Showing 162001 words to 165000 words out of 259215 words

Chapter 55 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16547

wani daga cikin jamian tsaron ya fada yana sake shiga rudani da shiga tashin hankali mara misaltuwa jiki a sanyaye suka juya suka fara tafiya kamar wadan da aka zarewa lakkan jiki suka koma cikin motacinsu’ har suka bar gurin mamaki abinda ya faru suke .”




Su jaguwa basu tsinci kansu akoina ba sai akan titin apo tsaye kamar yadda suke akan titin pape,
cike da matsanancin mamaki kowannensu yake kallon jaguwa ganin boyayyar bawar sirrinsa da babu wanda yasani acikinsu hatta babban aminisa anas bai san shi da wannan sirri ba kallonsa ya dinga yi kamar ranar ya fara ganinsa haka ma sauran “mu cigaba da tafiya ko “jaguwa yay mgnr kamar bai fahimci irin kallon mamakin da suke masa ba.
Kamar jira umarni eku yake ya sara masa kana ya cigaba da tafiya “na sara maka jaguwa na kuma na saraka maka,kai din dan baiwa ne ashe kasan abinda ka takata shiyasa kake ganin babu hukumar data isa taja da kai dan allah ka dan bamu sirrin “jubi ya fada yana sauke numfashi kamil yace “uhm yau dai mun tsalake rijiya da baya allah ka cigaba da karemu ai dole masu irin sanarmu mu kasance a shirye saboda ‘bacin rana irin wannna “.Ya karasa maganar yana dubansu “baiwa baiwa ne shi byn baiwa ma har da kwakwaluwa garesa na musamman mu dai dan allah ka shiryamu kamar yadda ka shirya kanka domin wannan aikin ya wuce aikin kwakwaluwa ko ba haka ba friends “? suka hada baki gurin cewa haka ne .
shi dai jaguwa bai ce uffan ba illa ciza lips disa da yayi da karfi dan bai san me zai ce musu ba ,
a ganinsa wannan sirrinsa ne ,bai so sun sani ba yanzu ma kamawa tayi suka ni dan ace gabansa bai fadi ba tabbass babu makawa zasu shiga hannun hukuma abinda bazai so faruwarsa ba kenan, daya shiga hannun hukuma araye gara gawarsa ta shiga ‘haka ma anas da mamakinsa ya zarta na kowa bai ce uhm ba bare uhm uhm kallonsa kawai yake .
da wannan tautaunawa suka karaso kabusa jection inda suka iske yansanda suna bincike “police again “?jubi ya furta cike da damuwa “kai kamil kayi karyar rashin lafiya kamar yadda aka saba” .
“okay an gama , take ya zube jikin jubi ya fara fidda numfashi sama sama yana rawar sanyi suna gama karasowa da hannu daya daga cikin police ya nuna musu gefen titi ,suka gangara sukai parking jaguwa yayi kasa da glass din motar “sunnuku da aiki !
“Sannuku daga ina kuke haka “?
“Daga kaduna muke mun d’auko mara lafiya ne zamu kai shi gida“ ya bashi amsa tare dan juyowa ya kalli anas dake numfarfashi da rawar sanyi .
police ya matso ya leka byn inda kamil yake ,daya byn daya ya karewa fuskokinsu kallo tsab yana duba hotun nan yan fashin da’a aka bashi gbdy babu fuskokinsu aciki kuma daman abinda yasa aka bazasu akan titi kenan ganin babu daya da yayi kama dasu yace “ku wuce allah ya bashi lfy “.
tun bai gama rufe baki ba eku ya figi mota ,kamil ya mike ya zauna yana sauke ajiyar zuciya “hotunan fuskokinmu da muka je gidan sani fefa ne a hannunsu da alamun ana bincike akanmu eku ya fada yana karya kwana “lallai haka ne kasan sky ya kira jaguwa a ranar da mukaje cewar police sunje gidan byn fitarmu .”
“aikin banza jaguwa ya furta alamun babu abinda suka isa suyi saboda yasan aikinsa shi mutun ne mai matukar baseera da amfani da kwakwaluwa komai nashi da aikinsa a tsare yake yinsu,fuskoki garesu bilaadadi duk wani sata da suke fita basa fita da fuskokinsu kowannensu da fuskar da yake amfani daita bare shi da fuskarsa ta musamman ce “.
Karfe daya daidai suka isa masaukinsu “.
Eku na gama yin parking suka firfito kamil yay mika sannan ya gyara zaman rigarsa da hannu jaguwa yayi musu umarnin su fito da ajirebi atare suka nufi boot din motar suka bude suka fito dashi ya hada uwar zufa numfashi ma da kyar yake fitarewa tsura masa ido sukayi “boss bazai yuwu mu shigar dashi haka ba zaa iya zarginmu eku ya fada ,dafe kai jaguwa yayi yana tunani can suka ga ya cire yar saman rigarsa ya cillo musu sannan ya nufi cikin hotel din.
Suka sakawa ajirebi suka jera da eku suka shige byn minti goma anas ya biyo bayansu daya byn daya suka dinga shiga har suka shige gbdy “.
A dakin jaguwa suka hadu gbdy kowannensu yayi cirko cirko suna jiran jaguwa ya kalli ajirebi dake durkushe kamar mai neman gafara yace “yau bakasan irin wahalar da muka sha ba kasancewar kana rakube a bayan boot amman duk da haka zakaji hakan ajikinka,abinda nake so da kai yanzu ka bari mu cima burimu cikin sauki mu rabu lafiya idan har kaki bari burimu ya cika akan galadima da garunmallam zan kasheka”.
ajirebi yayi narai narai da idanuwa cikin matsanancin tashin hankali,kallo daya zaka masa kasan baya cikin hankalinsa da natsuwarsa gbdy yanayinsa ya canza “yes haka nake nufi mu a lisafin daaka bamu mutun uku ne suka ci kudin amman tunda kai kace mutun biyar ne munji ,munyi aikin mutun uku kai kuma kana tare damu zakayi aikin mutun biyu daga yanzu ka fara tunanin yadda zaa yi su shigo hannun mu idan kuma kayi abinda suka gane akwai matsala suka shigo da hukuma ciki wallahi wallahi sai ka gwamaci mutuwa da abinda zai faru da kai , well ko ma hukuma tasani babu abinda zata iya dan munfi karfin hukuma yadda yake maganar hakan yake tabbatarwa ajirebi da haka ne har cikin zuciyarsa sun fi karfin hukuma kuma zai iya aikata masa komai muryarsa na rawa yace “karka samu damuwa bazan yarda su gane komai ba muddin dai zaku barni da raina da lafiyata why not ai muddin Kayi abinda kace shikenan zamu sake ka kayi tafiyarka .”
Jaguwa yayi shiru na wani lokacin haka ma dakin baka jin sautin komai sai na qarar ac dake aiki acikin dakin kafin daga bisa jaguwa ya sallamesu, kowannensu ya kama gabansa wasu suka nufi dakinsu domin yin wanka yayinda wasu suka fita zuwa club din hotel dan shakatawa ciki har da anas wani maaikin hotel din dake tsaye agurin ya karaso inda yake yana cewa “yallabai me zaa kawo maka ?anas na jinsa amman yayi masa shiru yaki motsa jikinsa bare bakinsa ya daura kafarsa daya akan daya yana girgizawa yana unanin rayuwa , tausayin kansu yake ji sosai, yana ganin lokaci yayi daya kama ta su bar wannan aikin domin shi dai ya fara gajiya sai dai bazai fita ya bar jaguwa ba ,yana jin idan ya barshi zai iya rasa ransa acikin aikin ne shi kuwa muddin babu shi tabbas shima mutuwa zai yi ,ganin shiru yaki yin magana maaikacin ya wucesa yaje ya kawo masa kwalbar giya mai sanyi kamar na jiya ya ajiye masa akan table din dake gabansa.
sai lokacin ya dago ya kallesa ya kalli kwalbar giyar dake gabansa haka nan yaji yau bai raayin shanta abinda jaguwa yayita fama ya rabashi yaki kenan “dauke wannan abar agabana ka kawo min soft drink “okay sir ya dauka da sauri ya juya ,ya runtse idanunshi sam yau baya jin dadin jikinsa wani irin sarawa kanshi ke masa kamar ana buga masa guduma bai sani ba ko yanayin da suka tsinci kansu ne yasashi jin matsanancin ciwon kai ba ,yana nan zaune maaikacin ya dawo ya sake ajiya masa ferless energy drink jiki a sanyaye ya dauka ya bude ya tsiyaya acikin glass cup ya kai bakinsa yana aiyana yadda zaiyi comfuse din jaguwa dan dole su ajiye aikin nan shi dai yana komawa lagos zai je ga ammi ta nemo masa matar da zai aura daman bashi da wacce zai aura kawai dai ya fadawa jaguwa yana daita ne dan shima ya maida hankali ya tsaida matar aure,aure ne kawai abu na farko da zai fara canza musu rayuwa ko kowa bai amince da barin wannan sanar ba lallai shi da jaguwa zasu bari nan kusa….”

byn kamar minti talatin sky ya karaso cike da girmanawa ya rusuna ya gaishe da jaguwa “boss barka da dare ,barka ya kake sky ?
“Lafiya lau boss ya amsa yana shafa sumar kanshi “ boss ya komai dai na tafiya daidai ?
“you are the best sky kasan aikinka komai na tafiya daidai “na gode boss duk da taimakonka ne ya dan waiga gefen hagunsa nan yaga ajirebi durkushe rike da hannunsa sosai yayi mamakin ganin ajirebi dan a tunaninsa idan sun gama karban kudin hannunsa basu da abunyi dashi “boss wannan fa me zaa yi dashi ko bashi bane cikon mutun uku “?
“Shine cewa yayi akwai sauran mutun biyu bayanshi ,jaguwa ya fada yana dafa kafarsa kana ya mike tsaye yajashi sukayi hanyar waje batare daya kulle kofar ba yana cewa “yaakayi sky akwai magana ne ?”
“Normal boss sai dai ya kamata muyi sauri mu bar garin nan bincike yayi tsanani akanmu “karka damu bazasu iya komai ba domin kuwa basu da sheida akanmu sannan kai kasan bamuyi amfani da duk wani abu da zaa ganemu ba “.
“Haka ne boss ai kai din mai baseera ne a hankali suka cigaba da tautaunawa har suka karaso inda anas yake zaune cikin tsananin damuwa suka samu guri suka zauna suna dubansa yayinda ajirebi ya zabura ya mike tsaye yana tunanin yadda zai kubuta ya dauki wayarsa zai kira police “kasan inda kake ne ko kuwa kiransu kawai zakayi”? Kwakwaluwarsa ta jeho masa tmby “bakasan a ina kake ba bare ka kirasu ka fada musu wannan tunanin da yayi yasa yayi saurin ajiye wayarsa a inda suka ajiye ya koma mazauninsa ya takure.”


“Anas tunanin me kake yi haka har muka zauna bakasani ba?” yayi firgigib ya dawo haiyacinsa kana ya sauke ajiyar zuciya “rayuwa !
Ya bashi amsa da hakan yana runtse idanunshi “rayuwa ?!
Jaguwa ya tambayesa yana dubansa sky ya mike domin jin abinda anas ya fada yayi gaba kadan ya fito da kwalin sigari ya zari daya ya kuna ya kai bakinsa “
“Adnan ! ya kira sunansa bai amsa ya cigaba da kallonsa alamun yana sauraronsa “nagaji da wannan rayuwar me zai hana mu barta mu tuba domin samun rabauta da kuma hawa tudun tsira mu tuba jaguwa daga …..”saurin daga masa hannu jaguwa yayi “zamuyi maganar idan mun koma gida but for ka dawo daidai banason ganin wannan yanayin a fuskarka ka tashi kaje kayi wanka yana gama
fadar hk ya mike ya karasa inda sky yake yana ganinsa ya saki sigarin hannunsa yasa kafa ya murje suka cigaba da zantawa har kusan karfe biyun dare da zai wuce aka sake fitowa da ajirebi byn an rufe masa ido aka sake turasa a byn boot aka nufi area 1 dashi a bakin wani madaidacin gida yayi parking eku da sky suka fito suka shiga dashi ranar yaga tashin hankali ganin idanunshi sannan yayi kwana tashin hankali yadda yaga rana haka yaga dare dayasani sani kuwa yayi sa yafi sau babu adadi inda zaa sake dawo da tarihin rayuwarsa da babu kudin wanda zai ci .”
Washegari 1:dot a gidan tayiwa su jaguwa da abokansa kallo daya yayiwa ajirebi wanda ya fita haiyacinsa sannan yace”kamil ina wayarsa?”Kamil ya ciro ya mika masa “amsa ka kira daya daga cikinsu galadima ko garunmallam jikinsa na rawa ya amsa yayi dialing number galadima jubi ya amshi wayar yasa a hands free kira daya ya dauka “hello ajirebi wai kana ina ne jiya byn mun gama waya nayita kiranka baka dauka fatan dai Lfy”?
“Lafiya kana ina ne ?”
Shiru galadima yayi kafin daga baya yace akwai abinda zan maka ne ?”ya fada saboda yana yin dayaji muryarsa “uhm daman …..”
Kit galadima ya katse kiran jaguwa ya fusata “haka ake magana da mutun ?ga dukkanin alamun ba haka suka saba magana ba allah yasa bai fahimci wani abu ba inji cewar anas jaguwa ya bugi table din dake dakin da karfi wanda yasa gbdy kayan dake kai suka hargitse har mutanen dake gurin most especially ajirebi dan tuni ya saki fitsarin wahala“wallahi ka kirasa kayi masa magana yadda ya dace muci nasara if not zaka bakunci lahira yanzu “kayi hakuri dan allah karka kasheni zanyi mgn da kyau banyi wani abu da zai gane cewar akwai damuwa ba,zaka san baka yi wani abu da zai gane ba oya sake kiransa inda yake kawai muke bukata” jikinsa na rawa ya sake kiran layin tare da sakata a hands free cikin saa galadima ya d’auka wani naunayen numfashi jaguwa ya sauke “sorry muna magna naji motsin shigowa shine na katse naje na duba kasan dole yanzu mu dinga be careful saboda wadan nan yan iskan mutanen ,“haka ne ajirebi ya fada yana sake danne tashin hankalin da yake ciki .
“Kana ina ne yanzu ina son nazo na sameka dan gbdy a tsorace nake “wata mahaukaciyar dariya kwashe dashi “tun bakaje hannu ba ka fara tsorata ai ka manta da inda nake kawai dan bazan fada maka inda nake ba kai dai ka fada min kana ina nazo” naunayen ajiyar zuciya ajirebi ya sauke domin rasa abinda zai ce .

jaguwa ya amshi wayar ya katse yana kiran sunan sky “kayi mana tracking inda yake nan da nan sky ya amshi number ya fara aikinsa dayafi kwarewa akai cikin kankanin lokaci ya gane inda yake ya dago a tsanake ya dubi jaguwa “boss yana ma kusa da nan yana area 11 ,good fito da hotonsa ajirebi ya fito dashi ya nuna musu suka amshi wayarsa suka dauke hoton galadima da wayarsa dan wayar ajirebi iPhone ce mai face id bazai yiwu su tafi da wayar ba dole sai da fuskarsa zata bude .
Location din unguwar da trancking ya basu suka bi tafe tafe har kusa isa kofar gidan get din gidan a kulle alamun babu kowa ciki
“anya kuwa gidan ne “? tabbas gidan ya nuna min ,wannan gidan babu alamun akwai mutun hasali ma garkeme yake “.
“Bari na sake dubawa ya maida idanunshi akan system byn minti biyar ya dago kansa “allah boss gidan duba kagani jaguwa ya kalla,tabbas gidan ne ya fito daga cikin motar ya jingina jikinsa da mota tare da crossing leg’s dinsa yana duban gidan a tsanake kafin a hankali ya fara shawagi agurin har kusan awa biyu babu wani wanda ya fito daga cikin gidan ko wanda zai shiga ya tsaya cak yana jan tsaki sannna ya bude gaban mota ya shga ya zauna yayi baya da kujera “yanzu boss ya zaa yi “?
“I dont know ya fada yana runtse ritattatun idanunshi wani duhu ne ya tsarke qirjinsa zuciyarsa na sake bushewa yanzu da bai tsaya ya amsarwa yaran nan dukiyarsu ba da a karshe sai sun yi bara a bakin titi, kai mutane babu imani aransu an kashe musu mahaifi baku barsu sunji da wannan radadin ba kuka dannewa yara dukiyarsu wannan wace irin rayuwa ce fi sabilila?”
Har kusan karfe duhu suna gurin jaguwa na zaune acikin mota kamar gunki takun tafiya suka ji ta glass din motar ya hango wani matashi bai tsaya akoina ba sai kofar wannan gidan ya ciro makulli daga cikin aljihunsa ya bude get mai layi layi dan daga waje zaka iya hango haraban gidan ya shiga ya maida kofar ya kulle ya bi hanyar baya “me ka fahimta anan “?
Sky ya danyi shru na second biyu yana nazari sannan yace”da alamun akwai mutun aciki gidan baddda kama akayi ta hanyar kawar da hankalin mutane shiyasa idan zaa fita sai a kulle ta baya hakan bazai sa mutane su fahimci akwai mutun aciki ba.”
Yana rufe bakinsa mai gadi ya fito ya zauna akan karamin banci ya ciro wayaraa yana dubawa,cike da jarumta suka fito gurin mai gadi suka nufa jaguwa ya mikawa mai gadi hannu shma ya mika masa suka gaisa “dan allah ko galadima na ciki ?kai tsaye suka tambayesa domin ya tabbatar da sun San shi.
“su waye ku?ya tambayesu shima,“abokinsa sani fafe ne?mai gadi yayi shiru yana tunani can yace “ ku kirasa tukun dan bai fada min zaa zo nemansa ba “kenan yana ciki?kwarai kuwa yana ciki amman bazan bari ku shiga ba sai da izininsa dan haka kirasa zai kirani sai na bude muku mai gadi ya fada yana kokarin komawa mazauninsa wani kallo ka kama kanka sky yayi masa sannan ya daga rigarsa sama kadan bindiga idanun mai gadi yaci karo dashi ya zaro ido waje ya durkushe kasa bisa gwiwowinsa “kuyi hakuri ai ban san ku bane ,kun ga ba sai kun kirasa ba kuzo ku shige kawai allah ya baku saa cikin rawar jiki ya bude musu suka shigo “can zaku bi akwai kofa da zata kaiku inda yake suna gama jin bayanisa suka amshe wayarsa sannan suka turasa cikin karamin dakinsa suka rufe sannan suka nufi hanyar daya nuna musu a hankali suka iso bakin wani iron door sukai knocking galadima dake zaune rike da jarida ya mike tsaye ya dawo bakin window ya tsaya ya yaye labule kadan ya leka yaga mutun biyu a bakin kofar bai san kamaninsu ba hasalima ranar ya fara ganinsu dan haka yaki budewa ya soma kira police .
“zaka bude mana kofa cikin girma ne ko zaka bata mana lokaci ne? Yana Jin’s yaki budewa gashi number police yana kira sunki dauka nan ya fara neman layin Alhaji sani cikin saa ya dauaka “dan allah ahj sani ka taimakeni ka kiramin police gasu nan sunzo gurina ….”
“idan ka bari muka balla kofar muka shigo zamu fanshe wahalarmu “.cikin galadima ya duri ruwa sai dai yaki budewa, suka yi amfani da kwarewarsu suka balla kofar suka gansa yayi mutuwar tsaye ya tsaya yana kallonsu saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login