Showing 27001 words to 30000 words out of 259215 words

Chapter 10 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16516

win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da'aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan zagaye yaje da flowers sannan yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa .


shewa ne ke tashi acikin parlou'n "mutunen da zasu ce meye namu acikin lamuran kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu, maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati "wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote "muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so acikin kasar nan da bamu samu ba da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ? "babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba'a so dole a dama damu kuma muyi abinda muke so "wannan gaskiya ne ...


"waɗan kananun maganganun yasa nake gudun shiga siyasa Gara na tsaya iya haka tunda duk abinda nake nema ina samu sannan ina juya waɗan da nake so na bada umarni kuma abi inji cewar Alh Tanko gote suna cikin hirar wayar Alhaji tanko gote ya ɗauki kara ya mike sanye da bakin kaya wando da riga da hula ya ɗauki glass cup ya dauki wayarsa ya miko dogon coridor din gidansa sannan ya ɗauki wayar ya soma magana kasa kasa "ranka ya dade aka fada daga dayan bangaren na turo da kudaden yanzu haka yarona na bakin get din estste " oooooo my god me yasa baka da fahimta ni da nace a wuce akai kudi banki shine zaka turo min yaro madadin ma ka kirani na turo body guad "am sorry sir gani nayi idan na turo kudin zaka fi maida hankali "haka ne kana da fahimta dan a daidai wannan lokacin ina tare da shi wanda zai saka hannu "to kagani sai ka bashi ayi agama komai dan so nake ya fito zuwa jibi dan Allah kasa a kashe wani a madadin falsa .." shikenan a gama karkaji komai " zan bada umarnin a shigo da yaron yanzu ya fada yana canza magana "you have to understand that you should know that what someone like us can do in this land be left ,ya maida wayar zuwa dayan kunnenshi tare da shiga karamin parlou'nsa ya bude window dining area "nasani ranka ya dade nasan zaka iya komai murmushi tanko gote yayi" ka kwantar da hankalinka komai zai tafi daidai cikin haka amaryarsa ta shigo tana taku day day ta nufi inda yake tsaye ta rike hannun daya daga cikin kujerun dake zagaye da dining yana ganinta yayi saurin "cewa I will call you later uhm alright "my dear ta matso jikinsa ya cire wayar a kunneshi yana rungumota jikinsa ya manna mata kiss tayi murmushi "darling har na fara kewarka da tunanin tsawon lokacin da zaka ɗauka idan ka tafi hong Kong dan Allah kar ka dade kamar sauran lokuta karka ɗauki lokaci mai tsawo bana son ka dade ka dawo da wuri duk yau sati ne fa da dawowarka "uhmmm gaskiya ne amman this time a round just 1 month zanyi na dawo nayi wata uku ban fita kowace kasa ba "really ? ya gyada mata kai "idan zan dawo zan biya ta itly "kai dan Allah tayi maganar a shagwa'be "dole na biya dan akwai abinda zai kai ni daga nan naga bilal ta soma tafiya tana farinciki yana biye daita abaya suka zauna akan farar kujera mai zaman mutun biyu har zai ajiye wayarsa ya tuna bai kira securitys ba ya soma ƙoƙarin kiransu kira ɗaya suka ɗauka "hello sir daga ɓangaren Tanko gote yayi shiru yana tsotsa keya yana ciza baki saboda bai tambayi sunan yaron da aka aiko gurinss ba iska ya furzar yaceb"akwai wani yaro yana ....
"Okay sir gashi nan ma "yauwa ku barshi ya shigo "okay sir ya katse kiran tare da janyo amaryarsa jikinsa ",zanyi missing din waɗan abubuwan ya kai hannu ya shafo qirjinta bata yi sanya a gwiwa ba ta kai hannunta ta soma wasa da sansar jikinsa kusan minti goma suna rungume da juna wayarsa ta sake ɗauka qara ya zareta ajikinsa yana ƙoƙarin d'aga wayar gabansa yayi wani irin muguwar faduwa yayi shiru rike da wayar ya kasa ɗauka babu abinda yake ji sai faduwar gaba.


Saurin mik'ewa yayi yana kallon parlou'n kansa na juyawa a matukar zabure amaryarsa ta mike "what happened ? "gabana ke fad'uwa da matsanancin karfi "gabanka ke faduwa ta maimaita tana kallonsa" ina jin kamar takun mutane "how is there tayi maganar tana kallon kofar parlou'n tayi maganar a tsorace ganin haka yasa ya riko hannunta "colm down never mind "what do You mean never mind ? tayi maganar a tsorace "don't leave the parlou "ban fahimceka ba ? " Ina zuwa yayi foring head d'inta kiss "i think I will back don't leave the parlou ya juya ta riko hannunsa da sauri "karki damu zan dawo yanzu ya sake rungumeta ya mannata mata kiss ita dai a sanyaye ta bishi da kallo "meke faruwa ne haka daga gabansa na faduwa yace na tsaya anan na jirasa zai dawo tafiya yake gabansa na faduwa ya biyo dogon coridor da zai kai mutun wata kofa data fuskanci hagu ya fito a hankali yana dube dube har inda wata motar take parke yana dubawa gabansa na faduwa wanda duk sanda yaji haka yasan akwai wani mummunar abu da zai samesa cigaba da dube dube yayi a hankali ya juyo yabi wani hanya stil bai ga kowa ba bai ga komai ba, ya tsaya yana waige waige hagu da dama sannan ya sake juyawa ya nufi kofar daya biyo "Alhaji tanko gote.........."
yaji sauti daga bayansa cak ya tsaya tare da juyowa gabansa na wani irin dokawa a hankali Jaguwa yake daga kafafunsa "waye kai ? tambaya kake ko neman sani ? "duka ya fada cike da tsoro , jaguwa yayi murmushin "colm don Tanko gote zaka san komai cikin second daya yayi mgnr haɗe da ciro bindigarsa daga maajinta ya soma gyarawa yana kusanto inda tanko gote yake tsaye a matukar tsorace yake kallonsa da bindigar hannunsa alama su shiga ciki yayi masa babu mutsu ya juya Jaguwa na biye dashi har suka shiga parlou'nsa na uku ya tsaya " ba wani abu ne ya kawoka ba illa kudin da'aka ...
"Dakata kafin wannan kamar baka ganeni ba ?ya girgiza masa kai "Jaguwa yayi murmushin "daman mutane irinka basa iya gane mutane abinda yafi haka ma zaka iya saboda mutun azzalumi irinka ba lallai ne ya zamanto mara mantuwa ba well ba wannan ne abinda ya kawoni ba shiga ka fito dan zuwa yanzu ka fahimceni "sosai ai idan kudi ne zaka samu har sai kabari ni Dai ka barni da Raina da lafiyata "ban soma wannan aikin dan na dauki ran wani ba sai dai a rashin sani amman kai wallahi zan iya daukar naka take jikin Tanko gote ya sake ɗaukar rawa ....


" muje inda kudin suke jikinsa na rawa ya nufi wani daki suna shiga sanyi ac ya ratsasu buhu ne cike da kudade daban daban na kasar negeria da kasashen ke tare ka ɗauki duk wanda yayi maka "Jaguwa yayi murmushin yana shafa qirjinshi da hannu "ai gaba-daya zan wuce dasu dan haka ka soma ɗauka daya bayan daya "ka bari na bada umarni a kai maka su cikin motarka tana ina "ance maka ni karamin kwaro ne karka bata min lokaci ka soma abinda ya kamata kafin na fasa maka kwakwaluwa .....


Darling's




💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*



WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


https://my.w.tt/lcJskJdtpbb


🅿️09


.....Mamakin jin furucin Jaguwa na karshe ya cika zuciyar Alh tanko gote mutumin daya shahara a cikin fadin duniya da aikata masha'a bangaren neman mata cin amana ,makirci, son abun duniya ba dan bashi dashi ba ,daurawa mara laifi laifi domin bawa mai laifi gsky saboda abun duniya ,idan kana son ka kasance dan ta'adda mai lasisi da neman gindin zama acikin kasar nan nemi tanko gote,idan aikinka garkuwa da mutane ne fayde zama dilan kwaya da sauransu nemi tanko gote duk zai tsaya maka asirce kaci karen babu babbaka ko an kamaka zai sa a sakoka cikin kankanin lokaci .............


Duk wannan mugun aikin daya ɗauki tsawon shekaru yana aikatawa adalilin connection din da yake da acikin yan siyasa babu wani mutun ko ɗan fashin da makamin daya taɓa kawowa rayuwarsa farmaki ,
hasalima yana jin sign dinsu ajikinsa kafin su karaso gareshi yake maganinsu , sai gashi yau da ranar Allah dan fashi kwaya daya tal ya farmaki rayuwarsa har yana masa barazana da rayuwarsa , jiki a matukar sanyaye ya soma jan buhun kudi jaguwa na gefensa "idan kayi wata alama da wani zai gane halin da ake ciki wallahi zan ɗauke numfashinka daga doron kasa sai dai nima a ɗauke nawa numfashin wanda daman ni da wannan shirin na fito mutuwa ko akasin haka ..... "


"Karka damu babu wanda zai fahimci komai ya fada hannusa na karkarwa, kai tsaye bayan but din motar Jaguwa suka nufa ya jefa buhun kudin da kyar yana haki , haka suka dinga jerewa suna shiga yana dauko buhun kudi har ya kwashe tasssss ya tsaya tare da nad'e hannunwansa guri daya har lokacin zuciyarsa cike take da mamakin irin gogewa da kwarewar jaguwa .


Jaguwa ya manna gun a gefen brain d'insa "muje ka kaini gurin yar gaban goshinka Alh tanko gote ya kalleshi a matukar frigice zuciyarsa na dokawa da karfi "karka taɓa lafiyar iyalina idan wadan nan kudin basu isheka ba zansa akawo ninkisu yanzu
" yayi kyau shugaban fataken dare sai dai kar kwakwaluwarka tayi maka wanann banzan tunani dan nasan daraja da kimar dan adam ba irinka ba wanɗa yake danne hakin dan Adam domin son duniya , a hankali ya dinga daga kafafunsa zufa na karyo masa a gaba-daya sansar jikinsa yana tunanin "waye shi wannan ? "da dukkanin alamun yasan shi farin sani har suka shigo parlou'n zuciyarsa na cikin frigici , yayinda har zuwa wannan lokacin amaryarsa na tsaye hankalinta a matukar tashe tana ganin bindiga a gefen brain din mijinta tayi saurin durkushewa bisa gwiwowinta tana furta "na shiga uku me zan gani haka ni salma ? Alama jaguwa yayi mata da bindiga take tayi shiru jikinta ya kama kyarma ..


"kin san me yasa na bukaci wannan azalumin mijin naki ya kawoni gareki ban bukaci ya kai ni gungu mattarar tsiya ba ? tayi saurin girgiza masa kanta jikinta na rawa "saboda nasan kece tauraruwar gidansa da dokarki ake aiwatar da komai na gidan nan , sai yadda kika so za'a yi dan tanko gote mijin tace ne agurinki sai yadda kikayi dashi "ki faɗa masa kar ya kuskura ya kawo wa aikina hauka , bayan wannan ya kamata ki san ko waye wanda ke tsaye a gabanki duk da idanunki a halin yanzu a makance suke ,"sunana jaguwa akaro na farko da wani a duniya zai san wani abu daya danganceni sannan ya san sunan dan fashin daya gagarin kasa da yan sanda "


" a wasu shekaru da suka gabata anyi wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da kane gudu hudu namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa ya cigaba da magana "abinda yasa na dan baki labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata sai dai na barshi da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba " idan mijinki yayi kuskuren ko gigin sako jami'an tsaro ciki aikina domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan.....
da sauri tace" he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace "shiga muje kou " Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya "karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma mutsu zaka min yanzu na harbeka na harbe kaina muyi mutuwar kasko ,babu mutsu ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ....


Suna karasowa bakin get securities suka tsaida shi warning glass din bangaren Alh tanko gote yayi suna ganinsa suka shiga rigerigen kawo gaisuwa cike da girmamawa, daya daga cikinsu ya bude tafkeken get din estate din jaguwa ya fita .......


Tafiya kaɗan jaguwa yayi ya soma motsa lip's d'insa "nasan kana mamakin kwarewata kou? tanko gote yayi saurin gyada kanshi " karka yi mamaki duk acikin rashin imanin daka dasawa zuciyata ne , idan har baka tuba bisa ayyukan da kake shukawa a doron duniya ba, ka zuba ido zaka haɗu da wanda zai daukeka daga doron duniya gabad'aya ..
ya k'arasa maganar yana murmushin gefen baki murmushin dake kashe zuciyar yammata dan duk sanda yayi irin wannan murmushin dole kaji ya shiga ranka sannan a take zaka rikice akanshi ,yayinda shi agurinsa duk sanda yayi irin murmushin to ya samu nasara ne akan aikinsa ,wayarsa ce ta soma babriting ya tura hannunsa d'aya cikin aljihun wandonsa ya ciro wayar sunan Anas ya gani yana yawo akan screen din wayar, maida wayar yayi ya ajiye batare daya ɗauka ba sai da suka fita daga area estate din sannan jaguwa ya tsaida mota a gefen titi "fitar min a mota har yanzu bazan hanaka kiran headquater na police ba ka kira ........"
Kamar jira yake ya bashi umarni ya bude murfin motar jikinsa na rawa ya fita ya tsaya a gefen titi jaguwa ya fixgi motarsa a guje ya barshi tsaye yana bin bayan motarsa da kallo ....


Bangaren su Anas kuwa sun shiga tashin hankali mara misaltuwa saboda ganin jaguwa yaki ɗaukar kiransu dan babu wanda bai yi amfani da layinsa ba amman jaguwa yaki ɗauka shi ana shi so yake yayi surprise dinsu kusan fitowa suka yi daga cikin gidan suna shawagi a wajen unguwar kowane zuciyarsa cike da matsanancin tashin hankali jubi ne yace "kunga irin halin nasa ko? "Ban san me yasa yake mana haka ba ana kiranshi yana kin ɗauka "karkace haka bakasan halin da yake ci ba a irin tsoron dake estate din ya cancanci fiyye da haka mu dai mu dai ya dawo lafiya shine kwanciyar hankalinmu inji cewar Anas wanda yayi magana hawaye na gangaro masa ....
ita kanta tanweer haka ta kasance zuciyarta na bugawa da karfin gaske ga zazzafan zazzaɓi daya ziyarci jikinta haka nan ta dinga jin wani iri ajikinta idanunta ta lumshe tare da kamkame jikinta guri daya zuwa yanzu zuciyarta cike take da kewar gida ..


Haka ma can gidan minister of health Kuka sosai Hajiya zainab take Alh Abubakar shima kuka yake babu mai rarrashin wani ganin Alh Abubakar na goge hawaye yasa hajiya zainab ta saki wani gigitaccen kuka mai karfi tace "nashiga uku ni Zainab diyar tawa kwaya daya take hannu yan fashi da makami yau kusan kwana biyu Allah idan wani laifi nayi maka ka hukuntani ni kad'ai karka hukunta yarinyata dan batayi laifin komai ba ,saurin toshe bakinta Alh Abubakar yayi "haba zainab karkiyi sabo mana kaddara ce kuma tana kan kowa tanweer will be fine da yarda Allah lafiya zamu ganta ina iyakacin kokarina akan lamarin ta ko ina jami'an tsaron na kan bincike sannan nasa a tsananta addu'a bana jin tanweer na cikin damuwa kamar yadda muke ciki ,nasan killa suna bukatar wasu ƙarin kudade ne daga garemu yasa suka riketa a shirye nake da ko nawa zasu bukata zan mallaka musu komai dana mallaka akan tanweer dan Allah ki kwantar da hankalinki "wani kwantar da hankalinka zanyi .."?
"Yan fashi da makami sun ɗauke min diyata kwaya daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login