Showing 222001 words to 225000 words out of 259215 words

Chapter 75 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16582

ya dan sauko da idanunshi ya dubesa yana dan sakar masa fuska ,dan allah ka saki fuskar nan taka “shikenan nayi “yayi mgn yana murmushin gefen baki “to ko kai fa wallahi har raina yayi sanyi gobe zan kai hally gurin ammi wata killa bazan samu shigowa da wuri ba ya gyada masa kai kawai alamun yaji suka yi sallama ya kama hanyar zuwa gida .”


Yau ma kamar jiya a bakin kofar shigowa falon ya tsaya yana sallama ta leko daga kitchen tana yi masa sannu da zuwa ,ya amsa yana cigaba da tsayuwa agurin yana kallonta cikin doguwar riga ya kashe masa idonsa daya “me kike jira da bazaki karaso ki tarbi mijinki ba tunda Kinsan abinda tsayuwatsa take nufi ?”kai ya anas!
“Kai ya Ana’s ko gskiya ina jira ta koma cikin kitchen din ta wanke hannunta ta fito ta tsaya a gabansa cike da shagwaba ya dage mata girarsa daya ya janyota kusa dashi sosai ta fada jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana sakin numfashi sai daya gama jin dumin jikinta sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya hade bakinsu guri daya ya shiga tsotsa “bayan runguma har da wannan nake bukata okay.


Ta zare jikinta taja shi zuwa ciki sosai ta zaunar dashi akan kujera tana shafa fuskarsa “ina ka tsaya yau ka dade ,ina tare da adnan tun fita ta bari na kawo maka ruwa ka sha da alamun akwai gajiya atare da kai ta mike ta shiga kitchen ta dauko ruwan gora mai sanyi da cup ta fito ta tsiyaya ta mika masa ya amsa hade da hannunta yana dubanta itama shi take kallo ya zaunar daita a cinyarsa ya kai cup bakinsa ya sha kadan ya mika mata ta ajiye cup din akan table “ki shirya gobe zan kaiki kiga ammi ,da gaske ta fada tana zubewa jikknsa gskiya naji dadi sosai amman kwana zanyi ko ?ya riko hannunta cikin nasa yana kallonta “kwana my princess?ta gyda masa kai “idan kika kwana ni kuma na kwana dawa?ta marairaice masa fuska ,kiyi hakuri kije kiyi ma ammi yini na rigada na saba kwana ajikinki amman idan ki yarda kawai sai mu kwana tare tayi saurin zaro ido waje ,yes dan gsky bazan iya kwana ni kadai yanzu ba “.


“Shikenan naji amman sai dare zakazo ka daukeni ?ya dage mata gira ,muje kayi wanka kaci abinci ,
Wanka dai amman abincin nan no space kamar jiya suna tsaka da hirar soyayyarsu aka kira sallah ya fita zuwa masallaci a daren ma kwanan farinciki sukayi rungume da juna sabanin tanwer da adnan .
washegari da safe ta tashi ta hada musu break suka ci suka fice ya bude mata gaban mota ta shiga ta zauna ta rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar suka bar gida bini bini zai jiyo ya kalleta sai murna take zata gida ,ya lalubo tafin hannunta cikin nashi yana murzawa yana janta da hira da tsokana har suka karaso unguwarsu yayi parking adaidai kofar get din gidansu zata bude bangarenta yayi saurin cewa “no my princess bari karki wahalar da kanki ya fita da sauri ya bude mata a hankali ta fito ya kulle motar suka jera suka shiga gidan ,”


A haraban gidan anas yaja ya tsaya ta shiga falon bakinta dauke da sallama ammi na zaune bisa kafet ita da haseera suna breakfast ammi ta dago ta kalleta ta kuma kalli bayanta “ina bin malik din yake ?ta karaso ta tsugunna a gabanta tana gaisheta ammi bata damu da ansa gaisuwar ba ta sake tmbyr anas “yana waje ammi ta bata rai “dan sakarci irin naki me yasa zaki bar min yaro a waje maza ki tashi kice ya shigo cike da mamakin irin wannan qaunar da ammi take masa ta mike tana riko hannun haseera “aunty hasera ya kwana biyu ?Lafiya lau auta duk kin wani canza kinyi kyau Kmr wata india tayi murmushi ta nufi kofar fita ta tsaya a gabansa “muje ko dan kasa mamanka tana min fada tai mgn tana zumboro masa baki yayi murmushi ta juya yana biye daita .”


Cike da ladabi da biyaya ya shigo bakinsa dauke da sallama ammi ta amsa tana fadada fuskarta da murmushi dan shima yayi kyau kamar yadda diyarta tayi hally ta dauko dadduma ta shimfida masa ya zauna kusa da ammi “anas ya aiki da hakuri da auta ? Alhamdullahi ammi babu abinda zance sai Godiya hasera na kallonsa amman bata ce masa uffan ba abun ya dan tsotsa ran hally shi dake mai saukin kai ne yace “hasera ina yini fuska a hade ta amsa da “Lfy! atakaice dan gani take har dashi acikin masu zuga adnan kar ya aureta hasera ta maida hankalinta gurin hally “hally uwar kyau wannan ai kinfi karfin akiraki mai kyau sai dai uwar kyau hally tayi mata banza “kinga kuwa yadda kika kara kyau kika murje?da kyar tace “na gode mumy kuwa abincin gabanta ta turawa Ana’s tana bashi umarnin yaci babu mutsu ya fara ci hally tasan ya koshi amman bazai iya mutsu daita ba ta tsura musu ido kawai tana jin dadin yadda ammi take qaunarsa byn ya danci kadan suka koma kan kujera suna hira ita ammi da anas da ita kanta hasera sunyi hira sosai cikin haka anas yayi wa ammi sallama ya ajiye mata kudi bandir din yan dubu day day na 50k “ga wannan babu yawa ni zan wuce ,haba anas har da wata hidima?babu wani hidima ammi ki samin albarka shine abinda nafi bukata daga gareki ,allah yayiwa rayuwarku albarka gbdy ya daukakaku a idanun duniya ya rufa muku asiri duniya da lahira Ameen ammi na gode sai anjima ya sa kai zai fita hally ta biyo bayansa domin masa rakiya ,”


A haraban gidan haseera ta samesu kamar zasu shige jikin juna ganinta yasa suka dan bawa junansu tazara ta karaso tana cewa hally ki dan mana exuse bata damu ba sai ma shigewa ciki da tayi haseera ta gyara tsayuwa tana tsura masa ido “ada tunanina kana cikin wadan da suke zuga adnan akan kin aurena amman a yanzu na fahimci Kai mutumin kirki ne sannan nasan kasan matsayin da nake dashi azuciyar abokinka ko zan iya sani wani abu karka min karya ka fad’a min gsky sbd allah ?” yayi shiru yana kallonta d’an ta dauresa tunda ta kira allah ,
“Adnan yana da burin aurena ko kuwa wata can yake da burin aura?Kamar yace mata eh sai kuma yayi shiru” idan ma bashi da burin aurena gara ya fada nasan matsayina ba nayita jiran gawon shanu ba “kibi komai a hankali haseera Kinsan shi alamarin na aure nufi ne na allah da zarar lokaci yayi kuma kece matarsa zaa yi idan bake bace haka zaki hakura“.


“Bama zai zamo bani bace matarsa dan da yaje ya kwaso wata gara ace nice zan shiga gidansa kai ni aurensa ko ba alkhairi bane ina rikon allah ya mallaka min shi yayi shiru yana kallonta yana hadiye wani dunkukallen abu daya tsaaya masa a makoshi
“jikina yana bani zuciyarsa naga wata amman nasan kowacece bazata fini da komai ba sannan bazata zamo min natsala ba ,ga sako ka fada masa idan ma zai dawo da hankalinsa gareni yayi idan bazai dawo ba sai dai ya mutu bai yi aure ba amman ko zanyi yawo tsirara sai na zama mata agidansa domin shi din nawa ni kadai , idan baka sani ba na fada maka wani abu mahaifina ne ya taimaka masa har ya kawo matsayin da yake a yanzu amman dake shi dan adam masu manta alkhairi , yanzu kai a ganinka ya dace sakayyar taimako da mahaifina yayi masa ya fada akan wata bani ba …?


Sai allah ya kaimu byn sallah ayi sallah lafiya karku manta da naman sallahna lol love you guy’s






Mmn sudais






💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


🅿️39






......Tunda ta fara magana yake kallon bakinta yana jin wani irin zallar'bacin rai mai tsanani ,dan idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa bai wuce yaga ana shiga rayuwar jaguwa ba ko ai bantashi , bai sake ce mata komai ba har sanda ta gama magnrta , sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci fuskarsa ta canza daga farinciki da yake ciki zuwa bakinciki ,tayi shiru ta zuba masa idanunta tana kallon fuskarsa da sam babu annuri kwance akai
a hankali ya dauke kansa daga kallonta .”
cigaba da kallonsa tayi tana jiran taji mai zai ce mata ,ganin yayi shiru yaki cewa komai yasa
ta gyara tsayuwarta tace "da fatan zaka fada masa sakona?."bai kalleta ba ya furta "a'a bazan fada masa wannan sakon ba amman idan ke kinji zaki iya to Ki samesa da kanki ki fad'a masa watakilla ma zai fi fahimtarki akaina ". yana gama fadar haka bai tsaya jiran me zata sake cewa ba ya juya a natse ya nufi get din gidan, bayansa tabi da kallo yana taku a hankali shima kamar adnan din yake ta fada a kasan ranta ,komai nashi mai kyau da tsari to ya ma za’ayi abokansa ba zasu kasance kamarsa ba ?."Jiki a sanyaye ta juya ta nufi cikin gidan tana nazarin yanayin daya shiga a lokacin da take masa magana akan adnan "kamar bai ji dadin maganarta ba ?tayiwa kanta tambayar ,tabe labbabta tayi tana cewa "kar allah yasa kaji babu dadi aranka tunda zaginsa nayi da zaka wani ‘bata rai taja tsaki tare da shigewa ciki ."


Ahankali anas ya bud'e motarsa ya shiga ya zauna da kamar ya kira hally ta fito suyi sallama sai ya fasa ya kira layin ta yana kokarin yiwa motar key har ya bar unguwar suna waya tana zuba masa shagwaba lokaci daya yaji ta yaye masa dukkanin damuwarsa ,bai tsaya akoina ba sai a kofar gidan jaguwa yayi hon mai gadi ya taso ya bude karamin hujin get, ganin shine ya soma kokarin bude masa babban get ya sanyo hancin motarsa cikin haraban gidan mai gadi na daga masa hannu ,ya karasa inda yake parking din motarsa yayi parking ya kashe motar ya fito yana gyara zaman rigarsa adaidai lokacin da mai gadi ya gama rufe get ya karaso gurinsa cike da girmamawa har zai rusuna masa Ana's yayi saurin dakatar dashi yana cewa "haba baba sau nawa zance maka ka daina duka min ? ai ko baka haifeni ba kayi kani kusan na biyar dani please ka daina bana so ,ya fda yana mika masa hannusa ,gaishesa mai gadi yayi yana murmushin jin dadi dan ba yau bane karo na farko da anas din ke hanashi rusuna masa sabanin sauran ya amsa masa gaisuwar a mutunce kamar koda yaushe sannan ya nufi ciki gida yana shafa sumar kanshi ,binsa mai gadi yayi da kallo gabadaya rayuwarsa ta sake sauyawa ,kamala da natsuwa sun samu kyakkyawan zama ajikinsa har wata yar kiba yayi ta kwanciyar hankali ."




Zaune ya iske jaguwa zaune akan kujera a parlour ya daura kafafunsa saman table jikinsa sanye da jajayen kaya wando da riga yana operating laptop , cup din coffee na daga gefen laptop dinsa ,yayinda jabir ,
kamil da jubi suke zaune suna kallon wani film din soyayya mai suna kuchi kuchi hotahe, sai faman murmushi suke ,sallamrsa ce ta dawo da hankalinsu bakin kofar shigowa har shi jaguwa sai daya dago kanshi a natse daga kallon laptop da yake ya maida idanunshi kan anas dake tsaye yana dubansu alokacin murmushin farinciki bayyane akan fuskarsa yace "da dai kunje kunyi aure da wannan kallon da kukeyi ,a aure ne kawai zakuji gardin soyayyar gaskiya ba irin wannan na film ba wanda nishadi kawai zai dinga saka ku .” ya karasa maganarsa yana mikawa jubi dake kusa dashi hannu domin su gaisa still fuskarsa dauke da murmushin tsokana ."




jubi ya hade hannuwansu guri daya ya tsarke sosai yana cewa "kai ma ba wayonka ne ya baka auren ba , taimaka maka akayi aka baka ko kuma nace shishigi da nemana gindi zama da kutse acikin arayuwar wasu yasa akabaka aure if not da haka zaka mutu babu aure dan babu wacce zata aureka da irin rayuwar da kake ,ko ka manta kai din dan giya ne ? sannan kuma mane min mata ?."
"Idan ka manta na tuna maka wane ne kai ,mu ka barmu a yadda muke din nan yafiye mana dadi da wata rayuwar aure can wanda babu komai acikinsa sai takura ,wani dadi kake ji a aure da mu bama ji ?." ya tambayesa yana kafesa da jajayen idanunshi
“kwana kake da mace muma idan muna bukatar kwana da mace zamuyi ko ba haka ?”saurin maida idanu jaguwa yayi akan jubi wanda ke maganarsa hankali kwance yana duban sauran abokansu babu wata shakka ko fargaba daya nuna a fuskarsa .”
jubi ya cigaba da magana a zafafe "shasha yana da kyau ka dinga iya bakinka akan komai dan zakewarka tana dada yawa idan ba haka ba zaka tsinci kanka cikin nadama .”ya saki hannunsa ya fusace ya maida idanunshi kan kallon da yake wanda hakan yasa sauran basu samu damar furta abinda ke cikin ransu ba dan duk abinda suke son fad'a jubi ya rigada ya fad'a masa hakan kuma ya wanke zuciyarsu."

hakan nan maganar jubi ta caki zuciyar jaguwa sosai har ya kasa dauke idanusnhi akansa bare ya cigaba da aikin da yake sai daya maimata maganar jubi kusan so uku acikin ransa kafin ya dauke idanusnhi ya kalli anas da yake tsaye kikam yana kallonsu jiki a sanyaye ,a kallon da yake masa ya fahimci jikinsa da kafafunsa rawa suke ,shi kansa cikin tsananin kaduwa da bugawar zuciya yake cigaba da kallonsa yayi sam bai ji dadin kalaman jubi garesa ba haka zalika yasan anas din ma bai ji dadi ba dan gabadaya yanayinsa ya sauya amman yasan babu matakin da zai dauka ,nemo jarumta Ana's yayi ya sanyawa jikinsa.”


"Friend !".


Ana's ya kira jaguwa a natse yana sakar masa murmushin dole dan da zaa bude zuciyarsa bakinkirin zaa gani tsabar bacin rai ,jaguwa bai
amsa ba illa kallonsa da ya cigaba da yi ,shi kuma ya samu guri ya zauna a kusa dashi yana basarwa tamkar maganar jubi bata ta’bashi ba a kallon da yakewa jaguwa ya Karanci damuwarsa ,hargaginsa yake gani tamkar daminsa daya ga abinsa kuma yake shirin rasashi domin nuna masa bai ji haushi ya ba ya maida hankalinsa gasu jubi yace "kuyi hakuri frindes ban san maganata zata bata maku rai ba da banyi ba amman ni da wasa nake muku tunda nasan komai yana da lokaci shi aure kamar mutuwa ne idan .." dan allah malam ka rufe mana baki kasani mana “. Kamil ya katseshi yana zaro masa ido kamar zai cinyesa tare da jan tsaki ,anas ya dan kallesu a firgice zuciyarsa na buguwa da karfi ".
“Tunda kayi aure ka karo sabon wulakanci akan wanda kake yi ,sai wasu abubuwa kake yi kamr akanka aka fara aure ko zinariya ka aura iyakcin abinda zakayi kenan bare ba zinariya bace mutun ce dai kamar kowa da zaka wani damu mutane ."


tsam jaguwa ya tashi daga shi har laptop da coffee dinsa ya soma tafiya tun kafin zuciyarsa ta tarwatse dan bazai dauki wannan rashin mutuncin akan jininsa ba ,idan kuma yace zai cigaba da zama to lallai zasaka bakinsa kuma hakan zai sa su yi korafi akan yayi side din anas ,shima Ana's ya tashi tsam ya biyosa zuciyarsa ta tafarfasa sai dai yana ta kokarin tausarta.”
kusa atare suka shiga dakin jaguwa ya samu guri ya zauna a kujerar falonsa qirjinsa na zafi da ciwo shima Ana's ya zauna a gefensa ,jaguwa bai kalli inda yake ba haka zalika bai ce masa komai ba dan bakaramin haushi ya bashi shi kansa anas ya fahimci haka dan haka ya motsa bakinsa "kayi hakuri ya fad'a yana kallonsa cikin tsananin damuwa ."
Jaguwa ya dan ciza lip's dinsa na kasa da karfi "me yasa Ana's ?"
"Me yasa kake yin abinda banaso ?"Am so sorry adnan bazan sake ba kuskure ne ya fad'a jiki a sanyaye yana gyara zamansa yana qawalo murmushin dole "tunda sun nuna basa son kana shige musu me yasa bazaka hakura ba ? .”
“Ko dole sai ka tsokanesu? shiru anas yayi yana dubansa “.ya kamata zuwa yanzu ka san yadda zaka dinga yin muamula dasu tunda sun nuna basa son kana masu irin wadan nan zantuttuka na tsokana please ka daina ." murmushi stil anas ya sake yi yana cewa "shikenan an daina inshaallahu "kai fa baka daukar tsanar da suke maka a kwanakin da mahimanci ,ni kuma na dauke shi da mahimancin daya zarta tunanin jama'a ,a nawa tunanin ma gani nake sun tsaneka ne tsana mai muni amman dai nasan yadda zanyi da...... ".


"Kai haba dai kai kuwa karka yi wani tunanin dabam akansu nifa bana ganin laifinsu ko kadan sai namu,duk kai ne ka jawo komai daga lokacin da'aka boye musu maganr aurena na fahimci basu ji dadi hakan ba shima dalilin sauyawarsu gbdy ,kuma ko ni ne haka zanji babu dadi araina."
" duk da haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login