Showing 237001 words to 240000 words out of 259215 words

Chapter 80 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16533

na sashi yin abinda ya jima bai yi ba sai dai ayi masa ,tuki mana ai shi ya tukoni ,sai anjima daman na kiraka né kasan ina cikin koshin lfy dan nasan hankalika bazai kwanta ba yana gama wayar yace "wa zaka kira acikin wadan da suke karkashinka ?
"Mataimakina !"
Ya fada yana sauke numfashi "ina jinka karanto numbersa bai bata lokaci ba ya kirawo masa number sai da jaguwa ya boye number sannan ya kira tare da sata a hands free ,kira biyu cikin na uku A kwantagora ya dauka jaguwa ya manna masa wayar a kunnensa cikin harshen turanci yace "hello kwantagora ni ne commissioner hope baka cikin mutane ?okay abinda nake son fada maka rayuwata tana cikin hatsari ,yanzu abinda nake da kai ka faki idanun kowa ka fito da yaron jaguwa da'aka kama idan ba haka ba sai dai ku tsinci gawata okay!!!
jaguwa ya katse wayar ya gyara zama .


Bayan kamar minti talatin suka sake kira "sir gashi na fito dashi ina zan kai shi ?kaje under bridge din iyanapaja zan turo wanda zai daukesa yaji sautin wata muryar amadadin yaji ta commissioner bance karaka ka tafi da ma’aikatan sirri ba kaje dasu ni kuma nan zanji da commissioner. babu wanda zanje dashi dan allah karku taba lafiyrsa dan ….”
Jaguwa bai tsaya jin me zai ce ba ya katse kiran
Hankali a tashe kwantagora ya figi mota ya dauki hanyar iyana paja shi kuma jaguwa ya kira layin eku ya bashi umarni zuwa iyana paja cikin mintuna talatin kwantogora ya isa sai dai dole yayi parking ya jira kira daga jaguwa ,alokacin shima eku ya karasa ya kira jaguwa ya sheida masa nan take ya kira number kwantagora yana dauka yace "kana daidai ina ?
"Ina daidai inda ake shiga motar ondo ,da uniform ne ajikinka ?eh !Ya katse kiran ya kira eku sukayi mgn sannan ya sake kira kwantagora yace ya bawa scorpion waya ya mika masa wayar sukayi mgn suna gama waya kawai yaga scorpion ya fito daga cikin mota yana dingisa kafasarsa tun yana iya hangosa har ya daina akan titin mowe ibafo jaguwa ya ajiye commissioner ya kara gaba ."


A tare jaguwa da eku suka karaso gida gbdynsu babu wanda bai yi mamaki ganin Scorpion dan basusa rai zai fito acikin kwana daya ba ,lokacin da jaguwa ya fad'a musu abinda yayi kafin scorpion ya dawo sunyi matukar jinjina masa,a daren ya kira likitansa tazo tayi masa allura ta rubuta masa magani sannan eku ya taimaka masa ya shiga bayi yayi wanka dan jikinsa Kmr gyenbo yake jinsa.
kwana daya kawai da yayi a hannun police yaji kamar kwanaki dubu yayi ya kalli jaguwa da idanunshi daya kunbura "police basu da Imani a gobe suke shirin min izaya ta karshe duk da bansan wacce irin izayya zasu min ba a fadar wani police naji tsoro ya kamani ."tausayinsa ya kama jaguwa muddin ina raye bazaku tagayyara ba kwana sukayi suna hirar irin azabar da akayiwa scorpion.”


washegari Ana's yazo shima yayi matukar murna da dawowar scorpion "su jaguwa na jin dadin su a gida yayinda headquarter ta hargitse da gulmace gulmace na neman scorpion da akayi aka rasa "akwai wani abu guda daya dana rigada na yarda dashi yanzu
Commissioner da mataimakinsa suna da saka hannu acikin abinda ya faru "me yasa ka fadi haka ? Inji asp isa .Dcp yace "yaron dan fashin guda aka kama amman dan an raina mana hankali aka nemi commissioner aka rasa bayan awa shida aka nemi scorpion tare da mataimakin commissioner aka rasa sannan bayan wasu awanni aka sako commissioner wannan kawai ya tabbatar min dole akwai hadin bakinsu ,kowa fa yanzu su yake tunhuma ,mu kasa kunne muji ne ig zai ce amman lallai nasan sai an tuhumesu.”


******


Bayan sati daya


Jaguwa na zaune a dakinsa sanye da wondo baki da Riga baki mai hula yana duba wasu takardu masu matukar mahimanci kawai yaga an turo kofar dakinsa an shigo ya dago kanshi a hankali ya kalli Kofar tanwer ya gani tsaye yana ganin itace ya dauke kansa ta karaso ta zauna gefensa ya mike zai wuce ta riko hannunsa da sauri "please adnan ka tsaya kaji me ya kawo ni, banza yayi mata ya fixge hannunsa ya cigaba da tafiya ta biyosa tana nasa mgn "wai me yasa kake min haka ne ?
"Bansani ba amman banason na tsaya dake bare nayi magana dake ,saboda ka tsaneni ko?duk ma yadda kika dauka haka ne kar kuma ki manta nace karki sake zuwa inda nake me ya kawoki yanzu ?
"Na kasa samun kwanciyar hankali ,wallahi ina cikin wani hali akan fushin da kake yi dani ,Idan kina cikin wani hali ina ruwana me zan miki karki sake fad'a min cewar kina cikin wani hali akaina wannnan sakaran zaki fadawa bani ba .”


Zagayowa tayi ta kwanta a gadon abanyasa ta daura hannuwanta a daidai qirjinsa dake bugawa a tun shigowarta dakin ,kayi hakuri adnan dina nasan ban kyauta maka ba tana magana tana shafa qirjinsa ,"
amman kai ma kasan daga ni har kai muke da laifi , da tsayuwar da kayi kana fad'a min mgn a gaban dr da daukata kayi ka tafi dani ka yanke min duk hukunci daya dace bazan damu ba amman a gaban dr ko wasu bazan ji ..."
Riko hannunta yayi tare da fixgota ta dawo gabansa suna fuskarta juna atare suka sauke numfashi ta matso shi sosai ta zagaye wuyansa da hannunta daya yayinda dayan hannunta ke fama shafa fuskarsa zuwa faffadan qirjinsa tana kokarin kai bakinta kan nashi ya kawar da fuskarsa gefe ya rike hannuta dake qirjinsa da wanda ke wuyansa ya soma tafiya daita har ya isa jikin bango ya mannata still kokarin matso shi take ta hade bakinsu domin tasan suna haduwa guri daya shikenan fushin da yake yi daita ya kare amman yaki yarda .


"wannan bakin yafi karfinki yanzu sai dai wata .” yana gama fadar haka ya sakar mata hannu ya nufi kofar fita tabi bayansa da kallo qirjinta na dokawa da karfi har ya fice daga dakin idanunta na kallon kofa taji kamar tasa kuka ta runtse idanunta tana kokarin danne damuwarta amman sai da kwalla ta zubo mata, a qalla ta dauki sama da minti goma tsaye idanunta a runtse suna tsiyayar hawaye sannan ta budesu suka sauka akan gadonsa inda takardu da yake aiki akansu suke zube ."
Jikinta a sanyaye ta karasa inda takardun suke zube ta soma dubawa a irin haka ta san alhji tahir ne ya aikosu gidansu domin fashi wa mahaifinta dukkanin ayyukansa suna rubuce kuma tare da hotunan mutanen da yayi wa aiki a hankali ta soma dubawa cikin haka ya dawo dakin tana ganinsa tayi saurin ture takardun ta mike tsaye yaja tsaki sannan ya nuna mata kofa da babban yatsansa "out !."
Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya tana jan tsaki “aikin banza kawai dan kaga na damu da kai shine kake wulakantani daga yau bazan sake zuwa inda kake ba kaje ka auri duk wacce kake so bazan damu ba “daidai kenan na kuma ji dadi da kika yankewa kanki shawara me kyau nima kuma na huta da naci .”


“Allah ya saka min cutar da kayi min bazan taba yafe maka ba mayaudari kuma makaryaci kawai , me muguwar zuciya har ta juya tana kuka ya riko hannunta ya dawo daita jikinsa yana kallon fuskarta da hawayen dake tsiyaya a idanunta “ni ne mayaudari tanwe ? Me yasa kika kirani da wannan kalmar ?tayi masa banza tana kokarin zare jikinta ya rike kugunta sosai “me lie tanwer ?kiyi bude baki ki min magana dont think am play with you ,”Who is playing with you too? bai yi mamaki dan yasan zata iya fiyye da haka .”


“You also call me makaryaci karya me nayi miki ? “bansani ba ka sakeni na kama gabanaba ,sai ka qara gani na arayuwarka sannan zaka cigaba da wulakantani “All these you can’t happy if they call you that and you are calling me mayaudari makaryaci why ?dan ban amincewa soyayyarki ba shine na zama makaryaci mayaudari me muguwar zuciya “?tsaki taja ta fixge jikinta ta fita da sauri murmushin gefe baki yayi yana cewa “tanwer kenan bazaki gane ba allah ya tsareki ,kamar wasa gbdy cikin kwanacinki tanwer bata kira shi ba sai kuma yaji ya kasa samu natsuwa a qalla sai da yayi kwana goma bai ga kiranta ba ko kiransa akayi yana allah ya duba ya gani ko itace sai yaga ba ita bace ya shiga damuwa sosai sai dai ya danne ."


********
Sannu a hankali scorpion ya samu sauki ya dawo tamkar yadda yake babu inda baya zuwa Adaidai wannan lokacin suka samu sakon gayyata daga nabel saboda suyi aiki dashi ,nabel jami'in tsaro ne da kasa take alfahari dashi kuma rikakken dan ta'adan ne da yan taada ke ji dashi ,shi kansa dila ne na safarar miyagun kwayoyi uniform dinsa ne kawai ke rufe da asirinsa , akarkashinsa akwai jami'an tsoron da suke attare dashi ciki har da shugaba efcc gashi mugu ne na karshe bashi da Imani abu kadan idan kayi masa zai aikaka lahira baya yafiya ."sai byn da jaguwa da Ana's suka zo suka fahimci bikin cikar shekararsa ake yi dan haka suka samu guri suka zauna suna kallon manya masu kudi na garin lagos ,da kusoshin gwanati dake shigowa sai dai har lokacin nabel bai samu damar shigowa ba ."




tsaye nabel yake cikin fararen suit yayinda gbdy yaransa ke tsaye cikin suit bakake , wani mutun tsaye a gefensa yana kuka yana bashi hakuri amman ko kallonsa bai yi ba ya kai Karan sigari bakinsa ya kunna ciki muryar kuka wannan mutumin yace "ranka ya dade dan allah ka taimakeni nasan nayi maka alkwarin bazan sake fita da sirrinka ba wannan ma Kuskuren né ka taimakeni ka gafarceni ya fada yana goge hawayensa "duk mutumin da bai yi Kuskuren ba bazai taba yin kuka ba ."
nan take mutumin ya fara dariya "ranka ya dade ai ba kuka nake yi ba gashi ina dariya " duk mutumin da bai yi Kuskuren ba tô bazai tabayin dariya da wuri haka ba, yana gama fadar haka ya soma tafiya wasu daga cikin yaransa suka biyosa ciki har da mutumin dake kuka ,cikin sauri mutun daya acikinsu ya bude masa kofa mutumin ya biyosa yana kuka " ni yanzu ranka ya dade ka fada min me zan maka ka huce abinda nayi maka lokaci "ni a yanzu babu abinda zan ka iya min nima kuma babu abinda zan maka yayi mgnr yana turesa da hannunsa "kar ka sake bina rayuwarka tazo karshe ya wucewarsa."


mutun biyu cikin yaran nabel suka rikesa ta karfin tsiya suka danne masa makoshi yana ihu ataimakesa amman ina cikin kankanin lokaci numfashinsa ya bar gangar jikinsa lokacin da nabel ya samu shigowa hadadden hall din dazaa gabatar da birthday dinsa dayawa mutane sun mike tsaye domin girmama da tayashi murna sai dai banda jaguwa anas yayi kokarin mikewa amman jaguwa ya dawo dashi a haka yazo ya wucesu yana dagawa mutane hannu wasu kuma yna mika musu hannu .”
ya zagayo ya sake dawowa inda jaguwa suke tare da babban yaronsa ya tsaya yana gabatar masa da jaguwa "boss wannan shine jaguwa ya mika masa hannu yana murmushi "jaguwa nice name "gaku yara daku wallahi amman kuna yin abubuwan da suka fi karfin shekarunku nabel ya matso da bakinsa daidai kunnen jaguwa "ka tsaya a iya matsayinka sannan ka nemi alhj tajudenni ka bashi hakurin wulakacin da kai da wannnan banzan abokin naka kukayi masa domin har idan kukayi Kuskuren kin bin umarnina ya dauke fauskarsa akan jaguwa zuwa ta Ana's "ina tabbatar maka zan harbeka zan fasa kwakwaluwarka ina fatan kun fahimceni ni ba kamar commissioner bane yana gama fadar haka ya wucesu ran jaguwa ya baci matuka a zahiri ake iya hango tashin hankalinsa tunda yake bai taba samun wanda yayi gaba da gaba haka ya fada masa magana ba sai yau hasalima shi mutane suna shakkar fada masa magana."


bai iya cigaba da zama agurin birthday din ba ya juya shima anas ya biyo bayansa suka shiga mota dukkanisnu agidan baya suka zauna eku ya tayar da mota sai dai babu wanda yayi magana acikinsu wanda hakan shi yafi daga hanakalin anas yaso yace wani abu akan nabel gdy yafishi shiga damuwa sai fesar da numfashi yake jikinsa na wani irin rawa "shiyasa nace bazan zo ba ka takuramin ga irinta nan "bashi da hanyar da zai iya ganawa damu bare ya samu damar fada mana mgn son ranshi sai ta wannan hanyar," kaga a haka ma munfi karfinsa domin kuwa yaji tsoron zuwa inda muke inji cewar jaguwa.


"har ya isa yayi mana kashedi da barazana "wai me yasa kake yin haka né Ana's ?yanzu kan d'an wannan abun zaka nemi ka daga hankalinka wallahi wannan karamin abu ne, ya fad'a adaidai lokacin da suka karaso bakin get din gidan anas jaguwa ya bude kasancewar yana da remut din get din gidan a hannunsa suka shiga anas ya fito koina ajikinsa rawa yake jaguwa ya kamosa ya shigar dashi cikin babban falonsa "karka kuskura ka sakawa zuciyarka tunani har matarka ta fahimci kana cikin damuwa "ko dai bakaji abinda ya fada mana bane ?"


"naji komai mana amman babu abinda zai iya "ina ban yarda ba wannan mutumin zai yi wani abu "byn shi sau daya kawai ya fada karka manta mutane nawa muka sha fadawa hakan kuma bamuyi komai akansu ba "mu muna da wankakkiyar zuciya né amman su fa ?xuciyarsu cike take da mugunta ni idan ma mutuwar ce gara ni na tafi, dan idan wani abu ya sameka gbdy babu wanda zai tsira dagamu har ahlinka "tô sai me ya gwada mana idan zai iya ."
anas ya girgiza kai dan shi bai taba jin wani abu zai faru dasu ba sai a wannann lokacin .”


jaguwa ya kira sunansa anas ka shiga ciki gurin matarka ka kwanta karka manta gidan gbdy a tsare yake da matakan tsaro tun daga get din gidan nan har zuwa katangar gidan to me zai tsorata?
" Kai fa idan wani abu ya sameka yaya kake son muyi babu abinda zai sameni kaima babu abinda zai sameka kamr yadda kayi auren haka nima zanyi ,
kalleni kaga ,anas ya dago ya kallesa nan da wata biyu zanyi aure inshaallahu ."
"What ?
“Abinda kaji na fada haka ne ,Ai ansa bai san lokacin da murmushin farinciki ya subuce masa ba ya rungume sa ajikinsa yana shafa bayansa " kai amman ka faranta min rai "saboda kai ne anas amman ban so nayi aure a yanzu ba ya fada yana zaresa ajikinsa yana cewa "sai dai safe ya juya ya fita anas ya kulle koina ya nufi dakin matarsa .
Koda jaguwa ya isa gida ya kwanta a gadonsa flat yana tunani maganar nabel bai yi zurfi cikin tunaninsa ba tunanin da yafi kowani tunani tasiri ya kawo masa ziyara daga nan bai san sanda bacci barawo ya sacesa ba .




*********
Washegari da yammaci ya isa asibitinta yayi parking ya kira layinta cikin kankanin lokaci ta fito sanye da doguwar riga zuciyarta cike da mamaki take takowa zuwa haraban hospital ta iske shi jikin motarsa tsaye fuskarsa a hade yayi mata alamar ta shiga mota tayi shiru tana kallonsa fuskarta dauke da alamr tambaya ,"shiga ina son magana dake "jiki a sanyaye ta bude gaban mota ta shiga ta zauna zuciyarta na rawa dan bata san da me yazo mata ba allhairi ko akasin haka ya zagaya ya bud'e bangaren direba ya shiga ya zauna ya tada motar "ya naga kana kokarin tafiya dani ina zaka kai ni byn mgn kace zamuyi ?
Tayi mgnr a matukar tsorace .


“zanje na cinyeki ne bata sake yin mgn ba shima haka bai tsaya akoina ba sai bakin maria beach byn yayi parking ya fito itama ta fito tana sauke numfashi dan sai yanzu hankalinta ya kwanata tana kallonsa ya jingina bayansa da mota itama tayi kamar yadda yayi bayan wasu mintuna ya juyo ya tsura mata idanunshi "Kinsan abinda yasa na kawoki nan gurin "?ban sani ba amman nasan ba dan saboda sumbata bane ,ke abinda ya fara zuwa zuciyarki kenan sumbata yayi taku daya biyu zuwa uku ya tsaya yana kallonta mace a rayuwarta sumbata , kywun jiki me kyau ,tsayu da kuma fadi qirji shi suke kira soyayya ,magana akan jiki tsayi ta wan bangare kenan gbdy a haka kake kallon qaunar da nake maka ?


Ya matso kusa daita sosai har suna iya jiyo bugun zuciyarsu da saukar numfashinsa "sam ba haka bane "to me kake nufi da lissafosu "?Ya rungume hannuwansa duka a faffadan qirjinsa yana kallonta itama cikin kwayar idanunsa take kallo "nasan zaki iya fadar abu bayan idona sannnan idan ina nan zaki iya fadar sa koma menene amman ni bazan taba canzawa ba naunayen ajiyar zuciya ta sauke taya akayi ka canza da sauri haka adnan ?”.


“nayi tsamanin kazo ka sake haukatani ne ."


“kiyi min shiru da wata magana shiru din tayi tana sauke numfashi." a wannnan zamanin mata suna daukar maza a wani abu da zarar sun samu wani abu daga gurinsu sai suyi murna da zarar kuma yayi masu abinda suke bukata sai suyi farinciki ,tsuke bakinta tayi sannan ta motsa lip's dinta sunayin haka ne ga wanda suke so ni ko galashinka na kalla farinciki nake sosai bare ka bani na gani shiru yayi yana cizan lip's dinsa na kasa yayinda idanunshi na kanta” idan wanda kike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login