Showing 216001 words to 219000 words out of 259215 words

Chapter 73 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16542

lafiya ba ?
idan wani ne me zai kawo mu nan bayan ga sadiq wata nazo gani ya karasa maganar yana kokarin parking din motarsa a inda aka tanada domin ajiye motoci ya soma kokarin fitowa yana duba agogon dake daure a hannunsa daya da rabi adaidai yana gama fitowa lokacin tanwer suka jero tare da doctor muyis da fadela abokiyar aikinta yayinda doctor muyis ke faman yi mata naci da magiya ."
suka tsaya a bakin motar tanwer fadela na cewa "haba tanwer ki tausaya masa mana ki dan samar masa gurbi azuciyarki ko babu yawa ne a soyayya baa son ka zurfafa kiyayya "barta kawai fadela só take ta kasheni , tanwer tayi murmushi "haba fadela wallahi a halin yanzu bazan iya wahalar da kowa a soyayya ba ,kai kuma dr allah bazai sa na kashe mutun ba ."da wahalar da zuciyata da kike ai gara ki kasheni zan fi bukatar mutuwa akan wannan rayuwar ko ba haka fadela? "aa bazaa yi haka ba dr ta dai amince cikin sauki da dadin rai mu sha biki ba sai an kai ga haka ba ,ta fada tana juyawa ni zan wuce ana jirana naso ma muje tare da tanwer ne amman yanzu ina cewa muje zata fara dojewa ita dai ban san abinda mutane suka mata ba da bata son shiga cikinsu ? ta nufi gurin motarta tana magana ta bude ta shiga gidan baya ta zauna tanwer taji wani abu acikin maganar fadela wasu kuma sun bi iska tayi murmushi har fararen hakoranta suka bayyana tana kokarin sake cewa wani abu kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya harde hannayensa a qirjinsa rikitattun idanunshi akanta yana kare mata kallo ,kasa magana tayi nan take kuma ta sanyawa jikinta natsuwa ta shiga hankalinta hatta murmushin dake kwance akan fuskarta ta dauke qirjinta ya shiga bugawa da karfi tamkar zai fasa qirjinta ya fito waje cigaba da kallonta jaguwa yayi fuskar nan nashi babu annuri sam "ya kika yi shiru madam dina inshaallahu ki fadi min abinda kike son nayi ki soni ,wallahi ni magana dake ma kadai yanasani farinciki , bata kallesa ba ta furta "dan allah dr muyis kayi shiru na shiga rudani né fadela data shiga motarta kam batasan wainar daake toyawa ba sai dai ta dan leko ta side din da take zaune domin tayi musu sallama direbanta yaja suka wuce .
a hankali jaguwa ya soma taku cikin isa da izza hannuwansa duka zube cikin aljihunsa yana kokarin karasowa inda take ai nan take zuciyarta ta shiga karkarwa ."


Mmn sudais






💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO




WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


🅿️38




......tafiya kawai yake fuskarshi babu annuri kana kallonsa zaka fahimci zallar 'bacin ran dake tattare dashi ,ran nan nashi yayi baki yayi kololuwar 'baci yana gama karasowa inda take tsaye bai kalli dr muyis ba ya kai kyakkyawa hannunsa ya rike tsintsiyar hannunta gam cikin nashi yana tsareta
da rikitattun idanunshi masu matukar firgitawa da hargitsawa mutun lissafi , a qalla ya dauki minti goma yana tsaye yana kallonta zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ,yana tunanin abinda ya kamata yay mata ,wata zuciyar ta bashi shawarar
ya hau dukanta yana yaryarfa mata maruka ko hakan zai sa yaji saukin zugin da zuciyarsa ke yi ,yayinda wata zuciyar ke gargadinsa ba dan jin tsoron abinda zai faru ba sai dan kasancewarta yarinya .
wasu minti goma suka shud’e yana tsaye yana kallon kyakkyawar fuskarsa , kafin daga baya ya jata zuwa gefe wanda tazaransu da dr muyis bai fi taku hudu ba kuma tana da tabbacin duk abinda jaguwa zai fada mata tabbas zai ji ,ita a tunaninta ma gurin da yayi parking din motarsa zai kai ta ko cikin motarsa sai taga sabanin haka, ganin zai soma magana cikin zafin rai tace “muje daga can ta nuna masa nesa da inda suke komai zai fada mata babu me ji ,amman da yake ransa a bace yake uwa uba kuma ga tsabar taurin kai sai cewa yayi “bazaa je
ba anan nayi niyyar magana banga uban daya isa yasa na kara taku daya daga nan ba tukun ma me kike yi tare da wannan mutumin ? qirjinta yayi mugun dokawa da matsanancin karfi har ta kasa bude bakinta,hakan ne ya bashi damar cigaba da magana "bakin san Idan mutane suna ganinki da maza kala dabam dabam ba zasu dauka kmr baki da kamun kai ne ba? “wallahi mutane zasu daukeki useless idan kika cigaba da kulaye kulayen maza “stil shiru tayi ta kasa magana duk da bakinta abinda yake son yi kenan ta tsaida shi daga abinda yake fad'a ."




hannunta dake cikin nashi ya sake matsewa sosai yana sake tambayarta cikin zafin rai "me yasa kika tsaya dashi ?"Ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "ban sani ba kai ne dai kake ganin kamar bani da kamun kai ,amman kowa agurin nan yasan ni wacece,sai abu na gaba ,adnan am not useless your sister’s your aunty’s I wont put your mother coz I use’s to respect mum, but your sisters are useless , your Aunty’s are useless even the children that you wont to born they wil be useless inshaallahu, in allah yaso ya yarda sune useless banice useless ba idan kaga dama karka kara zuwa inda nake ko yanzu ai ban kiraka ba kona kiraka ne da zaka fada min mgnr banza .”?
Shiru yay yana kallon karamin bakinta da take motsawa a hankali tamkar ba daga cikin zafafan magana ke fitowa ba yana jin wani irin zafi daga cikin kasan zuciyarsa idan yace bai ji zafi da ciwon maganarta ba yayiwa kansa karya "ita kuwa wani sanyi dadi ne mai tattare da farinciki ya lullubeta alokacin daya, duk da taji zafin kalamansa amman kishinta daya nuna qarara yayi mata dadi kamar tayi masa dariya mai hade da kukan zafin furucinsa amman tsoronsa ya hanata ,yanayinsa kawai zaka kallo ya tabbatar maka da abinda ke dawainiya dashi gbdy Kishinsa ya fallasa abinda ke cikin zuciyarsa ,yana mugu mugun qaunarta amman tsabar miskilanci da jin kai ya hanashi fallasa muradinsa .”




“Tanwer I want to ask you a question tayi shiru tana kawar da fuskarta gefe ya kai hannunsa ya dawo da fuskarta garesa “why did you abused my sisters and my aunts ,Since when me and you meet each other which day did i abused you da zaki sako sister’s dina cikin magana?adnan ka kirani da …..”shiiiiii !
Yay saurin katseta qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske "abinda nake so dake wannan ya zamo shine karonki na farko kuma ya zamo na karshe da zaki sake kula wannan mutumin koda kuwa gaisuwa ce bana só idan .."
"Idan na sake kulasa fa me zakayi?" tayi masa tambayar cikin karfin hali tana kallon tsakiyar idanunshi at the same time kuma qirjinta na luguden bugu " wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa "tmbyta abinda zanyi kike ko kuma zaki Kibi umarnina ?"bazanbi umarninka ba tunda ba aurena kayi ba ,baka aureni ba kaga ai bazaka hanani kula duk wanda raina yake so ba ,ko kai mijina ne ?ta sake jifa masa tambayar datasa zuciyarsa shiga tashin hankali ,magangunanta fa
sun doki zuciyarsa da kunnuwansa sosai sannan sun shiga kai kawo acikin kwakwaluwarsa sai yaji kamar ta sake kunno masa wutar kishinsa ne da yake ta kokarin dannewa acikin zuciyarsa ransa a matukar bace yace "kema a she kamar sauran mata kike da rashin mutunci ?kamar ta girgiza masa kanta alamun aa sai kuma ta fasa tunda tasan tayi rashin mutunci "ko da yake bai kamata nayi mamaki manyan maganganunji ba ,idan dai tsiwa da rashin kunya da rashin mutunci ne gidan nazo ko ba haka ba ?"
"Ban sani ba Karka sake kirana da wadan kalmomin bana.."Bata kai karshen maganarta ba ya dalle mata baki da dayan hanunsa da sauri ta dafe bakinta saboda azabar da taji ya ratsata nan take idanunta ya canza kala ta dan juya bayanta nan taga dr muyis tsaye ya kafesu da idanu yana Kallonsu yanayinsa
da alamun tashin hankali dukkanin alamu sun nuna yaji abinda ke tafiya ,daga can gefe kuma anas ta hango ya harde kafafunsa ya tallabe habarsa da hannunsa daya shima yana kallonsu ,numfashi ta sauke sannan ta dawo da kallonta garesa ta tsura masa idanunta cike da kwalla saboda har lokacin tana jin zafi a abakinta ."




Shi din ma kwayar Idanunshi suna kanta yana jin wani irin tuttukin bakinciki acikin ransa "ba laifinki bane tanwer samu kikayi nazo gurinki shiyasa kika samu damar yimin rashin kunya da wulakanci"ya girgiza kai yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa "I don't know that you are in responsible girl like this tanwer, kullum kina yaudarar kanki da kanki da sunan kina sona idan babu ni arayuwarki bazaki iya rayuwa ba amman kullum kina makale da wasu mazan kina shirmen banza dasu Alhamdulillahi for Almighty Allah who created me and you quickly show me the type and the kind of a girl you are ,sakarwa maza fuska, basu damar suga murmushinki a árha ,do you think that's life,wallahi what you're doing is a big shame for you ,my advice to you stop calling me or chart me again ,and I don't won't to see your face again in my life ,stay a way from me tanwer idan kuma kikayi taurin kai da gangancin zuwa inda nake ko kiran layina wallahi sai nayi kwallo dake na fasa kanki da harsashi "yana gama fadar haka ya sakar mata hannu da karfi yana jan tsaki sannan ya juya a matukar fusace ya soma tafiya cikin zafin rai kamar zai tashi sama ."




tsayuwa tayi agurin tamkar an dasata tana kallon every step of him wani irin tafarfasa zuciyarta keyi da sauri sauri tare da tsantsar nadama "me yasa tayi react irin haka ? me yasa tayi masa rashin kunya ?me yasa lokacin da yake maganarsa bata rabu dashi ta zuba masa ido ba tunda ta fahimci damuwa daita ne ya janyo haka ?"Why why tanwer!! jikinta ne ya kama rawa rawa taji kamar ta daura hannuwanta bisa kanta ta kurma ihun tare da kukan neman dauki amman haka nan ta tsinci kanta da kasa aiwatar da ko daya sai ma taji zuciyarta ta bushe tana kallonsa ya dafa kafad'ar anas cikin mawuyacin hali sannan ya zagaya ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna ."


Tayi tunanin anas zai karaso gareta ya tambayeta dalilin fushinsa ita kuma ta samu damar fahimtar dashi komai da matsayin dr muyis agurinta sannan ta nemi alfarmar ya shawo mata kanshi amman sai taga sabanin haka shima ya bude bangaren da yake jingine ya shige jaguwa ya figi motar da dan gudu suka nufi get ,dumi taji akan kuncinta ,ko bata duba ba tasan meye ya zubo akan kuncinta tana tsaye cikin wannan tashin hankali dr muyis ya karaso zai rike mata hannu ta goce da sauri dan ganinsa ma kara mata bakin ciki yayi tunda duk shine ya janyo mata wannan tashin hankalin da take ciki ,tana zaman zamanta tana neman hanyar da zai amince wa aurenta amman kuma ga abinda ya faru "meke faruwa tanwer ?wai waye shi wannan mutumi ne? "yau karo na uku kenan ina ganinsa tare dake please ki fada min waye shi ina da bukatar saninsa da sanin matsayinsa agurinki da har yake da karfin halin fada miki maganganun banza ?".bata ce masa uffan ba illa tsakin data ja sannan tabi gefensa ta karasa inda motarta take ya bi bayanta da kallo har sanda ta bude gidan baya ta cilla hand bag dinta ta rufe ta bude mazaunin direba ta shiga ta zauna tare da kunna motar ta nufi get stil yabi bayan motarta da kallo kamar yayi kuka yaso ta tsaya tayi masa bayanin matsayinsa dan yasan ta inda zai dauki mataki ,”




Wani irin mugun gudu jaguwa yake yi akan titi har sai da anas ya waiga yana kallonsa "kayi parking a gefen titi please ka bari na karasa damu gida gudun da kake yi yayi yawa ,Iska mai zafi ya furzar batare da yace uffan ba ya cigaba da tuki can kuma ya soma magana "ni tanwer zata fadawa magana alhalin bata san abinda ya kai gurinta ba ?tasan me zan fada mata da naje gurinta tayi min wulakanci ? daman na fada maka soyayya karya ce ba gaskiya ba ". ya karasa maganar yana dukan stearing mota da karfi."kamar ya kwashe masa da dariya amman kuma sai tausayinsa ya mamaye zuciyarsa dan ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya da ruhinsa "ni zata wulakanta akan wani banza wallahi tayi na farko tayi na karshe dan sai ta sake ganina arayuwarta sannan tayi tunanin sake min wulakanci."
"Cool dwn my friend karka ce haka yana da kyau ka tsaya ku fahimci juna idan da hali ma ka bata umarni daina sauraron kowa "karta fasa ta cigaba da sauraran kowani kato is not my business ko jikinta zata dauka ta bashi tayi bazan damu ba ,wai har da cemin idan ta sake kulashi me zan mata imagine anas wai ni tanwer take fadawa haka ?anas ya kawar da kansa gefe yana murmushin mugunta " wai aurenta nayi da zan hanata kula maza tunda ban aureta ba zata kula duk wanda take so well ta cigaba da kulasu ya fada cikin daga murya Ana's bai juyo ya kallesa ba saboda murmushin dake kwance a fuskarsa ,tanwer bata taba burgesa ba kamar yau abinda ya kamata tayi kenan tun farko ta zauna tana lallabashi ."




Tafiya kawai yake akan titi batare da yasan ina zai nufa ba lokaci lokaci anas ke waigosa ya kalli yanaynsa agogon hannunsa ya kalla yaga karfe biyu har ta dan wuce ,yace " dan allah ka dawo haiyacinka ka dauki hanyar zuwa gida sai yawo kake yi da mutane ,jiki babu Kwari ya dauki titin unguwarsu cikin minti goma suka karaso jiki babu kwari ya fito ya shiga parlour sai dai kafin ya shiga ya boye abinda ke ransa baya tunanin zai bari su jubi su san halin da yake ciki dan sai suyi masa dariya, tsabar fadin rai da bakinciki bai kula kowa ba acikin gidan ya wuce dakinsa ya zube akan kujerar yana sauke naunayen ajiyar zuciya."
Kwalin sigari dake ajiye akan karamin table ya dauka ya zaro guda daya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuka yana fitar da hayaki ta hanci ta baki zuciyarsa na sake shiga rudani da tashin tashin hankali "Ni zaki wulakanta tanwer wallahi baki isa ba " anas daya shigo ya zauna kusa dashi yace "dan allah ka samu natsuwa bafa haka akeyi ba ,barni kawai anas dan dai ba a gabanka tayi ba nasan da sai ka wanke min ita da mahaukacin mari da zai sa ta dawo haiyacinta tasan tayi Kuskure ,yarinyar nan sam bata da mutunci ai kuwa ganin idanunta zata ga aikin marasa mutunci dan wallahi tayi kuskuren takowa gidan nan sai na ballata naga uban daya tsaya mata "Wallahi adnan kai ma har da laifinka yarnyar nan sam bata da laifi , wani irin kallo ya waiga yayi masa yana kashe sauran sigarin hannunsa ya dauki wani ya kunna ya kai bakinsa ."


"yes bata da laifi adnan tunda tabika ta sadaukar maka da komai nata ,ta soka fi sabililla bata kyamaceka ba me kuma ya rage ta maka ?mu ajiye maganar wasa ta fika gsky tunda baka aureta ba kuma bakace zaka aureta ba kaga baka da damar bata umarni akan wa ya kamata ta kula " tashi yayi bai ce masa komai ba ya dauki kwali sigari da farantin zuba toka ya shige bedroom dinsa cikin fushi tashi anas yayi ya biyosa da sauri yana masa magana "oh biyoni kayi ka cigaba da qara min damuwa akan wanda nake ciki ? "kai dai adnan bazaka canza ba bafa haka ake yi ba, sai anyi hakuri ni nasan zata kiraka ta rarrasheka cikin lumana ta baka hakuri duk da bata maka laifin komai ba "a wajen ka kika ganin bata min laifi ba amman ni a wajena jin abinda tamin nayi kamar na mutu
mace bata taba min abinda tay min ba kai kasani ."




"Nasani adnan amman dan allah kayi hakuri kaji maganata har yanzu tanwer yarinya ce sai ka kara hakuri daita sannan kayi kokari ka fada mata cewar kana sonta zaka ga sauyi na ban mamaki "sai na furta ina sonta zata daina kula maza ?yayi masa tambayar a fusace yana fesar da hayaki idanun shi sunyi jawur sun canza kala tsabar tashin hankali da shan sigari dan ya kusan tashi da kwali daya ,"no adnan ba haka nufi ba zata dai ...."kaga ya isa ya isa !! kama hanya ka wuce gida kawai muradin ranka na can tana jiranka ," Ana's bai san sanda dariya ta subuce masa ba ai kuwa ya shiga yi yana kallon jaguwa ,shi kuwa tsaki ya ja ya soma zariya a dakin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login