Showing 165001 words to 168000 words out of 259215 words

Chapter 56 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16570

tsananin tsoro da kyar yake fitar da numfashi suka
shiga suka rufesa da duka
Sai daya daku sosai sannan suka nuna masa bindiga “Ina kudin marayu ?!
Tambayar da jaguwa yayi masa kenan babu musu ya fada musu inda suke “suna ckin motata a kasan motata na jerasu.
“wai ku masu wayo ba wannan kudi bazaku cisu ba ko sun cuyu sai na tabbatar da an dawo dasu hakane boss yanzu motar tana ina“?
Tana byn gida suka tasa keyarsa da bindiga sukayo waje “kar yaku ta kare sauran wacan dan iska shegu azzalamai kawai gbdy zuciyar galadima cike take da tsoro har suka isa inda motarsa take jikisa na rawa ya bude motar ya dinga zaro dalolin kudi suna tsaye aka shi har ya fito dasu duka basu barshi haka ba suka tasa keyarsa suka wuce dashi suka hadashi da ajirebi suka dauresu sannan suka kama gabansu suka barsu da sky da eku ”.


******


Da misalin karfe goma shadaya na daren ranar yana Kwance akan makeken gadon hotel din da suke ,
murdadden jikinsa sanye da fararen kayan bacci wondo da riga ya lullube rabin jikinsa da abun rufa yayinda jikinsa ke fitar da sihirtaccen kamshin tsadadden turarensa flower power wanda yayi order daga amercan turaren nada sanyi kamshi da kama jiki yana matukar qaunar turaren .
tunda ya shigo garin abuja bai zauna ya huta ba bare ya samu damar runtsa idanunshi domin bacci ko ya samu damar kiran tanwer sai yau daya san yana daf da kammala aikin daya kawosa amman duk da haka bai yi tunanin kiranta ba amman zuciyarsa na makale da tunaninta ,ya dai kira amminsa kafin ya kwanta yaji muryarta da lafiyar yanuwansa .
ya runtse idanunshi fuskarta ta shiga yi masa gezo acikin kwakwaluwarsa cike da murmushi tare da shigewa jikinsa tana kissing din nipples dinsa saurin bude idanunshi yayi acikin haske da bai gama haskaka dakin ba.
Ahankali ya motsa lips dinsa “tanwer! ya furta sunanta yana jin wani irin sauyi a sansar jikinsa “kinyi nasarar fixgo zuciyata da soyayyarki why tan? yayi tmbyr Kmr tana jikinsa ya gyara kwanciyarsa ya lalubo pillow ya makale a qirjinsa yana sake jinta atare dashi nan take jikinsa ya fara kadawa ya lula duniyar tunaninta ai kafin kace me jijiyarsa ta mike sambal ,da sauri ya dawo haiyacinsa “dan allah tanwer kiyi hakuri ki barni ki bar zuciyata ta huta haka duk da ina tsananin bukatarka ,zuciyata na cike da yunwarki ina tsananin bukatarki amman da wahala na mallakeki rayuwata bata dace dake ba,idan na aureki na cutar dake zan sake kuskurene akan *KUSKUREN BAYA*ki ya fe min budurcinki dana amsa ire iren sambatun daya dinga yi kenan yana jin kmr tana jiinsa .
Kasa runtsawa yayi sai faman juyi yake ,jijiyarsa ta dinga harbawa da sauri sauri alamun tana bukatar abincinta ya kai hannuwansa duka ya dafeta yana rarrashinta amman sai turjewa take ita dai lallai sai taci abincinta “wayyo allah wai meye haka ne?ya tambayeta yana mikewa zaune ya kunna wutan dakin yana tunhumar kansa gashi yanzu ya ballowa kansa ruwa.”
ya zuba ma jijiyarsa ido kawai yana kallon yadda take sake mikewa ,ya hadiye wani busashen miyo daya tsaya masa a makoshi”haba mana kayi hakuri nasan kana bukatar tanwe amman ka taimakeni kayi hakuri karki .
“Tanwer karki haukatani da wasa na sako tunaninta am sorry am sorry laifi na ne bari nayi wanka ya dan ji dama ya fad’a cikin mawuyacin hali dan gbdy jikinsa da muryarsa sun canza da matsanancin shaawa da soyayya abun ya hade masa biyu yana gama magana ya fara conrol din kansa yana kawar da tunaninta amman abun ya gagara dan ji yayi ta sake dawo masa ya zabura ya sauko” I love you more then my life but please live my side haba wannan wani irin naci né ya soma zariya a dakin hannunsa na cikin wondnsa yana shafa jijiyarsa dan ta kwanta amman taki kawai yaji hawaye ya cika idanunshi “nace kiyi hakuri yana gama fadar haka da sauri ya fada bathroom ya sakarwa jikinsa ruwa ya dade ruwa na sauka ajikinsa sannna ya fito ya daura towel ya kwanta ya cigaba da juyi sai goshin asuba bacci barawo ya sacesa batare daya sani ba da kyar ya tashi yayi sallah yana idarwa ya koma kwanta wani bacci mai nauyi ya daukesa.”
Satinsu jaguwa daya a Abuja still bai kira tanweer ba har sai da yayi kwana goma sannan ya kirata da misalin karfe daya na dare tana ganin kiransa ta d'auka da sauri muryarta a hankali tace"hello Adnan dina…”
Wani irin zirrrrrr yaji a gbdy ilahirin jikinsa Kmr an jona masa lantarki shaawarta dake dawainiya dashi acikin kwanakin.
cikin sanyayyiyar muryarsa mai tsananin kashe jiki da tsuma zuciyar wanda akayi domin sa
ya amsa da "na'am me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba ?” dadin jin muryarsa yasa kawai ta fashe masa da kuka , a hankali ya runtse idanunshi baya jin kukanta yana daga masa hankali .
Ya dinga sauraron sautin kukanta qirjinsa na bugawa da karfin gaske"tunaninka ya hanani sukuni da walwalar yin bacci , kullum kana raina ina maka addua Allah ya tsare min Kai har azumi nayi da nafilfili amman Kai ko ajikinka zaka iya komai batare dani ba "
ta k'arasa maganar tana fashe masa da kukan shawagaba ".
wannan kukan Jin dadin muryarta ne ko ?" ta cigaba da kukanta bata bashi ba amsa “zuciyata bazata iya saurar kukanki ba a halin yanzu da take cikin damuwa bari na kashe wayar gbdy idan kin daina kuka zan kiraki kafin tayi wani yunkuri tuni ya katse kiran gbdy daman dan yaji lafiyarta ne ya gani ko idan yaji muryarta zai rage jin yanayin da yake ji akanta.
ta sake fashewa da wani sabon kuka "oh Allah Adnan allah yasa karka kasheni ,ta fada ta na goge hawayenta kana ta soma bi layin amman shiru bai shiga ba a qalla ta kusan minti talatin tana neman layinsa bai shiga ba switch off ake ce mata babu yadda ta iya ta hakura ta kwanta sai dai tuaninsa ya hanata runtsawa.




Jaguwa yay shiru a tsakiyar yaransa yana lissafa yadda garunmallam zai shigo hannunsu
Sosai sukai busy acikin satin ko ammi bai sake wayar daita ba,a halin yanzu sun shirya yadda zasu kamashi tuni sky yana unguwr da garunmallam yake da zama cikin shirin hauka domin samo musu bayani .
alokacin dasu jaguwa suke rike da galadima da ajirebi suna harin garunmallam a wannan lokacin headquarters na yansanda jihar sun haukace domin neman hanyar da zaa ka masu musamman maaikatan dake bangaren computer cike da kwarewa suke aikinsu .
Sai dai duk iya bincikensu sunyi babu wata hanya da zasu iya kama jaguwa da yaransa ,daya daga cikin kwararrun masu sarrafa computer ya dago ya dubi mai gidansu “gsky sir wadan nan barayin kwararru ne sun san abinda suke yi abu na farko fuskokinsu gaba daya an duba babu shi acikin computer sadarwa haka zalika basu yi amfani da layi gurin neman alhj sani fefa ba kai tsaye suka doshi gidansa haka alhj usman gashi yanzu abincikenmu garunmallam ne next target dinsu tunda Alhaji sani ya kira cewar sun rutsa amininsa galadima har yanzu baa san inda yake ba tun byn daya kirasa yana neman dauki an kira layinsa a kashe,abinda zan iya cewa a yanzu a dakatar da bincike akansu sai mun shirya sir.”
“bangane sai mun shirya ba?”
cp ya fada yana goge gumin daya tsatsafo masa “sir mutanen nan suna da matukar wayo gashi da alamun akwai sihiri ajikinsu matocin police uku ne suka bibeyesu har suka cimmasu a satin da suka wuce da ajirebi sai dai abun mamaki a gabansu motar ta bace kaga dole nace kamasu sai an shirya .
cp ya sake sharce gumi dake faman tsatsofo masa kana yayi shiru yana nazarin maganarsa sauran ma’aikatan dake tsaye agurin gaba daya shiru sukayi domin rasa madafar dafawa shi yanzu cp yafi tunanin akwai abinda mutanen biyar din nan sukayiwa yan fashin da har suke bibiyarsu tunda dai basu kadai bane a garin abuja “aminai biyar kuma duk an bibiyesu banda mutun daya wanda shima yana karkashin kulawarmu?”meye hadinsu dasu lallai akwai lauje cikin nadi akwai wata a kasa kuma babu wadan da zasu bamu wannan amsar sai mutane nan biyar “. yana gama fadar haka ya juya da sauri ya fita a office din zuwa office na mussaman wanda aka killace garunmallam yaja kujera ya zauna ya fuskancesa “me kuka shuka atsakaninku “?ku biyar din nan akwai abinda kukayi ina son sanin meye shi idan kuma bazaka fada min ba yanzu yanzu ka tashi ka a maidaka gidansa……”


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




Mmn sudais






💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


🅿️31




………Tsura masa ido garunmallam yayi gabansa na wani irin faduwa da matsanancin karfi, gbdy kana kallonsa zaka fahimci tsoro ya rigada ya gama huda zuciyarsa da sansar jikinsa ,zaune kawai yake agurin amman ya dawo tamkar mutun mutumi sbd tsananin tsoro da fargaba ,zufa ce ta dinga karyowa garunmallam a gbdy ilahirin jikinsa “lallai idan basu yi taka tsantsan ba abinda suka shuka zai fito fili ,a hankali ya runtse idanunshi domin rasa me zai fadawa cp, shi da abokansa sun sha aikata laifika kala dambam dabam amman a yanzu laifin da ya tsargu acikin azuciyarsa shine wanda sukayi last akan honorable abdulaziz mutumin daya yarda dasu ya kuma aminta dasu, inda duk mutanen duniya zasu taru akansa su fada masa cewar zasu iya cin amanarsa ,zasu iya yausararsa ba zai yarda ba ,sai gashi sun hada kai su biyar sunci amanarsa sannan suka yi sanadin talauta iyalinsa byn sun yi sanadin mutuwarsa .”
Sune suka dasa masa mummunar ciwo a zuciya na tsawon lokaci akarshe suka hada karfi da karfi suka kirasa zuwa abuja batare dasanin kowa ba suka kashesa har lahira sannan suka yi védio gawarsa suka turawa iyalinsa da wata number dabam domin su fidda rai dashi ”.


“Uhm kai fa nake sauroro idan baka tashi magana ba na mike na kama gabana kai kuma nasa a maidaka gida kamar yadda na fada maka tun farko dan ina da abunyi”. yana karasa maganar ya dauki wayarsa ya kira matai makinsa da wasu daga cikin jami’an tsaro dan kar yaji mgnr shi kadai ,naunayen ajiyar zuciya garunmallam ya sauke yayinda zuciyarsa ke sake bugawa da karfin gaske kamar zata fasa qirjinsa tayo waje sai dai duk runtsi duk wuya yaci alwashin bazai fada masa sune suka kashe honorable Abdulaziz ba bama zai ji wani abu kamanciyar wannan maganar ba yasan yadda zai yi da bazasu fahimci komai ba shine fa .”

shigowar mataimakinsa da yaransa office din yay daidai da sauke numfashin da garunmallam yayi sannan ya fara magana cikin tsanani tashin hankali “tabbas mu biyar din nan mun aikata babban laifi ga wani mutumin kirki wanda mun jima muna alqalla siyan filaye domin hakar dayen gwal .
Alhj Abdulaziz mutumin kirki ne wanda yasan ya kamata anan
abuja allah ya hadamu dashi adalilin kasuwamcin siyen filaye domin hakar danye gwal ,alhj Abdulaziz yana matukar qaunarmu
domin a farko tafiya shine mutumin daya soma bamu kudi domin mu juya saboda bamu da jari a hannunmu sannan duk sanda wani daga cikinmu yaga fili wanda zai amfana yana kiransa ya sheida masa ya rike mu tamkar aminansa duk wata damuwarsa mun sani komai zai yi damu yake shawara amman mu har cikin zuciyarmu ba qaunarsa muke fi sabililahi ba dukiyarsa gbdy muke son ta dawo hannumu mu hamdame .
Kirkiraran business muka qulla da alhji Abdulaziz na kimanin million dari uku domin siyan danye gwal kamar yadda aka saba ba dan akwai shi akasa ba sai dan kawai makudan kudadensa su shigo hannunmu mu danne ”.
Maitaimakin cp kacalla ali yayi shiru cikin rudewa sai dai bai yi Kuskuren furta komai ba haka ma sauran jamian tsaro dake gurin tsaye cike da girmanawa suna sauraronsa sannan abar daukar maganarsu na daukar maganarsa a sirrance.”
Cikin tashin hankali ya cigaba da magana” ranar litinin shida ga watan daya shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu muka kira Alhaji Abdulaziz cewar an samu filaye guda uku anan cikin garin abuja masu kyau an auna an tabbatar da gbdy gurin zinari ne , cike da farinciki bai tsaya ja inja damu ba kasancewar an saba da juna yace “nawa sukace kudinsa ,kai tsaye galadima yace masa million dari uku ne “shiru yayi kafin a sanyaye yace “ yanzu dai babu wadan nan kudade a hannuna asiyar kawai sai zuwa nan gaba zan adana kudina idan an samu wani sai na siya .
Muka bar maganar sai dai atsakaninmu bamu barta tunda daman da niyya mukayi hakan , atsakaninmu muka tautauna yadda zamu samu kansa ,Alhaji usman ne ya hadamu da wani malami yay mana aiki akansa ,dan hk byn angama komai akasa mutun daya yayi amfashi da maganin domin cima burinmu .”

da yammacin wata ranar laraba muka kirasa muka bashi umarnin lallai kawai ya nemo kudi ta kowani hali ko aro ne a siya filayen nan dan bama son a rasa filayen dan zaa amfana dashi ,madadin yace mana ya amince batare da mutsu ba amman sai muka ga sabanin haka yace” shi dai bai da kudi a hannunsa idan ma yace zai bazama nema gaskiya bai zai ma lallai ya samu ba a wannan lokacin daake bukace da a siya filayen adai hakura zuwa gaba a siya .
“Yanzu ka yarda mu rasa wannan business din ?galadima ya fada cikin fushi abu biyu takaicin maganin da mukayi bai yi aiki ba da kuma rasa kudaden da zamuyi. “tô ya zanyi galadima tunda babu kudi akasa kudadena duk suna waje gurin Jamaa ,dama zai kai zuwa karshen wata ne da zan iya cewa zaa samu fiyye da ha…….”
tun kafin ya gama maganar cike da zafin zuciya galadima ya katse kiran saboda takaicin rashin sa’a.
Washegari alhj Abdulaziz ya kiramu cewar ya samo aron wasu kudi ya hada dana hannunsa amman duk da hk bazasu kai adadin daake bukata ba kai tsaye muka tambayesa nawa ya samu yace “millions dari biyu aka samu , dan haka muna gama wayar nan zai fita ya tura mana “nace a’a ya barshi an samu wanda zai siya filayen wanda munyi haka ne dan mu daga masa hankali .


Cikin tsananin tashin hankali yace “Haba garunmallam ya zakuyi fushi dani ai duk abun bai kai haka ba ,zan san yadda zan samo cikon kudin daga yanzu zaku iya ganin alert dina hakan ce ta kasance cikin account din Alhaji sani fafe ya saka kudin tunda ya tura kudin gbdynmu mukai blooking dinsa tare da rufesa a duk wata kafar sadarwar da zai ganmu byn wani lokaci sai labarin mutuwarsa muka samu allah ya karbi rayuwarsa a sanadin baki cikinmu .
yaja numfashi ya fesar zuciyarsa na bugawa da matsanancin karfi da tsaro dan a zahiri ake iya gane hakan .”
cp na gama jin bayaninsa ya mike tsam yana nazarin abubuwan daya fada ya nufi kofar fita haka ma mataimakinsa da yaransa suka baro dakin kai tsaye office din cp suka shiga suka tsaya tare da kamewa cp ne kawai a zaune yana ciza gefen lips dinsa “jamilu bude fridge din can ka dauko min ruwa “.okay sir jamilu ya nufi fridge ya dauko masa ruwan swan water mai sanyi kadan ya bude ya mika masa cike da girmamawa ,ya amsa ya kurbi kadan ya ajiye sauran akan makeken table din dake gabansa sannan ya fuskancesu “kaccala ali ya kira sunan mataimakinsa ya amsa da “yes sir !
“me ka fahimta a game da bayanin wannan mutunmin? duk naji abinda ya fada amman abu daya zan iya dauka wato sunyi cin amana sun danne kudaden mutumin ta karfin tsiya ,amman sauran bayaninsa duk karya ce zalla ya fada mana akwai sadidan gaskiya acikin zuciyarsa ya boye, yanzu sanin takaimamai abinda ya faru a tsakaninsu sai an nemo sauran biyu din da aka karbewa kudi muji ta bakinsu tunda su wadan can biyu din baa san inda suke ba “.
Cp ya gyada kai alamun ya gamsu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login