Showing 225001 words to 228000 words out of 259215 words
Chapter 76 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
bai kamata idan ma haka ne ai bai kamata su rike abun acikin zuciyarsu har haka ba ."lumshe ido anas yayi "babu komai zan sake basu hakuri kai ma ka basu hakuri mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba babu jin haushin juna babu kyashi ko hassada a junanmu sannan ya dauko wayar jaguwa dake ringing ya mika masa sunan da ya gani ne yasa ya ajiye wayar ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa yana kurba a hankali.”
kallon mamaki Ana's ya zuba masa sannan ya dauki wayar yana duba screen din wayar nan yaga sunan tanwer yana yawo ya waiga ya kalli jaguwa "ban fahimci kin daukar wayarta da kayi ba? batare daya kallesa ba yace "bashi da amfani ne shiyasa naki dauka "ya kamata kayi hakuri adnan haka ,komai na rayuwa fa mai wucewa ne wallahi this duniya is noting adnan yau idan mune gobe bamu bane yarinyar nan tayi nadama dan allah ka yafe mata tana sonka dayawa bazata iya rabuwa da kai ba yana da kyau kasan darajan soyayya me ye laifin wanda ke sonka ?.
"Babu !.
Ya bashi amsa atakaice "to why adnan kaima fa baka kyauta mata ba ,dan bai dace abinda kayi mata a gaban mutane ba ,kamata rashin mutunci a gaban saurayin da bata so sannan ka hadata da kalmar useless ai kowa ma kayi haka zai iya haukace maka .”jaguwa ya saki wani murmushi da ajiyar zuciya atare yana shafa gefen fuskarsa ko yanzu fuskarta ke masa yawo acikin kwakwa luwarsa ,ita kadai ce ta samu wannan matsayin acikin arayuwarsa, dan bai iya mantata duk abinda yake tana nan makale a ransa tana yawo a jinin jikinsa tun yana mamakin matsayin da take dashi a zuciyarsa har ya zo ya daina."
Sai daya numfasa kana ya motsa lip's dinsa "kenan ta kiraka ta fada maka na kirata da useless?".sosai kuwa dan abun ya dame ta matuka tana min bayani tana kuka "idan har ta fada maka daidai a maganata babu inda nace mata useless ,i said that who is doing that they will be thinking that is useless that's ol ,duk da haka dai bai dace ka fadi haka ba ,a natse Ana's ya dinga rarrashinsa yana bashi hakuri ya yafewa tanwer sannan ya amince da soyayyarta shi kuwa sai murmushi yake yake wa anas yana jijiga kafarsa daya ."
Ana's ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa "ka hakura ta kiranka komai ya wuce ?"Kira kuma na sau nawa ai tun jiya take kirana ban dauka ba dan banga amfanin kiran ba bare na dauka ,dazu da safe ma naga shigowar sakonta ya karbi wayarsa yana nuna masa sakonta ,"Assalamu alaikum ,Good morning how are you doing my love"how was your night ? hope you had a great night?let us thank allah for the gift of another day and please forgive me and forget what I did to you " girgiza kai kawai anas yayi yana cewa "kai dai anyi mugu mai taurin zuciya ,
yanzu kai bakajin tausayin yarinyar nan ?ya girgiza kai batare daya kallesa ba .
“Kaga kuwa ni ina jin tausayinta wallahi har hawaye nake zubar mata dan tana mutuwar sonka ,kaso mai sonka adnan ka tausaya mai sonka ko da yake ai kana sonta soyayyarta ma ta musamman ce a zuciyarka ya fada ta tsigar tsoka , jaguwa ya waigo ya kallesa a natse sai dai bai ce masa komai ba hakan kuma ya nuna bazai ce din ba “allah dai ya shiryeka sarkin zuciya da taurin kai jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa ,bari naje na sake bawa friend's hakuri magana ta wuce banason ina tare da mutane naga na bata musu rai “jaguwa yace “sauka lafiya aminin kirki .”anas ya mike ya fita daga dakin shi kuma ya cigaba da aikinsa yana murmushi yana tuna tanwer ".
Suna zaune har lokacin a falon ya samu guri ya zauna yana fuskantarsu sunga shigowarsa da zamansa amman sukai masa banza tamkar basu san da zaman mutun agurin ba ya gyara zamansa ya kirasu "friends!" amman babu wanda ya juyo daga cikinsu ya kallesa bare yasa rai zasu amsa masa "please kuyi hakuri idan akwai wani laifi da nayi muku yasa kuka tsaneni yanzu ,ni dan adam ne ta yiwu nayi muku Kuskuren bisa rashin sani amman ni atunanina idan nayiwa daya daga cikinku laifi kamata yayi ku kirani ya fad'a min domin in gyara kuskurena ,dan idan ni ne bazan rikeku araina ba zan fada muku komai ya wuce mu cigaba da rayuwarmu cikin soyayya da walwala ,dan allah kuyi hakuri ku yafe min ."
shiru falon yayi babu wanda yace masa uffan ya mike daga inda yake zaune ya karaso ya zauna akan table din dake tsakiyar dakin ya riko hannun jubi domin a komai shi ke fara daukar zafi "kayi hakuri abokina duk da wallahi ban san nayi muku laifi ba amman ita rayuwa haka take wani abu Kalilan zai iya kawo fitinar da zai shiga tsakaninka da kowa ya fad'a yana kallonsu daya bayan daya a tare suka sakar masa murmushi wanda da gani na yake ne "karka damu komai ya wuce inji cewar jubi "na gode Kwarai da gaske amman dan allah me nayi maku ?ina son sanin abinda nayi muku saboda na kiyaye dan gaba "me ye amfanin aita tada magana anas bashi da wani amfani allah dai ya yafemu gbdy jubi na rufe baki anas ya mike ya juya yana masu godiya sai ganin jaguwa yayi tsaye ya rungume duk hannunwansa a qirjinsa fuskarsa da alamun annurin farinciki dan yaji dadi kwarai da suka fahimcesa ."
"Ya ka tsaya ka karaso ka zauna ka karasa bayyana murmushin farinciki dake ranka?inji cewar kamil .
jubi yace "ai dole kaga farinciki a fuskarsa tunda anas ne bakaga dazu fushi yayi ya tashi ya bar gurin saboda an taba zuciyarsa ba ," ya karasa maganar yana fakar idanun jaguwa ya zabgawa anas harara dan shi hakurin dole yayi da yafiyar dole saboda ganin tsayuwar jaguwa daya gani ,kuma idan suna son cima burinsu akan anas lallai sai sunbi komai a hankali."
"ai dole na tashi na bar maku guri tunda naga abun naku har da wulakanci so kuke ku tarwatsa min zuciya, ga ciwa aminina mutunci ga tabo jinina ai abun yayi min yawa suka sa dariya gbdynsu a hankali ya cigaba da mgn yana takowa ya tsaya a tsakiyar falon "rayuwarmu a tun farko a tsare take babu wanda ke jin haushin wani hakan kuma yana min dadi ,wannan yace ayi kaza wannan yace ayi wannnan kuma duk muna bin tsarin juna babu mutsu ko jayya a yanzu ma yana da kyau mu cigaba a yadda muka dauko dan babu cin amana a tsakaninmu .”
“ban hana kowa aure acikinku ba ,wallahi duk wanda yake bukatar aure acikinku ya nemo mata zan tsaya masa da iyakacin karfina na taimakeku
sai dai idan abun ya gagareni idan kuma hakan ta kasance zan shigo da wasu ciki ayi komai cikin sauki da nasara .”
Yayi shiru yana kallonsu daya bayan daya yana nazarinsu alhamdulillah ya fahimci duk sun sauko daga mummunar fushin da suka jubi ya kallesa yana murmushi wanda bai kai har cikin zuciyarsa ba sannan bai jin zai canza daga idar da nufin sa,wani irin zafi yake ji acikin zuciyarsa "tunda ya basu damar aure yace mahaifiyarsa ta haifo masu mata kamar yadda ta haifawa Ana's wannan shine maganar dake kwance akan harshensa sai dai yasan matsawar yayi ganganci ta fito daga bakinsa allah ne kadai yasan maseefun dazasu faru ."
A natse jaguwa ya dinga jansu da hira yana bawa kansu shawarar har suka shigo da wata hirar cikin nishadi kowannensu na tofa albarkacin bakinsa shi dai anas yanata taka tsantsan da abinda zai fada dan hararar da suke fakar idanun jaguwa suna masa ya tsaya masa arai sallah ne kawai ke ta dasu har biyar tayi anas ya mike alamun zai wuce jaguwa ya kallesa “har zaka wuce ?ya gyada masa kai zanje na dauko hallay a gidan ammi mu wuce gida ,okay gobe ka shigo da wuri saboda fitar sconpio ya gyada kai sannan yayi musu sallama ."
*****
Karfe shida daidai a kofar gidan ammi tayi ma anas ya shigo a natse ya gaishe da ammi ,hally tana ganinsa ta mike tsam ta soma shirin tafiya ta dauki bakar ledar da ammi ta bata wanda yake cike da kayan sawa wanda ta dinka masu ita da shafiq sai wata leda dake dauke da magungun Kara ni!ima sukayi mata sallama hasera har bakin mota ta
rakasu suka shiga mota suka kama hanyar zuwa gida da zarar yaga tayi shiru zai tsokanota ita kuwa kewar amminta take dan ji tayi kamar karta koma gidanta ta cigaba da zama tare da amminta.
Ana's yayita kokarin kawar mata da tunaninta da hirar soyayyarsa mai cike da zolayar da ban dariya wanda yayi nasarar share dukkanin wata damuwar anas .
Suna shiga gida ta shiga gida dakinta ta ajiye kayan data zo dasu sannan ta cire mayafinta ta fito ta shiga kitchen ya biyo bayanta ya rike kugunta yana cewa "kada ki daura komai ki hutawarki zanyi mana order abinci hakan daya fad'a yasa ta ajiye abun kunna gas ta biyosa suka fito daga kitchen yana manne daita "sannu duk kin gaji ko?".
"Babu wani gajiya ina dai son hutawa ne ."yayi murmushi "ai gani indai hutawa kike son yi sai muyi tare ai zaki fi jin dadi yayi mgnr tana daura gabarsa a wuyanta ta hararesa tana cewa "kai ko".
"Ni ko me ? kodan na fiyye sonki dayawa haka allah yayi ni ni mai son hally ne kuma hakan abun alfahari ne agurina ta dan yi murmushi ya zareta ajikinsa ya fita bai shigo ba sai byn sallahr ishai wannan shine kaidarsa tunda ta tare a gidan baya shigowa sai yayi ishai ,a fadarsa tace mata ana karatu a masalacin dan haka yake zama har a idar da ishai sannan ya shigo, sai byn takwas da rabi ya shigo masu da lafiyayyen abinci byn sun ci suka makale juna suna kallo wannan daren ma sun more junansu cikin tsabanin so da kulawa ."
washegari bai tashi da wuri ba saboda gajiyar sex sai gurin karfe goma ya tashi da wani matsanancin ciwo kai ya dafe goshinsa da hannunsa daya bai tasheta ba ya shiga bayi ya fara sakarwa kanshi ruwa kafin yayi wanka a daddafe ya fito ruwa na kwance a sansar jikinsa still tana kwance cikin bargo tana baccinta hankali kwance ,ya goge jikinsa yana ciza lips dinsa ya shafa lotion ajikinsa yana sake jin yadda kansa ke mugun sara masa wardrobe dinsa ya nufa idanushi na kanta yana kallonta ya shirya cikin kananan kaya ya karaso ya zauna a bakin gadon yana kallonta tana sauke numfashi a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta yana jin kamar ya cigaba da mata numfashi ta huta .”
bakinsa ya kai daidai idanunta yayi kiss a hankali ta bude idanunta dake cike da bacci dishi dishi take kallonsa wani murmushi ya sakar mata yana dage mata gira "zan fita my princess sai dai wata killa zan dade yau ban dawo gida ba ki kular min da kanki .
Ahankali ta motsa lip's dinta "a dawo lafiya allah ya tsare min kai ,kai ma ka kular min da kanka please matsota yayi sosai Kmr zai shige jikinta dan baya gajiya daita ,suka dan zubawa juna ido ko kyaftawa basayi ahankali ta maida idanunta ta rufe saboda baccin dake cikinsu shima naunayen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike yana duba time agogon dake daure a hannunsa ya karasa inda ya ajiye wayarsa ya dauka yana kokarin sakata aljihunsa kira ya shigo ya daga "me kake yi ne har yanzu ?".
Da kyar ya bude baki yace gani nan fitowa yanzu "me ya faru naji muryarka haka jin muryarka ya daga min hankali?".
Ya nufi kofar fita yana cewa "wallahi da ciwon kai na tashi mai tsanani ban kwanta dashi ba amman na tashi dashi "oh sorry my dear ina hally take ?tana bacci ya fada yana shiga dakinsa ya zuge mirrow dinsa wata karamar kofa ta bayyana ya shiga ya dauki bindiga pestol ya soke ajikinsa "kana jina?
"Eh ina jinka ya bashi amsa yana runtse idanunshi "karka fito kayi zamanka a gida ka huta tunda baka da Lfy idan scopion ya dawo daga aiki zan zo da kaina muje hospital a duba min kai wannan ciwon kan yayi yawa "okay !"
“Ni kaina na fara tunanin ganin likita,okay shikenan
Amman ka bar wayarka a kunne bana son na kira naji akashe anas yace "to! ajiye bindigar yayi ya fito ya maida kofar ya rufe ya dawo falo ya kwanta dafe da goshinsa gurin karfe shabiyu saura hally ta tashi ta fara gyara dakinta sannan ta fito zuwa falo domin ta gyara turus tayi sakamakon ganinsa kwance dafe da goshinsa ,da sauri ta karaso gurinsa ta durkusa agabansa ta riko dayan hannunsa cikin nata tana murzawa wani zafi taji ya ratsata ."
Bude idanunshi yayi da kyar yana kallonta “kace zaka fita kuma zaka jima baka dawo ba ?ya lunshe mata ido “kaina ke ciwo bazan iya fita ba “sannu !.”
Ta fada tana dafe masa goshi “ka sha magani ma kuwa ?ya girgiza mata kai alamun a’a ta mike da sauri ta nufi dakinta tana cewa “me yasa zaka zauna baka sha magani ?.”
Yana kwance ta dawo hannunta rike da magani ta shiga kitchen ta dauko ruwan mara sanyi ta fito ta mika masa magani tana rike da goran ruwan ya amsa ya kai bakinsa ta mika masa ruwa tana masa sannu da kyar ya sha magani dan bai son shan magani sannu tayita jera masa tana jin kamar ta maida ciwon kanta ya tashi ya tafi inda zashi ya koma ya kwanta ita kuma ta cigaba da aikinta .”
Da misalin karfe daya daidai na rana sconpio suka fito tare da jaguwa zuwa haraban gidan suna magana kasa kasa wanda duk nacinka baka isa kajiyo me suke cewa ba ,jaguwa ya dafa kafadansa yana kallon shigar jikinsa , manya kaya ne sanye ajikinsa su bama su haske can ba haka zalika ba masu dotti ba , kansa har da rawani wuyansa zagaye da manyan carbi tamkar dai irin shirin da malaman darika suke kafafunsa rufe cikin black shoe’s ,
yadda kafafunsa suke rufe da bakaken takalmin haka jikinsa suke sanye da bakaken kaya rigarsa ce kawai multcolour amman hatta jeans din jikinsa baki ne gefe da gefen west dinsa na makale da bindigar pestol kai tsaye inda machinan aikinsu suke jere jaguwa ya nufa dashi ya damka masa key yana cewa “ka hau wannan .” ya hau wanda jaguwa ya nuna masa yana kokarin ta dashi yaji ya cigaba da magana “ka kula sosai scorpion banason kuskure a aiki sannan ka kula da abun kunnenka daga yadda yake din nan zan dinga jin komai dake tafiya haka zalika zan dinga ganinka ina maka fatan nasara yana rufe bakinsa scorpion ya nufi get yana tsaye agurin mai gadi ya bude masa karamin get ya fita sannan ya juya ya koma ciki hannuwansa duka goye a bayansa.”
Scorpion na fita cid ya kira headquarters na polisawa kai tsaye aka dauka da “hello ! “kana ina dcp ? Okay to kayi hanzari ku isa address din dana tura maka , yanzu haka yaronsa ya fita kuma shi kadansa kamar yadda na sheida maka naji suna tautaunawa, yana sanye cikin fararen kaya shirin malunta “dan allah karka bari mu rasa wannnan damar at least ko mutun daya muyi nasarar kama wa acikinsu .”
“karka damu zamuyi iyakar kokarin mu sannan ka tabbatar duk abinda ka gani ka daukar mana komai da komai akansa da yaransa a wayarka domin itace hujarmu ,da zarar ya shigo hannu sai mun tona masa asiri a idanun duniya ,shi kuma yaronsa idan ya shigo hannumu yaki bamu damar muyi binkice akan mai gidansa harbesa kawai zanyi mu huta.”
cid na katse kiran dcp ya shiga kiran yaransa daya bayan daya kafin kace me sun hadu a wani daki na musamman nan ya shiga basu umarni daman kuma a shiryensu suke kusan atare suka fito suka shiga motocinsu suka fita yayinda scorpion ya isa inda me gidansa ya aikesa cikin nasara ya samu guri nesa kadan da inda aka aikesa yayi parking bisa umarnin ogansa ya sauka akan mashin din ya soma tafiya a natse tamkar mutumin kirki yana jin jaguwa nace masa “karka kuskura ka waiga bayanka cigaba da tafiya kawai domin waigawarka zai sa polisawa dake aiki agurin suyi suspecting dinka sannnan ka fara neman taimako gurin mutanen dake kai kawo agurin .”
Bai yi magana ba ya kebe kansa gefe guda ya zaro daya daga cikin carbuna wuyansa ya soma ja yana motsa bakinsa a hankali yana mikawa mutanen dake kai kawo agurin hannunsa ,nan take mutane suka shiga mamaki ganinsa domin dai baa bara a kofar get din maaikatar hasalima korar masu bara ake agurin amman cikin ikon allah sai gashi shi ko kallonsa da tsigar kora babu wanda yayi ,wasu daga cikin mutane suka fara bashi sadaka yayinda wasu ke wucesa suna ganin wani sadaka zasu bashi bayan shi din ba nakkasashe bane kawai malunta ce tayi masa yawa ,wasu ma ko kallosa basayi ba .
wata mata ya hango sanye cikin doguwar rigar after dress yanayinta tsam bahausheciya tana daf da wucesa ya biyota da sauri yana rokonta “dan allah ki taimaka min da abinda zan ci saboda allah rabona da abinci tun jiya “ta tsaya tana kare