Showing 57001 words to 60000 words out of 259215 words

Chapter 20 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16561

ya d'auki shiru ciki kuwa har da jami'an tsaro dake aiki agurin kowa nason rayuwarsa dan da ganinsu an san ba kananun yan fashi bane ."


Loakaci zuwa lokaci yake duba agogo dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Bayan kamar minti talatin sai ga wata mota fara sol ta shigo gurin. tun da suka shigo tsoro ya kama na cikin motar sakamakon ganin gurin shiru babu motsin mutane jaguwa ya gyra bluetooth din dake manne da kunnensa "eku ga mutumin da muka zo dominsa nan ya shigo "okay boss I will do my duty .cike da matsanacin tsoro direban motar yaja burki yana k'okarin juyawa sakamakon ganinsu take eku ya harbi tayar motar .
tsayawar motar ke da wuya yaga mutane sun zagaye motar kamar almara sai ga jaguwa ya bayyana a tsakiyarsu direban yayi saurin kife kanshi akan stearing motar yana rawar jiki , jubi ya bude murfin site din baya Inda alhj aminu ke zaune ya fito dashi yayi cilli dashi gaban jaguwa ya tsaita kanshi da bakin bindiga "where's the money jikin mutumin na rawa yace "it's inside the car ya fad'a yana nuna motar "cheek ! inji cewar jaguwa".Anas da kamil suka nufi motar suka duba can byn second biyu anas yace "comform it's there "okay fine ,move move kamil ya fad'a yana ture alhj aminu " face the grand if you do nonsense i will kill you ,nan take alhji aminu yay sujjada gbdy ilahirin jikinsa na kyarma .


Suka jefa jakar kudin byn motarsu jaguwa ya shiga byn mota sauran dake shirin shiga sai ga jiniyar motacin police suna harbi ,ai nan take qarar harbi ya karad'e gurin police na harbi Suma suna yi kowa ya shiga mota har sun fara ja ya saura kamil ne bai samu damar shiga ba ya biyo motar aguje yayinda sauran yan'
uwansa ke harbin yansanda suna Kiran sunansa "km run kayi gudu mana suna miko masa hannu shi kuwa gudu yake da iyakar karfinsa yana k'okarin Isa ga motar gabad'aya suka mika masa hannuwansu suka had'a baki "zo kamil zo gamu maza mana kamil ka kara gudu suka fad'a hankalinsu a tashe .ganin halin da ake ciki yasa hankalin jaguwa yayi matukar tashi nan fa ya shiga bud'ewa police wuta daf da kamil zai shiga mota wani police yayi nasarar harbinsa a kafa wata razananniyar qara ya saki ya durkushe kasa cikin azaban ciwo tare da rike kafarsa "...


Mmn sudas




💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO



WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


🅿️14


.....Cike da zafin rai da zafin zuciya jaguwa ya soma k'okarin fitowa daga cikin motar yana gyara bindigar hannunsa nan fa hankalinsu anas yayi kololuwar tashi , anas ya rud'e yay saurin dakatar dashi ta hanyar Kai hannunsa qirjinsa "karka fita jaguwa , kaucewa yayi yana cewa "ku wuce kawai zanji da komai "dan Allah jaguwa karkayi wannan kasadar ". bai sake saurararsa ba ya soma harbi gumi na karyo masa , hakan yasa da sauri kowannensu ya cigaba harbi da iyakacin kwarewarsa ."
da mugun gudu jaguwa ya isa inda kamil yake durkushe rike da kafarsa yana cewa "km bani hannunka " , cikin tsananin tashi hankali kamil ya d'ago kai sai dai bashi da kuzarin da zai mika masa hannunsa " nace ka bani hannunka ya sake mika masa hannu shima kamil ya mika masa ya rike hannunsa gam cikin nashi yana cewa "taho km ka mike dan allah karka bari mu rasaka " kamil ya fara k'okarin mikewa adaidai lokacin da sky ya juya kan mota zuwa inda suke tare da yi musu tsakani da police officer's , cikin azama jaguwa yace " maza mike km da taimako allah jaguwa ya shigar da kamil cikin mota ai kuwa shigarsu motar keda wuya suka figi motar aguje nan motocin 'yansanda suka biyosu da mugun gudu suna harbi suna danna jiniya , haka suma bangaren jaguwa harbinsu suke , gudu sosai motacin jaguwa sukayi har suka yiwa police nisa a karshe suka daina hangosu ."


a matukar wahale suka k'araso gida jaguwa yay saurin fitowa daga cikin mota ya k'arasa da sauri ya bud'e kofar shiga cikin ainihin falon gidan , su jubi suka kamo kamil suna tafiya dashi a hankali kafafunsa babu takalmi dan tuni sun cire masa tun acikin mota ,Kai tsaye suka nufi hanyar falon jaguwa na mussaman dashi suna masa sannu, a hankali suka kwantar dashi akan wani k'aramin madaidai gado wanda daman an tanadesa domin irin haka ,kamil ya runtse idanunshi saboda azabar ciwo , cike da hanzari jaguwa ya nufi Inda first aid box dinsa yake ya d'auko ya dawo da sauri , eku ya janyo masa kujera ya zauna a gaban kamil yana masa sannu ."


jin motsin shigowar motocinsu da maganar wasu daga cikin yaransa sama sama yasa tanweer lalla'bowa babu takalmi a ka'fafunta tai hanyar babban falon gidan tana bin bango tana qarasowa bakin kofar falon ta tsaya a hankali ta bud'e kofar ta shiga bata ga kowa a falon ba, kasa kasa take jiyo magangansu , kawai ta nufi wani dogon korido Inda take zaton daga nan sautinsu yake fitowa , a hankali ta tsinci kanta acikinsu kowannensu cikin tsananin tashin hankali , jaguwa zaune a gaban kamil cike da tausayawa yana k'okarin cire masa harsashi . binsa tayi da kallon mamaki qirjinta na wani irin bugawa da matsanacin karfi shafa idanunta tai hade da runtsesu na second biyu sannan ta bud'e tana sake sauke idanunta akanshi wanda zuwa lokacin har yay nasarar ciro bulet din yana kallo sannan ya saka acikin farantin silver dake rike a hannun jubi, yayinda sauran ke zaune cikin tsananin tashin hankali gbdy idanunsu ya rufe babu wanda hankalinsa ya Kai Inda take tsaye ."


naunaye ajiyar zuciya suka sauke lokacin da jaguwa ya cire wa kamil bulet ita Kuwa tanweer zuciyarta ta shiga rawa had'e da tsinkewa ."me zata gani yau ? daman likita ne shi ko kuwa mafarki take ? yes wannan ba mafarki take ba shine tagani zaune ya cire bulet a kafar abokinsa, kasa tayi da idanunta tana kallon bayansa nan idanunta ya hango bindiga pestol soke a abayan wandon jaguwa ,nan take ta sake fita daga haiyacinta "bindiga ....! ta furta a kasan ranta " me Kuma yake yi da bindiga ? ya Allah karka sa abinda zuciyata ke hasashe akansa ya zama gaskiya dan bai cancanci haka ba " wani kuka ya kufce mata ta juya da sauri tana shesheka wanda hakan yasa gbdy suka d'ago suka ganta tana sarsarfa , cike da matsanacin firgici suka tsura ma jaguwa Ido dan jin abinda zai ce bai yi magana ba haka zalika bai nuna alamun damuwa atattare dashi ba , ya mike tsaye yana
furzar da numfashi tare da yiwa kamil sannu" ka kwanta ka huta kafin akawo maka abinci ya gyada masa Kai yana cewa" na gode abokina Ina alfahari da Kai ,nima haka ."


jubi ya dube jaguwa yana cewa "wallahi ban ta'ba shiga tashin hankali ba irin na wannan lokacin na tsorata matuka na sadaukar zamu rasa kamil "ba kai kad'ai ba inji cewar anas tafiya jaguwa ya fara a hankali suka biyosa a baya har gurin shakatawarsa "da'ace sunyi nasara akanmu zamu iya rasa rayukanmu gbdy". sai lokacin jaguwa ya motsa lip's dinsa "ina ai sai dai idan tawa ta kare sannan zaku iya shiga wannan hali amman muddin Ina tsaye akan kafafuna babu wanda zai yi nasara bare har mu rasa rayuka " ya karasa maganar tare da tsayawa cak ya rike karfen runfar dake kafe acikin gurin shakatawar , "hakika Nima na karaya inji cewar jabir " Karku ta'ba rungumar Karaya arayuwarku duk halin da zamu shiga karku karaya saboda rashin samun nasara ba namu bane ,a duk lokacin da naga Kun Karaya sai naga kamar tun asalin ku din ba jaruman gaske bane, sannan baku ne jarum da mukayi gasar mutuwa dasu ba ."


murmushi sukayi gbdy suna sauke numfashi "uhm wannan fa ba kamar gasar mutuwa bace ,gasar mutuwa kowa yasan mun saida rayukanmu ne dan biyan bukatarmu wannan fa ?"bayan sai da rai har da tozarci zamu janyowa gangar jikinmu idan muka tsinci kanmu a hannun jami'an tsaro ".anas ya karasa maganar yana dafa kafad'ar jaguwa "yanzu dai barkanmu allah ya k'ara karemu ." ameen jaguwa ya fad'a acikin zuciyarsa. "ka zauna kana bukatar hutu, jaguwa ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun gurin yana lumshe idanunshi " me za'a kawo maka ka d'an sha ? ya girgiza masa Kai alamun bai bukatar komai , zama anas yayi kamar yadda sauran abokansa sukayi yana cewa "ya za'a yi da wannan yarinyar ta rigada taga komai , koma nace taji wasu abubuwa akanmu ? ,yana d'aya daga cikin abinda yasa kaga banason yarinyar nan agidan nan "."me taji ?."Ko me mu kace ?yay masa tambayar a dan kufule " idan Kuma taji taji kenan shikenan daman abinda take bukatar sani kenan tasan su waye mu " ya k'arasa maganar yana jan dogon tsaki tare da jin bakinciki da takaici, haka nan Kuma ya tsinci Kansa da Jin fad'uwar gaba mai tsanani ".


Koda tanweer ta koma d'aki ta kasa tsaye ta kasa zaune sai zariya take acikin d'akin ita kad'ai, ta saka wancan ta kwance , kwakwaluwarta ta shiga tunani mai zurfi, babu abinda zuciyarta bata kisama mata ba akansu , abu uku zuciyarta ta tsayu akansa shi din dan fashin ne ko Kuma jami'in sirri ,ko likita , idan ba haka ba me yake yi da bindiga ajikinsa ? ta kasa hakuri dan haka ta sake fitowa tai hanyar boys quarter nan fa hankalinta ya sake tashi ganin yadda yaran jaguwa ke fitowa da manya bindigu suna adanawa a maboyarsu ,mutuwar tsaye tayi har sanda suka kwashe komai suka d'auki katuwar jakar kudin da suka shigo dashi suka nufi hanyar Inda jaguwa yake tare da abokansa suna tautaunawa , cike da matsanacin tsoro ta biyo bayansu a tare suka k'araso ta ra'be jikin wata bishiya kasancewar yaran jaguwa suna gabanta yasa jaguwa da abokansa kasa ganinta ."


sky ya ajiye jakar kudin a gaban jaguwa yana cewa "boss ga kudin operation din ". operation ? ta furta a kasan ranta zuciyarta na tsananta bugu kamar zai fasa qirjinta ya fito waje , tayita tunanin abinda manufar operation yake nufi acikin ranta .
a natse Jaguwa ya d'ago idanunshi yana ciza lips dinsa na kasa sai daya d'auki minti biyar sannan ya gyada Kai , yay musu alamun su wuce suka soma k'okarin juyawa tana ganin haka tayi baya da sauri ta la'be dan karsu ganta , gbdy kwakwaluwarta
ta gama tabbatar mata da manufar operation fashi ne ".barin wannan bishiyar tayi ta dawo kusa dasu sosai ta sake makalewa a wata bishiyar ta kasa kunne daga Inda take boye take jiyo duk abinda suke cewa "mun gama da operation din yau yanzu dai a kasa kudin gida uku nasan inamdi na nan zuwa komai dare ya amshi kasonsa dan bashi da hakuri kmr alhj Tahir yake "kamar alhj Tahir ta maimaita sunan ?tunanin Inda tasan sunan take gbdy ta kasa tuno Inda ta ta'ba Jin sunan amman tabbas kwakwaluwarta na hasko mata tasan sunan Kuma na kusa da jikinta ne ".
ko gama rufe baki jaguwa bai yi ba sai ga inamdi da eku remo , inamdi ya mikawa jaguwa da abokansa hannu suka gaisa shi Kuma eku ya juya ya kama gabansa .
guri jaguwa ya nuna masa da hannunsa , ya zauna yana cewa "sannuku Kun sha da kyar lokacin dana ga police sun harbi d'aya daga cikinku naji tsoro matuka, hankalina yayi matukar tashi "sa'anar armrobber's akwai dadi akwai saida rai ,bancin kwarewa irin naka da yanzu kuna hannun police.
"inna lilli wa inna lillahi rajiun" tanweer ta shiga furtawa tana maimaiwa tasa hannunta duka ta rufe bakinta dan kar sautin kukanta ya fito "ya dai tabbata su din 'barayi ne ........? " wannan shine dalilin da yasa ya fad'a mata da tasan shi ko waye shi da bata kamu da soyayyarsa ba ?wayyohhhly Allah nah ! "wayyohhhly Allah Adnan me yasa? " me yasa ka zabi wannan sa'anar ? jikinta banda rawa babu abinda yake tana kallo aka kasafta kudin aka bawa inamdi nasa kason ya ciro wata karamar jaka a aljihunsa ya shiga d'aukar bandir din daloli yana zubawa cikin jakar har ya gama ya mike ya sake mimika musu hannu sukayi sallama ya wuce cikin sauri ."


A hankali ta dinga d'aga ka'fafunta tana takowa zuwa Inda suke zaune , jaguwa ne ya d'ago idanunshi suka sauka akanta, cikin tsananin tashin hankali da damuwa mara misaltuwa yake kallonta ,bakinta na rawa ta soma magana cikin firgici "daman 'yan fashi ne ku ?".ta fad'a tana kallonsu d'aya byn d'aya .a rud'e abokan jaguwa suka had'a baki gurin cewa" no mu ba 'yan fashi bane armrobber's ne" jaguwa ya mike a natse cike da bakinciki taji sirrinsu yayinda gbdy abokansa suka rud'e da ganinta har suka kasa bambamce tsakanin abinda tace da amsar da suka bata , fuskarsa a murtuke tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya kallesu d'aya bayan d'aya kana ya soma mgn "babu bambamci da abinda kuka ce da wanda tace duk abu d'aya ne mu din barayi ne wato armrobber's ..... ".
ta zaro idanuwanta duka waje da sauri qirjinta na dokawa da karfin gaske ,yayinda numfashinta ke fita da sauri sauri. ya gyada mata Kai alamun "eh".wani abu mai duhu taga ya gilma cikin idanunta, zuciyarta ce ta tsaya cak ta daina
aiki na wani lokaci kafin daga baya ta dawo tana bugawa fiyye da kaida , ta rike kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login