Showing 132001 words to 135000 words out of 259215 words

Chapter 45 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16530

rayuwa tanwer amman kiyi hakuri da sannu komai zai daidaita ,"sannan kiyi kokari ki rage damuwar nan duk da tasan komai dake faruwa daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
" ki kara imani da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne kawai dai Allah ya bamu Ikon cinye jarabawarmu rukayya ta fadi haka ne dan takaita maganar .
"nima ina son na rage tunanin Adnan acikin zuciyata amman na rasa dalili da tunaninsa kullum sai gaba yake , wallahi ina masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi ba sai ranar dana ji an shafa fatihan aurensa ta k'arasa maganar tana mai runtse idanunta."


"Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa "? tanweer ta gyada mata kai alamun "eh! "gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi .
Tanweer ta gyara zama tana kallonta "na fahimceki yar'uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki "to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace "na gode rukayya inshallahu zan daina .
." Ki kwantar da hankalinki kinji dan Allah karki sake daga hankalinki akansa Ki fara nemi zabin Allah kiyi k'okari kiyi istahara domin neman zabin Allah "rukayya ko ya min wani irin adduar istaharar da zanyi".?
"zan koya miki , mu nemi zabin Allah bamu sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku idan babu idan kinyi zaki ga komai ya tafi daidai amman Karki yarda ki bari wani yayi miki kiyi da kanki ,zaki iya yi kullum idan zaki kwanta raka biyu zaki yi sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki hatta wannan radadin da kike ji akanshi zaki rage jinsa ."
Jiki a sanyaye tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta amsa ta fara rubuta mata adduar "Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as'aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta'alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi."inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure "na gode rukayya inshallahu zanyi ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta'ba sanin zama da mutun guri d'aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k'okarin kawar mata da dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau ."
Da misalin karfe goma na dare kowa ya shige d'akinsa tanweer ta shiga bathroom dinta tayi alwala ta fito ta sanya dogon hijab dinta tare da shimfida sallaya tayi sallahrta raka biyu sannan ta gabatar da adduar istaharar da rukayya ta rubuta mata sannan ta nemi guri ta kwanta akan katifa zuciyarta cike da tunanin Adnan kala kala a hankali wani bacci mai ni'imal ya d'auketa ."


Dare ya raba bacci yaki zama cikin kwayar idanun jaguwa saboda zafi biyu sun had'e masa takura masa akan auren hasera da amminsa take so ga Kuma takaicin kin zubar da cikin da tanwer tayi uwa uba tsakin data had'a mashi dashi har yanzu abun nayi masa zafi a zuciya idan ya tuna kalamanta ya kanji kamar ya mutu wai shi ne zai haifi magajin fashi ?"
Idanunshi suka cika da hawaye amman ya danne .
haka ya wayi gari da rashin bacci shiyasa da gari ya waye yake ta jin kasala ajikinsa.
Shigowar Anas yasa ya dan ji dama ya dan mike ya zauna rigingine dan yasan dole zai dawo dashi daidai "mutumina ina fatan dai lafiya ba wata matsalar bace ?"
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke yace "matsaloli ne ba matsala Kawai ba, sai dai fatan samun sauki daga Allah .
"ammi ta matsa lallai sai an saka ranar aurena da haseera karshen watan nan da zara an gama bikin Shafik kenan ,ga matsalar yarinyar nan wai ni tanwer zata wa haka ina bata umarni tana wani butsarewa wai har da cewa bazata cire ciki ba zata haifa ko na kar'ba ko ta Kawo wa ammi," ni ba kaiwa ammi ne ma yafi damuna ba wai ta haifar min wanda zai gajeni a fashi ba sai nayi training yayan wasu ba ,wallahi wannan abu yayi min ciwo ko ance mata wannan sana'ar muna yinta ne dn dadin rai ?"
"Kana ji ko muyi magana ta fahimtar juna Allah kuma yasa ka saurarrni ,Jaguwa ya kara matsoshi sosai"me zai hana Anas ka fad'a komai zan saurara dan mafuta yake nema tun kafin komai ya kwabe masa ."


"Abinda kakewa yarinyar nan Sam bai da kyau , duk fa kai ka jawo abinda ta fad'a maka ba wai wulakanci tayi maka ba ,sai abu na gaba adnan Kana yiwa yarinyar nan wani so na dabam haka itama tana sonka sosai fiyye da komai irin son da zata iya rabuwa da Kowa nata dan ta rayu da kai hasalima soyayyar da take maka ne yasa ta kasa zubar da cikinka ba wai ina takura maka akan kana son yarinyar nan bane ,sai dai ina son ka sani har abada bazaka daina sonta ba , itama haka . zanyi farinciki idan ka sauke komai ka rungumeta ka aureta , nasan muddin iyayenka sukaje neman aurenta zata yarda ta zubar da cikin duk da shima zubar da cikin babban laifi ne .
Jaguwa ya numfasa tausayin kansa dana tanwer ya rufesa tabbas shima ya fara jin wani abu akanta a yanzu ma babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai hotunanta , yayi saurin ya bud'e idanunshi da suka kada "kayi hakuri wannan shawarar taka ba abar d'auka bace yanzu agurina kasan komai nawa Koda zanyi aure bazan Iya aurar mace sama da daya ba ," kaga Kenan bazan iya bin zabin Kowa ba sai na mahaifiyata dan haka maganar auren tanwer ma bata taso ba ka bani wata shawarar yadda zanyi ta cire cikin nan dan ko bata samu hanyar kaiwa mahaifiyata ba ta cuceni muddin ta bari dana Ko y'ata sukazo duniya ta wannan hanyar ."
"Komai fa muqaddari ne daga Allah amman ka sake lallabata ka gani may be zata yarda "babu irin abinda ban mata ba anas babu irin rarrashin da ban mata ba ingaya maka yarinyar nan taki d'an Karan taurin kai gareta ,anas yayi murmshi yace "zanice ta tarar da muje kai daita duk abu daya kenan " sun dade suna magana akan cikin tanweer a karshe ya tsaida shawarar zai nemota da kanshi ya kaita acire mata cikin ya huta da damuwar dake damun zuciyarsa."


******
Tunda yaran alhj Tahir suka Kawo masa labarin rashin nasarar da suka samu gurin kashe nazifi ya kasa samun sukuni, ranar a zaune ya kwana saboda tsananin tashin hankali addua yake Allah yasa ba hannun Jamin tsaro nazifi ya shiga ba .
haka ya raya daren batare daya runtsa ba haka washegari tsumayi yake yaji ta inda za'a aiko masa da sammaci amman shiru kake ji ,haka yayi kwana biyu adaddafe duk ya zube Kamar wanda yayi shekara yana ciwo baya Iya zuwa koina ganin har lokaci babu wani sammaci daga hukumar yansanda ya dan kwantar da hankalinsa .
Yau ta kama jumma'a alhj Tahir yaje massalacin sallar jumma'a kai tsaye daga massalacin gidansa ya nufo shi direbansa Sai dai kafin ya karaso get din gidansa wata mota marcende tasha gaban motarsa take direbansa ya tsaya cak cikin tsananin tashin hankali .
wasu mutane masu siffar karfi da bai san ko suwaye ba fuskokinsu rufe da bakin face mark sukai attacking dinsu. duniya juyi juyi yau shi akayi attack shi da yake turawa mutane fataken dare yau Shi aka turowa ,hankalinsa bai wani tashi ba a tunaninsa kudi sukazo nema sai dai yadda suka karaso tamkar zakuna suka hau bud'e kofar inda yake zaune a gidan baya suna cewa "fito muje shine yasa cikinsa ya turu ruwa "ya fito suje ina ?"yayiwa kanshi tmbyr a kasan ransa ,amman a zahiri cewa yayi "nasan kudi ne ya Kawo gani ga gidana can tafiyar mintuna kadan zai kai mu muje zan baku duk abinda kuke bukata ni dai ku barni da raina."


"ba kudi ya kawomu gurinka ba cewa akayi muzo da kai Idan kaki biyo mu mu d'auki ranka" nan take jikin alhj Tahir ya d'auki kyarma kmr mazari yana zare Ido gaba da gabanta kenan, bai tsaya bata musu lokaci ba ya fito yana gyara babban rigarsa suka tasa keyarsa gaba har gurin matarsu suka saka shi a gidan baya mutun biyu suka sakashi a tsakiyar suka bar gurin aguje.. suna barin gurin direbansa ya fito tare da daura hannuwansa duka saman kanshi yana kururuwa neman d'auki ya bi bayansu sai dai akin banza yayi dan babu wanda ya fito ,daman kuma haka unguwar take duk abinda zai samu mutun da wuya ataimaka masa kuwarka banza barinsa ma haka ."


*****


9:am daidai motar jaguwa ta karaso bakin get din asibitin tanwer , yayi parking nesa kad'an da asibiti yana zaune sai ga direbanta yazo da wata hadadiyar mota Kirar land cruiser jeep sai sheki take .
tun daga nesa ya tsura mata Ido fuskarta a had'e tamkar bata ta'ba murmushi ba sai dai yanayinta kamar zatayi kuka tayi masa kyau aini yaushe rabon ya sanyata akwayar idanunshi .
driver ya sa kai zuwa cikin hospital din shima ya biyo bayansu , direba bai tsaya akoina ba sai a daidai hanyar da zata Kaita office dinta yayi parking ya fito da sauri ya bud'e mata gidan baya .
A hankali ta yunkura ta fito tana jin wani faduwar gaba ......"
ta tsaya shiru tana bin haraban gurin da kallo kafin daga bisani ta soma d'aga kafafunta zuwa ciki yayinda driver ya Shiga motar ya tayar ya soma k'okarin barin gurin .


Tana tafiya tana sake jin faduwar gaba tare da jin motsin tafiya a bayanta ta tsaya cak ta juyo bayanta a natse wayam babu Kowa sai ita kad'ai sai mutanen Dake kai Kawo ta gabanta ta cigaba da tafiya adaidai bakin corridor da zai Kaita office dinta suka hadu da doctor muyis cike da fara'a ta tsaya suka gaisa yana k'okarin janta da magana ta wuce ganin fara'a a fuskarta yau yasa shi jin sanyi aranshi dan haka yabiyota abaya har ta karaso bakin kofar office dinta bata daina jin faduwar gaba ta tsaya tana k'okarin bud'e jakarta ta ciro key Dr muyis ya amshi jakar hannunta dan ta Samu damar bud'e kofar a tare suka Shiga ya maida kofar ya rufe batare da yasa key ba .
Ya ajiye Jakarta akan makeken table din dake office din ta zagaya ta zauna shima ya samu guri ya zauna suna fuskatar juna office din ya dauki shiru na minti goma sannan ya fara magana zuciyarsa na rawa dan fargaba. "jiya dr Safina bata fad'a miki sakona bane ?" sai da tayi jim sannan tace "sakon me Kenan ?tayi mgnr batare da ta d'ago ba. ya gyara zama yana sakar mata murmushin sai lokacin ta d'ago ta dubeshi suka had'a Ido
"ya'akayi Dr muyis ?"yace "babu komai Kawai so nake muyi hira "ta sauke numfashi tana cewa "Ai yanzu ba lokacin hira bane lokaci ne na aiki zai fi kyau ka kama gabanka kaje kayi aikin gabanka" ta maida Kanta ta sunkuyar tare da numfasawa.


"nasan kin fahimci wani abu akaina , ta sake d'ago ta dubansa tace "ban fahimci komai ba idan akwai wani abu ka sanar min ina da tarin ayyuka a gabana ya sauke numfashi yace "nasan kin fahimci yadda nake sonki Ko?"ta numfasa sai dai bata ce uffan ba "wallahi ina sonki tanweer kuma da aure ta runtse idanunta tausayinsa ya kamata tayi sauri ta bud'e idanunta a sanyaye take cewa" kayi hakuri kayi addua Allah ya sauya maka wata dan ni zuciyata tayi nisa a soyayyar waninka inshaallah nan kusa za'a shafa fatiha
"inshaallahu Ke rabona ce bata Wani ba ba kuma zan hakura ba har sai an shafa fatiha wanda nake fatan da ni ne "to wannan kuma yana ga Allah domin shi Ke shirya yadda yaso amman dai ina maka fatan samun wacce ta fini domin Ko da zan zamo mallakinka gangar jikina Kawai zaka rayu dashi amman zuciyata baza ka taba galaba akanta ba ".
Ya gyara zama yana kallonta "shikenan na fahimceki amman fa bana jin zan hakura dake ki bani dama mu dinga zantawa koda kuwa a office ne kafin nasamu matsayin zuwa gida .
ta kallesa sai ma ya bata dariya "kaje ka nemi mata tun kafin a fara kiranka da gwaro dan nasan shekarunka sun kai hamsi ta k'arasa maganar tana murmushi "ki bari na rasa wacce nake so tukun na sai na rufe ido na kwashi Ko wacece inyi maneji "no karkayi haka ai ita rayuwa .."
turo kofar office din akayi tare da shigowa ya katse mata maganarta aka maida kofar office din aka rufe garam cikin zafin nama da zafin zuciya .
a natse ta d'ago zuciyarta cike da mamaki rashin neman izini da ba'a yi ba kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya soke duka hannuwansa ciki aljihun wandonsa ta gaba ,ya balain kafeta da rikitattun idanunshi yana jifanta da mugun kallo ,
yayinda take zuciyarta ya soma bugun tara tara ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa ta sunkuyar da Kanta Kasa sannan ta cigaba da duba file din data fara aiki akansa sai dai gbdy komai nata ya tsaya dan batayi tsammanin ganinsa ba ji tayi kmr an zari wani abu ajikinta " me ya Kawo Shi gurinta ?" tayiwa Kanta tmbyr da babu mai bata amsa sai Shi .
Dr muyis ya juyo a hankali ganin Kowa ye ya shigo babu neman izini ,shima sai da gabansa yayi mugun bugu da karfi ganin ingarma nmj tsaye sai dai cikin kamala yake sanye cikin bakaken kaya har facing cap dinsa da takalmin kafafunsa da agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa , ya juyo a hankali ya dubi tanwer fuskarsa da alamar tmbya "dr muyis nayi bako ka dan bamu guri ".
"okay my tanwer zan dawo
zuwa anjima mukarasa mgnrmu ya mike tsaye tare da juyawa ya mikawa jaguwa hannu amman kememe yaki bashi hannu illa kallon hadarin kaji da yayi masa yana yatsina face, dr muyis yayi mamaki active dinsa zuciyarsa cike da damuwa ya d'aga kafadunsa ya bud'e kofa ya fita .
kusan minti biyar shi bai fita ba sannan shi bai karaso inda take ba, dan haka ta mike tsaye da zumar bar masa office din idan ya gaji yasan inda dare yayi masa ta gefensa tabi zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa daya ya dawo daita ya tsayar daita a gabansa batare daya ce mata komai ba ya tsura mata rikitattun Idanunshi masu bugar mata da zuciya ....."
wani yanayi mai tsarkakiya da wuyar fassarawa ya ziyarci gangar jikin duka masoyan guda biyu a bangaren tanwer tsantsar soyayyar da qaunar jaguwa ne yake bin dukkan ilahirin sansar jikinta ,ji take Kamar ta mutu ta huta akan wahalar da take sha akansa . "
Shim abinda yake ji Kenan a sansar jikinsa ji yake Kamar ya zarta dukkan maza sa'a a duniya data makance akanshi, sun shiga wata duniya wanda ma'abota so da shauki ne suka san zakinta a hankali yake Jin qaunarta na sake huda zuciyarsa yayi taku biyu ya had'eta da qirjinsa yana fidda wani wahalallen numfashi.."
saurin dauke numfashi tayi tana so shi kamr ranta ita Kanta tana mamakin zazzafan soyayyar da take ma jaguwa mai tafiyar da dukkan wani motsi da bugun zuciyarta da numfashinta .
yadda soyayya Ke walagigi da zuciyar tanwer haka ne yake faruwa da zuciyar jaguwa a sukwane ya motsa lips dinsa ",waye wancan mutumin daya tasaki gaba kamar zan ciyeki "? ya k'arasa maganar cikin zafin rai ."
Shiru ya biyo bayan tambayarsa dan bata jin zata iya bashi amsa idan tace lallai sai ta bud'e bakinta to kuka ne zai biyo baya ta juya a hankali zatabi ta gefensa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login