Showing 204001 words to 207000 words out of 259215 words
Chapter 69 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
yaron nan tanwer babu ni babu ke sai dai ki nemi wani uban bani ba, “to ai dady bana halaka da kowa bare batun soyayya ko Ibrahim ma ni a mutunci na daukesa daga baya kamai ya sauya ni adnan kawai nake so bayan shi bazan iya rayuwa da kowani nmj ba , da dashi na yarda na amince in zauna in mutu a gidansa sai dai bazan só naga kun samu sabani a tsakaninku ba “ karki ce bakya son mu samu sabani mana kina so dan gashi kin janyo uwar ki tana jin haushina bayan bamu taba samun sabani daita ba sai akanki “ina sonku iyayena bazan so naga kun samu sabani akaina ba kune farincikina kune garkuwa,bangon jingina agareni ,wallahi ina sonku domin kunyi matuqar kokari akan kuga tarbiyyarta ta gyaru wallahi dady nasani ban maka adalci ba amman ban san yadda zanyi bane dady ka min addua ko zan daina jin abinda nake ji akansa ta karasa mgnr tana fashewa da kuka “wallahi da akwai abinda zanyi na daina son shi dady zanyi dan nima na gaji da wannan wahalar sai kuma jikin dady yayi sanyi , jiki a sanyaye ya fito daga dakin dan bazai iya jurar ganinta tana kuka ba ya shiga dakin mumy tana zaune ya karaso ya bude kular abincin daaka kawo mata bata ci ba ya kalleta ta kawar da kai alamun bata son ganinsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta “kiyi hakuri uwar gidana na fahimci halin da kike ciki ,na fahimci son da kikewa diyarmu ne yasa kike son biye mata amman kisani baa rayuwar aure a haka zainba wallahi aurawa tanwer yaron nan bashine karshen matsalarmu ba .”
“ kiyi hakuri banason ganin tanwer cikin wahala ne duk abinda zai sameta dole ya sameni nan hawaye ya soma gangaro mata ba kakkautawa murya kasa kasa tace “kayi musu fatan alkhairi babu abinda ya gagari allah wannan auren idan ba alkhairi bane allah ya dakatar dashi idan kuma alkhairi ne fa ?
”inshaallahu ma bazai tabbata ba kawai ni abinda nake so dake ki tsaya a bazaa yi ba, Kiyi min wannan alkwarin “gaskiya bazanyi ba tana gama fadar haka ta mike ta dauki wayarta ta fito ta bar masa dakin babu kowa a falon sai tv dake aiki da ac ta soma tafiya a hankali tana karewa falon kallo har ta isa kofar dakin dake kallon nata wanda suke saukar baki ciki ta soma neman layin uncle bashir kira daya ya dauka cike da girmamawa tace ya hau online haka ma uncle jamil shi daman soja kullum yana online da wahala ka hau baka sameshi ba conference ta hadasu a vedio call kowannensu yana kallon danuwansa “na kiraku ne akan matsalar tanwer da wannan yaron adnan ,bashir ina ganin lokaci yayi da zan dauki shawararka na amince tanwer ta aure shi amman kai jamil da Aliyu me kuka gani akai ?”nan take uncle jamil yace “minister ya yarda da hakan ne ? ta sauke numfashi da karfi “bai yarda ba gskiya.
Yayi min daidai gsky nima ban goyo baya ba kai yaya saboda me zaka bata wannan shawarar ?” Wannan ai abun kunya ne da torzarci gsky karki amince aunty sam sam wannan shawarar batay ba mu dai san yadda zamu nisanta tsakaninsu idan garin zaa mu bari daita zuwa wata kasar to adai san yadda zaayi.”
“Shikenan kai Aliyu fa me zaka ce ?
“Ni dai gsky na yarda ta auresa idan dai har adnan din dana sani ne lallai zai rike miki ita da gaskiya wallahi adnan din danasani me kirki ne dasanin yakamata…”kai dan allah malam ka rufewa mutane baki maganar riko akeyi ko sanin yakamata ?” ya katse shi ta hanyar fadar haka “ana magana ne akan sana’arsa duk kirkinsa tunda bashi da hali ai na banza ne “ni kaina banason auren nan jamil amman da ta dinga binsa suna aikata zina suna ciki ana cirewa me zai hana mu taimaka masa tunda muna da halin yin haka “ kayi hakuri kaji kanina nasani abun akwai ciwo amman ya zamuyi da qaddara?ta karasa maganar tana zubar da hawaye nan fa duk suka rude suka shiga rarrashinta “ban taba tsamanin rayuwarta zata dawo haka ba tanwer da kanta ke binsa kuma nasan da wahala su hadu wani abu bai shiga tsakaninsu ba ,nasan tanwer nasan yanayinta sai dai kawai na share dan yin maganar bashi da amfani sun dan dade suna tautaunawa a karshe dai dole jamil ya sadaukar ya hakura suka amince akan ta auresa wannan yasa mumy taji kwarin gwiwa suka sallama ta fito ta nufi dakin tnwer ta murda handle ta kusa cikin dakin alokacin tanwer tayi zurfi cikin tunani .”
ta zauna kusa daita tana shafa sumar kanta a dan firgice ta waigo suka hada ido daita mumy ta sakar mata murmushi itama tanwer murmushi ta sakar mata mai hade da kuka "na amince da zabinki tanweer ,na amince ki auri adnan kice masa ya turo iyayensa ..”tanweer tayi tsuru tana duban mumy tana jin mgnrta kmr a mafarki kafin daga baya ta mintsini fatan jikinta domin ta tabbatar da mafarki take ko kuwa gaske ne abinda taji mumy ta fada .
"tunda kin amince kina son Adnan kice masa ya turo magabantansa suyi magana da mahaifinki karasa mgnr hawaye na zubawa daga kwarnin idanunta .”allah yasa yayi miki adalci tanwer amman kiyi min alkawari zaki yaki sanarsa kafin aurenku “nayi miki alkwari mumy .”
zuciyarta tanweer sol da jin abinda mumy tace nan take ta sauko ta durkusa kasa gabanta tana kwalla tace "na gode mumy Kuma Ina Kara baku hakuri dan Allah ku yafe min Mumy ta share hawaye tana cewa "ai ya wuce tanweer amman kibi a hankali banason ki Kara zuwa inda yake kice masa ya dinga zuwa , hawayen farinciki ta dinga zubawa muryarta a sanyaye tace “mumy dady ya amince ne ?
Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke tare da cewa “eh yanzu nayi masa magana ya kuma amince tana gama fadar haka ta mike ta fita .”
Tana fita tanweer ta soma neman layin jaguwa amman wayarsa bata shiga , dole ta hakura ta fito da gudu ta nufi d'akin rukayya tana shiga ta kamo hannunwata duka cikin nata ta fara juyi daita acikin d'akin tana cewa"yau dai naga amfani addua ruky mumy da dady sun amince na auri Adnan rukayya ta kamota ta zaunar daita "Kai amman na tayaki murna Allah ya tabbatar da alkhairi rukayya tasan tanweer nason adnan sosai amman batasan dan fashi bane daga mahaifinta sai mahaifiyarta da kannenata da alhj Usman ne suka san da wannan maganar washegari da farinciki ta tashi ta tafi aiki hatta maaikatanta sun fahimci halin da take ciki na samun sukuni sai dai babu wanda yasan abinda ya jefata cikin farinciki a office dinta ma a qalla ta kusan minti talatin tana neman layinsa ko dan tayi masa albishiri amman bata samu ba haka har washegari numbersa kawai take kira but no answer a lokacin shi jaguwa yana kan wani aiki daman kuma idan yana kan aiki bai kunna wayoyinsa har sai ya kammala abinda dake gabansa sannan ya kunna waya .”
*******
Karfe goma na safiya anas bai yi shirin fita ba kamar yadda ya saba sai kallon dayasa gaba yanayi sosai hankalinsa yana kan film din dan ko motsin kirki bayayi hally wacce ta fito ta zauna kusa dashi more than 30 minutes ta rasa mai yake gani aciki har ya dauki hankalinsa ta dai kara arawa kanta lokaci ta cigaba da zama tana bin katuwar flazma din da kallo tana karanta translation din tana fuskantar film din amman sam bata gano wata maana da zata saka mutun ya dauke hankalinsa kacokan akan film din ba .”
Ya dan gyara zamansa lokacin da yarinyar cikin film din ta fito daga cikin ruwa kayan jikinta sun manne ajikinta surarta ta bayyana sosai ta dan saci kallonsa cikin kunyar data shigeta na ganin wannan yarinyar wani murmushi tagani a fuskarshi ji tayi zuciyarta ta buga nan take ta hade rai “wai meye amfanin wannan kallon da kake ina ganin gara kayi abinda ya dace ?” .ya waigo ya kalleta ya kawar da kanshi yana karantar abinda ya bata mata rai ya dauki remut yayi rewarning ya dawo baya kadan daidai inda yarinyar ta fito daga ruwa ya tsaya ya cigaba da kalla har aka dauke gurin sannan ya dawo da idanunshi kanta bai damu da cikar da take tana batsewa ba dan daman da biyu ya sako film din ya cigaba da kallonsa ganin haka ta tashi tsam ta koma dakinta ta kwanta wani takaici ya ziyarceta damuwar da batayi zato akan anas ba ta dabaibayeta wannan shine kishi itama ta fuskanci hakan amman bata san hanyar da zata kawar da kishin nashi ba .”
Bata jima da kwanciya ba ta tashi da niyyar ta leka domin ganin ko har lokaci yana zaune a hankali ta bude kofar ta turo da kanta waje nan ta fara jiyo tahowarsa sosai suka hada ido dashi kuma tasan ya ganta da sauri ta koma cikin dakin shiru bai shigo ba kunya kuma sai ta hanata sake yunkurin fitowa amman a yanzu kunyarsa da take ji bazata kaita ga hanata kawo abinda zai kawo masa farincikiba .
Dan haka ta daure ta fito parlour alokacin ya gama kallon ya mike akan doguwar kujera da “alamun yau dai babu inda zashi domin ko wanka baiyi ba ta zauna kusa da kujerar da yake kwance ta dube shi anatse “amman dai yau babu inda zaka ?ta fada tana kallonsa kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya dago kai “me kikagani? Ya dawo mata da tmbyr ta dan dauke kanta daga kallonsa saboda kasa jure hada ido dashi tace” aa kawai dai na ganka ne kwance baka da alamun fita “mai zai hanani fita tunda zaman gidan ba wani abu zai amfanar min dashi ba kiran yayanki kawai nake jira na kama gabana “.
Magana ya fada mata d’an haka ta maida kanta ga kallon kofa fuskarta ta sauya launi sai taji batayi masa tambayar abinda shima ya lura dashi kenan ya dai dan samata ido yana kallonta ganin ta juya tana kallonsa ya dauke idanu shi ya cigaba da yin shiru kamar mai bacci ta mike a hankali ta nufi kitchen dan rana ta fara shadaya da rabi tayi zuciyarta babu dadi duk abinda yayi mata bata bashi laifi ba kanta ta bawa domin kuwa ita ta masa laifi T unanin yadda zata shawo kanshi ta nuna mishi qaunar da yake muradi daga gareta itace halalinsa halaka malak dole yana da bukatarta, ita kanta zuwa yanzu tana da bukatarsa amman bata jin zata iya kai masa kanta bazata iya wannan rashin kunyar ba sai daga yanzu a shirye take duk lokacin dayazo zata faranta masa rai ta nuna masa itama tana kwadayinsa domin ta tabbatar hakan zai dawo masa da walwalarsa .”
da damuwarsa bata wuce nuna koinkuka da take masa ba har ta isa bakin barandar da zata kaita kitchen ta dan juyo ta dan saci kallon fuskarsa,
idanuwanshi tsaye kyam abayanta ita yake kallon ,suna hada ido ya kawar da kai cikin nuna rashin kallonta .
Ta tsaya tana kare masa kallo ta tuna maganarsa kuma ta gasgantashi laifinta kunya tabbas ba karya yayi ba dole akwai muradina a tattare dashi ya zama dole ta cire kunya da tsoro ta bashi hakinsa sai dai ita kunyar ba zata barta ta kai masa kanta ba koda kuwa rike hannunsa ne tayi murmushi ta fice ta shiga kitchen tana tunani rayuwarsu da suka gudanar , to abu ne duk an hada da yarinyata sai hakuri dan ita din duka shekarunta basu wuce sha bakwai ba dole daman a samu irin haka bugu da kari bata da waye wa irin na matan daya saba muamula dasu .
Tana tsaka da aiki taji alamun tsayuwar mutun ta juyo bayanta shi ta gani tsaye yana kallonta ta juya sosai ta kallesa sai taga ya shafa sumar kanshi tare da kiran sunanta “hally !
Ta amsa hade da bashi duka hankalinta tana tsamanin akwai abinda zai sanar mata ya tsura mata idanunshi yana kallonta “jikina yana bani kamar kina fushi dani ?
“Fushi kuma da kai da akai yi me zanyi fushi da kai ?ya dan tsotsa kai kawai ya juya tayi murmushi kafin yayi nisa tace “am mai kake son a girka maka ?bai juyo ba yace “komai ma .”
Ta dan yi turus amsar shi bata mata dadi ba dan tun da ta soma girki abinda yake so take girka masa ta share ta cigaba da aiki ta taliya ta zaba ta girka domin ta fahimci yafi sonta ta hada komai sannan ta fita dan bata d’an lokaci baya falon amman da zamanta bai fi minti uku ba sai gashi ya fito daga dakinsa tana son ta faranta masa rai amamn ta rasa ta ina zata fara da me ma zata fara wani abu yazo mata rai dan haka tayi hanzarin daidaita natsuwarta “tun dana tare ko sai daya banga an gyara dakinka ba ko baka bukatar a gyara maka ne ?
Ya dan dubi kofar dakin ya kawar da kai yace “shi dakin ne baya bukatar a gyara shi ba mai shi na amsar daya bata sam bata mata dadi ba amman kuma saboda me bai bata amsar data dace daita ba“?
“Ko me yasa dakin baya bukata ?
Saboda babu wani abu da akeyi ajikinsa komai daidai ne very nit .”
Ta rausayar masa da kwayar idanuwanta cikin tsigar harara tace “ to amman dai naki ko baa komai acikinsa bai kamata a wayi gari batare da an gyara shi ba “shi dai wannnan dakin baya bukata gyara ya fada cikin son abar maganar dan tunda ta nuna bata bukatarsa shima zai barta bazai dameta ba yadda ya share ya bar maganar haka itama ta share a ranta tace wannan dabarar bata yi ba uhm wane ma zatayi duk wanda ta dauko zatayi baya karbarta yadda ya kamata tsam ta mike ta koma kitchen ta sauke abinci ta shirya yadda ya kamata a food flaks ta fito dashi akan faranti ta ajiye shi a table ,duk da tasan ba yanzu zai bukata ba amman sai data tsokano magana “ga abinci fa har yayi .
Bai bata amsa ba jaguwa ya shigo sai dai ya zube akan kujera kamar bai ganta ba ya dauke kanshi suna gaisawa dashi ta mike ta koma dakinta ta dauko mayafi ta yafa tazo suka gaisa kallo daya yayi mata da amsa war ma ba a wadace ba, ganin haka taji gabanta ya fadi tasan ba haka ya saba mata ba duk yadda akayi tayi laifi tunda ba yau tasan shi ba shekara d shekaru tasan halinsa muddin ba wani laifi tayi ba bazai mata haka ba ko Ada can idan suna son su gane ammi ta fada masa sunyi laifi daga amsa gaisuwarsa suke fahimtar ta fad’a masa .
Hira ce ta barka a tsakninsu ita dai tana jinsu sai dai tabi duk wanda yayi magana da kallo gbdy ta rasa abinda tayiwa yayanta da yau yayi mata haka gbdy Ana’s shima ko kallonta bai yi ba sai ma sako labarin film din daya kalla yayi ta mike ta basu guri tana tashi taji ya sauya hira tana zaune a daki dake bata rufe kofar ba tana jiyo wata hirarsu wata kuma tana wucewa anan itama ta shiga hira da zuciyarta yadda zata samo kan mijita dan ta lura tsiraicin da yarinyar film din dazu tayi ya burgeshi ya matukar daukar hankalinsa akanta ,dole ta kawar da tsoronsa da fargaba da take ji tunda da kanshi yaso su kasance tare itace kawar dashi rike hannunta idan yayi zarewa take ya zama dole tayi wani abu .”
shiru tayi tana tunanin kayan da yarinyar ta saka cikin film kaya ne matsasu masu nuna siffar jiki Kuma ko shafiq ta sha fad’a mata alokacin ana shirin bikinta irin shigar daya kamata ta dinga yi kenan muddin yana gida amman kuma batayi amfani da abinda ta fada ba koda kwanciyar barci zatayi ta nuna mata irin kayan da zatasa amman sai taki koda ta saka sai saka kayan da zasu rufesu wannan yana nufin da bataji maganarta ba kuma dole da laifin hada matsayinsa datayi da yayanta ta tashi ta ta bude wordrob din kayanta idanunta ya sauka a inda ta jera kayan bacci ta fara dubansu daya bayan daya wacce zata saka mashi yau, duk wanda suke gurin da zarar ta kalla sai ta sauke ajiyar zuciya ta jinjina kai tana hango girman abinda zai biyo baya .”
Har ta gama bataga wacce zata iya dauriyar sawa ba tayi tsaye jikinta à sanyaye wannan ita kadai ce hanyar da zakibi ki jawo hanakalin mijnki gareki dan Samar masa farinciki wata zuciyar ta kawo mata nata agajin.
Akwai kananun kayan daya siyo mata atarewarta gidan bata jima da fara dubasu ba taci karo da irin kayan da yarinyar film ta saka sari ne mai sharara ta tsura wa matar dake jin kwalin ido shigar iri daya ce dana wannann matar ta film kayan ya rufe mata jiki amman fa koina ya fito ya nuna kodan da ruwa ajikinta ne batasani ba .
Ta dan yi murmushi domin hangota datayi aciki kayan ta ajiyeta gefe yau zata ajiye kunyarta da tsoronsa ta saka mashi wannnan kayan ta rufe komai ta shiga bayi jin har an fara kiran sallar azahar tayi alwala alokacin har sun fita ta gabatar da sallar bayan ta idar shiru basu dawo ba abincin ma basu ci ba haka tayita jin haushi amman koma menene laifinta take gani taci nata har bayan laasar bai dawo ba ita kuwa tana zaune