Showing 249001 words to 252000 words out of 259215 words
Chapter 84 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
cikin haraban gidansa ya tsaya a kofar gida batare daya kashe motarsa ba ya sallami masu zuwa amsar kudin taimako a duk safiyar duniya ,cike da farinciki suke saka masa albarka yaja motarsa yayi gaba ,a natse yake tuqi zuciyarsa na tunanin tanwer amman sai yayi sauri kawar daita ya sako wani tunani dabam a haka har ya qaraso kofar gidansu yayi parking ya fito yana taku a hankali tamkar baya son taka kasa nan ma dai mutane sukai masa casaaa yan maula ya tura hannu cikin ajihunsa ya zaro bandir din kudi ya mimika masu sannan ya shiga gidansu bakinsa dauke da sallama yayi mamakin da yaji baa amsa ba dan da wahala ka shigo gidan kana sallama ammi bata jiyo ta amsa ba ."
Yana kokarin kutsa kai cikin falon ammi hasera ta fito da sauri hannunta rike da plet tana cin soyayyar kaza sauran kadan ta fada jikinsa yayi saurin ja da baya yana kakkabe jikinsa murmushi ya bayyana akan fuskarsa "a'a danuwana sannu da zuwa haka nan ya tsinci kanshi da jin haushin ta tamkar ba dan ita yazo gidan ga , yaja tsaki batare daya amsa ba , ta kada kafadanta alamun bata damu ba ta cigaba da yagar kazarta shi kuwa yayi matukar hade fuska yana sake jin damuwa yaji komai ya sauya masa ba karamar yadda yazo da niyyar zai karbeta ba ,yadda ma take cin kazar ma kamar wata mayunwaciya "ina ammi ? yayi tmbyr a can kasan makoshi tare da juya wa ya nufi part dinsa na gidan "me kace ? ta biyosa da plet tana tmbyrsa "mara kwakwaluwa kawai yanzu zakice bakiji me nace ba da zaki min wata irin tmby ?".ya fada a zafafe yana cigaba da tafiya ."
"Allah ya baka hakuri ai banji abinda kace bane shiyasa da zaka wani ce min mara kwakwaluwa ."ya waigo inda take a bayansa ya kalleta a natse ,gata dai Kmr goggagiya amman sam villager ce ko magana bata iya ba komai da hauka take yi ,to daman yaushe zaa hada mutumin da yazo daga maiduguri da wanda yake rayuwa a lagos ?".ita kwakwaluwa bata aiki yadda ya kamata idan ana dankara mata nama dan allah malama ki ajiye kazar nan haka kin wani rungume kaza Kmr baki taba ci ba yasa kafa ya buge plet din hannunta ya shige part dinsa shiru tayi tana kallon kazarta a kasa ba tace masa komai ba dan ta fahimci rigima yake ji dashi ta zuba wa kazarta ido tana kallo ."Ta dauki lokaci tana kallon kazar kamar ta dauka amman ta guji ta disga kanta ta hakura tabiyosa dakin ta samu guri ta zauna tana fuskantarshi tare da sha gala da kallonsa atsawa ce yace "ke !.
"Tayi firgigib ta dawo haiyacinta “naam danuwa ta amsa da hakan batare data nuna damuwar da ke din daya kirata dashi ba ita da zai dinga shiga tsabgarta koda zagi ne ai zataji dadi ,"kawo min ruwan sha a cup". ta mike ta juya da sauri yabi tafiyarta da kallo sam babu natsuwa kamar tanwer ya lumshe rikitattun idanushi “Anya kuwa zan iya karbarta na hakura da tanwer “ ? Yana wannan tunanin taje ta kawo masa ta mika masa ya bude idanunshi da kyar yace "sha !
Ta bisa da kallon mamaki dan ita bata bukatar wani ruwa "ki sha ki samu natsuwar wannan bare baren kallon da kikyi wa mutane Kmr zaki cinyesu ya sake bata umarni ta narke masa fuska alamun baza tayi ba "ke wasa nake dake ne ? nan take tayi kamar yadda ya umarceta ta shanye ruwan tasss ta rike cup din tana kallonsa ," kije ki ajiye cup din ki dawo,tana fita ya zaro kwalin sigari acikin aljihunsa ya kunna yana zuka a hankali har ta shigo a matukar tsorace take dubansa "danuwa daman kana shan sigari ne ?meye sabo aciki ? ai duk suna cikin munanan dabi'una dana fada miki ko ma nace kadan daga ciki dan idan kikaji sauran ko kika gani bub zuciyarki zatayi ta buga "babu komai ina sonka a haka dan ni ko warin sigarin ma banji ba ta fada tana kokarin zama “bala’i ! Ya fada a kasan ranshi yana kallonta a kaskance abinda tanwer take mugun kyama shine ita wai ko warinsa bataji ba ?“nace ki zauna né ? ya fada a matukar fusace tayi sauri ta mike tsaye tana dubansa ya cigaba da abinda yake batare daya sake cewa komai ba ."
Bata zauana ba ta cigaba da tsayuwa tana dubansa tana murmushi d'an duk abinda yayi mata bata ji zafi ko haushi acikin zuciyarta ba bahasalima dadi taji dan tana mugun son kusancinta dashi wani irin kallon soyayya take masa idanuwansa suna matukar mata kyau a duk sanda ta kallesu sai taji kamar ta sunbaceau amman babu hali ya mike tsaye ya fito itama ta biyosa abaya sai ga ammi ta dawo "a'a yaushe kazo adnan ?Na dan jima da zuwa ya fada yana shafa sumar kanshi ina kikaje? "nan kusa na shiga nayi barka ne jikar gidan baba yaro ce ta haihu .ta shiga ciki bangarenta hasera ta biyota da sauri tana yi mata rada shima dole yabiyota bangarenta ta zauna akan kujera me zaman mutun biyu suka gaisa ta tamvayesa aikinsa da abokan aikinsa duk yace mata suna lfy ta kira hasera "ki kawowa yayanki abinci mana "aa ammi a koshe nake daman akwai wani aiki da zamu fita ne yana da matukar hatsari muna bukatar adduarki.
Aikawa nan take ta shiga zubo masa sun dan ta'ba hira yace "ammi ni zan wuce tô shikenan adnan allah yayiwa rayuwa albarka ke hasera kibi yayanki ya kaiki shopping din tunda baki da me kaiki dan allah ka sauke min hasera a wannan plaza din dake ayabo zata dan yi siyayyan kayan amafninta ne idan ma da hali ka tsaya har ta gama ka dawo min daita kaji dan alabarka ."
ya hade rai sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa sai dai bai amsa mata da zai kaita ba ko bazai kai ba har sanda hasera ta shigo falon "dan allah ku tafi tare mana kaji yarona ai ba kullum né zaka dinga kaita ba yau ne kawai ta fadi haka ne saboda ganin yadda ya hade rai ".aransa yace zamu fita tare amman babu inda zani daita a rabin hanya zan ajiyeta na qara gaba ".
Muryarsa a matukar hargitse yace "minti biyar na baki ki shirya idan ba haka ba sai dai ki nemi wanda zai kai ki ya fada yana shan kamshi tare da zira hannunsa daya cikin ajihinsa "kiyi maza ki shirya ki fito tun kafin ammi ta karasa maganar ta fada daki a wulakamce yabi bayanta da kallo sam sam bata da natsuwa da kamun kai wannan sai tanwer ita kuma dan taga ta samu kanshi shine take son juya zuciyarsa da rayuwarsa."
Minti biyar din ma bata gama cika ba ta fito da sauri kamar an korota yayi gaba yana sake yiwa ammi sallama kanta kawai ta girgiza wannan zuciya bata san ranar da zai daina ta ba abun zuciya da wanda bana zuciya ba duk fushin né agurinsa allah dai ya kawo maka sauki ta kalli haseera dake kokarin sanya baby shoe akafafunta "kiyi sauri fa kinsan halinsa zai iya wucewa ya barki ki dai san yadda zakiyi ki dan shawo kansa ku fahimci juna dan ina son ayi komai cikin kankanin lokaci a wuce gurin qarar hon din motarsa yasa ammi ta takaita maganarta "maza wuce gashi can ya fara danna hon dinsa me hargitsa lissafi da sauri tayo waje ta bude murfin mota "kayi hakuri please na tsaya saka takalmi ne "wa ya tambayeki wannan shirmen sannan da zaki wani bude min mota nace ki shiga ne ?ke me yasa baki da natsuwa ne bare wani abu shi class?ranta yayi mugun mugun baci zuciyarta ta soma zafi da tuttukin bakinciki amman dai ta danne ta tsaya tana dubansa batare data shiga din ba ,shima kallonta yake yana son yaga wani abu ajikinta wanda zai dauki hankalinsa ko guda daya kawai ya aureta ya manta da wata tanwer a rayuwarsa amman sam ya kasa hango komai bare ya dauka zallar shirme ne ke tattare daita sai daya gama wulakantata sannan ya motsa bakinsa"shigowa !"
A ranta taja tsaki tana cewa duk ka gama iskancinka da wulakancinka zaka shigo hannu ne zaka gane baka da wayo sai kaga kudi kace kashi ne dan iskan me daurin kai da zafin zuciya kawai ta shiga ta zauna bata gama rufe murfin motar ba yaja da gudu tayi sauri ta qarasa rufewa tana dubansa kamar zatai kuka ."
Gudu kawai yake a natse akan titi batare daya waigo inda take zaune ba bare ya kalli fuskarta ta waigo a tsanake tana kallonsa da kallon hannunsa daya dake kife yana motsawa a hankali ,taji kamar ta daura hannunta aka kyakkyawan hannunsa masu matukar haske da sheki ,wani sanyi dadi ke ratsata hade da sanyi ac wanda ke sake tsokano da matsanancin soyayyrsa dake daskare acikin zuciyarta ,hagu da dama shine kawai zuciyarta take muradi wani irin tuqi yake cikin salo me kashe wa duk wanda ake tukawa jiki .”
sai da sukayi rabin hanya taga ya tsaya a tsakiyar titi batare daya kashe motar ba sannan bai kalli inda take ba "maza sauka ki kama gabanki "
A matukar tsaro ce ta kallesa "bana da kudi ajikina fa tayi Kmr zatai kuka wani abu ya daga a gefensa ya ciro bandir din yan dubu day day na dubu dari ya daura mata akan cinyarta "ki sauka zaki samu wata motar da zata kai ki duk inda kike so kai tsaye dan ni bani da wannan lokacin "haba danuwna me yasa zaka min haka ?Sam bai kyautu ba da zaka barni anan abun sam babu dadi "Shiiiiiiii bance ki dameni da hauka ba just ki fita nace kuma karki qara kirana da danuwa kirani da sunan da kowa yake kirana dashi okay dan ni ba danuwanki bane ".
"Wai ma me yasa ka tsaneni baka sona haka ?,me na rasa ya adnan ?tayi masa tmbyr tana tsareshi da idanunta "amman daka soni da karka soni duk daya ne aurena ne dai babu fashi sai ka aureni kuma sai kayi rayuwar aure dani tamkar sauran ma'aurata "ai bazaki ta'ba samun wannan damar ba arayuwarki ,
oya dauki kudin nan kiyi out yayi maganar a tsawa bata san sanda ta wawiro hand bag dinta ta fito ta koma gefen titi ta tsaya tana kallonsa yaja motarsa ya qara gaba da mugun gudu.”
Hankalinta yayi kololuwar tashi da gatanta da komai arzikin ma da yake takama dashi byn mahaifinta ne silar samunsa da ba dan shi ba da yanzu killa ma bara suke yi akantiti gashi yace shi ba danuwanta bane , taji kamar ta kira mahaifinta ta fada masa wulakanci da yayi mata "amman kuma idan kika kira zaki lalata komai dan adnan ba mutunci garesa ba zai iya fadawa mahaifinki ido ido baya sonki alhalin shi bai san da wannan matsalar kinga kin kunnowa kanki huta gara ki share ki cigaba da hakuri da sannu komai zai daidaita tunda ammi tana son aurenki dashi ai ko baya só sai ya aureki dole ta numfasa kana ta soma kokarin tsaida mota wata mota “tsaya ta fada cikin harshen turanci mai mota ya tsaya, ta fada mata inda zata " babban gurin siyayya dake kusa da nan zaka kai ni ya gyada mata kai ta shiga mai motar yaja ".
*****
Da misalin karfe biyar daidai na yammacin rana acikin shopright dake ikeja tayi musu kowannensu sanye da kananan kaya idan kagansu zaka d’auka shopping zasuyi ,daya bayan d’aya suka raba kawunansu bangare dabam dabam cikin salon kawar da hankalin mutane akansu ,kamil né zaune akan keken guragu yayinda anas ke tsaye abayansa yana turasa sai dai bada siffar bara ba dan sam shigar jikinsu batayi kama da wadan da suka zo neman taimako ba ,kowanne daga cikinsu kunnensa manne da abun jiyo sautin maganar jaguwa, haka zalika sauran jubi da jabir suna saman gurin suna baza idanu suka ta inda indoor zai shigo domin har zuwa wannan lokacin da suka rigada suka shigo suka fara bincikensu babu wata alama daya shigo gurin .”
Ahankali jaguwa ke hawowa saman lift hannunsa rike da wani had’adden karfe wanda marasa idanu ke amfani dashi ,idanunshi rufe cikin bakin glass me shegen kyau da tsada jikinsa sanye cikin kayan dark army green sai dai riga ta kasance me hula ce yayinda wando ma ya kasance kalar rigar jikinsa sai dai daga kasan wandon a tsukakken yake , jikinsa na wani irin fitar da kamshi turare flower ross .”
a natse yake komai nashi hankalin wasu daga cikin mutane dake gurin ya raja’a akansa most especially mata domin yayi matukar yin kyau sai dai fahimtar da sukayi makaho né yasa fuskarsu ta sauya ta nuna alamun tausayawa garesa ,ya dan waiga kasa inda yaga shigowar wasu fararen mutane su biyu suna magana da juna kamar ya juya ya sauko sai yaga kamar mutanen dake kallonsa zasu fahimci wani ba dan haka ya cigaba da kallonsu yana motsa lip’s dinsa a hankali domin hankaltal da yaransa kamar ance ya dago kansa idanunsa suka sauka akan sanyin idaniyansa ,soyayyarsa ,haukansa ,rayuwarsa tanwer ce ke saukowa sanye cikin doguwar riga hannunta rike da farar leda suna hada ido gabanta yayi wata irin mummunar faduwa shima faduwar gaba yaji ta riskeshi kwayar idaunta ta tsaida akanshi wanda yasashi jin wani abu na ratsa jiki da zuciyarsa take yaji komai ya sauya masa wasu abubuwa suka shiga yawo ajikinsa suna zaga jinin jikinsa gabadaya .”
So yayi ya dauke idanunshi daga kallonta saboda yanzu ba lokacinta bane idan yace zai biye mata komai zai wargaje masa amman ya tsinci kansa da kasa aiwatar da haka ‘wani irin kallo me daga hankali take binsa dashi tsigar jikinta na mikewa, Kallonsa take tun daga kan fuskarsa da kafafunsa dake rufe har zuwa yatsun hannunsa dake rufe cikin bakar safa babu wani abu daya nuna shine mutumin da ko baiyi amfani da ainihin fuskarsa idan ta gansa zuciyarta na fahimtar shine .”
saitin zuciyarsa tabi da kallo wanda hakan ya tabbatar mata da shi din ne tsaye a gabanta zuciyarta ta cigaba da dukan tara tara wanda yasata gaugauwan dauke idanunta daga kallon juna da suke shi kuwa har lokacin ya kasa dauke idanunshi akanta yana kallonta har ta sauka ta barshi zuciyarsa na wani irin dokawa da sauri ya biyota yana tsaidaita a hankali cikin sanyayyar murya batare da yayi amfani da sunanta ba só yake ya gano wani abu ba tayi mamaki jin ya tsaidaita ba .”
Ta ta juyo a natse aiko idanunta suka tsarke cikin nashi yana tsaye abayanta still rike da sanda naunayen numfashi ya sauke ita kuwa ganin rauninsa yasa ta sake had’e rai sosai tamkar bata ta’ba yin dariya ba ,muryarsa a tsarke yace “kamar naso na sanki sai dai na manta inda na sanki yayi mata tmbyr yana shafa sumar kanshi “wannan ba wacce kasani bace ko akwai taimakon da zan iya maka ?”kankance idanunshi yayi ya saka cikin nata qirjinsa na wani irin luguden bugu “okay ina ganin kamace “. baiyi mamaki ba dan a irin shigar da yayi ba lallai ta ganeshi ba, ya soma qakarin kusantota da niyyar fitar daita daga gurin dan kar hargitse ya faru tana ciki hankalinsa zai rabu gida biyu amman yaga ta qara taku ta matsa baya ita anata tasan muddin shine mutumin da zuciyarta ke dokawa akanshi yana gama qarasowa ba qaramin aikinsa bane ya had’eta da faffadan qirjinsa sake motsota yayi da sauri ta dakatar dashi “malam ka tsaya a iyakarka karka sake ka karaso inda nake adnan ko ka dauka bazan ganeka bane .”ta fada a matukar firgice.
step daya ya qara yana cewa waye kuma haka ?ya tamabayeta cikin wata irin murya “maganar wasa ta wuce ni nasan kai ne , ko wani irin canzawa zakayi hakan bazai sa na kasa ganeka ba kai ne dai adnan ahmed já…”Shiru tayi sakamakon karfen hannunsa daya saki a kasa kuma san dan katse mata maganarta yasa yayi hakan ,”ai kece kawai kakisan wannan.” tana gama jin abinda ya fada ta juya fuuuuuu tana rausaya tamkar wata bishiya
Bashi da yabi bayanta da kallo ba mutane dayawa sun bi bayanta da kallo sakamakon tafiyarta me d’aukar hankali nan take yaji wani kishi me tsanani ya caki kahon zuciyarta soyaytarta ta shiga masa kuwa acikin zuciya .”ahankali ya shiga daga kafafunsa domin biyota alokacin indoor ya shigo tare da yaransa shima kamar jaguwa da yaransa haka suka raba kawunansu ai kuwa nan take hankalinsa ya rabu gida biyu “.ya waiga yabi indoor da kallo sannan ya waiga hanyar da tanwer tabi da kallo har lokacin tafiya take na daukar hankali wanda ke sake kunno wutar soyayyarta…”
Manage please 🙏
Mmm Sudai
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina