Showing 120001 words to 123000 words out of 259215 words

Chapter 41 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16523

da Ido kawai jama'a suka dinga binsa .


Har karfe goma sha biyu saura na dare hjy Zainab bata ga shigowar minister ba zuciyarta cike da mamakin Inda ya tafi a daidai wannan lokacin dan rabon da yayi nisan kiwo irin haka har ta manta tun kafin a d'auke tanweer.
ta kira dukkanin layukansa basa shiga abu daya ake fad'a mata switch off gashi bazata iya runtsawa batare datasan halin da yake ciki ba.
tana cikin wannan halin sai ga wayarta ta soma ringing cike da tsinkewar zuciya ta Kai hannu kan bedside dinta Inda wayar take ajiye ta d'auka tana duba screen din wayar sunan minister ta gani yana yawo da sauri ta d'auka tare da Jan Koren madanni ta manna wayar a kunnenta tana furta "Assalamu alaikum". bai tsaya amsa mata sallamarta ba yace "ki shirya yanzu dolapo zaizo ya daukeki ya kawoki ST hospital". "Hospital Kuma"? "Lafiya ?
"waye bashi da Lafiya? ta furta a lokaci daya muryarta na rawa. "karki damu idan kinzo zakiga ko waye bashi da Lafiya "a'a dan Allah ka fad'a min wallahi gbdy ka d'aga min hankali gabana banda faduwa babu abinda yake a yanzu . "Kai Zainab matsalata dake kenan saurin d'aukar abu da zafi kiyi abinda nace dolapo zai zo ya daukeki. "banason irin haka fa kasan a yanzu komai na iya faruwa dani, ni dai ka fad'a min nasani tun kafin nazo "nima banason yadda kike d'aga min hankalinki ki karaso zaki ga komai yana gama fadar haka yayi disconnecting din Kiran hankalinta a matukar tashe ta mike ta soma shiri, tun kafin dolapo ya karaso har ta gama ta fito suka d'auki hanya cikin kankanin lokaci suka karaso hospital dolapo na gaba tana biye dashi Allah Allah take takaraso taga waye bashi da Lafiya.
dolapo bai tsaya a koina ba sai a bakin kofar d'akin da minister yayi masa kwatance yasa hannu ya kwankwasa kofar daga cikin d'akin aka bada umarmin shigowa ya tura kofar batare daya shiga ba sai hjy Zainab ce ta sa Kai ciki d'akin tana shiga dakin idanunta suka sauka akan tilon diyar kwance Kamar a mafarki kusan mutuwar tsaye tayi kafin daga bisani ta dafe bangon d'akin ta manne sosai tana murza idanunta da hannunwata duka " .


a hankali minister ya k'arasa Inda take ya rikota "dan Allah ka barni karka tasheni a mafarkina "cool down Zainab wannan ba mafarki kike yi ba it really gaske ne tanweer diyarmu ce kwance a gabanki tana jin abinda ya fad'a ta gyara tsayuwarta sosai ta tsaya bisa kafafunta tana maida hankalinta sosai akan tilon diyarta da sauri ta shiga daga kafafunta tana mai zubar da hawaye Wanda take Jin radadinsu har cikin ranta ta k'arasa Inda take kwance ta d'aura hannunta akan sumar kanta mai tsantsi ,ta dinga binta da Kallo "mai ya sameta na ganta haka ?sun cutar min da yarinya ko ?"sun lalata min rayuwar yarinyata ko? tayi masa tambayar ajere hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta "ki kwantar da hankalinki tukun nan ba'a dubata ba tana dai hutawa ne ".
"Allah kasa basu cutar min da yarinyata ba ta k'arasa maganar tana sheshekan kuka tare da tsurawa tanweer idanunta , qauna da tausayin diyarta suka lullu'beta gbdy ta kasa d'auke idanunta akanta ,yarinyata tayi kyau sosai tamkar ba daga hannun yan'ta'adda ta fito ba skin dinta sai wani sheki yake ."naunayen ajiyar zuciya hjy zainab ta sauke tana cewa"Kasan san Allah zuciyata rawa take sosai akan tanweer jikina na bani an ta'ba min yarinya. "ki kwantar da hankalinki sannan ki sawa ranki komai ya faru damu daga Allah ne mu ma godewa Allah da muka ganta a raye Kuma cikin koshin lfy ...."inshallahu ma babu wani abu nasan Kai din mutumin kirki ne da yarda Allah kamewarka da jin tsoron Allah'nka bazai sa wani abu ya samu tilon diyarmu ba tana gama fadar haka ta mike rike da wayarta tana kokarin neman layin hjy baseera "
da sauri Minister ya rike mata hannu "wazaki kira a daidai wannan lokacin"? " hjy baseera ta bashi amsa da haka "karki fara Kiran kowa tukun nan mubari musan matsayin da diyarmu take ciki, yanzu ma gida zamu wuce mu Barta har zuwa gobe idan Allah ya Kai mu sai dawo.
"Da wani kallo tabishi dashi sannan tace "kana tunanin zan iya barin tanweer ne a wannan halin "?idan ma naje gidan me zanyi "?ai zuciyoyinkmu bazasu samu natsuwa ba gara dai mu zauna tare daita ya sauke numfashi yace "haka ne ya fad'a a filin dan yana wa tanweer wani so da bai tabawa wani hallita a duniya ba .
Duk maganar da suke tanweer na jinsu dan tuni ta Farka tun shigowar mumy sai dai ta Kara runtse idanunta sosai dan karsu fahimci ta Farka tausayin iyayenta ya sake rufeta "kuyi hakuri iyayena komai muqaddari ne daga Allah Kuyi min addua kawai domin abinda kuke gudun faruwarsa tuni ya faru an raba tanweer dinku da budurcinta..


shiru tayi hawaye na gangarowa akan pillow da kanta yake kwance tana kukan zuci gefe guda Kuma bata ganin hotunan kowa face na Adnan dinta tana tsananin sonshi tasan ba Abu ne mai sauki ta daina tunaninsa ba.
a hankali hjy zainab ta dafa kanta wani zafi taji ya ratsa tafin hannunta ta bud'e baki kenan da niyyar yin magana sai sukaji an turo kofar d'akin an shigo wasu likitoci ne suka shigo d'akin sanye da kayansu na aiki sai dai puppy ne amadadin fari suna ganinsu suka dan ja baya domin basu damar suyi aikinsu .
Byn sun gaisa d'aya daga cikin likintan tace "Dan Allah ku dan je daga waje ta basu umarmin fita jiki a sanyaye suka fita .
Cikin kankanin lokaci likitan ta fara aikinta cikin iyawa da kwarewa har ta gano komai akan abinda minister yake bukatar sani, tana gamawa tayi rubuce rubuce a file din tanweer da'aka bude mata har za ta juya domin barin d'akin zuwa office dinta tanweer tayi saurin riko mata hannu tana cewa"doctor dan Allah karki fad'awa iyayena komai da kika gani .
"why "? doctor ta tambayeta shiru tan tayi kafin daga baya ta sake Bude baki da kyar "banason iyayena su shiga damuwa ne".
ba haka aikinmu yake ba dole zan sanar musu domin idan wani abu ya faru a gaba zasuyi kuka dani doctor na gama fadar ta fice dan oready dayar likitan ta fita ."


Minister na gani fitowar doctor ya biyo bayanta da sauri kusan atare suka shiga office dinta .
zaune yake a gaban doctor yana sauraren bayaninta daki daki a natse take sanar masa diyarsa ta san nmj ba kamar yadda yayi tunani ba . wani irin bugawa qirjinsa yayi da matsanacin karfi take gumi ya shiga tsatsafo masa ta koina ajikinsa "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun allumma ajirni Fi musibatihi waklifni khairan minha "an yiwa diyarsa fyade kenan "? inna lillahi ya sake furtawa, kenan ta wannan hanyar Allah zai yiwa ya'yan mutane sakayya ? Allah yayi iKonsa da qudirarsa bai san lokacin da hawaye ya shiga zubo masa ba abun yayi matukar taba zuciyarsa Kuma yaji zafin abun sosai "likita ta maida kanta ta cigaba da rubuce rubuce hanky ya ciro a gaban aljihunsa ya goge hawayensa "likita Ina son ayi mata wanki mara ".likita ta sake dagowa tana dubansa sannan ta lumshe masa Ido alamun taji.
ya mike ya dawo d'akin Inda ya iske hjy zainab ta tasa tanweer gaba tana dubanta cike da farinciki ita Kuma tan hannunta rike da cup din ruwan zafi tana kurban tea a hankali , kallo d'aya tanweer tayiwa mahaifinta ta fahimci an fad'a masa komai .
"Mai likita tace "?
bai boye mata komai ba ya fad'a mata har ma da abinda yace likita tayi ,a razane hjy zainab take kallonsa sannan ta juya ta surawa tanweer Ido "da gaske sunyi Miki fyade "? Tan tabi mahaifiyarta da Kallo domin rasa abinda zata ce mata.
Ganin tayi shiru kawai hjy zainab ta fashe da kuka .
Kuka take sosai tana tsinewa jaguwa Allah bazai barsu ba hakika ya zalinceni ko ta wacce hanya sai Allah ya Saka min sai yaga sakayya sai ..." tanweer tayi saurin matsowa kusa daita "no mumy stop "!
"Stop what "?
"Me kike nufi da stop "?
"Bana nufin komai mumy amman ki daina tsine musu ki barni naji da abinda nake ji a halin yanzu ,mumy wallahi nafiki shiga bakinciki abinda ya faru dani ta fada tana goge mata hawaye "ki daina kuka mumy na yarda da qaddara muyi Imani daita su Kuma idan masu shiryuwa ne Allah ya shiryesu idan bama su shiryuwa bane Allah ya tona musu asiri...." Bata gama magana ba mumy ta karbe "nifa wallahi bazan daina tsine musu ba har na koma ga Allah tan ta runtse idanunta"oh !Ni dai nace ki barsu ta fad'a tana d'aura kanta a kirjin mumy "mumy banason wankin marar nan Allah zafi garesa kice wa dady abarshi kawai .
"Ina bazai yiwu ba gara dai ayi idan ma da wani abu yayi gaba shi dai dady shiru yayi kawai yana kukan zuci ba shakka ba'a cin bashin Allah duk daren dadewa sai ya d'auki fansa bama mutuen kirki ba suka d'auki fansa yan fashi yan taada wannan abu da ciwo yake ciwon da bai san ranar da zai daina jinsa ba ."


"Mumy bari nayi sallah ko ? ta fad'a tana kokarin saukowa Ina ne bayin? Shi dai dady tsaye yayi yana kallon ta zuciyarsa na bugawa ta zura takalminta tana sake kallon dady "dan Allah dady kar min wankin mara da zafi sosai" ke dai kije kiyi alwala kiyi sallah Amman bazamu barki haka ba dole ayi tan tace "uhm dad tare da shigewa bayi .
Tayo alwala ta fito mumy ta shimfida mata dankwalinta tayi sallah suna zaune suna jira ita Kuma taki tashi dan bazata yarda a mata wakin mara ba zafi garesa tayi shiru akan sallaya tana zullumi gbdy a tsorace take ta marairace fuskarta "dan Allah dad mumy kuyi hakuri wallahi bawai banaso bane zafi garesa "karki tsorata ki bari ayi a gama komai shine kwanciyar hankalinmu kefa likitace kinsan illar abinda kike son yiwa rayuwarki". tayi yar murmushi yake wanda yafi kuka ciwo "shikenan zanyi da kaina. "yarinya jikinki zai gaya Miki gara ki bari ayi Miki allurar bacci ayi Miki cikin sauki inji cewar mumy taja kujera ta zauna tana nuna damuwarta .
tan ta kauda fuska "ni dai gsky zanyi da kaina dama mun wuce gida a yanzu tayi mgnr cike da shagwaba .
"iKon allah akwai aiki a gabansu inji cewar mumy "kinsan Allah baki Isa ba bazan d'auki wannan kasardar ba "to mumy amman Ina rokonki ki barni babu abinda zai faru nasan kan aikina bama lallai sai anyi wanki mara ba akwai table din da zan sha da zai maye gurbin wanki mara ganin ta nace sai da tayi da kanta suka hakura tunda sun san tasan aikinta dady ya zauna akan Baki gado ya d'aga kan tan ya d'aura akan cinyarsa yana shafa sumar kanta ."


*****
Wahegari tun da asuban fari fari nazifi yayi wa gidan alhj Tahir diran makiya Koda ya karaso ib na bacci hakan kuwa yayi masa daidai dan zai samu aiwatar da shirinsa, domin a Shirin da yake son yayi domin fitar dashi Ibrahim baya son kowa yasani daga shi sai mahaifiyarsa dan haka ya Kara masa da allurar bacci wanda zai d'auki lokaci yana aiki ajikinsa sannan ya d'ago ya Kalli hjy baseera "kin tabbatar kin sakawa dady maganin cikin abincinsa jiya ?"eh baccinsa ma yayi nauyi sosai dan ko d'aga yatsunsa baya iyawa ,"very good yanzu zan nade ib cikin kayan wanki domin wannan hanyar ce kad'ai zata mana saukin fitar dashi "duk yadda kayi daidai ne nazifi bani da ta cewa tana kallo ya d'aure ka'fafun ib ya curesa guri d'aya sannan ya nadesa yanzu abinda za'a yi ki kira masu aikin gidan su taimaka min na fita dashi. "
shiru umma tayi na second biyu kafin daga baya ta yi mgn "ince kace dani za'a yi tafiyar ?yace "eh dake zaa yi mana "kaga kenan nice yakamata na fidar dashi da hannuna idan ya kasance kana ciki zai zamo da matsala tunda nasan idan ya nememu ya rasa dole zai yi bincike sosai akai ".
"haka ne Kuma kin kawo shawara bari na fita sai mu had'u a airport "to shikenan na gode sosai .
nazifi ya bar gidan yayinda hjy baseera ta kira masu aikinta da taimakonsu ta fitar da gangar jikin Ib zuwa haraban gidan suka Saka a bayan motar hjy basera su kansu sunji nauyi matuka sai dai babu halin tambaya suka juya zuwa cikin gidan suna haki .
Hjy basera ta dawo ta Bawa kowacce aikin yi sannan ta shiga d'akinta bayan kmr minti goma ta fito lokacin duk suna kitchen tana k'okarin shiga mota direbanta ya taso da sauri ta dakatar dashi yayi mamaki matuka ya dai koma ya zauna a mazauninsa da kanta ta tuka motar bata tsaya akoina ba sai airport Inda suka hadu da nazifi cikin kankanin lokaci akayi komai aka gama jirginsu ya tashi ...."


D'aure jaguwa yake da dan karamin towel a kungunsa yayinda hannunsa ke rike da Daya yana tsane jikinsa a gaban mirror Wanda da gani wanka ya fito anas ne ya turo kofar d'akin ya shigo "yanzu wanka ne sama da awa biyu jaguwa "?
"ya son ranka bafa na son damuwa "? to Dan Allah kayi sauri tun dazu bakin can ke zaman jiranka aiki suka zo dashi mai nauyi "idan sun matsu su wuce idan Kuma zasu iya jira su jira. ya fad'a yana daukar body lotion ya fara shafawa ajikinsa "ai bazasuyi fushi ba suna can suna jira ka daiyi hakuri ka takaita kawai anas na tsaye har ya gama shirya Kansa ya fito zuwa inda bakinsa suke zaune zaman jiransa ya samu guri ya zauna anas ya juya cikin sauri ya fad'awa su jubi jaguwa ya fito babu yadda suka iya haka suka fito suna cika suna batsewa dan har lokacin basu daina Jin haushin abinda jaguwa yayi musu ba , shi Kuwa ko ajikinsa yayi watse dasu yaki bi ta kansu kowannensu ya samu guri ya zauna sannan bakin suka fara magana akan abinda ya kawosu har sanda suka dasa Aya "Kuna nufin Aysha oil and gas ?"sosai Mai gidan man yayanamu ne uwa daya Uba sai dai sam bama amfana da dukiyarsa daga shi sai matarsa da yayansa suke ci Kuma hasali wannan dan'uwana ne silar arzikina nasa "dakata ban tamabyeka duk wannan ba aiki dai kuke bukata Kuma za'a yi dae yarda Allah "to to shikenan Amman dan Allah kuyi yadda asiri bazai tono ba "shiiiiiii ku tashi ku kama gabanku .
jikinsu na rawa suka mike suka bar gidan daga nan su jaguwa suka cigaba da tautaunawa tare da tsara yadda komai zai tafi daidai wanda aranar suka shirya dasu jubi ,a ranar basu kwana a gidan ba a gidansa na oluwale suka kwana gbdy har da yaran aikinsa .
Wadhegari a hankali jaguwa yake saukowa akan matattakalar bene jikinsa sanye da bakaken kaya wondo da riga bayan rigar an rubuta jaguwa hannunwansa duka cikin aljihun wandonsa tun kafin ya k'araso kunnensa ke jiyo masa tautaunawar yaransa
"Ina da tabbacin har da tsananin tsoron allahnsa da kyautatawa mutane yasa muke samun nasara akoda yaushe "wannan haka ne duk da abinda muke yi ya sa'bawa shari'a Amman hanyar da kudaden suke bi na alkhairi ne "sosai kuwa " inji cewar anas.
"you all know there's no time when we can't do what we want suka fara sakar masa murmushi gbdy yaransa suka mike suna Sara masa ban da abokansa "safe da dare babu lokacin da bazamuyi abinda muke so ba kawai abu mafi mahimmam ku karkafa zuciyoyonku akan komai ,ko da yake ku din gwanaye mutane ne da sukayi gasar mutuwa meye bazasu iya ba ?"
gbdy suka gyada masa Kai suna murmushin Jin dadi "wannan haka yake Kuma babu gudun babu ja da baya Kuma duk abinda ka shirya dole ya tabbata tunda kana da maganin kwalaye " akwai mutane dayawa da suke son su zama fadera kamar ka Amman abun ya faskara sai dai sun tsaya a matsayin local government domin Kai kadai ne kawai zaka zama fadera ka zama state a karshe Kuma ka zama ceo the only armed robber's international plc you're the most supreme leader of us all ".
jaguwa duk runtse duk wuya Muna tare da Kai muna jinjina maka Kai kadai ne acikin garin Nan daka gagari kowa we hail you jaguwa inji cewar jabir ya fad'a yana Kai ta'ba wi bakinsa " muna sonka kmr yadda anas ke qaunarka dan Allah ka daina zarginmu da cin amanarka da hannu ya dakatar dasu gbdy yana gyada musu Kai .


A hankali ya fara tafiya a tsakiyarsu Yana dubansu daya bayan d'aya kafin daga bisani ya fara motsa labbansa a hankali " my name is Adnan amad jaguwa and iam of different body dimensions duk Wanda yace bazamu muyi bacci ba shine bazai ba, Wanda ya barmu da lafiyarmu shima zai zauna lafiya Wanda yace zai damemu to muma zamu damesa am jaguwa and iam ceasar as well so give unto jaguwa what's belong to him Yana gama fad'ar haka ya d'auki bindigar pesto su kuma sauran suka d'auki AK 47 ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa suka shiga mota suka bar gidan zuwa Aysha oil and gas dake cikin apapa."


Da misalin karfe Tara na safiyar ranar tanweer ta matsa lallai sai an sallameta tunda babu Inda ke mata ciwo akan hanyarsu ta koma gida ne "dad !
ta kira sunansa "yes my tan ya amsa yana dubanta "dady banason ka sheidawa kowa na dawo gida ka bar mutane a yadda suke dakon jiran dawowata "ko me yasa kika fadi haka ?"ina da dalili amman idan lokaci yayi da kanka zaka fahimci haka "har jaminan tsaro dake kokari binciko Inda kike kar a sheida musu "? "Eh !
"to shikenan anything for my baby bani da ja duk abinda kike so nima Ina sonshi ya k'arasa fad'ar haka yana cigaba da kallonta "kema mumy please "naji .."
suna karasowa gida minister ya gargadi dolapo da kar ya sheidawa kowa dan shi kad'ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login