Showing 147001 words to 150000 words out of 259215 words
Chapter 50 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
jin wani irin yanayi gbdy tsigar jikinta sun tashi ,ji take kmr ta kasance dashi a haka muddin rai
"Ki cire tsoro duk tsanani ba'a gudun iyaye dan wani dalili domin duk duniya baki da tamkarsu ,kiyiwa iyayenki biyayya duk d'a na gari yana son ya rabu da iyayensa lafiya dan haka ki sawa ranki a gidanku zaki kwana,Kuma Ina baki hakuri saboda nasan ni ne nasadin da dad dinki ya d'auki zafi akanki Kuma duk abinda zasu ce karki kuskura kiyi wata magana wacce zata sake fusatasu."
d'ago idanunta da suke zubar da hawaye ta kallesa gani tayi kamr bashi yake mata wanda nan maganganun ba ,shiyasa a kullum take ganin shin din mutumin kirki ne qaddara ce ke yawo da rayuwarsa .
ya sauke mata numfashi a kunnenta sannan ya zare jikinsa a nata ya riko tsintsiyar hannunta ya nufi hanyar waje daita har inda motarsa take ya bud'e gidan gaba ta shiga mota suka bar gidan .
shiru motar babu wanda yayi magana Kowa da abinda yake sakawa Aransa har ya Kawo hospital ya sauketa ya kara gaba.
taje tabi hanyar daya bi kallo har sai data daina ganin motarsa sannan ta shiga motarta ta nufi gida Aikuwa ranar taga balain da bata ta'ba gani ba agurin iyayenta ,mumy Kam har da duka ta rufeta dashi byn ta sauke mata maruka biyu ajire , Shi kuwa dady sai faman cewa yake "yanzu haka zaki min tanweer ?
"ina alkwarin da kika min kafin ki bar gidan nan ? shikenan tanweer na gode ! na gode !!tunda da abinda zaki saka min Kenan yana gama fadar haka ya shige d'akinsa zuciyarsa kamar zata kama da wuta mumy ta bishi ,yayinda tanweer ta kwashi tsimar rayuwar tayi d'aki zuciyarta cike da gardin soyayyar da jaguwa .
Soyayyar daya d'and'ana mata shi ya hanata jin zafin duka da fadan da mumy tai mata ta zube akan katifa tana shafa kuncinta Inda momy ta sauke mata mari tana tuno abubuwan da jaguwa yayi mata a awannin da suka wuce m".
Tun dagan ranar tanwer bata sake haduwa da jaguwa ba haka zalika kota Kira baya d'aukar kiranta amman dai tana makale a ransa".
Tanweer tayi addua,tayi sadaka amman kullum ji take kmr qara mata maseefar qaunarsa ake hakan nan sai ta zauna tai ta kuka tana magana a fili "wa zai yaye min wannan damuwa ?"
" wa ye zai min wannna aikin da Adnan zai soni ya damu dani ?
A hankali zuciyarta ta bata amsa da "sai Allah ,Allah ne kawai zai miki ,ki sake dagewa da addua "Allah ka yaye min wannan damuwar Allah idan Adnan alkhairi ne a rayuwata Allah ka ta'ba zuciyarsa akaina , idan ba alkhairi bane allah ka cire min sonshi araina ,Allah ka mantar dani waye Adnan a rayuwata .."
*****
Kwance tashi ba wuya agurin Allah kullum bikin shafiq da gali na Kara matsowa har yau sauran kwana bakwai Sadiq ne yayi rabon IV duk Inda ya dace ya Kai jaguwa kuwa tun satin Biki ya ajiye komai da za'a ci a Sha , yanuwa da abokan arziki na nesa dana kusa duk sun hallara Kowa ka gani farinciki yake har jaguwa sai dai Idan ya tuna shima ana daf da saka nashi ranar da hasera hankalinsa sai ya tashi shrye shirye yayi nisa har yau friday akayi kamu amarya anan unguwarsu bakaramin kudi jaguwa ya kashe ba, anyi biki na yar gata domin a hall akayi , mata kuwa Kamar zasu cinyesa duk inda yayi idanunsa na kanshi .
bayan an gama biki hakan nan zuciyarsa ta umarcesa ya sake gwada haseera dan haka ya aika karamar kanwarsa halima ta kira masa ita hasera na tare dasu baraka da suka zo biki suna hira hally ta shigo tace "aunty hasera yaya Adnan na kiranki yana d'akin ya Sadiq ta fice abunta, haseera ta dubi baraka tace "Ina zuwa oga yayi kira ta figi mayafinta ta nufi dakin ta sameshi zaune da fuskarsa a d'aure sai da gabanta ya fadi muryarta a raunane tace "Ina wuni?" bai amsa ba illa idanunshi daya tsura mata yana qare mata kallo tsab "wai kana kirana gani ? ya mike yana cewa biyoni , jiki a sanyaye ta biyosa har gidin motarsa ya bud'e ya shiga yayi kasa da glass din motar shiru bai yi mgn ba Kuma bai wuce ba,dan hk ta fahimci shigowa yake son tayi .
ta bud'e ta shiga ta zauna yaja basu tsaya a koina Sai adiaraba daidai wani rubabben gida ginin kasa gbdy ginin babu cement da zallar kasa akayi , ya fito itama ta fito tana biye dashi suka shiga gidan suka tsaya a tsakar gidan , ya dubeta yace "kinga gidan nan "? Tace "na gani gidan waye"?
"Gidan da zakiyi rayuwar aure dani Kenan ."
Ta d'ago ta sake dubansa tace "me zamuyi da wannan gidan da matsayinka da komai ka zabi rayuwa a irin wannan muhali gsky ni dai bazan iya zama anan area ba ma bare wannan gidan ka canza tunani ya numfasa yace "haka ne diyar professor kmrki tafi karfi zama anan amman karki manta kece kike bukatar aurena bani ba dan haka muddin zaki rayu dani to anan zaki zauna, Idan kin amince a saka rana a karshen watan kmr yadda kuka bukata idan baki amince ba kije ki sanar da iyayenki a fasa ."
"Wallahi bazan zauna ba aure Kuma dole a daurashi babu fashi zan fad'awa mahaifina ya Siya mana gida a duk area da kake so amman nan wallahi bazan iya zama ba ai sai na mutu gbdy unguwar ma wari yake taya ma zan fara rayuwa anan idanunta sun rufe sai zuba maganganun take ya wuce ta ya shiga mota ta fito tana cika tana batsewa ta bud'e dayan bangaren ta shiga bata gama zama ba ya fige motar kamar sanda zasuzo babu Wanda yacewa danuwansa komai har suka karaso bakin kofar gidan ya tsaya batare daya fito ba sannan bai kashe motar ba tana fita ya ja motarsa da gudu ."
****
Da sassafe Ko abinci ɓata tsaya ci ba karfe bakwai daidai ta fice daga gidan babu wanda ya sani ta nufi gurin aiki ,dan zaman gidan ya isheita sai data gama ayyukanta karfe biyu ta soma Kiran layin jaguwa kmr koda yaushe bai d'auka ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa gidansa yana kwnace yana sharar bacci daga shi sai boxes , ta tashesa ta hanyar shafa qirjinsa ya d'ago ya kalleta sannan ya sake maida kansa ya dan juyo ya kalleta "me Kuma kikazo nema ya fad'a kmr bai ji dadin zuwanta ba ,nan kuwa jin zuciyarsa yayi fesss "kai me yasa idan na Kira wayarka baka d'auka ?" idan muna tare ka dinga nuna kmr duk duniya kafi sona akan kowa amman da zarar mun rabu shikenan baka da lokacina .
"me yasa zan d'auki wayarki?
"idan na d'auka nace miki me saboda Allah ?ta tsura masa Ido kamar zatayi kuka dan idanunta sun cika da kwalla muryarta na rawa tace "haba adnan laifi ne dan na kiraka Ko muryarka naji banganka ba zanji sanyi araina ,
yanzu dana zo naga lafiyarka shima haushi Kaji, me kake son dani ?" ni kaina banajin dadin wannan rayuwar da nake ,baka sona haka iyayena basa sona da kai zaku taru Ku kasheni ...."ta k'arasa maganar idanunta na cikowa da kwalla .
ya sauke numfashi yana kallonta ta goge kwallan shima ya tsura mata Ido"meye Kuma abun kuka ba wai ban damu dake bane duk abinda bazai yiwu agareni ba Kuma na Lura zai janyo min matsala arayuwata gudunsa nake tarayyarmu bazata Yiwu ba yanzu da bakinki kince iyanyenki basa sona amman ni ban damu su soni ba tunda bani da abinda zaa so agurina ki hakura Kawai ."
tanweer ta sake Shiga tashin hankali"To ni dai ina sonka kuma ka dinga d'aukar wayata dan shine dalilin zuwa na " yanzu Kawai dan ban d'auki wayarki ba Kawai kikazo ?"
"ba Kawai bane Adnan daidai da second daya idan ban ji muryarka ba zuciyata babu zaman lafiya yayi murmushi daga zuciyarsa yana tausaya mata sosai . "Allah Ko to shikenan zan tattara na dawo gidanku dan gara na dawo gbdy ki daina wahalar da kanki ta
kwanto jikinsa tana sakar masa tsadadden murmu shinta "kasan Allah da ka kyauta min shikenan kullum sai na dinga ganinka. "uhmm lalle kuruciya yana janki dayawa tanwer ,ya mike tsaye ya fita ya barta kan katifarsa kusan minti talatin sannan ya dawo hannunsa rike da farar Leda dake dauke da soyayyar kaza da Kwai had'e doya ya sata ta hada masa shayi suka ci tare taci sosai dan yunwa take ji.
ranar ma anan ta k'arasa yinta suna makale da juna Sai dai bai yi kuskuren yin romancing dinta ba bare ta kai su ga having sex , ita kuwa taso yayi mata abubuwan daya saba mata koda kuwa bazai kusanceta ba ."
A gida kuwa tunda suka Lura bata gidan hankalinsu yayi kololuwar tashi bakinciki Kamar ya kashesu har karfe goma na safe basu Karya ba ,dady ya shirya ya tafi hospital da kanshi da doctor muyis yaci Karo yake tambayarsa yace " tazo hospital amman bata jima ba ta wuce yayi jim yana tunaninta dan yasan tana gurin dan fashi , zuciyarsa sai rawa take ya fad'a yayansa zai sanar da hukuma amman yace ya dakata ,duk yadda doctor muyis Ke masa bayanin akan yana son tanwer da aure idan ya bashi dama zai turo ayi magana, Bata Shiga jikinsa i bai cigaba da sauraronsa ba yasa kai ya wuce inda motarsa take ya fad'a direbansa yaja suka d'auki hanyar komawa gida ."
Bangaren tanwer kuwa a hankali take jan jaguwa da hira da yadda take so shi "dan girman Allah ki kwantar da hankalinki
ki cireni aranki wannan aure namu ba mai yiwu bane Ko na amince iyanyenki bai Zama lallia su amince ba "me yasa kake min kora da hali ne da wannan hujjar ni Kawai ka canza sana'an zanyi confused dinsu ".
"ki daina fad'a min wannan maganar banza iya ba idan na canza wani sanar zanyi ?
" Zan nemomaka Sana'a "ki min shiru wannan ne Karo na karshe da zaki kwaso jiki kizo ta narke ajikinsa tana masa kukan shagwaba muryarta na rawa tace " dan Allah karka min haka mana ina tabbatar maka muddin baka bar wannan sanar ka aureni ba zan kashe kaina ya cire hannunta ajikinsa "ni ban aikeki ba ya dai kamata ki gane ba dole Sai na aureki ba kinga dan Allah daga yau Karki kara zuwa inda nake da fari na d'aukoki ne sabod wulakantani da kikayi,na biyu Kuma domin tabbatar da ciki da kikace kina da, kinga ina da kanne Mata bazanso suyi irin wannan rayuwar ba ,dole idan mun hadu sai na tabaki kinga haka ba daidai bane .
ta marairaice masa Kamar ranta xai fita "ni dai ina sonka Kuma zan cigaba da zuwa tunda kai baxaka zo ba ,ya had'e rai sosai Kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa "dan girman Allah ki kyaleni bana son surutu tashi muje na saukeki Karki manta Kar na sake ganin kafafunki ta cigaba da share hawaye ,wallahi Shi kansa yana son kasancewarsu tare amman bazai biyewa zuciyarsa ba Idan an ciza a dinga hutawa .
ya d'ago ya dubeta tana zubar da hawaye cike da tashin hankali yake kallonta yana jin zafin digarsu ",kayi hakuri dan Allah karka rabani da kai "yana jinta yayi mata banza ", please kayi hakuri dan Allah ta fad'a tare da rike tafin hannunsa wani irin zirrrrrr yaji a gbdy ilahirin jikinsa bai san lokacin daya ce "nayi hakuri amman ki Tashi muje na rakaki ki koma gida inshaallahu zanyi tunani akanki "zakazo gidanmu yace "eh zanzo ki share hawayenki ya fada dan ya raba kansa da matsalarta ."
da sauri ta hau share hawaye ta fad'a jikinsa gbdy ta rungumeshi very tayt "Na gode Sosai masoyi ajiyar zuciya ya sauke ya cire hannunwanta ajikinsa dan bazai juri jinta ajikinsa ba komai zai iya faruwa "muje Ko kafin ta sake cewa Wani abu ya fice daga d'akin dole ta biyosa .
ya bud'e mata gaban Mota ta Shige ya zagaya ya Shiga suka bar gidan sun yi tafiya me dan nisa har suka karasowa gurin shakatawa wanda ke had'e da cinima cike da farinciki tace ",dan Allah ka bari mu shiga gurin shakatawar nan".
"Muyi me ?"ya fad'a a taikace "Na dade banje gurin shakatawa ba Sau d'aya Kawai ka bari muje tare da kai bai ce uffan ba Kai tsaye Wani gurin shakarawa ya nufa daita suna zuwa mai gurin ya karaso ya taresa yana cewa "yallabai daman kayi aure ne baka sanar damu ba, Ai ya Kamata ka sanar damu muzo tayaka murna amman dai matarka tana da kyau sosai , "shiiii ...dan Allah kayi shiru haka mana,".
" ranki ya dade gsky kin shiga uku da dade jaguwa yayi saurin zaro masa Ido cikin tsanani tashin hankali yana d'aga masa yatsa ya sake bud'e baki zai mgn yace" haba duk waya tambayeka wannan surutun ?"
ita kuwa tanwer banda murmushin farinciki babu abinda take" yauwa ke bazaki gane ba kinyi saar miji ba, wallahi mutumin kirki ne muje na sammarmuku guri na musamman ,mutumin yayi gaba suka biyosa Abaya ta sakalo hannunta acikin na jaguwa shi kuma mutumin yana cewa "bazaki taba samun miji mai kirki kamrsa ba ,yauwa ga guri ku zauna atare suka zauna mutumin yaje ya Kawo musu abun sha ya tsiyaya mata a glass cup ya bata ta amsa tana masa godiya " na gode sosai .
gbdy ta kasa boye murnanta,dan taji dadin yadda mutumin ya yabesa ya tsura mata Ido Kawai yana kallonta batare daya ce uffan ba ,jikinta ya Bata ita yake kallo ta waigo inda yake zaune suka had'a Ido nan take ta hadiye rai tana jijiga kafarta d'aya "Ina ganin fa soyayyata ta fara fasa ruhinka ya bud'e baki zai mgn domin bata amsa kiran Anas ya shigo ya d'auka"kana ina ne ?
"Ina gurin shakarawa.
ita yarinyar fa a ina ka barta? "dan matsala muna tare daita " okay to shikenan "ba dai kaki samawar zuciyarka abinda take so ba wallahi zaka aikata kuskure akan kuskure.
Shiru jaguwa yayi yana ciza lips dinsa na kasa "Ko yaakayi yasan tanwer tazo gurinsa kai Anas akwai saka Ido "a ina ma kasan tazo "?"A camera naje bincika wasu abubuwane naga shigowarta ."
"Wai ya za'a da mutumin nan ne ya kamata ka ga gansa fa ?"okay gani nan zuwa yanzu ya mike yana katse wayar "Ke Tashi mu tafi na saukeki "haba mana ka bari zuwa anjima, lokaci na tafiya kinsan side dinku akwai nisa gashi banason na janyo miki damuwa agurin iyayenki ".
ya soma tafiya dole ta biyosa ,a daf da gidansu ya sauketa ya juya da mugun gudu .
ta wuce gida da sanda tana daf da shigewa d'akinta mumy tace "Ke dawo nan tsuru tsuru ta juyo cike da tsoro Kamar wata mummuna tayi kasa da Kanta "yanzu rayuwar da kika daukarwa kanki Kenan tanwer "?
"Babu kunya ba tsoron Allah kifita har kije gurin aiki sannan kisa kafa ki kama gabanki saboda kin rika daga gurin aikin Ina kika wuce ?
Naunayyen ajiyar zuciya ta sauke muryarta can kasa tace "gurin adnan ".
Ran mumy yay matukar baci dan ubanki ni zaki fadawa gurin adnan kikaje?"
" akanki aka fara sanin da nmj ?gaban tanwer yayi mummunar faduwa "Allah mumy ba abinda Kike tunani bane Babu komai a tsakaninmu Kawai muna yin hi ..."
Kiyi min shiru kafin na tsinka miki mari wallahi wannan shine karonki na farko Kuma na karshe da Zaki sake fita daga gidan nan kinji Ko bakiji ba ?
"Naji ta fad'a ataikace ta shige d'akinta mumy ta Samu guri ta zauna tana zama Kiran uncle bashir ya shigo ta d'auka suka gaisa ya tambayata labarin tanwer "tana nan a yadda kuka tafi kuka Barta abun yafi nada dan binsa take yanzu "dan Allah aunty ki kwantar da hankalinki kiyi addua zamu san abunyi Karki saka bakinciki aranki "Ai ya Zama dole bakinciki Kam ,kiyi Imani aunty bakinciki baya taba zama tarihi sai da Imani Allah dai ya banu Ikon cinye jarabawarmu .
ta numfasa hawaye na zubo mata tace "ameen Bashir "
"Kinsan Wani abu aunty ?
Tace a'a bashir Sai ka fad'a "ni da minister zai yarda da an aura masa ita sai mu zauna dashi yaron Muga ta inda zamu iya canza masa rayuwa ".
"Wani zunubi na aikata a rayuwata hka da zan ga wannan mugun Abu ?
"Bashir baki maganarka ba amman bazan Iya ba, rayuwarta zata qare cikin wahala ...."
ta k'arasa maganar tana zubar da hawaye cike da tashin hankali yace "kiyi hakuri mu cigaba da addua amman ina tabbatar miki yadda take ji a yanzu tafi qaunarsa akanmu Allah dai ya kyauta ta amsa da ameen suka cigaba da hira ."
****
Satin biyu kenan babu shiga ba fita gbdy ta fita haiyacinta saboda zuciyarta na cike da soyayyar jaguwa da kewarsa dan haka da yammaci ranar talata byn sallar laasar kafin karfe biyar gbdy ta manta da fadan da mumy da dady suke mata babu abinda take so face ganin jaguwa kewarsa ta gigita kwakwa
luwarta ta birkitata adduar istaharar da take ma ji take kmr ta barshi dan babu abinda take ji yana raguwa daga cikin son