Showing 39001 words to 42000 words out of 259215 words

Chapter 14 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16518

masa suna masa kirari gutun wiwin dake rike a hannun jubi ya amsa ya Ι—an zuka yana fitar da hayaki ta hancinsa da bakinsa sannan ya fita ta kofar baya yana tunanin mugun hali irin na Alh Tahir ko me zai yiwa Ζ™aramar yarinya kamar wannan gashi kuma shi din aminin mahaifinta ne?
Kusan minti goma yana tunanin agurin "


*****


"Wai Ibrahim kana so ka kashe kanka ne akan mace". Momynsa tayi maganar cike b'acin rai wanda ke had'e da tsantsar damuwar halin da d'anta ke ciki. "Momy I can't live without Tan, ta riga ta zama rayuwa ta, inda abunda nakeso bai wuce Tanweer ba Mo...". "Dakata!". Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu da tare da mai tsawa. "Ibrahim bazan taba son ka rasa ranka akanta ba duk da nima ina matukar kaunarta saboda irin son da kake mata ,but at least ka duba lamarina kai kad'ane d'ana taya zanso akan wata 'ya mace wani abu ya sameka ?".
Tayi maganar tana kallon Ibrahim wanda tunda ta soma maganar idanunsa ke runtse.
"Ibrahim!". Ta kira sunansa cikin wani irin yanayi wanda bai taba saninta dashi a rayuwarsa ba" gaba daya Inaso kayi hakuri da Tanweer!". Ta karashe maganar cikin dakiya tana kallonsa ganin yadda har ya samu courage d'in tashi zaune shida tun b'atan Tanweer bata ganshi a zaune ba.


"Mom!". Ya fada cikin daga murya tare da gyara zamansa yana binta da wani irin kallo idanunsa ko kiftawa ba yayi, already ya gama zazzarosu waje gaba daya what !". Yayi maganar yana kallonta kamar bai fahimci abunda yake faruwa ba musamman furucinta. "Mom!". Ya Kuma fad'a yana kallonta cike da mamakin furucinta."Haba Momy, taya zakiyi wannan furucin na rabu da Tanweer bacin kinfi kowa sanin irin son da nake mata? How could you utter such words uhm?!". Ya jero mata tambayoyin cike da damuwa lumshe idanu tayi tare da fadad'a murmushinta tana shafa sumar kanshi.


"Ibrahim kenan,". Ta fada tana kad'a kanta ,sannan ta tashi ta soma taku yana binta da koda'dd'un idanunsa da suka sha wahala saboda rashin ganin abincin su Tan, har ta Kai k'ofa sai Kuma ta juyo tayi murmushi me sauti tana kallonsa lokaci guda Kuma fara'a dake tattare da fuskarta ya d'auke nan take bacin rai ya maye gurbinshi."Hmm! Yaro yarone nan gaba zaka gane da kanka nasan dalilin da yasa nace ka hakura da yarinyar nan ". Tana fad'in haka ta fice ta barshi zaune zuciyarsa cike da tunanin zantukan ta musamman bacin rai daya hango cikin idannun Momyn nasa wanda kusan ya jima baiga hakan tattare da fuskarta ba. Wayarsa da ta soma ruri ne ya katse mishi tunanin daya shiga ya soma zurfi, hannunsa na rawa ya kai hannunsa ganin me kiran, da sauri ya manna wayar a kunnensa banajin me ake fada masa a can d'aya bangaren naga ya tashi da sauri. "What?!". Ya furta da d'an k'arfi tare da runtse jajayen idanunsa ya bude su tuni suka k'ara rinewa tare da k'ara tiruwa zuwa ja sosai kamar jan gauta. "Alright I am coming". Ya fad'a da sauri tare da wullar da wayar kan bed d'insa.
Yunku'rin k'arasawa wardrobe yayi amma me wani irin jirine ya kwasheshi da sauri yasa hannayensa akansa saboda wani irin nauyi da rada'dd'i da suke masa, yana ciza pink lips d'insa kanana wanda suka sauya colour saboda azabar ciwo a d'an bushe "Ya Salam I.B!". Dadynsa ya furta wanda ya bud'e ko'farsa kenan a daidai lokacin da I.B ke ko'k'arin k'arasawa k'as, cike da matsanancin tashin hankali Alh.Tahir ya k'arasa ya tallafoshi zuwa jikinsa inda yak'arasa sauke su kan bed d'in. "Ta...Ta...Tan! Da....". Karasa kulle idanunsa yayi hankalin Alh.Tahir ya tashi a wannan lokacin banda ihun kiran sunan matarsa cikin tashin hankali babu abinda yake dan ya fara tsorata da yanayin dan nasa .."


Darling's


πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
KUSKUREN BAYA
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


PAID BOOK


WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO



WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.


πŸ…ΏοΈ12


......Cike da dakiyar zuciya alqali ya cigaba da bin bayan motar jaguwa land cruiser prador yana sake neman layin IB domin bashi direction din Inda yake a daidai wannan lokacin sai dai Kiran na shiga ba'a d'auka ,ya kira ya kai sau goma bai d'auka ba wanda a wannan lokacin nazifi da alhj Tahir da hjy baseera ne tsaye a kanshi nazifi na qakokarin bashi taimakon gaugauwa , haushi ya kama alqali ya ciza gefen lips dinsa yana dukan sitiyarin motarsa "oh my goodness ko me yasa yaki d'aukar Kiran yanzu bayan bamu gama wayar ba ya ajiye ? yayiwa kanshi tambaya yana d'an rage gudun motarsa dan kar jaguwa ya fahimci su yake bi ."


yayinda a hankali motar jaguwa ke sharara gudu akan titin onipan a natse ya d'an juyo gefen da tanweer ke zaune shiru sanye da doguwar riga pinky colour ta yane kanta da mayafi baki haka ka'fafunta sanye suke cikin baby shoe baki masu matukar kyau tsintsiyar hannunta d'aure da agogo fata baki duk jaguwa ne ya bata su a wannin da suka gaba tare da yi mata albishir din maidata gidan iyayenta , kayan sun amshi jikinta sosai kamar dan ita aka yisu .
a hankali itama ta juyo cike da natsuwa fuskarta d'auke da murmushin jin dadi zata gida taga iyayenta cikin sa'a shima ya Kalli Inda take idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin bugawa qirjinsu yayi , alokaci d'aya sukai shiru tare da tsurawa juna idanu gbdy suka kasa d'auke idanunsu .
a cikin zuciyarsa yake yabawa kyawunta "hakika tsarki ya tabbata ga ubangiji daya halicci wannan yarinyar , kallo d'aya zaka mata kasan kyakkyawa ce ajin farko ."


a natse ya d'auke kyawawan idanunshi acikin nata sakamakon ganin yadda ta kafe shi da nata idanunta da suka wadatu da zararan gashi Ido gashi ko kifta su bata yi shi kuma mutun ne da bai fiyye son kallo ba bare kallo irin nata dake saukar masa da kasala tare da sha'awa me tsayawa arai , dan nan take kallonta kesa yanayin mutun ya sauya batare daya shiryawa hakan ba." kasa d'auke idanunta tayi daga kallonsa saboda baiwar kyau da Allah yayi masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika idan ta Kalli kanta a mirrow tana tabbatar da abinda mutane ke yawon fad'a akan tsarin jiki da kyawunta sai dai ko kusa bata kai shi komai ba , dan idan tana gabansa raina komai nata take domin gani take ya fita komai bama za'a a had'a ba .


muryarsa a kasalance ta fito kmr baya son yin magana "ki daina yiwa namiji irin wannan kallon domin duk macen dake kallon nmj haka yana nuna alamun bata da cikakken tarbiya ,mace da kunya da kauda Kai aka santa " ya qarasa maganar yana jan dogon tsaki dake 'batawa duk wanda akayi dominsa rai , runtse idanunta tayi gam tana zance zuci "nice mara tarbiya sannan mara kunya ?"tayiwa kanta tambayar ranta na quna da tuttukin bakincikin daya maye gurbin farincikin dake kwance a fuskarta , idan akwai abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce wulakanci irin wannan ba , kusan second biyu tayi idanunta na runtse kamar bataji abinda yace ba , cikin natsuwa taje d'aura laulausan tafin hannunta saman kushin din kujera domin gyara zamanta taji ya sauka akan laulausan hannunshi nan take yaji qirjinsa ya cigaba da bugawar da yake , itama qirjinta ya shiga dukan uku uku dan wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa .


ya sauke wani zazzafan ajiyar zuciya da numfashi alokaci d'aya ,
a hankali tayi karfin halin d'auke hannunta dake saman nashi a dalilin jikinta dake kyarma ta soma magana cikin fushi da bacin rai "karka sake furta min wannan kalmar domin kuwa kallon nmj bashi ke nuna rashin tarbiya ko rashin kunya ba dan haka bana son sake jin kalmar gareni domin ni din macece me tarbiya da kima idan Kai baka ganin kimata akwai dayawa masu gani ta k'arasa maganar hawaye na gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai tana goge hawayenta dake tsiyaya "wani kallon banza ya watsa mata mai hade da harara " lallai yarinyar nan ma ta sameshi yadda ya kamata ,shi take maidawa magana ?ai duk laifinka ne da baka gyara mata zama ba ka tsaya kana tattalinta, yarinyar da yaka mata ka wulakantata ta hanyar keta mata haddi tunda abinda yasa ka d'aukota kenan " zuciyarsa ta fad'a masa
haka numfashi ya fesar yana jin zafin acikin zuciyarsa , sam bai ji d'acin Kalmar daya fad'a mata ba, dan haka yayi tunani sake musguna mata jikinsa a sanyaye ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta yana sake watsa mata kallon bazan tayi saurin gocewa tana furzar da numfashi tare da hura hanci sannan taki waigowa ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta barshi tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda ya sha fad'a mata ."


ya matso kusa daita Sosai yana busa mata iskar bakinsa , bakinciki da takaici yasa tayi saurin janye jikinta daga nashi tana kallon gefen titi ,shiru yayi yana kallon gefen fuskarta numfashi ma da kyar take fesarwa bai san yadda akayi ba ya sake matsowa sosai ya d'aura kanshi a saman kafad'arta ,shiru tayi taki motsi sannan taki waigowa, jin shiru taki motsawa ya tabbatar masa da lallai fushi tayi dashi tsintar Kansa yayi da rashin jin dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had'e da jan dogon tsaki "me yasa zan ji babu dadi araina dan tayi fushi dani ?ya jefawa kwakwaluwarsa tambayar " Kiran daya shigo wayarsa ya katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu'bo wayarsa daga cikin aljihun wandonsa ya mannata a kunnensa batare daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar amminsa ce yasa shi barin jikinta da hanzarinsa dan yana expecting jin dadd'adan labari daga bakinta dan jiya da sukayi waya yake sheida mata ya kamata ace yaron dake son shefiqa ya turo iyayensa ayi maganar aure ,a lokacin ammi ta tabbatar masa da zatayiwa shafiqa din magana , ai kuwa abinda yake expecting ji shi ta fara fad'a masa yasa wayar a hands free ya d'aura wayar a kafad'arsa ya jingina jikinsa sosai a kujera."


"yaron nan gali wai zai turo iyayensa ranar lahadi tare da saka rana gbdy " murmushi jaguwa ya saki na farinciki yana cewa " Allah ya nuna mana ranar lafiya so nake na aurar dasu gbdy kafin nawa auren . "a'a ban yarda da wannan tsarin ba ,idan ma son samu ne a had'a auren da naka ba qaramin farinciki zanyi ba "shinkenan ammina yadda kikace haka za'a yi bani da za'bin da ya wuce naki zanyi k'okari naga anyi auren da nawa sai dai ki qara addua akan wanda kike min Allah yasa na samu me sona tsakani da Allah "zaka samu da iKon allah dan baka da makusar da wata diya mace zata kika ni dai fatana kayi kokari ka cika min alkawarina Ina son kyakkyawar suruka me nagarta idan son samu ne wacce ta fika kyau". wani narkakken murmushi ya saki kamar yana gabanta kana yace "kin samu kin gama ammina dan sai na kawo miki irin matan hurul'ain dan irinta kike bukata ta zama surukarki ya k'arasa maganar yana dariya tare da matsowa ya kamo yatsun hannun tanweer ya rike gam cikin nashi yana massaging a hankali , itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan take so , ita Kuwa tanweer gbdy ranta a dagule yake sbd haushin abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa dan duk tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa sannan tana Jin amsar da yake Bata cike da fushi ta soma k'okarin zare hannunta cikin nashi tana sauke wahalalle numfashi sai dai ta kasa kwatar hannunta dan haka tayita jan tsaki babu kaukautawa ganin hk yasa yayi sallama da ammi tun kafin ta tunhumeshi ,ya katse Kiran yana cewa "ki daina wahalar da kanki bake ba ko namiji dan'uwana na rike bai Isa ya kwace ba bare ke " ko kina tunani ni din irin lusaran samarinkanki ne da zaki gwada karfi dani ..?"ya karasa tmyr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa."


danne abinda taji ya tsaya mata arai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login