Showing 90001 words to 93000 words out of 259215 words
Chapter 31 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
ka dai qara min lokaci ka cigaba da aikin nan karshensa ma yazo ".
nazifi ya furza da wani huci Yana tsinewa alhj Tahir a zuciyarsa ya mike tare da yi masa sallama har ya kusan Kaiwa bakin kofa yaji muryar alhj Tahir "karka kuskura ka fadawa kowa wannan shiri dan bazan fad'a maka abinda zai biyo baya ba sai dai kawai ka tsinci kanka cikin tsaka me wuya abinda bazan so faruwarsa ba kenan dan har yanzu kana nan a matsayin d'ana" . gyada Kai kawai nazifi yayi ya fice .
Hajiya baseera zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga nazifi ya shigo hannunsa rike da leda wanda da gani kasan na asibiti ne dan a zahiri ake iya ganin abinda ke ciki ,hjy baseera na ganinsa ta saki fuska duk da zuciyarta cunkushe take da damuwar rashina lfyr Ibrahim ,
sosai tayi farincikin ganinsa tana qaunarsa tamkar yadda take qaunar Ib .ya dan rusuna cike da girmamawa ya gaisheta "Ina yi mumy ?"lafiya lau son ya fama da jama'a da kokari Kuma ?
"alhamdulillah mun godewa Allah ya Ib da jiki ? alhamdulillah Lafiya na ta samuwa ta nuna masa gurin zama da hannunta "ka zauna son "ya samu guri ya zauna yana cewa daga bangaren dady nake gbdy lamarinsa babu sauki a yadda yake kokarin son kassara rayuwar Ib,wallahi mumy abun na matukar bani mamaki haka nan sai na zauna Ina tunanin Anya kuwa mahaifinsa ne da yayi silar zuwansa duniya ?"mahaifinsa ne nazifi kama daina tantama shi mutun da son abun duniya ke sama da farincikin iyalinsa ".
runtse idanuwanshi yayi "dady na bukatar rayuwar Ib domin kuwa wadan nan magungunan da yake bukata a dinga bashi da allurai daidai suke da mutuwarsa dan watan wata rana za'a wayi gari babu shi ."
"Da naji wannan mummunar labari zanfi bukatar na bar gidan nan dashi sai dai ban san yadda zan bar gidan dashi ba batare da sanin mahaifinsa ba". ta k'arasa maganar cike da damuwa .
shiru suka yi na second biyar sannan nazifi ya cigaba da magana a tsanake "karki damu mumy daga yau kisa a ranki Ibrahim zai dawo rayuwa kamar yadda sauran mutanen suke yi "zan d'auki nauyin ib bama garin nan ba kasar ma zan bari dashi gabad'aya Cikin dakiyar zuciya hjy baseera tace "wannan hukuncin naka yayi daidai Kuma na gamsu dari bisa dari dashi wallahi , dan haka babu abinda zance maka sai godiya ,yadda kake son ka nisanta tsakanin Ibrahim da mahaifinsa ta k'arasa maganar tana Kuka sosai tmkr wacce aka Aiko mata da sakon mutuwar ta ko akace mutuwa Ibrahim zaiyi ".
"lamarin alhj Tahir akwai ban tsoro da rashin tausayi da Imani "sosai kuwa yanzu dai a sirrance zamuyi komai ta yadda bazai fargaba "Allah ya d'aura mu akansa Allah ya kawar da tunaninsa akanmu "Ameen mumy ni zan wuce duk abinda ake ciki zan kiraki a waya. "To na gode na gode sosai Allah yayiwa rayuwa albarka ya mike ya fice ."yana jinina girman alamrin dady ,gbdy ya gama ganosa Kuma yana tare da kwararrun hujojin da zai sa jami'an tsaro su tunhumeshi dashi idan bukatar haka ya taso , idan ta kama ya tsaya gaban alqali zai tsaya ya bada sheida domin kuwa mutumi kirki ake karewa da rufawa asiri irinsu dady kuwa sai dai a fallasasu duniya tayi Allah wadai dashi ."
***""
Da misalin karfe goma na daren ranar litini jaguwa ya shigo d'akin jikinsa sanye da kayan shan iska farare sol yayinda hannunsa ke rike da farar leda dake d'auke da roban takeway guda biyu wayam ya ga d'akin babu ita babu alamun ta jiki a sanyaye ya ajiye ledar hannunsa ya karasa ya zauna abakin gado a tunaninsa wanka take shiru har minti biyar ta wuce bata fito ba ya kira sunanta yana duba agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa still shiru ya Kara five minute bai ji motsin saukar ruwa ba ya mike tsam ya Isa bakin kofar bayi yayi knowking still babu respond Kara knowking yayi no answer a hankali yaji zuciyarsa ta buga da sauri ya d'aura hannunsa kan handle din kofar ya murd'a yaji murfin a bud'e ya sanya kanshi cikin ya leka wayam ya gani nan ma babu ita yayi mamaki Inda taje ya fito a rud'e yana duba sauran dakunan gidan nan ma shiru babu ita ..
Wata uwar ashar ya saki ya wuce su anas ya fito zuwa haraban gidan da sauri da mugun sauri yanzu kam jikinsa ya fara bashi akwai matsala yana tafiya anas ,jubi,jabir ,har ma da kamil dake dingisa kafarsa suka biyosa suna Kiran sunansa amman bai juyo ba sai faman dube dube yake yana Kiran me gadinsa da sauri ya k'araso ya rusuna cike da girmamawa "ka budewa yarinyar nan kofa ne ?me gadi ya girgiza masa Kai alamun a'a , cikin fushi ya d'auke shi da mari "ka bud'e baki kamin magana zaka wani girgiza min Kai kamar kadangare "a'a sir ban budewa kowa get ba tun safe ma babu wanda ya fita daga gidan nan bayan Kai ".
ya Salam ya furta yana rike kugunsa da hannu d'aya ya shiga sintiri a haraban gidan ya bar me gadi dafe
da quncinsa "gidan ubanwa ta shiga ?wallahi idan banganta ba sai naci ubanka ya fad'a a fusace yana juyowa tare da nuna me gadi da yatsansa gbdy abokansa suka k'araso garesa alokacin d'aya anas ya dafa shi "wai meke damunka ne "ban sani ba duk banga amfaninku ba ace Kuna zaune tanweer ta fito baku sheida min ba "
"ta fito taje Ina ?"tun byn sallahr isha'i muke zaune a falo bana tunanin ta fito zo muje mu sake dubata tana ciki may be ko tana bathroom ne ya kamo hannun jaguwa ,ya fixge a fusace "bata nan na duba koina bata nan bata cikin gidan nan wallahi idan banganta ba duk sai na kasheku d'aya bayan d'aya cikin kankanin lokaci gabad'ayansu suka shiga tashin hankali anas ya basu umarnin nemota duk suka raba kansu suna nemanta shi kuwa jaguwa tuni ya dawo tamkar wani zarare shi kad'ai yasan irin tashin hankali dayake ciki "Ina tabi tunda me gadi yace bai bud'ewa kowa get ba ?ya d'aga Idanunsa da suka rikid'e suka canza kala zuwa katangar gidan da sauri ya girgiza Kanshi "muddin ta tsallaka katangar nan lallai zata mutu idan Bata mutu ba zata nakkasa gashi bayan gidan babu wasu gidaje sai kango .
ya fito a gigice anas da jubi suka biyosa suna cewa "Ina zaka ? "dan Allah ka natsu bazata iya tsallaka katangar nan ba , bai tsaya sauraronsu ba dan kwata kwata hankalinsa bai jikinsa Kai tsaye bayan gidan ya nufa yana haska gurin da wayarsa yana Kiran sunanta babu ita babu alamunta ya juyo
a harzuke yana masu wani irin kallo mai d'auke da rashin mutunci suna kallo ya dungule hannunsa, gbdynsu suka yi matukar tsorata shi kuwa anas byn tsoro har da kallon mamaki yake masa sai dai ya kasa ce masa komai wani irin kallo jaguwa ya cigaba da yi musu da jajayen idanunshi .."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️18
....Anas ya Kalli jaguwa yaga gbdy yanayinsa ya sauya ,
dukkanin wani jijiya dake Kansa sun gama fitowa sunyi rud'u rud'u babu abinda qirjinsa yake sai d'agawa sama da kasa kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa .ya d'aga hannunsa sama zai naushi jabir dake tsaye kusa dashi yayi saurin matsawa baya, ya sauke hannunsa ya naushi iska kana ya zagayesu ya wuce cikin tsananin fushi, suka biyo bayansa suna fad'a masa tautausan kalamai masu sanyi "kayi wa Allah ka samu natsuwa inshallahu za'a ganta " bai kulasu ba ya shiga gidan kmar mayunwanci zaki yana haki ya rike kugunsa da hannu d'aya yayinda d'ayan hannunsa ke rike da goshinsa yana shafawa saboda saran da yake masa .anas da sauran mutanen dake zaune acikin gidan suka cigaba da duba ciki da wajen gidan ko Allah zai sa su ganta har Inda suka duba da farko sun sake dubawa babu ita babu alamunta, gabad'ayansu a matukar tsorace suke dan sun san muddin ba'a ganta ba sun zama abun zargi agurinsa me gadi yafi kowa shiga rud'ani , jikinsa banda rawa babu abinda yake ,da zarar zasu had'a Idanu da jaguwa zai yi saurin kawar da fuskarsa yana salati .
Tsayawa jaguwa yayi cak qirjinsa na wani irin luguden bugawa da matsanacin karfin gaske, ya tsaida idanunshi daidai Inda durom din ruwa yake wanda suke zuba shara acikinsa, haka nan yake Jin fad'uwar gaba me tsanani a yanzu da Idanunsa suka sauka akansa ,ahankali ya soma taku domin k'arasawa gurin , taku uku yayi sai ga anas ya k'araso da sauri "jaguwa !" ya kira sunansa cak ya tsaya yana sauraronsa dan a tunaninsa zai ce masa an ganta "munata wahalar da kanmu muje a duba cctv camera Ina da tabbacin zamu san inda take ."
wani irin juyowa jaguwa yayi da sauri tare da yiwa anas kallon second d'aya sannan da sauri ya soma tafiya cikin sauri kamar zai tashi sama ya nufi d'akin da camera yake , anas ne kad'ai ya biyosa daman Kuma daga shi sai anas ne suke shiga bangaren suna shiga d'akin anas ya kunna cctv camera bayan ya kunna yayi rewarning sai ga hotunan mutanen dake zaune a gidan ya soma bayyana .
a hankali suke kallo har zuwa sanda tanweer ta fito tana sand'a har ta fita zuwa haraban gidan har zata nufi get sai Kuma ta fasa ta Isa jikin window me gadi ta la'be tana dube dube da neman mafaka , cike da tsoro ta waigo bayanta nan taga alamun fitowar aliyu wanda shi sam hankalinsa bai je gurinta ba ganinsa yasa cikin sauri tasa hannunta ta bud'e durom din ruwa ta shiga.
wani irin naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke da karfin gaske sannan ya juya da sauri yana cewa "daman zuciyata da jikina sun bani naje na duba cikin durom din a she tana cikin ". ya Allah kasa wani abu bai sameta ba tafiya yake cikin sauri kamar zai tashi sama anas na biye dashi a falo suka wuce sauran abokansa da yaransa suma suna ganin haka suka biyousu cikin sarsarfa ya k'araso gurin ya bud'e duron din sai gata durkushe ta rufe bakinta da hannunta d'aya dan kar kukanta ya fito , gashi ta dungule jikinta guri d'aya tana haki bai san sanda yasa hannuwansa duka ya kamo kafad'unta ya fito daita waje ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke wahalalle numfashi . fuskata ya manna adaidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfin gaske , ita Kuwa haushi da bakinciki ne suka had'e mata a lokaci daya, ita da take ganin wa'adin zamanta ya kare a gidan dan har ta hango barinta gidan a yau din nan sai gashi ya rusa mata Komai .
a hankali ta d'auke kanta a daidai saitin zuciyarsa ta cusa cikin qirjinsa ta rushe da wani irin rikitaccen kuka me ban tausayi , shafa kanta kawai jaguwa yake yana sauke ajiyar zuciya batare daya ce uhm ba bare uhm uhm , godiya ya shiga yiwa Allah mara adadi ,
data fita cikin daren nan Allah ne kadai yasan abinda zai faru daita bare wananan unguwar tasu da koina shiru sam babu hayaniyar mutane , in kaga mutane to da safe ne yawanci ma masu zuwa neman taimako gurinsa ne ,komai zai iya faruwa daita batare da wani ya kawo mata d'auki ba. shine mutun na farko daya dace ya tsiratar da rayuwarta dan shine silar komai ,muryarsa a kasalance yace "me yasa kika shiga cikin durom din shara tanweer da kin mutu fa ? ya fad'a yana cigaba da shafa kanta zuwa gadon bayanta ,
tsaki taja aranta zuciyarta na tuttukin bakincikin rashin samun nasara .
Anas ya kafesu da idanunshi yana kallonsu yayinda sauran abokansa suka kama gabansu tunda an ganta sun fita cikin zargi , gurin yayi shiru baka Jin motsin komai sai na saukar numfashinsu da yanayin na kasantuwar dare .gbdy anas ya fuskanci yarinyar ta zamo Jinin jikin jaguwa sosai , bazai iya rayuwa babu ita ba . kallonsa ya cigaba da yi yana ganin kamar shima kukan yake son yi sakamakon idanunshi da suka sake rikid'ewa sukayi jawur .
a hankali natsuwa ta dinga zuwa mata ta dinga sauke ajiyar zuciya tana k'okarin zare jikinta daga nashi amman rikon da yayi mata ba wanda zata iya kwacewa bane, dan haka ta fara mutsu mutsu lallai so take ya rabu daita , a natse ya cire hannunsa dake kanta ya zagaye kugunta dashi yana sauke numfashi ,ya lalu'bo tafin hannunta cikin nashi ya tsarke cikin juna tare da matsewa gam yana sauke naunayen ajiyar zuciya duk anas na tsaye yana kallonsu cike da mamaki .
a natse muryar jaguwa ta fito "why tanweer ?"karki sake min irin wannan ganganci kinji ?".
"ni ni gida nake son zuwa bazan sake cigaba da zama daku ba ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka "wai bamun gama wannan maganar bane "ni babu ruwana da wannan maganar , bazan sake taking time a gidan nan ba just ka maidani Inda ka d'aukoni ko Kabani damar na fita na kama gabana".
"shikenan kukan ya Isa haka naji zan kaiki " ka min wannan alkwarin zaka mayardani gida gobe dan Ina ji ajikina kamar zaka cutar dani ne , dan Allah ka mayardani gidanmu ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka.
shiru yayi yaki cewa komai illa mammatsa mata kugunta da yake yana Jin wani sanyi from know where yana ratsa sansar jikinsa , jin yaki yin magana sai wani shige mata jiki yake yana narkewa yasa ta fixge jikinta da iyakacin karfinta bata tsaya wata wata ba ta d'auke shi da mari tana cewa "ka fad'a min ranar da zaka mayar dani ga iyayena ba wai ka dinga wani shige min ba ?"dan iska kawai sai wani shige min kake kmr wani mijina "ta fad'a tana haki "You slap me again ? "na mareka ka rama ko ka kasheni tunda kaji ciwon marin da nai maka ..."
Take yanayinsa ya sauya daga farincikin ganinta zuwa mummunar 'bacin rai ,shiru yayi na tsawon minti biyar yana tsaye yana kallonta kafin daga baya ya juya a matukar fusace ya soma tafiya, a tsorace tabi bayansa da kallon yadda yake tafiya cikin sarsarfa hakan kuwa ya mugun d'aga mata hankali dan bayansa kawai zaka kalla kasan yana cikin fushi me tsanani ,alama anas yayi mata data bishi ta bashi hakuri, da kamar baza ta bishi ba sai tayi saurin canza tunani dan baza ta'ba manta sanadin mari data yi masa bane yasa ta kasance acikinsu " .
da mugun sauri ta biyo bayansa tana Kiran sunansa "Adnan !". Banza yayi mata ya cigaba da tafiya yana furzar iska mai zafi daga bakinsa , yayinda take biye dashi tana cigaba da kiransa ,Kai tsaye d'akinsa ya wuce ya tsaya a tsakiyar d'akin yana huci kamar zaki , ta k'araso ta tsaya a bayansa qirjinta na wani irin bugawa da karfi , hakan nan taji ta sake shiga tashin hankalin mai tsanani akan marin da tayi masa.
yaji tsayuwarta da saukar numfashinta a bayansa dan tana daf dashi amman yaki juyowa tana kallonsa ya d'auki wayarsa ya soma neman layin mahaifiyarsa tare da sa wayar a handsfree kira d'aya ammi ta d'auka cike da farincikin ganin kiransa "ammi tunda kika haifeni kin ta'ba dukana ? shiru tayi tana nazarin maganarsa da muryarsa yaushe rabon taji muryar d'an lelenta haka ? duk Kuma sanda muryarsa tayi haka tabbas an ta'boshi ko yana cikin damuwa . shiru yayi yana sauraron ammi domin Jin abinda zata fad'a masa "dan Allah ammi ki amsa min tambayata idan kin ta'ba dukana ko marina ki fad'a min ? muryarta a sanyaye tace "ban ta'ba dukanka ba d'ana". "mahaifina fa ya ta'ba dukana "wai me ya kawo batun duka da daddaren nan ?"ni dai ki fad'a min ammi ? "taya ma mahaifinka zai yi tunanin dukan dan lelensa ai sam bazai yiwu ba wai meke faruwa da Kai ne ka fad'a min zuciyata ta fara tsinkewa ?" babu komai ammi zan kiraki zuwa da safe yana gama fad'ar haka ya katse Kiran tare da kashe wayar gbdy dan yasan muddin bai kashe wayar ba zata biyo Kiran. ya juyo batare daya Kalli Inda take tsaye ba yabi gefenta cikin tsananin fushi ya fice daga d'aki ya barta ".
naunayen ajiyar zuciya ta sauke idanunta na sake cikowa da ruwan hawaye ta sake biyo bayansa tana furta"wayyohhhly Allah na shiga uku nah Allah ka taimakeni kar ya harbeni da bindigarsa yau ". bai tsaya akoina ba sai a lambun gidansa ya k'arasa Inda suke ajiye kayan shaye shayensu ta'ba sigari ya d'auka ya Kai bakinsa ya kunna ya fara zuka da karfi, yana tsaye yana zukar taba ta karaso jiki a sanyaye ta had'e hannunwata duka cikin juna , yaji alamun tsayuwarta amman still yaki juyowa zuciyarsa ban da bugawa babu abinda take .
Cikin tsananin tsoro da fargaba ta Kai hannunta kan kafad'arsa tana fixgo numfashi da kyar ta janyosa amman kamar dutse ta ta'ba dan ko gezau bai motsa ba ya cigaba da zukar tabarsa . hannuwanta duka tasa ta riko damtsen hannunsa zuwa jikinta ya fixge ya yar da sauran tabar