Showing 81001 words to 84000 words out of 153964 words

Chapter 28 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3790

samu ka taho a yau, don gobe za'ayi jana'izarsa."

Sau d'aya kawai zuciyarsa ta buga amma ya tabbata Kamaal dake gefensa yaji k'ararta har cikin kunnuwansa!

***

Habiba ta tafi neman halaka Bintu.

Fadeelah ta shirya tunkarar k'alubalen dake jiranta a Ikara.

Adam zai koma lauyan Bintun da bai gani ba har yanzu?"

Ga license ga kuma rasuwar Mahaifinsa, wanne Al'ameen zai dauka?


BAYAN NA MUTU!

*?AYSHA SHAFI'EE*

*27*

*(&_&)*

Daddyna mutum ne mai sauk'in kai Fadeelah, bashi da hayaniya ko kad'an sannan bashi da matsala a komai, wad'annan halayen nasa su suka sa Mami ta samu damar juya gidanmu baki d'aya, amma yanzu girma yazo masa kuma ya dawo gida, don haka abubuwa zasu canja deelah, baki da fargabar komai insha Allah.

Ta tsamo wannan maganar a cikin kanta ne daga d'imbin lokutan da Al'ameen yayi mata maganar mahaifinsa kuma d'aidaiku da zancen ya had'o dana mahaifiyarsa, Bata tab'a ganinsa a zahiri ba amma yasha turo mata hotunansa da kuma nasu tare wanda saboda yawansu har tana ganin ma kamar ta san shi a gasken ne... Ya Allah! Bata san yaya Al'ameen yake ji a yanzu ba, ya rasa mahaifinsa, ya rasa Uba a lokacin da ya d'auki fata da yawa na cigaban rayuwarsa ya d'ora a kansa, ya rasa wani jigo na rayuwa dake d'aga darajar mutum a duniya.

Ta san irin wannan yanayin, don a yanzu da kwakwalwarta ta dawo daidai, ta san cewa a baya ta shige shi na sau d'aya ba, ba kuma sau biyu ba.

"Eh, Daddy ma ya biyo jirgin safe d'azun nan."

Muryar Mami Saffiya ta fad'a cikin wayar da take yi da wata 'yaruwarsu Daddyn dake can washington.

"Anyi jana'izar ne?" Ta sake tambaya cikin wayar.

Kafin Fadeelah ta fahimci amsar da aka bata, hannun Aunty Hadiza ya kamo nata a hankali.

"Deelah, yaya kike jin jikin naki?"

Idanunta na k'asa, don bata fiye son yawan d'ago kanta da take jin kamar bulo guda aka jingine akansa ba tace.

"Aunty da sauk'i, babu ciwon yanzu sai dai kawai nauyin da kan yake min."

"Allah ya sawwake, insha Allah shima zai daina kwanan nan... Ki ajiye duk wata damuwa a ranki kinji? An riga an samu lauyan da zai kare ki, sun yi magana da Daddyn jiya kafin tafiyarsa, watak'ila yanzu kafin a sallame ki ma ya shigo."

Ba tace komai ba, tayi shiru kawai tana k'ifta idanunta, tunda ta farka a daren jiya, ta fahimci hankalinsu Mami gabad'aya a tashe yake kuma suna cike da mutuk'ar tausayinta, basu san cewa ita kuma su take tausayi a yanzu ba, yadda ta d'ora musu tulin d'awaniyarta a baya alhali babu hakkinsu a kanta, sannan a yanzu kuma tana shirin sawa su fuskanci abinda ko a cikin danginsu bai tab'a faruwa ba sai akanta... Ita baren da ta shigo cikinsu. Ta rasa sai zuwa yaushe hargitsin rayuwarta zai barsu su huta.

Ganin bata da niyyar magana yasa Aunty Hadiza ta saki hannunta sannan ta matsa wajen Mami da ta gama wayar.

"Kunyi magana da Baba Habibu?" Ta tambayeta cikin sauti k'asa-k'asa amma duk da haka ta ji ta.

Mami ta d'auke wata guntuwar kwalla da yatsanta d'aya sannan ta amsa.

"Na kira shi d'azu yaya amma yace ba zai sami damar zuwa ba."

Maganar tasa Fadeelah ta dago da kanta da kyar ta kalle ta, saboda haka ne har take hawaye? Toh fisabilillahi meye laifin Baba Habibu anan? Bashi da wata alak'a da ita don me zai kashe ayyukansa ya bisu Zariya akan shari'arta? Ba tun yau ba tasha fahimtar ba'a kullum ne ake samun mutane masu zama da mutum zuciya d'aya irin Mami ba, saboda duba alak'ar fa... 'Yar tsintuwa daga dangin miji zata dinga nunawa kulawa haka?

"... Amma yace yayi magana da wani abokinsa an sama mana gidan da zamu zauna a can din, ya bawa Abdullahi numbersa idan munje zai karbo mukullin."

"To ai ba wani abu bane Safiyya tunda da Abdullahi ma, sannan gashi d'anuwan nata na can ya samo mata lauya insha Allah ina ganin bamu da matsala, tunda shima Daddyn ba zai fi kwana uku ba ai na san."

A duk maganar Aunty Hadiza, abu daya ne ya dauki hankalin Fadeelah, '... d'anuwan nata na can daya samo mata lauya...' Tunaninta ya k'ulle a lokaci d'aya, waye d'anuwanta a Ikara da zai sama mata lauya, dama har akwai wani sauran mai jin k'anta a Babban gida? Kafin ta samu wad'annan amsoshin Mami ta k'araso gare ta, ta zauna a kujerar gefe sannan ta rik'o hannunta d'aya kamar yadda Aunty Hadiza tayi.

"Ya kike ji yanzu?" Muryarta na nuna tsantsar kulawa.

"Da sauki Mami, babu wani ciwo."

Ta gyad'a kanta sannan tace.

"Yaya Hadiza ta tafi kiran Nurse a cire miki allurar."

Sai a sannan ta d'aga kanta taga ledar jinin da ake k'ara mata saura kad'an a ciki, kowanne lokaci daga yanzu, inya k'are nata jinin ne zai fara tafiya cikin ledar.

"Al'ameen yaso ganinki kafin ta tafi deelah, babu yadda ya iya ne amma wallahi yayi iya kokarinsa a cikin kwanaki hud'un nan, har license sai da ya samu na shiga kotu yace zai karb'i shariar taki, wallahi ya damu sosai, dalilin da yasa ya dakatar da d'aurin auren kenan, yace kowacce mace na farin ciki ranar aurenta, bai zai so ke kuma ace ba kya cikin haiyacinki ba a ranar.

"Allah ne bai nufa ba kawai Allah ne bai nufi komai kamar yadda muka tsara ba, wallahi abinda suke zargina k'arya ne Mami, ban kashe kowa ba, ban tab'a..."

"Shhhhhh." Mamin tayi saurin katse ta.

"Kar ki sake fad'a min haka Fadeelah, na san baza kiyi kisan nan ba, kuma na san baki yi ba don haka mu rufe babin nan, mu fuskanci abinda ke gabanmu shine yadda za'a tabbatar da hakan a gaban shari'a. Zaki iya tunawa a cikin 'yan uwan mahaifinki akwai wani..."

Wani wa? Zuciyarta tayi hanzarin tambaya sanda maganar Mamin ta katse, sai dai itama tana d'ago da kanta tata tambayar ta katse sakamakon bud'e k'ofar d'akin da akayi.

Taji kamar an saka adda an sara tsakiyar kanta mai nauyi a lokaci guda, don babu wani makari tayi IDO DA IDO da mutanen Ikara, mutanen da tsawon shekaru suka shafe a cikin tunani da kwakwalwarta, sai a yanzu cikin sati d'aya kawai komai ya baiyana, komai d'in dake barazanar tarwatsa rayuwarta ta biyu.

Kawu Yahya ne a farko, mutumin da a baya zuciyarta ta riga ta manna masa wani tambari da ba zai tab'a rabuwa da siffarsa ba.

"Allah ya yiwa yaya Bukar rasuwa Saratu, Babu yadda muka iya sai hak'uri, yanzu aka shiga da gawarsa Babban gida...

Wannan ranar, wannan ranar da yazo da labarin rasuwar mahaifinta tsaye daga k'ofar d'akin Inna Saratu, wata rana ce da ba zata tab'a gogewa cikin idanunta ba.

Bayan shi, Kawu Sulaiman ne ya shigo wanda shima ba baya bane tun a da wajen nunawa Innarta kiyaiyarsa. Fadeelah taji dad'in yadda Mami tayi shiru bata gaishe dasu ba don ba Mamin kad'ai ba idan har itama suna tunanin samun gaisuwarta ne to zasu dauwama inda suke ne.

"Sannunku." Kawu yahya yaga damar yanke shirun.

"Yauwa sannu." Mami ta amsa a hankali.

"Ke." Muryarsa da kauri ta biyo baya, Fadeelah ta d'ago a hankali ta sake kallonsa don ta san da ita yake.

"Kin gane mu?" Ya tambaya.

Sai ta gyad'a kanta ba tare da ta d'auke idanunta daga cikin nasa ba.

"Na gane ku Kawu Yahya Barka da zuwa."

Bai amsa ba sai ya kalli Kawu Sulaiman yace.

"Ai ni na san k'arya ne ace wai ta manta komai, kuma ita k'arya dama ai ba'a yinta kusa da gida ma balle a gidan..."

Ya dawo idonsa gare ta.

"... Bama zanyi mamaki ba da kin nuna baki sanmu ba, wadda ta tsallake gida tabi duniya meye ba zata aikata ba. Kinga nan..." Ya d'ago wata takarda a hannunsa.

"Sallamarki ce don haka ki shirya komawa tushenki a yau ki girbi abinda kika shuka, insha Allahu yau sai kwanan kotun da za'a bi mana hakkin mahaifiyar mu a cikinta."

Kai tsaye tace.

"Ai dama mun shirya Kawu, zuwanku kawai muke jira."

Watak'ila maganar ta bashi mamaki don saida ya d'an tsaya kamar kwakwalwarsa na gaya masa cewa da kunya ne fad'ar wad'annan maganganun wa yarinya k'arama kamar Bintu sa'ar 'yar cikinsa. Kafin ya sake magana sai wayar hannunsa ta shiga kara don haka yayi amfani da damar ya fita daga d'akin.

"Idan su basu gaya miki ba, to akwai 'yan sanda k'ofar koda zaki sake tunanin guduwa." Cewar Kawu sulaiman kafin shima yabi bayansa.

"Kar ki saurari zancensu dan Allah deelah, ki barsu..."

"Basu da laifi Mami, ina tunanin ko waye a matsayinsu zaiyi hakan, mahaifiyarsu fa suke zargin na kashe, Uwa wadda ta kawo su duniya..."

Sai ta kasa k'arasawa saboda kukan da taji yana shirin kunyata dauriyarta.

"Deelah kin tuna wani a 'yanuwan mahaifinki wai Kawu Ibrahim?"

Ta d'aga kanta a lokaci guda.

"Na tuna kowa ai Mami, shi wa ne a wajen Babana amma ba nahaifiyarsu d'aya ba, a baya shi kad'ai ne mai tausayina a cikinsu, shi kad'ai ne nake samun sauk'i a wajensa."

"To a yanzun ma bai canja ba Fadeela, shi ya kira Daddy yace ya sama miki lauyan da zai kare ki, wallahi baki san yadda hankalina ya kwanta da hakan ba, saboda halayyarsu har tsoro take bani.. Wace irin k'iyayya ce wannan?"

"Mami tun asali basa sonmu dama..."

"Mairo ta riga ta gaya mana komai ba sai kin maimaita ba."

A lokaci d'aya taji azabar cikin kanta ta d'auke, ta d'ago ta kalli Mamin da tsantsar mamaki.

"Mairo?" Ta furta sunan da take jinsa bak'o a wajensa.

"Kwananta uku a asibitin nan Deelah tunda aka kawo ki a waiting area take kwana, sai a jiya ne kafin farkawarki ni da yaya Hadiza muka matsa mata kan taje gida ta d'an kintsa kanta, don baki ga yadda ta fita daga haiyacinta ba daga ita har mijin dake ta zarya..."

Sai ta d'ago da wayarta tana fad'in.

"Tun jiya ma da akace kin farka zan kira ta, Yaya Hadiza tace in kyaleta ta huta don ana fad'a zata taho, amma yanzu gwara a gaya mata tunda tafiya..."

Bata k'arasa ba Fadeelah ta mik'o hannunta dake d'aure da syringe da wani irin sauri ta damk'e wayar Mamin, a lokacin jinin dake cikin ledar ya k'are, k'arfin yadda ta rik'e wayar kuma yasa nata ya koma shiga ciki.

"Kar ki kirata Mami, Dan Allah kar ki kirata, bana son ganinta... Wallahi har duniya ta k'are bana son sake ganinta.

Da tsananin mamaki Mamin ke kallon Fadeelah, ta san Mairo ta gaya musu cewa laifi tayi shi yasa su Kawu Yahyan da suka zo suka k'i kulata, to amma wane irin laifi ne da har a wannan halin ma Fadeelan da suke uwa d'aya uba d'aya zata juya mata baya?

Wai wani irin DANGI ne su Fadeelah haka?

______

3:43 PM.

Kawu Ibrahim na tsaye a harabar Babbar kotun cikin birnin Zariya yana tsumayin isowar motocin su Yahya da suka fad'a masa cewa suna dab da shigowa cikin garin. Sai dai daga lokacin da suka yi wayar zuwa yanzu yaci ace sun iso, amma bai sani ba ko Yahyan k'arya yake masa tunda zuwa yanzu ya san sun samu labari abinda yayi daga wajen Kawu D'anjuman da suke bin umarninsa.

Ya jingina da wata mota dake ajiye a harabar wajen sanda kwakwalwarsa ta shiga tariyo masa maganganun Kawu D'anjuma lokacin da ya sake tunkararsa da zancen ya taimaka a janye shari'ar.

Ban yi mamaki ba da ka k'ara samuna da wannan zancen Ibrahim, Hajiya uwa ce a wajenka amma iya baki kawai, yau da ace ita ta tsugunna ta haife ka wallahi wannan tunanin ba zai tab'a zuwa kanka ba, amma baka san ciwonta ba balle ka san na mutuwarta.

Kai kaso ka auri uwar yarinyar nan tun kafin Abubakar marigayi yazo mana da zancenta, shi yasa baka tab'a ganin aibunta balle na 'ya'yan, shi yasa a baya har kayi kokarin had'a d'anka aure da 'yarta, ba don yarinyar ta nuna halinsu na 'yan tsintuwa ta gudu ba da yanzu yaro yana nan ka had'a shi baragurbi.

Sannan banyi tunanin cewa har zance mai girma irin wannan na kisan uwa a garemu zai zo ka d'auko tsohuwar soyayyarka ka d'ora akansa ba, ko ka manta Aminar ta mutu ne Ibrahim? Idan don ita kake duk wad'annan abubuwan to yanzu bata nan, ya kamata ka bud'e idonka ka bari gaskiya tayi halinta, don gara ma ka sani, yau idan Sadiya da muke uwa d'aya ake zargi da kashe Hajiya, wallahi sai na saka an gurfanar da ita a kotu balle wannan yarinyar."

Ba zai manta kallon da Kawu Danjuman ya bishi dashi ba lokacin da ya furta.

"Na fahimci dukkan kalamanka Kawu, kuma banga laifinka ko kad'an ba don ra'ayinka ne, sai dai abinda zance shine ayi hakuri don Adamu ba zai samu damar karb'ar shari'arku ba, na riga na bashi umarnin cewa ya kare Bintu!"

Ba zai manta idanun Kawu D'anjuma a lokacin ba, ba zai manta kallon dake fitowa daga cikinsu ba, don sawa suka yi yaji kamar yasa gatari ne ya raba Babban gida b'ari biyu, ya d'auki wani b'arin daban da nasu, amma bai damu ba, don in har yayi iya k'ok'arinsa wajen kare Bintu koda kuwa babu nasara ya san cewa bai bagarar da yardar da yayansa marigayi ya bashi akan iyalansa ba, ya san kuma ko ba komai, bai bari jinin Amina ya wulak'anta a duniya ba.

Bayan k'arasowar su Yahya, a yanzu jiran Adam ne kawai ya rage masa, wanda ya bashi tabbacin cewa gobe da safe shima zai biyo jirgi ya taho tare da Sa'id, don sai ya k'arasa wani cike-cike da k'ungiyar da yake aiki ne sannan zai, Tunaninsa ya katse, sanda jerin motoci guda biyu suka shigo harabar kotun, ta ukunsu k'atuwar jeep ce ta 'yan sanda wanda ya tabbata a ciki Bintu take.

Motocin suka tsaya a gefe guda na wajen sannan mutane suka shiga fitowa daga cikinsu, ta farko wata tsohuwar golf ce dasu Yahyan ke ciki, wanda saurin fitowarsu ya shaida gajiya da kuma takurar da suka sha a cikinta, ta biyun kuma wata mulmulalliyar mota ce k'irar da Kawu Ibrahim d'in bai taba gani ba rufe ruf! Cikin gilashin dake shaida ni'imar Ac dake cikinta, mata biyu ne suka fito daga baya, sai namiji d'aya da kuma wata matashiyar budurwa daga gaba. Ba sai wani ya gaya masa ba ya fahimci sune marik'an Bintun da komai ke faruwa saboda ita.

Idon sa ya juya kan motar 'yan sandan da suka diro rik'e da bindigoginsu, a sannan ne yaga sanda d'aya daga cikin 'yan sandan ya bud'e gaban motar dake rufe da bak'in gilashi, a sannan ne kuma idanunsa suka hango masa Fatima Bintun dake zaune cikin bak'ar jallabiya da bak'in mayafe yafe a kanta.

Ya k'ifta idonsa ya sake bud'ewa amma ya kasa yarda wai Bintun da ya sani a baya yake gani a yanzu, wannan yarinyar dake shafe yinin ranarta a kullum cikin bautar Hajiya, wannan marainiyar data rasa duk wani gata da tallafin duniya bayan rasuwar iyayenta, wannan Bintun dai da ta bar gida da wannan cukurkud'adden hijabin da yayi mata gani na k'arshe a cikinsa.

Ta yaya Sadiya ta iya gane ta a wannan kammanin? Ya san ita fara ce amma wannan farin nata ya zarce na Bintun daya sani, kamannin ma sun fik'e sun zarta na wannan yasasshiyar?marainiyar daya sani a Babban gida.

Ba don 'yansandan da kuma su Yahya ba, ya tabbata ba zai shaida cewa wannan ce Bintun da shari'a ke jiran zuwanta ba.

_____

4:06PM.

Ba'a bari Kawu Ibrahim ya samu ganinta ba har saida aka gama duk wasu cike-cike da tsare-tsare wanda Bintun tayi su babu musu kamar injin da aka saita akan hakan, daga nan aka bata cell a cikin kotun kuma aka umarce shi da sai yabi hanyar da mutum ke bi don ganin mai laifi.

A d'akin da ake ganin masu laifin ya zauna sannan mai tsaro guda d'aya ya fito da ita, ta k'araso ta zauna a kujerar dake fuskantarsa yayin da mai tsaron ya koma ya tsaya daga gefe.

Sai a yanzu da yake kusa da ita, sannan yaga kammanin Bintun daya sani a baya, ya d'an tsaya ya kalle ta? idanunsa cike taf da alhini, kafin ta gaishe shi da muryarta mai rawa, sai yace.

"Yaya jikin naki? Ance yau aka sallamo ki koh?"

Sautin muryarsa ya dawowa da Fadeelah komai game dashi, zuciyarta ta tare ta kuma goge tsawon wannan lokacin data bar gida, taji a ranta cewa a jiya ne kawai komai ya faru, a jiya ne yazo ya tashe ta tsakar dare yake shaida mata cewa za'a kaita police station da safe, a yau kuma gari ya waye gasu a cikinsa, saboda haka maimakon ta amsa sai tace.

"Kawu kayi hak'uri, rashin mafita ne yasa na gudu na bar gida, amma wallahi bani na kashe Hajiya ba, ban kashe ta ba kuma ba zan tab'a iya kashe ta ba, na fad'a maka tun a wancan lokacin."

"Na sani Bintu, na fahimci komai ba sai kin maimaita ba, don komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci abinda ke gabanmu a yanzu, na samo lauyan da zai kare ki, d'anuwanki ne ma, d'an k'anina Ahmadu da kike ji a baya ana cewa ya b'ata, shine ya nemo mu bayan bakya nan yazo har Babban gida a cikakken lauyansa, munyi maganar dashi kuma zai zo ya ganki gobe insha Allah, ina so ki fad'a masa duk wani abu da zaki iya tunawa don Allah."

Sai ta d'ago da idonta ta kalle shi, har sai an rok'e ta ma? ita da a yanzu take neman duk wata hanyar da zata iya samun nasara akan Habiba da kuma su Kawu D'anjuma, don ta karyata tunaninsu akanta ta kuma nuna musu darajarta na d'iyar 'yar gudun hijirar da suke gudu.

"Kawu, naga Mairo ma a can."

Ya gyad'a kansa sau d'aya.

"Haka Sadiya tace, har ana tunanin tare kuke sai daga baya su Yahya suka ce itama taje nemanki ne a lokacin."

"Wallahi tun bayan tafiyata ban taba ganinta ba sai a ranar da Aunty Sadiyan ta ganni itama."

"Kar ki damu Bintu, zancen Mairo mai sauk'i ne, naki daya had'a da hukuma shine a gabanmu yanzu, amma na san Adam zai yi duk kokarinsa don ganin munyi nasara akansu."

Jimlar sunan Adam ta dawo da wani tunani akanta, tunanin wannan Id card d'in dake cikin purse a kuma k'arkashin kayanta, amma sai tayi saurin ture shi, hakan ba abu ne mai muhimmanci yanzu ba.

"Bintu mutanen da suka rik'e ki masu karamci ne, munyi magana dashi Alhajin kafin yayi tafiyar data kama shi, Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login