen ya isa gida wajen k'arfe hud'u saboda yawan motocin da kowa ke haramar komawa gida, a falon boys quarters d'in da yake zaune ya tarar da Faruk da Usman da wasu abokansu suna game d'in kwallon k'afa irin na jikin Television, suka gaisa har yana tsokanarsu cewa shima gashi nan zuwa a matsa masa wuri, kafin ya nufi cikin d'akin da yake kwana, baiyi wata-wata ba kuwa ya fad'a wanka don sauke gajiyarsa.

A lokacin da ruwan daya kunna mai d'umi daga shower yake zuba a kansa ne zuciyarsa ta shiga laluben fuskarta, fuskar Fadeelah da kullum yake son nesanta kansa daga ita, don ko giftawarta ya gani cikin gidan, sai yaji kamar dauriyar daya k'ulle zuciyarsa da ita tana barazanar kwancewa, musamnan in ta kalle shi da wad'annan idanun nata masu shek'i sai yaji kamar kar ya janye nasa har tsawon rayuwarsa, idan kuwa ya hango murmushinta daga nesa tare dasu Zahra sai yaji kamar an gaya masa ne cewa za'a amsa dukkan burikansa na duniya.

Ya sunkuya a hankali ruwan ya koma zuba a kansa ta baya.. yana nutsewa cikin gashinsa mai santsi daya manne kamar leda, ya san cewa abinda tayi masa a baya shine sanadin da yasa ya dake zuciyarsa ya karb'i ra'ayin mahaifiyarsa akanta, amma a yanzu ya fahimci nasa laifin a ciki shima. Laifin gaya mata cewa yana sonta ba tare da wani tsari ba, kuma a d'an lokacin da daga shi har ita suka fara fahimtar junansu, ya fara saka mata fatan samun mai tallafa mata tunda ya gaya mata cewa zai taimaketa ta duk hanyar da zai iya, sai yazo kuma ya lalata komai a dare d'aya... ya dagargaza zuciyar data fara yarda dashi a d'an k'ank'anin lokaci, ta yaya ma zata karbi tayinsa a wancan karon?

A lokacin daya fito daga wankan yake shiryawa, d'aya wayarsa mai rik'e da personal layin daya siya zuwansa Nigeria ta shigo ruri akan teburin durowar dake gefen gado, baya son d'aukar waya a lokacin amma ya san cewa kiran ba zai wuce daga Kamaal ba ko mahaifiyarsa saboda haka ya matsa ya d'auka, Kamal d'in ne kuwa ya shiga taya shi murnar cewa an turo da bayanan aikinsu kuma yaga irin namiji k'ok'arin da yayi kan yadda suka binciko kamfanin k'arya suke akan duk wata shaidar matsala da suka bayar.

Murmushi ya sub'uce a gefen kumatunsa jin cewa labarin aikinsa har ya k'arasa can.

"Ka bari kawai sai mun had'u zaka ji komai ma, jiya na nemeka amma baka d'aga waya ba."

"Yes, naje ganin wani case da Adam yake fighting ne akan wani tsohon mai kud'i da aka kashe."

Adam! mutumin da yake kwaikwayo kamar me, yake son samun irin nasarori da cigabansa, yake fatan sunansa ya shahara kamar nasa a cikin turawa, duk da cewa kuwa shi Corporate lawyer ne Adam d'in kuma Criminal defense lawyer!

"Anyi nisa a case d'in?"

"Zama na gaba za'a yanke hukunci, amma kar ka damu Adam ne fa... zai yi nasara akan case d'in kamar kowanne."

Kwarai kuwa! ya amsa a ransa don kowa ya kwana da sanin cewa a shekara guda data wuce, da mutuk'ar wuya ne Adam ya karb'i case baiyi nasara akansa ba.

Suka d'an tab'a hira kafin suyi sallama, daga nan ya lalubo number wayar Mahaifinsa da zai koma gida can Washington a yau bayan samun ritayarsa da yayi, amma har ta gama rurinta sau biyu ta tsinke ba'a d'aga ba, ya ajiye wayar sannan ya shirya cikin wata doguwar jallabiya kalar ruwan k'asa, kamar kullum ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ebi duka wayoyinsa ya nufi cikin gidan, inda k'aida ne a kullum abincin Mami da Fadeelah na nan yana jiransa.

"Ya Al'ameen zaka taya ni rubuta presentation d'ina na ranar abokai? (Freindship day.)"

Iman ta tare shi tun daga k'ofar Falon hannunta rik'e da takarda da kuma 'yan fensiranta harda masu kala. Ya d'an sunkuyo daidai kanta sannan yace.

"Kwarai kuwa Imani, me zai hana in..."

Bata ko jira ya k'arasa ba ta daka tsalle sannan a lokaci d'aya ta tarkata masa takardar da fensiran cikin hannunsa.

"Nagode sosai Ya Al'ameen, bari inje in bawa Trivo (Magen gidan) abinci."

Ya kalli paper da ba ko d'igo a ciki, da sauri yace.

"Na d'auka kince taya ki zanyi, ai baki fara rubuta komai a jiki ba."

"Ai abinda nake nufi kenan, ka taya ni rubutawa ka rubuta min duka."

Bata ko jira amsarsa ba ta juya da sauri tayi hanyar kicin. Ya d'an dafe kansa kad'an, daya sani bai amsa ba, don shi ya manta duk irin wad'annan abubuwan, ta yaya zai fara rubuta wani jawabi akan abokai yanzu? In dai ba shari'a zai rattaba tsakaninsu ba.

Ya d'ago da idonsa ya kalli Zahra da take tsakiyar couch d'in falon tana kallon wani indian series yace.

"Ke 'yar Aljana me yasa baki rubuta mata ba kina zaune kina kallo."

Ta cuno bakinta kad'an don bata son irin sunayen da yake saka mata, sannan ta d'ago masa wasu zungura-zunguran takardu guda biyu.

"Guda uku na rubatawa yarinyar nan, amma d'ayan ma yaga shi tayi tace wai abinda na fad'a yayi iyayi da yawa ciki, dama Aunty Fadeelah ce ke rubuta mata, yau tunda bata da lafiya kowa ya shiga uku a gidan nan daga naka wajen su Farouk zata tafi, watakila ma har ta tsallaka mak'ota."

Yadda take maganar hausarta na fita fil-fil, ba wanda zai yarda tayi zaman k'asar turai kuma a shekara guda baya bata iya hausar sosai ba, yawan zama dasu Sameera da kuma sawa kanta kar ta banbanta dasu ya taimaka mata sosai.

"Al'ameen ka dawo?"

Muryar Mami ta katse kokarin tambayar me ya sami Fadeela da yake shirin yi. Ya juyo ya kalle ta, cikin kayanta masu kyau tsaf take, sai dai da alamun damuwa kad'an a fuskarta.

"Eh na dawo Mami, na same ku lafiya?"

"Alhmdlilah, dama yanzu nake son kiran wani daga cikinku ya dawo ko kai ko Daddy."

"Lafiya dai? wani abu ya faru ne?"

Muryarsa mai taushi ta tambaya cike da damuwa saboda a yanayin muryarta kawai ya fahimci akwai wani abun.

"Fadeelah ce bata da lafiya tun safe, ko makaranta bata je ba, nayi-nayi da ita kuma muje asibiti amma tak'i yarda."

"Ya salam!" ya furta a hankali yana rik'e da hannun kujerar gefensa.

"Ya jikin nata yanzu?"

"Ba kamar da safe ba dai, amma har yanzu tana kwance."

Ya kalli k'ofar data fito daga cikinta, hanyar wani d'an k'aramin falo ne mai d'auke da kujeru uku a ciki, da alama Fadeelan tana ciki ne, don haka ba tare da yayi tunani sau biyu ba bakinsa ya furta.

"Bari in shiga in dubata."

Ya ture duk wani gargad'i da jar fitilar dake kad'awa akansa ya nufi cikin falon, ya san d'akin yana da d'an duhu kad'an amma fitilar a kunne take saboda haka a take ya hango ta akan kujera ta duk'unk'une cikin wani lallausan bargo kalar ruwan hoda, zuciyarsa ta narke gabad'aya sanda ya kalli fuskarta, idanunta a k'ank'ance suke alamun rashin bacci, da alama kuma bata yi tsammanin shigowar kowa ba, saboda tana ganinsa tayi motsi da sauri alamun gyara kwanciyarta.

"I'm sorry na tashe ki ne?"

Sai ta girgiza kanta a hankali tana k'ara gyara kwanciyar, ya k'araso ya zauna a hannun kujerar gefe.

"Mami tace baki da lafiya, ya jikin naki?"

Yaji alamun taja hanci kad'an kafin kai tsaye tace.

"Naji sauk'i."

"Kin sha magani?"

Idonsa na kanta saboda haka yaga lokacin da ta girgiza kanta a hankali.

"Saboda me?"

"Saboda naji sauk'i."

"Ta yaya kika sa.."

"Naji sauk'i Al'ameen ba sai ka tabbatar ba."

Ya Allah! ashe bata manta sunansa ba?

Ya ayyana hakan a ransa yana kallon fuskarta ta cikin hasken d'akin, ya san me take nufi sarai, don tayi maganar ne da muryar wannan Fadeelan daya sani a baya, mai k'arfin hali da dauriyar b'oye rauninta a gaban mutane.

Sai ya karkato daga kujerar da yake kai, ya k'ara fuskantar ta.

"In haka ne me yasa kike kwance tun safe?"

"Bacci ne bai gama saki na ba."

"Shi yasa idanunki suka canja?"

Sai ta lumshe idanun nata can k'asa har ya daina ganin kwayarsu sannan ta amsa.

"Har shi d'inma."

"Fadeelah rayuwa bata da adalci, ba komai d'an adam yake samun yadda yake so a cikinta ba, Allah yayi miki Rahmomin da mutane da yawa har da wanda suka fi ki a wani abin ke kwad'ayin samu, na fahimci uzirinki idan kin b'oye ciwonki a idanun jama'a, amma babu hujjar da zata sa ke da kanki ki dinga cutar kanki."

A hankali ta ware gashin idon nata ta kalle shi, Ashe har yanzu da guntuwar damuwar Al'ameen akanta? tayi zaton yayi cilli da komai na rayuwarta ne kamar yadda ya daina kulata.

Maganarsa kuma ta sata gajeren tunani, kusan abinda ya fad'a haka ne, duk da nakasarta tana da d'imbin rahamomin da yatsu baza su iya k'irga su ba, Allah ya sanyata cikin karamtacciyar zuri'ar da suka karb'eta cikinsu da hannu hiyu, suke kyautata mata kamar yadda zasu kyautatawa jininsu, ga damar karatu data samu, irin karatun da ta san bata yishi a rayuwarta ta baya ba, sannan ga tarin experience d'in da take dashi na rayuwa data samo a wani b'angare na duniya.

"Ki daina sawa zuciyarki ta yarda cewa baki da matsala kuma zaki iya daure duk abinda ya same ki ba tare da wani tallafi ba, in kina son ki cigaba a al'amuranki dole ne a karan kanki sai kin yarda cewa kina da rauni ta wani b'angaren, kin amincewa kanki da na kusa dake kun taimake rayuwarki, akwai mutane da yawa a duniyar nan da suke cikin hali wanda yafi naki, amma babu alamar da take nuna hakan saboda iya kokari suna taimakon kansu ta hanyar da zasu iya. Kar ki sa dauriya a kodayaushe ta dinga rarake ki ba tare da kin ankara ba."

Wai ta manta ne cewar Al'ameen ya iya kwantar da damuwa? meye sanadin da yasa ta saba dashi a d'an k'ank'anin lokaci a baya? amma saboda kaifin akidarta sai ta girgiza kai tace.

"Watakila ka manta ne, amma na gaya maka cewa na dad'e da daina karb'ar tausayin mutane akaina, kuma ina ganin amfanin hanyar da nake bi sosai, don haka ka rik'e tausayinka, Nagode."

Sakan d'aya, biyu, uku, hud'u... yayi shiru kawai yana kallonta, gefen lebb'ensa a cije kamar mai sak'a wani abun cikin ransa, sai kuma ya mik'e zaune akan hannun kujerar sannan ya zaro wayarsa ya shiga dannawa.

Idanun Fadeela suka bi wayar da kallo sannan shi d'in kansa.

Me zai yi?

?%O??%

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

15

(&_&)

"Hello Ibrahim, ka bar office ne?... Okay eh na bashi su, dama wannan Family doctor naku da kayi min maganarsa nake son in tambayeka zai iya zuwa gida?"

Shiru mai tsawo ya biyo baya, idonsa a tsaye kyam! alamun saurare kafin daga bisani ya gyad'a kai sannan yace.

"Nagode, zan turo maka da address d'in yanzu."

"Ki shirya, likita zai zo ya duba ki."

Ya fad'a sanda yake danna wata number a wayarsa da niyyar kira. Fadeelah ta tsuke bakinta kad'an tana kallonsa, ba don yayi amfani da kalmar mace ba, baza tace da ita yake ba saboda yadda yayi maganar hankalinsa baya kanta.

Haka kurum sai taji wani fata na cewar dama wannan ne farkon saninta dashi, dama k'addara bata had'a su a baya ba, da watakila hakan ya gyara alak'arsu yanzu.

"Babu likitan da zan gani Al'ameen, nagode da tausayawar ka."

Ta fad'a kanta tsaye tana kallon fuskarsa, sai ya juyo shima ya kalle ta, karo na farko data tsinewa idonta kenan, don ta tabbata fatanta ya nuna tar! cikin idon.

"Watakila kin manta ne, amma na gaya miki tun farko cewa bana tausayinki, taimakon da kika kasa yiwa kanki zanyi yanzu... don Mami kawai."

Yana fad'in hakan ya mik'e ya fita, tabi fad'in kafad'unsa da kallo da tafiyarsa mai cike da aji...

Don Mami kawai! ta furta a hankali.

***

Ya riga ya saba b'oye damuwarsa, ya saba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login