Showing 171001 words to 174000 words out of 259215 words

Chapter 58 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16589

ya fada ma matarsa cewar ya bamu kudi ajiya ba .
Wata biyu daya wuce ina zaune sai alhj usman ya kiramu yace mana wanda ya kashe alhj Abdulaziz ya kirasa yana tambayarsa kudin daya bamu ajiya da budar bakina nace masa yayi blooking dinsa hakance ta kasance yayi blooking dinsa tun daga ranar duk number daaka kira mu dashi muddin ba suna bama dauka ana cikin haka sai wasu da bamu san ko su waye ba suka fara bibiyarmu har sukayi nasara akanmu a yanzu dai gbdy babu wanda baa karbi kudi a hannunsa ba a yanzu abinda ya tsargu a zuciyata duk yadda akayi wanda ya kashe Alhaji Abdulaziz ne ya turo wadan mutanen ya karasa maganar yana Jan dogon numfashi tundaya fara magana dcp da kwararrun maaikata dake fuskantarsa suke sauraronsa har sanda ya dasa aya..”
Suka numfasa atare saboda maganarsu ta bambamta abinda garunmallam ya sheidamusu a wancan ranar da dabam abinda shima ya fada musu dabam suka tsura masa ido yana goge zufar rashin gsky dake tsatsafo masa sannan suka mike suka bar dakin zuwa wanda aka ajiye alhj usman suna shiga kowanne ya samu guri ya zauna akan kujera daya daga cikinsu ya kunna abun daukar magana “da fari ya sunanka?sunana alhaji usman “Meye sanarka ko aikin da kake ?ni tsohon farm sectry ne ,bayan nayi ritaya na koma harkar kasuwanci .
“Meye halakarka da marigayi alhj Abdulaziz ?abokina ne tare mukayi karatu dashi,meye sanarsa?shi dan siyasa ne,babu wata halaka ta kudi dake tsakaninsa dashi?shiru yayi gabansa na faduwa saboda tsananin tsoron tambayarsa daake sai daya dauki sama da minti goma sannan yace “aa.
“Ko kasan irin mutuwar da yayi da inda ya mutu “wannan wace irin tambaya ce ? “ ka tambayeni halakarmu na fada maka bayan wannan ni ban san komai ba dan banga abinda ya hadani da sanin irin mutuwar da yayi ba da kuma inda ya mutu ni dai ance min ya rasu kuma munje munyiwa iyalinsa taaziya shikenan iya abinda nasani kenan “.ya karasa maganar yana goge gumi dan gudun ac dake aiki a dakin bai hana gumi tsatsafo masa da alamun shima dai karya ya shirya musu gbdy suka tattara bayani suka nufi dakin cp “sir gbdy bincikenmu a yanzu ya nuna mana wadan mutanen masu laifi né zaa tabbatar da haka ne idan aka tsananta bincike akansu dan ina ji araina akwai boyayyen abu da suka haka suka binne a tsakaninsu damu bamusani ba .
“babu shakka akwai kuma boyayyayen abun ba komai bane illa sun taru sun kashe mutumin nan dan su dannen kudinsa haka zuciyata tafi raya min cp ya fada cikin zafin rai yana jujjuya a hankali akan kujera “karka samu damuwa zamu tsananta bincike yanzu bari mu hadasu guri daya .
cp yace “kuje kuyi abinda ya kamata duk suka juya cike da girmamawa office dinsu na bincike suka shiga suka fara tsara yadda zasu bullo musu sun dauki sama da awa daya suna tautaunawa sannan duk suka mike a wani babban daki aka hadasu babu wanda bai firgita da ganin danuwansa ba,a yanzu suka fahimci anyi haka ne domin suji bayanin kowannensu allah kasa babu wanda ya tona sirrin daaka binne a tsakaninsu gbdynsu kana kallonsu kasan sun shiga cikin tashin hankali matuka “.
jiki a sanyaye suka samu guri suka zauna gaban kowanne daga cikinsu yana dukan uku uku .




“Me yasa kuka taru kuka Kashe alhj Abdulaziz ? sam ba haka bane yallabai,” alhji sani ya fada a firgice “haka né mana kune kuka kashesa “.garunmallam yayi shiru gabansa na faduwa ya kasa cewa komai ”ku fada mana gsky me yasa kuka kashesa ? mu bamu kashesa ba wannan karon suka hada baki su biyar gurin fadar haka”karku manta yiwa dansanda karya babban laifi né domin idan ya gano gsky da kansa hukuncinsa zai zarta laifin da yayi dan haka muna jinku ku fada mana gsky kune kuka kashesa”.?
Juyin duniya suka tsaya akan basu ne suka kashesa ba “me yasa kuka danne masa kudadadensa to “?shiru suka yi “me yasa kuka takura masa lallai sai ya siyi fili alhalin bashi dashi har kuka hada masa da asiri ?nan ma shiru suka yi .
“Me yasa kuka nemi ku juya masa baya alokacin da yace bazai siya filin ba?duk duniya babu wanda ya yarda dasu tamkarku me yasa ya kawo maku kudadensa ajiya kuka danne ?idan kuma duk kunce ba haka bane ku fada min gskyar abinda ya faru kafin mu fada muku yadda kuka bi kuka kashesa saboda mun san komai akwai sheidu a hannunmu yanzu ya rage naku ku fadi gsky ko kuma mu mufito da gskyar da kuke boyewa .”
Shiru babu wanda yayi magana acikinsu sai zufa data rufe kowannensu gbdy tattare suke da tsoro da firgici alhj sani ya kalli alhj usman shi kuma ya kalli garunmallam haka suka dinga kallon juna “wannan shi ake kira da anyaka tatashi “bari mu tashi mu baku guri kuyi shawara a tsakaninku amman fa kusani mun san komai “.wanda ke maganar yana gama fadar haka ya mike tsaye ya shiga tattara kayan aikinsa har ya juya alhj sani yace “tsaya!
cak ya tsaya tare da juyowa ya zuba masa ido yana sauraronsa “kana ji ko”.
,ami’an bincike wanda ake kira da Interlleget suka cigaba da kallonsu suna karanta yanayinsu,zamu iya gyarota cikin sauki ku fada mana abinda zamu baku a rufe case din nan, grgiza kai habib yayi a ransa yace “tabbas sun aikata abinda ake zarginsu dashi amman dake suna da matukar wayo gyarota suke son ayi muryarsa a fusace yace “kaga munyi muku kama da wadan da zaku bawa cin hanci?duk jami’in dake zagaye daku babu wanda zai anshi cin hanci a hannunku ku dai ku fadi gsky domin mun san komai .
Yana gama fadar haka ya juya sauran ma suka rufa masa baya suna zaune suna kallon tafiyarsu har suka fice daga office din , sannan suka dawo kallon juna suna tunanin yadda zasu kubuta batare da asirinsu ya tono ba “wannan fa shi ake kira anyanka ta tashi “.


******




Ahankali jaguwa ya fito daga cikin motarsa range rover ya tsaya a bakin titi mile 2 sanye yake cikin kananan kaya riga light blue da bakin wondo gaban rigar bai kulle botir guda daya daga sama ba wanda ya bayyana farar singlet dinsa ,kunnensa manne da waya ,yana cewa "shikenan abu salma gamu mun karaso yanzu haka ina kasan gidan kai nake jira musan yadda komai zai tafi cikin tsari .
“no wannan ba matsala bane agurina wuyarta mu samu damar shigowa komai zai tafi daidai yana kokarin cire wayar a kunnensa on-expeting ya jiyo sautin muryarta ta bayansa "adnan dina ......"
A hankali ya juyo bayansa alokacin har ta karaso kusa dashi sosai suka fuskanci juna wata irin soyayyarta ce ya taso masa daga zuciya yana jin idan babu ita wani mummunar abu zai samesa gdy sai yaji qirjinsa yayi masa nauyi .
ajiyar zuciya suka sauke alokaci daya "ina yini ?ta fada cikin sanyayyar muryarta wacce ta sake kashe masa sansar jiki dan gbdy ji iyayi Kmr ya fixgota zuwa faffandan qirjiinsa yayi mata kyakkyawan masauki .
Kanshi kawai ya samu damar gyada mata yana kallon mutun biyu din dake tsaye abayanta suna kallonta “ yaushe ka dawo ?
“ tun last week ya fada ataikaice ,okay amman shine baka nemi ba gashi kona kiraka baka dauka,baice mata komai ba ya cigaba da kallon bayanta.
a hankali ta juya taga su rukky da muyis yake kallo,” nida yaruwata rukayya ne da doctor muyis abokin aikina munzo mu dan yi siyaya ne daga nan mu wuce gurin shakatawa "fuskar macen bai santa ba koma yace yau ce rana ta farko daya fara ganinta, shi kuwa nmj bazai taba manta face dinsa ba ya taba ganinsa a office dinta ranar daya je daukota ya kaita gidansa aduba masa ita.
"Muna tsaye na hangoka shine nace nazo ,naji dadin ganinka sosai tayi mgnr tana sauke numfashi.


shiru yayi yana kare mata kallo tsab tun daga Samanta har kasa sanye take da doguwar riga ja tayi rolling kanta da bakin mayafi haka takalman kafafunta da agogon hannunta da jakarta duk bakake tayi kyau sosai duk tafi lokutan baya daya saba ganinta kyau sai dai ta rame ,cike da shaukinsa ta kamo yatsun hannunsa cikin nata "muje tare mana"?ya girgiza mata kai yana jin tashin hankali daga cikin , haka nan ya dinga jin zuciyarsa na zafi baya raba dayan biyu na ganinta da wancan sokon abokin akin nata ne.
"pls mana zanji dadi idan mukaje tare "shi wancan katon fa maye amfaninsa kiji dadinki dashi mana "karka min mummunar fahimta ka rigada kasan komai kasan kaine zuciyar surayya babu komai acikinta sai...."
“Shiiiiiii ya dakatar daita aiki ne mai mahimmanci ya kawoni"zan jiraka .
Yayi murmushi daga cikin zuciyarsa "karki jira domin kuwa bansan lokacin da zan dauka ba ke bani da ma tabbaci lokacin da zan dauka zai fi kyau ki kama gabanki karki jira ni".
Shiru tayi tana dubansa tare da nazarinsa da nazarin maganarsa gbdy ta lura bai ji dadin ganinta da doctor muyis ba kishi ne daskare a cikin kwayar idanunshi amman da yake shi din tsayayyen mutun ne mai dakiya da dauriya zuciya yasa ba kowane zai gane hakan ba.


shima shiru yayi yana kallonta cikin yanayi na tashin hankali qirjinsa na mugun bugawa fiyye da kaida har sanda abokansa da yaransa suka firfito daga cikin mota suka ya tsaya suna dubansu a tsanake ,domin a kullum tana burgesu ta yadda take sonshi da rashin nuna kyankyamisu .
Da hannu ta gaishesu sannan ta juya a hankali tana cewa
"shikenan sai anjima allah ya tsareka .”
kansa kawai ya gyada mata yana kallon bayanta a hankali ya lumshe idanunshi yana jin wani zirrrrrrrr a gbdy ilahirin jikinsa gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa gashi dai shine ya bata damar tafiya amman ji yake Kmr ya hanata sosai abubuwan da suke faruwa atsakaninsu idan sun hadu ya shiga dawo masa uwa uba kamshin turarenta .
tafiya take a natse tana waigensa wannan shine karo na farko da taganshi da rana akan aiki dan babu tantama fashin rana suka fito yi , ko kuma tsara yadda fashin zai kasance kafin lokacin fashin.
Murmushi ta sakar masa shima bai san sanda murmushi gefe baki ya subuce masa ba kuma har lokacin bai dauke kwayar idanunshi akanta ba ,yayinda doctor muyis ya zama dan kallo yana ayyana duk yadda akayi wannan hadadden gayen shine ya sace zuciyar surayyarsa .
A hankali sky ya matso kusa dashi "a yanzu na sake fahimtar wani abu a game da kai da yarinyar nan a duk sanda oga anas yayi magana akanta sai inga kamar karya ya fahimta akanka saboda a lisaafina baka da wannan lokacin amman a yanzu dole itama a dinga bata girma na musamman.
jaguwa ya juyo a natse idanunshi na kansa yana kallonsa fuskarsa dauke da murmushin soyayya wanda shi kanshi bai san sanda ya bayyana akan fuskar ba , sai dai jin abinda sky ya fada ya dauke wuta dip kamar an aiko masa da sakon mutuwa fuskarsa ta sauya daga murmushi ta koma kamar ta zaki babu shiri Sky ya kama kansa tare da juyawa da sauri .


Shi kuma ya sake juyowa inda tanwer take adaidai lokacin data sake juyowa idanunsu suka hade cikin juna yana tsaye ya tura duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa ,Tana tafiya tana kallonsa cikin haka wata mota marcend tayi awon gaba daita kafin kace me tanwer ta zube a tsakiyar titi cikin tsananin tashin hankali yayo kanta da mugun gudu ya tsallake mai kekenep din daya sha gabansa ya karaso inda take kwance a gefen titi ya durkusa a gabanta yana taba ta yana kiran sunata "tanwer !!!
sai dai ina tuni tafita haiyacinta" sky magnet eku anas ku taimakeni ku tada mota mu kaita hospital"
“anas ka hanzarta mana dan allah kayi sauri gbdynsu sun rude sun gigice ganin halin da tanwer take ciki da tashin hankali mai gidansu duk suka nufi gurin motorsu .
haka ma rukayya ta shiga tashin hankali ta durkosa gabanta tana kiran sunata "inna lillahi tanwer still shiru .
doctor muyis ya matso shima hankali sa a tashe zai amshi tanwer a hannun jaguwa yaji saukan wani lafiyayyen mari a hannunsa bai sanda ya mike tsaye yana shafa hannunsa yana kallonsu ba .
Cike da tsananin tashin hankali jaguwa ya dauketa ya rungumeta tsam ajikinsa hankalinsa a matukar tashe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa sbd ganin jini ya wanke mata fuska tun kafin ya karaso gurin motorsu tuni an bude masa gidan baya ya shigar da gangar jikknta sannan ya shiga .


rukayya tashiga gaban motar ta zuna tana waigen tanwer ta baya.
A hankali ya daura kanta a saman cinyoyinsa hawayensa na dinga a fuskarta yayinda eku ya ja motar da sauri su Ana’s suka shiga motar haya suka biyosu abaya .
Sosai ya rike kanta tare da mannawa a qirjinsa yana shafa sumar kanta dan tuni mayafin da tayi rolling din kanta dashi ya cire muryarsa cikin tashin yake bawa eku umarnin qara gudu .
Sosai motar ke gudu amman shi gani yake sam bata gudu yasa hannunsa ya dauke hawayensa ya rungumeta tsam ajikinsa .
wani asibiti dake kusa suka nufa daita ,motar na tsayawa ya fito rungume daita ya nufi cikin hospital din yana kiran sunan doctor da karfi..”


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




Mmn sudais




💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


🅿️32






……….Gabadaya ilahirin jikinsa tsuma yake yana kallon fuskarta ga wani irin gumi na tashin hankali dake tsatsafo masa , gbdy ya gama rikicewa sai cewa yake “doctor’s please save her life, dan allah ku taimaka min karku bari ta mutu , yayinda rukayya da anas ke binsa abaya cikin tsananin tashin hankali tanwer baiwar allah kuwa bata ma san halin da’ake ciki ba , likitoci guda uku sukayo gurinsa suna tamabayarsa ganin jini na diga har ya bata masa jiki sukai saurin nuna masa wani daki da aka rubuta emargency yayinda rukayya ke wani irin kuka tana sake neman layin mumy .
Jaguwa ya shigar daita dakin ya shimfideta akan gadon idanunshi sunyi jaa sosai yana kokarin zare hannunsa yaji ta rike masa yatsun hannu gam.”
ya tsura mata ido yana kallonta yaga still bata cikin haiyacinta hasalima bata san ta rike masa hannu ba ,dr yace “dan sakar mata hannu mu bata taimakon daya dace “kuyi mata duk abinda zaku mata agabana babu inda zani , suka sake bashi umarnin fita “bafa zan fita waje na tsaya na barta tana shan wahala ba, ya fada arikice batare da ma yasan me yake yi ba ,yana tsaye aka mata allura aka goge jinin goshinta sannan aka fara dinke mata goshinta dake tsiyayar jini har lokacin .
wani qara ta saki sannan tayi shiru bata sake motsawa ba”.tausayinta ya kamashi bai ankara ba yaji saukar hawaye akan kuncinsa yana sake rike mata hannu dr dake tsaye rike da kayan aiki tayi masa kuri da ido tana kallonsa a zuciyarta take yaba irin wannan tsantsar soyayyar da yake mata jaguwa bai bar dakin ba yana tare daita har aka gama treatment aka daure kafarta daya da bandej sannan aka canza mata daki “


Jaguwa,anas,kamil duk suka shigo dakin daaka kwantar daita suka zuba mata idanunsu cike da tausayawa suna dubanta ,a hankali jaguwa ya lumshe idanunshi tare da kai hannunsa daidai saitin qirjinsa dake bugawa very fast yana shafawa ko zai samu sausauci yanayin da yake ji ,kodaudun idanunshi ya bude sosai akanta tana kwance tana sauke wahalallin numfashi ,ya sauke ajiyar zuciya ahankali wani abu mai daci daya tsaya masa a makoshi ya hadiye a tun sanda hatsarin ya faru .
“da wani abu ya sameta bai san yadda zaiyi da rayuwarsa ba ,ya qara taku biyu ya matso kusa daita sosai ya kai hannunshi bisa suman kanta dake zube akafadanta yana shafawa yana maida numfashi a hankali .”wasu irin abubuwa yake jin suna masa yawo a sansar jiki suna ratsa jinin jikinsa gbdy , nan take tsigar jikinsa suka mike yana jin ina ma ciwon ya dawo jikinsa ……”
Cike da natsuwa anas ya matsoshi ya dafa kafadanshi gbdy yanayinsa ya canza kallo daya zaka masa ka fahimci baya cikin natsuwarsa idanunshi sun canza kala sun sake cika taf da ruwan hawaye alamun zai iya zubar da hawaye akowani lokaci ,cikin tsarkewar muryar anas yace “please adnan ka kwantar da hankalinka inshaallahu babu abinda zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login