Showing 18001 words to 21000 words out of 153964 words

Chapter 7 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3767

san menene ba ya wuce ta cikin mak'ogwaronta, akasin tunanin kowa a wajen nan shine nata tunanin, kowa na gudun mutanen dake tozarta su, ita kuma a yanzu take shirin kai kanta ga d'aya daga cikinsu.

A take fuskar Adam ta haska a cikin idanunta, ko kuma yanayin fuskar, tunda bata tab'a bawa kanta damar k'are masa kallo ba balle har kammaninsa su zauna cikin kanta. Wane tabbaci take dashi a yanzu cewa alak'ar dake shirin faruwa a tsakaninsu bata da aibu?

Abinda Melissa ta fad'a gaskiya ne, ya kamata ta binciki dalilin da yasa ya kawo kansa cikin rayuwarta, ba zai yiwu ace daga Mr. Hawkins yayi masa magana ne zai amince ya b'ata lokacinsa akanta ba, ita d'in dake cikin jerin al'ummar da yake nuna tsanarsu a fili.

A lokacin da taron ya k'are suka koma cikin mota don tafiya gida, a lokacin ta d'auko jotarta ta rubuta.

Asabar, 11:30am

Bani da tabbacin abinda nake shirin yi.

***

Adam yasha had'uwa da mata kala-kala, dubunnai ma a tak'aice, manya da k'anana, masu burin cusa kansu cikin rayuwarsa ko don wani abun daban. Kuma a duk cikin yawansu, baya tab'a maida hankalinsa kan rik'e sunayensu, sanin kamanninsu ko kuma tuna wasu 'yan k'ananan abubuwan daban, misali idanunsu.

Saboda kusan duka d'auke suke da sak'onni iri d'aya, hank'oro, fata, buri, naci, ko kuma jin kai. Amma nata idanun suna da banbanci, banbanci daga na duk wata halitta da ya tab'a gani a duniyar nan.

Ya tuna ranar daya fara lura da hakan, wata safiyar laraba, tana tsaye daga jikin allon sanarwa tana karanta wani abu, wani abu da ya riga ya gama sanin menene, domin duk sanda zai hangota a wajen, zai kasance sanda suka gama manna fastocin ne. Yaji zuciyarsa ta tsaya kamar yadda yake faruwa duk sanda ya ganta, yaji ba zai iya yin gaba ba tare da yaga yanayinta ba, yanayinta da baya tab'a canjawa a duk irin lokutan da yake ganinta tsaye a jikin lokarta.

Saboda haka ya juyo ya dawo wajen allon, ya samu kansa da tsayawa daidai bayanta sannan ya karanta abinda ya rubata da hannayensa cikin harshen turanci.

Zanga-Zangar da za'a gudanar don hana mata saka Hijaab!

Jin alamun mutum a bayanta yasa ta juyo da sauri, yana tsaye dab! da ita ne don haka fuskokinsu suka yi kusa sosai, idanunsu suka had'u na wasu sakanni kafin ta matsa baya da sauri.

Sai dai shi ya kasa motsin ya kuma kasa d'auke idonsa daga kanta, rana ta farko kenan a rayuwarsa da ya fara tsayawa kusa da ita haka, ya kasa daina kallon kyakkyawar fuskarta dake nad'e cikin mayafin dake nuna shaidar addininta, sannan kamar kullum idanunta na manne da siraran glass d'in da ya k'ara fito da ilhamarta, idanunta kyawawa masu maik'o da kyalli, suna haskawa kamar an kunna wuta ta k'asansu.

Sai dai mafi rincab'ewar al'amarin tana masa kallon tsana ne! tsana wadda ke tasowa tun daga k'asan zuciyarta, tsana wadda baya tunanin wani mahaluki ya tab'a yiwa waninsa, sannan tsana irin wadda bai san dalilin wanzuwarta ba, don ko a cikin...

Wani dunk'ulallen naushi ya ziyarce shi a tsakiyar bayansa, bai tab'a wajen ba balle ya juya sai ya d'ora tissuen hannunsa kawai akan hancinsa dake zubar jini.

"Meye haka kuma Alex, na zata kun gama wasan?"

Muryar Matar dake amsa sunan mahaifiyarsa ta fad'a lokacin da take k'arasowa hannunta d'auke da towel da kuma robar ruwan d'umi.

Kowacce ranar Asabar, rana ce da suke wasan dambe (Boxing) shi da mahaifinsa kuma yawanci shi yake yin nasara, amma yau rana d'aya da Mahaifin nasa 'Alex Steve' ya cinye shi sai murna yake yana k'ara kawo masa wani naushin akai-akai yana fad'in cewa kar ya damu kansa da zafin, zai rayu.

"Nasha fad'a muku bana son wasan nan ko kad'an don banga amfaninsa ba, ta yaya ma za'a kira wannan da sunan wasa? Kalli fa irin raunin dake jikinka, meye amfanin hakan yanzu?"

Ta fad'a tana danna masa tawul d'in a gefen idonsa, Adam ya lumshe idonsa a hankali yana sauraren mitar tata, sannan kuma yana jin yadda jikinsa ke amsawa da ciwo, kamar gab'ob'insa sun kumbura ne saboda tsabar duka da naushin daya sha kota'ina. Wanda abu d'aya ne ya jawo masa hakan, tunanin wad'annan idanun da bai tab'a ganin abu makamancinsu ba.

"Ka tabbata ba abinda ya sameka?" Ta tambaya tana zuro kanta gefen fuskarsa.

Yana jin yadda dogon gashinta ya sauka a jikinsa sai ya mik'e tsaye kawai ya girgiza kansa.

"Ba abinda ya same ni, ina jin na gaji ne kawai."

Kusan hakan ne kuma, ciwon jikinsa bai dame shi ba, gajiya ce kawai a tare dashi, gajiyar da yake so yaje ya kwanta yayi barci ko ya samu ma kwakwalwarsa ta wanke tunanin da ya tashi dashi a yau.

Tunanin idon wata yarinya.

"Ina ganin zanje in d'an kwanta."

Ya fada sanda ya k'ara share jinin hancinsa.

"Amma baka ci abinci ba fa, ta yaya zaka kwanta cikinka ba komai?"

"Bana jin yunwa.."

"Ban yarda ba, dole ne kaci wani abun, ba zai yiwu weekends ma ace baza kaci wani abun kirkin ba..."

"Mum..!" Ya kira ta da sunan da ya san dole ne ta saurare shi, sai ta juyo daga k'ok'arin tafiya hanyar kitchen d'in da take ta kalle shi, hannunta rik'e da towel d'in nan.

"Bana jin yunwa, zan ci idan na tashi okay?"

Ba zata iya yi masa musu a yanayin da yake yanzu ba, baza ta taba iyawa ba... saboda haka ta d'aga kanta kawai tana kallonsa da idanunta masu cike da ramin da take so ya cike su, wani abu kuma da ta san ba zai taba faruwa ba.

Ya nufi hanyar d'akinsa a hankali, d'akin da ya shafe shekaru a cikinsa yana gina rayuwar da ba tasa bace, rayuwar da kuma baza ta tab'a zama tasa ba.

Ya saka muk'ulli ya k'ulle kofar sannan ya kife akan gadonsa, fatan iyayensa a yanzu wani abu ne da yake wa kallon fitar rak'umi ta ramin allura, don ba zai tab'a kasancewa ba, lokaci ya riga ya tafi da abinda ya shud'e kuma babu wanda ya isa ya dawo dashi baya!

A yanzu ba abinda yake fata da buri, irin tsarinsa ya tafi daidai, komai ya tafi babu tangard'a, kuma da alamun nasara tunda a yanzu zai fara taka mataki na farko a hanyar samun mafitarsa.

Oh God!

Idanunta suka haska cikin kansa, Me yasa ne k'addara ta had'a hanyarsa da tata? wane tabbaci yake dashi a yanzu cewa alak'ar dake shirin faruwa a tsakaninsu baza ta kawo masa matsala ba?

Da daddare a wannan ranar, bayan dukkan harkokinsa basu goge hoton idanunta daga cikin kansa ba, wani b'ari na zuciyarsa ya tabbatar masa cewa bashi da tabbacin abinda yake shirin yi.

***

RANAR MONDAY.

Fadeelah ta kalli kanta a mudubi, ta gyara zaman nad'in d'in hijaab d'inta sannan ta furtawa kanta cewa zata iya!

*?%O??%*


*BAYAN NA MUTU!*

?AYSHA SHAFI'EE

*06*

*(&_&)*

A karo na goma sha ya d'aga kansa ya kalli k'ofar, babu alamun an tab'a ta ma balle yasa ran shigowar wani, ko kuma ita d'in da ya ke zaman jira fiye da mintuna goma sha biyar a yanzu. Ya sake kallon agogonsa, ya rantse a cikin ransa cewa minti biyar in ta k'aru akai zaiyi tafiyarsa ne, ba zai b'ata awa gudar daya sadaukar cikin lokacinsa a banza ba.

Baza ta so kasancewarta tare dashi ba ya sani, don haka ba zaiyi mamaki ba in har bata zo, sai dai in bata zo ba zata b'ata masa tsarinsa ne, zata k'ara masa nisan hanyar da zai kai ga manufarsa alhalin yana ganin ya biyo gajeriyar hanya.

Ya janyo jakarsa dake gefe ya bud'a aljihun gaba, ya san ba zai rasa wani abin ci ba, don ka'ida ne kullum mamansa sai ta saka kayan cima kala-kala cikin jakar, a nata tunanin wannan sabuwar kulawar zata sa ya manta komai, zata sa ya manta k'aryar da suka raine shi a ciki.

Ya zaro ledar wani biscuit mai chocolate, ya bud'e ya fara ci a hankali yana lumshe idonsa, a shekarun baya rayuwarsa bai-bai take, kamar wanda ya saka riga gaba a baya ne yake ta harkokinsa, sai a yanzu daya ankara ya shiga fafutukar juya ta.

Ya jingina sosai da kujerar da yake kai sannan ya sake kai biscuit d'in bakinsa a karo na biyu ya tauna, zuciyarsa na gaya masa cewa zai cimma manufarsa, zai tsallake duk abubuwan dake gabansa kuma zai kai ga manufarsa da yardar ubangijinsa!

Abinda bashi da tabbacinsa guda biyu ne, gwagwarmayar da zai gamu da ita, da kuma lokacin da komai zai k'are, sannan ga matsalar ciwonsa ma, bai sani ba ko hakan zai shigo cikin hanyarsa, amma alkawari yayi wa kansa cewa ba zai k'ara dosar hanyar asibiti ba, yana da nasa hanyoyin da zai saita kansa.

A daidai wannan lokacin k'ofar ta bud'e, Idanunsa ma suka bud'e a lokaci d'aya, ita d'in da yake jira ce ta shigo, sanye cikin doguwar riga da nad'in da ya rufe gashinta, ta rataya jakarta sannan ta rik'o wannan folder a hannunta. Ya sake bud'e girman idonsa ya kalli fuskar tata sosai, yanayi kala-kala a jikinta, ba wanda zaka iya tsinta ya zama jigo musamman daga idanunta, Ya Allah! wad'annan idanun da suka hana shi sukuni tsawon kwanaki biyu. Asabar, Lahadi... akan wani dalili da bai san shi ba.

Bai san cewa ya tsira mata ido ne ba sai sanda ta juyo daga kallon kujerar Mr. David da take ta kalle shi, wani gefen zuciyarsa ya gaya masa cewa ya d'auke kansa kafin ta fahimci kallonta yake amma ita ta riga shi, ta juya ta sake kallon kujerar.

Ta san cewa an tashi daga makaranta ne a lokacin, don haka ba d'alibin da zata gani, amma mai zaman wajen fa? (Librarian) ya kamata ace shi yana zaune akan kujerarsa da take kallo fanko a gefenta.

"Mr. David baya nan."

Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ba don ta san cewa haka take a baya ba, zata ce ya rage sautinsa ne don a d'akin karatu suke. Ta juyo ta sake kallonsa, yana jingine da kujerar da yake kai yana kallonta ta k'asan lumsassun idanunsa. Taji tana son ta waska masa mari yadda zai dad'e bai sake bud'e idanun ba.

Sai kawai ta d'auke nata idon gefe sannan ta k'araso wajen teburin, ba yadda zata yi dole ne ta tsaya wajen mutumin da ada, bata tab'a barin zuciyarta ta yarda cewa ma yana raye.

"Me ya tsaida ke har mintuna goma sha biyar?"

Lallausan turancinsa ya nad'o kalmomin cikin sautinsa, wannan sautin nasa data tsana kamar me. Ya Allah ta tsani komai nasa ma.

"Naje sallah ne."

Muryarta ta fito kai tsaye babu gargada, a wayewar safiyar yau, ta furtawa kanta cewa 'zata iya' yafi sau cikin carbi, sannan ta nunawa su Melisaa dake ta sukar abin dauriyarta da kuma tabbacin cewa zata iya d'in, me yasa sai a gabansa zata k'aryata kanta?

"Na d'auka Sallar bata wuce minti biyar."

Ba tambaya yayi ba, fad'a yayi kamar kamar yana bata tabbaci ne. A cikin shawarar da Melissa ta bata harda cewa tayi k'ok'arin b'oye addininta a gabansa, amma saboda me? ta tambayi zuciyarta, zata yi mu'amala dashi na tsawon lokacin da bata tantance ba kuma a daidai lokacin da sallar azahar ke shiga, toh saboda me zata b'oye kanta bayan ya riga ya san ko ita wace ce?

"Baka da hurumin da zaka yi magana akan addinina, don ba abinda ya kawo ni nan kenan ba."

Abinda ta koya a k'ungiyar 'Musulm Support' sanin hanyoyi ne na yadda zasu kare kansu daga mutane irinsa masu k'alubalantarsu, amma Allah ya sani, ko kad'an zuciyarta bata kwanta da wannan tsarin ba, saboda ta yarda cewa a lokacin da mutum ya nuna tsoronsa, a lokacin hanyoyin da za'a sami galaba akansa ke k'aruwa.

Ga mamakinta sai ya gyad'a kansa a hankali sannan ya nuna mata kujerar gefenta alamun ta zauna. Ta dire jakarta akan table d'in dake tsakanin kujerar da tasa sannan ta zauna.

Ya mik'e zaune sosai.

"Yaya ma kika ce sunanki?"

"Fadeelah."

"Right, leelah..."

"It's Fadeelah." Ta katse shi da sauri.

"Fadlah?"

Sai ta juya idanunta kawai ba tare da ta kalle shi ba tace.

"Ka fad'a kawai yadda zaka iya."

Ya sake gyad'a kansa a hankali sannan ya juya jakarsa d'auko wani abin, sai a lokacin ta kalli fuskarsa sosai, fuskar dake b'oye halayyarsa a idanun mutane, fari ne sosai amma ba irin farin turawa ba Allah kad'ai ya san daga wace k'abila ya fito, dogon gashin idonsa ya kwanta akan na k'asa yabi saitin cikin jakar da kallo.

Zuciyarta ta matse da tunanin suna zaune a waje guda ne kuma suna shak'ar iska d'aya, daga yadda take jin k'amshin turarensa wanda ta haddace a gefen lokarta, k'amshin da tayi wa tambari da NASA.

Ya fito da tarin takardu fal! sannan ya d'ago ya kalleta, sai ta zame idanunta kan jakarta.

"Kafin mu fara komai, in kina da abin cewa, wannan ce damarki."

Kanta yaso ya d'aure, abin cewa kamar me? in ba addu'a yake nufin ta bud'e taron da ita ba ita bata san me yake nufi ba.

"Baki da wani abu da zaki fad'a min?"

Ya sake tambaya a hankali. A can cikin kwakwalwarta ta rubuta cewa dole ne ta sabawa kanta da wannan sautin muryar tasa.

"Abinda zan fad'a maka kamar me? na d'auka nazo nan ne don ka koya min lissafin da ban iya ba, ba don na fad'a maka wani abu ba."

Ta fad'a a lokacin da ta d'ago tana kallonsa ta cikin glass d'in idonta.

"Eh na san abinda ya kawo ki ai, amma ina tunanin kafin mu fara komai akwai wani abu da ya kamata mu fara tattaunawa, don hakan ne kawai zai sa mu san irin hanyar da zamu bi."

Fadeelah ta hard'e hannayenta a kirji, zuciyarta cike da d'acin yadda yake maganarsa hankali a kwance alhalin ita dukkan nata tunanin a dagule yake.

"Bani da wani abu da zan tattauna da kai in ba lissafi ba, saboda haka ko ta wacce hanya ne ma ka bi."

A cikin kanta ta fassara kallon da yake mata da na rainin hankali, kamar yana kallon wata k'aramar yarinyar da bata iya kirga 'one plus one' ba.

Sai ya mik'o mata wata paper da babu komai a jiki, ta karb'a.

"Bari mu gwada wannan hanyar, ki rubuta min sunayen subject guda biyar a wanda na baki friday."

Bata ko kalle shi ba ta zaro biro a cikin jakarta ta shiga rubutu, sai da ta jero su guda ashirin da biyu sannan ta mik'o masa ba tare da ta d'ago da kanta.

"Kinyi k'okari." ya fad'a ganin ta rubuce su duka.

Sai ka fara gyara tunaninka akaina!

"Wanne kike ganin kinfi iyawa a ciki?"

Kamar ta zab'i wasu a cikinsu ta nuna, sai kuma taga meye amfanin zuwanta kenan, saboda haka kai tsaye tace.

"Kowanne ina da matsala dashi."

"Haka na gani a takardunki."

Ta d'ago da kanta lokacin da yake fito da gabad'aya papers d'in ayyukanta na Maths wanda Mr. Hawkins ya tattaro masa, sai ta had'iye yawu sannan ta godewa zuciyarta da bata yi k'arya ba.

"Kin taba tambayar kanki me yasa bakya gane lissafi?"

Tambayar tasa ta d'ago da kanta a lokaci d'aya ta kalle shi, wani abu ya motsa a cikin kanta, kwakwalwarta ta maimata tambayar, Me yasa bata gane lissafi?_ Taji a jikinta cewar tambaya ce da ya kamata ace ta dad'e da yiwa kanta tun farko, me yasa take gane komai amma banda lissafi.

"Bud'a takardunki ki gani."

A hankali tasa hannunta ta janyo papers d'in dake kan table d'in, ta shiga bud'a su d'aya bayan d'aya, a jikin kowacce, a kan kowanne lissafi akwai iya wani waje da aka zagaye da jan biro.

"Duk inda kika ganshi a zagaye daidai kika amsa tambayar, daga k'asan sa ne kika kuskure wani wajen, saboda haka in kin kula zaki ga kowacce tambaya kin amsa rabinta daidai ne, rabi kuma yake fad'ar dake.

Saboda haka dole ne da akwai dalilin da yasa kike gane farkon kowanne lissafi kuma kike fad'uwa k'arshen kowanne."

Tayi shiru tana bin takardun da kallo, ita bata tab'a tunanin tana yin wani abu daidai ma a Maths ba, ta d'auka komai shirme take yi saboda data fara take jin kwakwalwarta ta cushe komai ya d'auke mata.

"Shi yasa na tambayeki idan akwai wani abu da zaki gaya min kafin mu fara."

"Ni bani da wani abun da zan fad'a maka, ban san komai ba."

"Kinga leelah..."

"Its Fadeelah..."

"Na kasa fad'ar hakan, kince zan iya fad'ar yadda zan iya."

Muryarsa da zurfi ta fad'a, sai ta gyad'a kanta kawai ba tare da tace komai ba.

"Idan muka ce zamu fara karatun nan a haka, baza a sami banbanci da yadda kike ganewa a aji ba, idan akwai matsala a abu dole ne sai an magance ta in ba haka ba, baza'a tab'a cigaba ba."

"Kana nufin akwai abinda ke hana ni ganewa kenan?"

"Haka nake nufi, kuma ke kin san kanki, idan kina da wata matsala ko yaya take, say it! zai taimaka miki sosai."

Tayi shiru tana murza yatsunta, bayan matsalar 'Memory loss' d'inta bata san wani abu dake damunta ba, sai dai in har ta bud'e baki a yanzu ta fad'i hakan, ta fad'a masa wani rauninta ne a matsayinsa na mak'iyinta.

Wani abu da baza ta tab'a bari ya faru ba, baza ta tab'a bari yaga gazawarta ta koina ba balle har ya samu damar danganta hakan ga sauran musulmai 'yan uwanta.

"Zan baki lokaci kiyi tunanin sosai, nan da zuwa kwana biyu."

"Kwana biyu?" Ta tambaya da mamaki.

"Subject ashirin da biyu nake dashi a cikin kwanakin da basu fi wata d'aya ba, amma har za'a sami kwana biyun kawai da zan zauna ina tunani?"

Ya cije gefen lebbensa na k'asa yana kallonta da idonsa a lumshe.

"Na fad'a miki baza mu iya fara komai ba sai mun san matsalarki, sauran karatun abu mai sauki ne da zamu iya gama shi in har ba matsalar."

Ta tsani yadda yake amfani da kalmar 'Mu' tsakanin shi da ita, kamar ta sake cewa wani abin sai zuciyarta ta gaya mata ai itama hutun ta ne baza taga fuskarsa har na kwanaki biyu ba, saboda haka ta mik'e tsaye ta d'auki jakarta.

"Ina ga ba amfanin zama na anan kenan."

Da haka ta juya ta fita daga cikin library d'in. Ta isa daidai gate d'in makarantar sanda yazo ya wuce ta cikin motarsa.

***

"Hace tiempo que no te veo!"

(Na dad'e rabon da in ganki)

Direban Bus d'in ya fad'a sanda yake mik'o mata metro-card d'inta bayan ya d'auki kud'insa.

"Abubuwa ne suka d'an min yawa, amma ina nan..." Ta amsa masa cikin harshen turanci sanna ta k'ara da..

"...muchas gracias." Hakan na nufin ta gode sosai.

Sanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login