Showing 168001 words to 171000 words out of 259215 words

Chapter 57 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16567

da shawarar da mataimakinsa ya kawo ,ya kalli Jamilu da kabiru, “kuje ku fara bincike akan alhj sani fafe da alhj usman da kuma mutuwar shi magari alhj abdulaziz , kai kuma adamu ka samu yahya a tsara yadda zaa kama barayin nan dake bibiyarsu lallai suma aka musu .
“Okay sir ya fada sannan ya juyo da sauri cike da girmamawa sauran ma suka kama gabansu suka koma dakin da garunmallam yake suna shiga suka fara magana.
“yau a gidanka zaka kwana sai dai da kanka zaka koma batare da wani daga cikinsu ba sbd muna bukatar mu kama masu bibiyarku dan haka idan kaje gida ka tabbatar da duk wani kudi da’aka raba aka baka ka hadasu guri daya kasa acikin jaka idan har basu zo a daren yau ba gobe da safe ka fito da kudin ka nufi duk inda yayi maka dadi zasu zo su sameka domin amsar kudin saboda daman kudin ne agabansu baku ba ,mu kuma inshaallahu duk inda kake muna biye da kai ,karka kira kowa a waya ,sannan karka daga wayar kowa har zuwa sanda komai zai daidaita yayi shiru cike da fargaba bakinsa ya dan motsa alamun yana son yayi magana “karka damu duk wani motsinka zamu sani hatta abokanka alhj sani da alhji usman karka kirasu yana gama maganar ya sallamesa cike da tsinkewar zuciya garunmallam ya fito sai dai zuciyarsa rawa take yana jin tsaron abinda zai biyo baya yana matukar qaunar rayuwarsa data iyalinsa baya son rasa ransa data iyalinsa drop din mota ya dauka a daidai bakin get din estate dinsu motar ta tsaya saboda baa barin kowace mota na shiga ,ko wani yaxo nemansa dole sai ya kirasa
shi kuma ya kira securities din bakin get ya fada musu sunan mai shi sannan su barka ka shiga.
Ahankali yayi kasa da glass din motar inda fuskarsa ta sauka akan sky yana surutai irin na masu tabin hankali shiru yayi yana cigaba da kare masa kallo sama da kasa har idanunshi ya sauka akan yatsun kafafunsa komai nashi tsaf illa gashin kansa da yake a hargitse da kuma fuskarsa da tayi baki amman kafafunsa babu dotti irin na Mahaukata .
sky ya karaso jikin motar yana kokarin kamo hannun garunmallam
dake sakake da murfin mota “kilo de towo,were alaso ,se modun wo fu e ni “ai da mugun sauri ya zare hannunsa sannan da karfi ya kira daya daga cikin securities din da suke duty .
“Succeed!
Ya amsa da “yes sir ! Kana ya karaso da mugun sauri ya tsaya ajikin motar yana cewa “welcome sir “ gyada masa kai yayi “me yasa kuke barin irin wadan nan mahaukanta na tsaya wa anan ?
“sir tun shejaranjiya muke fama dashi ya bar gurin nan yaki kasan irin sababbin shiga haukan nan naci garesu amman karka damu yanzu zan masa mugun bugun da zai bace “better gara ku korasa yayi gaba i dont wont see his face dan yanzu duniya ta zama abar tsora , ku bude min get please “okay sir ya fada yana bude masa makeken get din direban daya daukosa ya sanya hancin motarsa ciki a daidai kofar get din gidansa yace ya tsaya ya ciro kudi ya mika masa ,yana tsaye yayi revers ya juya ya kama gabansa,shi kuwa gabansa na faduwa ya shiga buga karamin get gidansa ma gadinsa ya leko ta karamin huji ganin shine ya bude masa da sauri yana masa sannu da zuwa bai kulasa ba ya shige ciki .
A babban falo ya wuce matarsa da yaransa matarsa ta mike ta biyosa atare suka shiga parlounsa tana masa sannu da zuwa “yauwa harira sannu ya gida?lafiya ta fada masa tare da karasawa inda fridge yake ta dauko masa lemunsa da yake sha da glas cup ta dawo ta tsaya agabansa ta tsiyaya masa a cup ta mika masa,ya karba ya kurbi kadan ya mika mata saura ta amsa ta zauna agefensa tana cewa “yaake ciki ne?
“ anyi nasarar kanasu ne ?.
“Ina fa akayi nasara da wani sabon tashin hankali na dawo gida ya bata amsa da hakan “ya ka kawo mana sauki numfashi ya sauke ya yunkura ya mike dakin baccinsa yayi duk yadda yahya ya fada masa ya dawo falonsa ya zauna da jakar kudin a gefensa yana jiran zuwansu bai fi minti goma da zama ba hjy harira ta shigo ta dubesa tace “akawo abinci ne ?”wannan jakar kuma fa menene aciki ? “Kudaden mutane ne aciki ya fada atakaice gbdy jikinsa a sanyaye yake “kicewa yaran nan kowa ya koma part dinsa ina bukatar natsuwa “okay ta fada tare juyawa har karfe biyun dare idanunshi biyu ya kasa samun natsuwar zuciya sannan ya kasa runtsawa hatta abincin da aka kawo masa ya kasa ci jira kawai yake yaga ta inda zasu shigo masa sai dai wani abun mamaki basu zo ba gari na wayewa yayi wanka ya shirya cikin manya kaya ya fito ya shiga motarsa kai tsaye hanyar da zata kai sa airport ya dauka sbd ya rasa inda zai dosa ,yana tafiya yana kallon glass din bangaren da yake zaune domin ganin ko ana binsa abaya sai dai motoci ya gani bilaadadin suna wucesa wasu kuma suna bayansa ya cigaba da tafiya har ya karaso airport yana karasowa ya wuce inda aka tanada domin parking , ya kashe motar ya fito yana waige waige sannan ya bude murfin bayan mota ya fito da jakar kudin ya juya ya soma tafiya a hankali qirjinsa na bugawa Kmr zai fito waje.
ya dan yi tafiya me nisa kawai ya hango wani mutun sanye da bakaken kaya yana kallonsa take yaji gabansa yay mummnar faduwa nan take zuciyarsa ta shiga wasi wasi ko shine dan fashin ? to idan ma shine dan fashin ba lallai ya kashesa ba ,idan kuma yayi yunkurin kashesa jakar hannunsa kawai zai bashi “.
shi kuwa jaguwa shi da eku suka biyosa tunda ya samu labarin dawowarsa gida a jiya yaso suzo amman a bincikensa yasan jami’an tsaro na biye dashi, dan duk kwanakin da sukai suna nemansa yasan yana hannunsu haka fitowarsa a safiyar nan ma yasani ne abakinki sky ya jima yana yawo da jakar kudin a hannunsa bai hadu da wanda ya kamashi ba ko ya karbi jakar kudin ba har laasar.
shi kuwa jaguwa ya fahimci jami’an tsaro har lokacin suna biye dashi jira suke ya isa garesa su kamashi amman shi din barawo ne mai matukar wayo da baseera da sanin kan aikinsa dan haka bai tsaya bata ma kansa lokaci ba suka shiga mota suka juya suka bar gurin zuwa masaukinsu inda ya iske anas zaune a dakinsa shiru yana tunani “wai kai bazaka raba kanka da wannan tunanin iskan ba ,wallahi zan fita harkarka idan baka ajiye komai munyi abinda ya kawo mu ba “ya fada yana jan tsaki anas ya riko hannuwansa duka biyu, jaguwa ya fizge ya cigaba da tafiya yana balle mabalin gaban rigarsa a rude ya bishi cikin sauri “haba aboki am so bazan sake ba“.


Ya bude idanunshi da kyar yana cewa nayi sai ka sakar min hannu ya fada yana fixge hannunsa cikin na anas, ya dafe kansa yana cewa “allah banason ganinka cikin damuwa bare damuwar ma akaina yayi mgnr zai durkusa masa jaguwa yace “no karka durkusa min please kar ma ka sake min irin haka kai fa aminina ne kuma danuwana ba iya halakar aminta kawai ke tsakaninmu ba akwai soyayya me karfi ya fada yana ciro hanky da sauri ya soma goge masa hawayensa “kana dani meye abun kuka “?karka damu nayi maka alkwarin muna komawa zaa tura manya ne mammaka aure “.
“Allah sarki aminina kana sona dayawa “yes ina sonka sosai sbd kai ma kana sona maimakon anas yayi magana sai ya daura kansa akafadar jaguwa yana jin yadda yake sauke numfashi da ajiyar zuciya wanda yasa hawaye ya gangaro masa jaguawa ya dagosa “me kuma abun zubar da hawaye kai da ka kusan an gwancewa da amaryarka”? a yanzu nafika matsuwa naga wace zata auri bin malik dina “amman kai nafi son kayi tunda kana da wacce take sonka “share kawai ni aure yanzu baya gabana na haseera zamewa zan……”
“please jaguwa karkayiwa Ammin haka yayi saurin katsesa “koda yake samun mahaifiyar kayi ni nayi mana “ya karasa mgnr muryasa na rawa “zaka fara ko ?to shikenan zanyi duk abinda take jubi ya bude kofar ya shigo ya tsaya yana kallonsu kamar zasu shige jikin juna…”
Ranar haka garunmallam ya dinga zagaye airport allah yasa da jami’an tsaro da an zargesa tun safe har yamma yna zagaye gurin kafin daga bisani ya koma gida agajiye yana shiga gida ya kira headquarters na police yace ga kudin fa ,tun jiya banga kowa ba, yau ma tun safe nake yawo har airport ban hadu da kowa ba .
“mun sani saboda muna biye da kai sun ma sun zo fahimta sukayi ana biye da kai amman lallai zasu zo yau” ranar bai runtsa ba da zarar ya rufe idanunshi sai yayi firgigib ya bude rana a zaune ya kwana, wasa wasa har kwana shida basu zo ba jami’an yansanda suka turo masa jami’an sirri aka musu kyakkyawan masauki abakin get din gidan wanda hakan ya kwantar da hankalinsa.
su jaguwa basu zo ba sai randa sati ya cika garunmallam na zaune yana tunanin ta yadda zai rabu da kudin hankalinsa ya kwanta kawai yaji kamar ana duro gidansa yana yunkura tashi yaga manya karta maza majiya karfi na shigowa falonsa a firgice ya koma ya zauna arasa yace “sai yau allah yayi ?
a natse suka gama shigowa kowane ya rufe fuskarsa da bakin kyale wanda yafi kama da yadi .
mamaki ne ya kamashi ta yadda akayi suka shigo gidan har cikin falonsa byn akwai jami’an sirri a bakin get dinsa nan da nan suka kewayesa da bakin bindigar dake rike a hannunsu cike da rashin jin tsoro jaguwa ya karaso inda yake rike da bindigarsa “garnakaki uban shegu barawo ne ni amman mai mugun wayo , yau dai dubunka ya cika,ina kariyar daake baka take? ya fada tare da karasowa zuwa gabansa ya tsaya kikam sannan ya cire glass din daya rufe masa rabin fuska tare da cewa “ina kudin suke? cike da rawar jiki yace “gasu can ya tashi yaje ya dauko jakar kudin ya dawo da sauri ya ajiye musu a gabansu “lallai ka kyautawa kanka sai dai ka tabbatar da kudin da suke ciki sun cika cif ,ko kwandala ban taba ba yadda akabani haka suke “very gud ,eku shiga dakunan gidan ka fito min da duk wanda kagani “ok sir!.ya nufi hanyar shiga dogon falon da idanunshi ya kai .
Garunmallam yayi saurin durkushewa kasa ya rike lafafun eku yayinda idanunshi ke kallon jaguwa “dan girman allah karka taba min lafiyar iyalina ,abinda kuka bukata gashi nan na baku ku tausaya min “a she kuna son a tausaya muku amman ku bakwa tausayawa mutane”? eku kayi abinda na saka ,gama jin haka ke da wuya eku ya fizge karfarsa ya nufi dogon falon .
a hanakli ya dinga bin daki daki yana fito da mutanen gidan cikin tashin hankali fuskar data fito karshe ce ta janyo hankalin jaguwa da tawagarsa gbdy suka zuba mata ido suna dubanta, sosai jaguwa yake kallon fuskar tabbas fuskar da ya gani ce ba kuma zata bace masa ba yayi murmushin takaici” lallai ana burouba a duniya kamar yarinyar da muka gani da ajirebi a hotel ?”inji cewar kamil .
“ba kama bace itace “kaga tsantsar cin amana ko ? a junansu ma basu bar junansu ba suna kwana da yayan juna jaguwa ya fada yana gaurawa garunmallam wani lafiyayyyen mari wanda yasa yayi yar dungure ya fada byn kujera mai zaman mutun uku yana haki wata irin zufa na tsatsafo masa bisa goshinsa “kaci saa muna kan hanya ne wallahi da kasha azabar da har sai ka gwamaci mutuwa da rayuwarka ,sannan ya juya a natse yayi taku biyu ya tsaya a inda yarinyar ke rakube cike da matsanancin tsoro.
taji tsayuwar mutun amman tsoro bai barta ta iya dagowa ba cike da bakin ciki yake mata wani irin mugun kallo mai dauke da sansar tsana “wallahi bai dauka yayan masu arziki nabi maza ba sai yayan talakawa marasa galihu keyi, ko da yake ta yuwa ba dan kudi take ba tana da manufar yin haka ,sai daya gama mata kallon kasa da sama na banza sannan a matukar tsawa ce yace “ke …!
Ta dago a rikice tana runtse idanunta “ki canza rayuwarki !.
Ta bude idanunta a rikice tana dubansa “yes dake nake ,ki canza rayuwarki ko bake muka gani tare da ajirebi a hotel ba a wacan ranar? Saurin girgiza masa kanta tayi cike da matsanancin tsoro alamun aa .
A zuciye ya daura bakin bindiga a tsakiyar kanta “ni zakicewa aa?kece ko bake bace kafin na fasa kanki yanzu ?eh..ni nice, ta fada muryarta na rawa” very gud tun yaushe yake kwana dake?ta nuna masa yatsunta uku ,ya juyo ya kalli garunmallam dake barin jiki “ka gani ko diyar cikinka da amininka suna kwana da juna mutumin daka yarda dashi na ma barka da wannan ciwon ya isa ya karar da rayuwarka.
tunda jaguwa ya fara magana akan diyarsa nabeela kwalkwaluwarsa ke juya maganar babu ta inda zai karyata tunda gashi ta tabbatar da gaske anyi ,wani duhu ya gilma acikin idanunshi ,zuciyarsa ta jagule kamar ya fasa ihu sai ma yaji duk wani tsoro da fargaba ya kau a zuciyarsa ya daina kallonsu jaguwa ya dawo kallon diyarsa “.
“Eku ku taho da mutun biyu a cikin manyan yayansa maza dasu zamu fita bazamu sakesu ba sai mun kammala aikinmu ,”okay boss nan take eku ya cakumi wuyan Abbas da muhd da sauri suka mike yayi waje dasu “.a tsawace jaguwa yace “Ina makulin get din baya? tsawar da jaguwa ya buga masa ne yasa ya dawo haiyacinsa jikinsa na rawa ya dauko ya bashi har ya juya ya tsaya batare daya juyo ba “zan wuce da yaranka ya rage naka ka kira jami’an tsaro , idan kayi min ganganci zan maka ganganci zan nuna maka sheidancina ya wuce yadda kayi tsammani ,daga haka bai sake cewa komai ba ya da kai ya cigaba da tafiya sauran tawagarsa suka marasa baya suka fice daya bayan daya .
Atare gbdy ahalin gidan suka sauke ajiyar zuciya yau su suka ga tashin hankali babu wanda cikinsa bai duri ruwa ba ,Anas ya jarbi key a hannun jaguwa ya bude musu karamin get ,Ahankali suka fara fita daya bayan daya suka shiga motocinsu dan daman dasu suka zo aguje suka ba unguwa .
sai da suka kammala da abinda ya kai su abuja sannnan suka dawo lagos cike da nasarori bai sheidawa tanwer ya dawo ba ,washegarin randa suka dawo malam mudi yazo sakamakon kiran daya samu daga jaguwa suna zaune a babban parlour’nsa sconpio ya shgo da katuwar ghna most go da hannu jaguwa yayiwa sconpio umarnin ya wuce ya juya da sauri ya bar gurin.“Malam mudi ga kudi nan mun samu nasarar amsowa babu abinda yayi ciwon kai aciki sai ka dauka ka kai wa mahaifiyar yaran allah kuma ya jikan mahaifinsu“sannuka da kokari adnan ,allah ya cigaba da kareka inshaallahu karshenka sai yayi kyua da albarka ,allah yasa ka gama da duniya lafiya sannu da kokari nasan kun sha wahala sosai ? “babu komai malam mudi mun rigada mun saba, kuma mun bada rayuwarmu a irin wadan nan ayyukan, wahala kuma idan da sabo mun saba tunda dama gbdy rayuwar wahala tafi yawa acikinta ni rayuwata na dauketa qaddara,
“Qaddara kuma tana fadowa bawa daidai yadda allah ya hukunto masa sai dai addua tana sausauta qaddara ya karasa maganar muryarsa na rawa “.
“inshaallahu komai zai zama tarihi
Malam mudi ya fada cikin sare wa sannan ta numfasa yace “ya kamata ka duba bangren masu safarar hodar iblis suma iyayen yaran na kuka da wannnan matsalar bayan tafiyarka abuja wallahi kimanin mutanen da suka mutu adalilin shanta bazasu kirgu ba “matsalr manya kasar ne ,
dayawa daga cikin masu kudin kasar nan suna da sa hannu acikin tafiyar da harkar kasuwancinsa acikin kasar nan,bibiyarsu zai ballo ruwa gara abarsu kawai ,”.
“aa kayi iyakar kokarinka zamu tautauna daga baya zanyi maka bincike sosai kafin mu shiga cikin aiki “to shikenan na gode sai naji daga gareka ya mika sama hannu sukai musabaha sannan ya wuce.




*****


Bayan sati biyu bincike ya tashi zanga zanga dan cp ya bada umarnin a kamo alhj sani fefa da alhj usman ,alhj sani aka fara kawowa akai kaishi dakin bincike aka fara tambayarsa halakarsa da honorable “aboikin kasuwancina ne , ya bada amsa da hakan “babu wata magana ta kudi atsakaninku ? Dcp habib ya tambayesa shiru yayi kafin daga baya yace “akwai Ina zaune honorable Abdulaziz ya kawo min ajiyar kudi amman dolar’s ne na kimanin million dari uku a lokacin ya sheida mana akwai wanda yake nemansa zai kwace kudin a hannunsa amman yarda da amana da yayi mana tasa ya bani ajiyarsu sai dai ya sako sheidu wato alhj Usman galadima ajirebi, garunmallam,bayan wani lokaci kawai sai muka ji labarin mutuwarsa ,sosai mutuwarsa ta girgizamu matuka gabadayanmu mukaje janaizarsa sai dai acikinmu babu wanda ya fito ya fadawa iyalinsa batun kudin daya bayar ajiya muka bi ta kan kudin muka rabe a tsakaninmu kwatsam muna zaune sai iyalinsa wato matarsa ta kira daya daga cikinmu “ ina kudin da mijinta ya bawa daya daga cikinmu ajiya?a lokacin sai muka hada baki mukace aa babu kudinsa ahannumu ,wanda alokacin mu bamu san cewar ya rigada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login