Showing 30001 words to 33000 words out of 259215 words

Chapter 11 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16512

tal yarinyata mafi soyuwa acikin raina ta yaya kake tunanin zan iya kwantar da hankalina ?
" waɗan nan yan sanda dake rike da case din basu san aikinsu ba basa komai kawai lamuran gabansu suke idan bazasu nemo min yarinyata ba ni na fita na nemota a duk inda take, gabad'aya ta gama fita haiyacinta sambatu kawai take zubawa hawaye na gangarowa daga cikin kwayar idanunta "wayyohlly tanweer ko a wani hali kike ciki" ?"Allah kasa tana cikin koshin lafiya , Allah kasa basu taba min lafiyarta ba .."


Hajiya Zainab ta zabura daga zaunen da take ta mike tsaye kamar an mintsineta jikinta na wani irin rawa ,ta soma neman police headquater ganin take kamar basa komai akan bincike wasu abubuwa take kamar zarariya ko mahaukaciya sabuwar kamu ..


"Sp me ake ciki akan batun 'batan yarinyata har yanzu shiru banga aikinku ba ?" idan har haka aikin police yake hakika bashi da wani amfani gareni yau tsawon kwana biyu har yanzu babu wani tsayayyen magana akan batan yarinyata "
"muna kan aiki ranki ya dade ya fadi haka yana cizan gefen lip's dinsa da tsotsa geyarsa "dakata ni ba wannan na tambayeka ba Kawai inda yarinyata take nake son sani tayi maganar wasu zafafan hawaye na sake wanke mata fuska "ranki ya dade hakuri dai zaki sake yi, babu wata hanya da zamu samu damar gano inda waɗan yan fashi suke sai Kira daga yan fashi domin bukatar wani abu daga gareku ta haka ne kawai zamuyi saurin kamasu " Alh Abubakar dake tsaye a bayanta a tun sanda ta soma magana yayi gyaran murya ya amshi wayar hannunta yayi disconneting din kiran "kiyi hakuri zainab tayi saurin zubewa ajikinsa tana kuka"yarinyata tanweer " "inshallahu za'a kamasu nan kusa ,
Dole akamosu sannan dole a hukuntasu da hukunci mai tsanani domin laifinsu daidai yake da wadan da sukayi kisa..


****


Gudu jaguwa yake akan titi ya yaga wata mota baka kiran marcende C class na bin bayansa duk inda yabi sai motar tabi a karshe ya dauke bakin glass ya rufe kwayar idanunshi ya dauki hanyar da zata kai mutun aja ,gudu yake sosai har ya 'bacewa motar ya bi wata hanya mai ciyayi ya ja numfashi ya fesar jikinsa na bashi Alh tanko gote ya kira mahaikata, yanzu kam a hankali yake murza stearing motar yana sakin murmushin cin nasara Idanunshi ya ɗan lumshe ya ci-gaba da driving dukkanin alamu ya nuna yana cikin jin dadi ya gama da Tanko gote bai yi tunanin abun zai zo masa cikin sauki ba sai gashi yayi nasara kara lumshe idanunshi yayi .....


yayinda sp yusif ke tsaye a cikin wani kango sanye da bakin suit tare da wasu daga cikin yaransa da suka biyosa aiki daman kuma ya rabasu kashi kashi ne kowanensu da bangaren daya ɗauka ,wayarsa ce tayi ƙara ya ciro wayar daga aljihunsa cikin sauri yana duba screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya dauki kiran da sauri tare da mannawa a kunneshi "hello "
"Yes noted "
Inspector hasan dake fuskantar shi yace "how far ?
"We have to move immediatly "boss there won't be a problem there be danger today let us move ,let's move suka faɗa gaba-daya a hankali motar Jaguwa ke gudu ganin hanyar so silet ga duwatsu kaca kaca dole ko yana son yin gudu yabi a hankali yayinda yan-sanda ke la'be hagu da dama domin ƙoƙarin cafkarsa ..


A tsanake sp yusif ya fito daga maboyarsa ya sha gaban motar Jaguwa hade da tsaita bakin bindigarsa ga glass din motar Jaguwa slow motar Jaguwa ta koma tafiya a hankali har yayi kusa da sp cikin haka yaran sp dake boye hagu da dama suka bayyana suka saita bakin bindigarsu pistor "crack and shut basu tsaya wata wata ba suka budewa motar wuta bisa umarnin da'aka basu harbi motar suke da iyakacin kwarewarsu har sai da suka tabbatar da sun yiwa glass din motar ratsatsa...


DARLING'S




💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*



WATTPAD @HAUESH


bismillahirrahmanirrahim


https://my.w.tt/lcJskJdtpbb


🅿️10


...A hankali sp yusif ya sauke bakin bindigarsa yana haki yana takowa a hankali har ya karaso jikin murfin motar jaguwa ya ja ya tsaya tare da d'aura hannunsa ɗaya a saman mota "the wages of sin is death ......."
ya furta haka yana duban inda yaransa ke tsaye rike da bindiga "yau dai munyi nasara kashe tantirin ɗan fashin daya addabi kasa da kasa ,Allah na gode maka daka bani dama da ikon kawar dashi daga doron duniya , isar da gawarsa headquater ma wani matakin d'aukaka ne garemu ,na dade ina addu'a akan zuwan wannan rana sai gashi tazo mana cikin sauki dole mu samu double promotion...... " ya karasa maganar yana kallon sararin samaniya zuciyarsa fes cike da matsanancin farincikin samun nasara .


"ya sake buɗe bakinsa da niyyar sake yin magana yaji an daki murfin kofar motar da karfin gaske kofar ta buɗe wanda hakan yayi sanadiyyar da hannun jaguwa ya bugu da murfin kofar dashi kanshi sp yusif dake tsaye yayi taga taga ya koma baya sannan ya tsaya bisa kafafunsa yana kallon motar .


Mutuwar tsaye suka yi gabad'aya suna kallonsa take bindigar hannun sp yusif ta subuce yayi saurin sake ja da baya idanunshi na kan jaguwa dake ƙoƙarin fitowa daga cikin motar, duk ilahirin jikinsu rawa yake har sp yusif wanda hankalinsa kusan yafi na sauran tashi dan yanayin bugawar zuciyarsa da yanayin tsoronsa sai ya baka mamaki tamkar ba jami'in tsaro ba "


cikin isa da izza jaguwa yake takowa zuwa inda sp yusif yake tsaye , ya tsaya nisa kaɗan dashi wanda bai fi taku biyu su fuskanci juna ba , idanunshi dake a lumshe ya ware su fesss akan sp yusif yana ciza gefen lip's d'insa na kasa,sp yusif ya kalli jaguwa kamar zai yi kuka saboda gigita da ganinsa a raye da yayi , tunda yake bai taɓa ganin abinda ya d'aga masa hankali irin wannan ba , "bai taɓa ganin dan adam din da aka yiwa harbi irin wanda suka yiwa motar jaguwa ba amman ya rayu har ya samu damar fitowa daga cikin motar cikin isa da izza ,tabbas yasan akwai wata a kasa ,wannan abu akwai tsarkakkiya acikinta "


Jaguwa ya had'iye dariyar sp yusif dake neman kufce masa saboda gabad'aya ya gama karantar yadda sp yusif da yaransa suka tsorata dashi ,dan gabadaya fuskokinsu ya sauya daga farinciki zuwa matsanancin tsoro da firgici kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tashin hankali mai tsanani ...


"waye kai sp yusif karaye ? mutumin da cin hanci da rashawa ya aura tun kana ƙaramin mataki har zuwa yanzu daka taka wannan matsayin , har kake godiya ga Allah bisa samun nasara akaina "wani mataki ka taka tukunan ma a rayuwarka da zaka so kama mutun irina "?yayi masa tambayar yana kafeshi da kyawawan idanushi hade da sauke numfashi .


"Ya kamata kusan ko waye ni kafin ku dinga bibiyar rayuwata kana min kallon mamakin ko ? "Kana mamakin yadda na rayu ko ? Zan so bude maka hanyar da zaka fahimci ko wanene ni da kai da sauran tawagar dake bibiyar rayuwata amman bazan yi ba zan barku cikin duhu da wasi wasi da kai da waɗan nan yaran naka daka taso gaba " babu abinda zaku iya akan jaguwa sp yusif karaye , ba ku ba hatta shugaban tawagarku gaba-daya wato commition of police yayi kankatar da zai iya gaba da gaba dani bare kai da yaranka ya karasa maganar a fusace yana nuna sp yusif da yatsansa "


"a kasar nan kowa abinda ranshi yake so yake tare da aiwatar da son zuciya akan kaskantattu marasa galihu , "to bari kaji wani labari da baku isa ba dubunku ma basu isa suja da yaran jaguwa ba bare shi kanshi jaguwa , ni nan nafi karfinku nafi karfin hukuma kuma yanzu na sama addabar rayuwar manyan kasar nan ya karasa maganar yana dukan qirjinshi yana murmushi ......


"Anyway nasan daga inda shiriku yake kowanen daga cikinku ƙoƙarin raya kanshi da ahlinsa yake ba domin kare kasa da kasa kuke yin komai ba domin raya kanku kuke ,dana soma wannan aikin domin ɗaukar ran wani to da ina tabbatar maka kai ne mutun na biyu bayan wancan tantarin tanko gote ...."


duk wannan Maganar da yake yana yi yana jujjuya jikinsa ne kafin daga baya ya shafa fuskarsa ya cire fuskar dake manne da fuskarsa wata fuskar ta bayyana da tsananin kyau da sage zagaye daita "ka kalleni da kyau sp yusif muddin akaina zaka samu double promotion ina tabbatar maka bazaka taba samu ba har duniya ta nade saboda jaguwa mutun ɗaya ne mai fuska daban daban yana gama maganar ya zaro bindiga daga kugunsa ya saita daidai gwiwar sp yusif ya sakar masa bullet biyu a jere wata irin razananniyar qara ya saki tare da durkushewa a gurin "jaguwa ya nuna sa da bakin bindiga "bance ku daina farautata ba , sai dai ku shirya iya shiryawa kafin ku tunkareni yana gama fadar haka ya juya a fusace tamkar mayunwacin zaki yana taku kamar baya son taka kasa ya buɗe motarsa ya shiga yayi mata key a hankali motar ke motsawa tana moving gbdy suka bi bayan motar da kallon mamaki har sanda motar tayi musu nisa .....


*****


A natse yake murza stearing motarsa, lokacin daya shigo unguwar aguje su Anas dake tsaye a kofar gidan sukayi gurin motarsa suna murnar ganinsa, kanshi kawai ya girgiza yana murmushin sannan ya saita hancin motarsa get din gidan , kamil ya zundumawa mai gadi kira ganin zai 'bata musu lokaci yasa suka shiga sauri saurin buɗe masa tafkeken get din gidan yana gama karasa shigowa ko gama daidaita tsayuwar motar bai yi ba suka hau kiciniyar bude motar suka fito dashi tare da d'aga shi sama suna ihun jin dadin sake ganinsa "Winner ooo winner Winner ooo winner ,Winner we don win ooo winner
Pata pata we go win forever winner suka nufi babban parlou'n gidan dashi suka zaunar dashi akan kujera mai zaman mutun uku , Anas ya karasa da sauri ya bude fridge ya d'auko masa power horse mai sanyi ya bude ya mika masa yana zama kusa dashi cike da tsananin murna jubi ya d'auko ruwa mai sanyi ",wayyo Allah nah jaguwa nasan kasha wahala ko da ganin yadda motarka tayi " "babu wata wahala tunda gani a gabanku yanzu"
a tare sukayi dariyar jin dadi sannan sukace "Allah mun gode maka daka dawo mana da farincikinmu lafiya "shine abun godiya ya fada yana furzar da iska "gasky kai din na daban ne namijin duniya ,jaguwa ya ɗan lumshe idanunshi sannan ya gyara zamansa ya soma ƙoƙarin cire yar saman rigarsa Anas yayi saurin cire masa jubi ya dawo gabansa ya soma cire masa takalmin kafafunsa ya saura safa kallonsu kawai yake yana girgiza kai "kasan tun da ka bar gidan nan babu wanda ya sakawa cikinsa wani abu tsabar tashin hankali inji cewar jabir "


"uhmm bari jabir ban taba tsintar kaina cikin tashin hankali irin na yau ba wallahi da zarar na runtse idanuna sai inga kamar wani abu zai same shi anas ya fada yana shafa fuskar jaguwa ,ya ɗan juyo ya kalle shi yana haɗe rai "duk cikin murna dan ban maka kiss ba suka sa dariya gabadaya "yau fa akwai celebrate jubi ya fada yana dauko musu kwaban win ya jere a gabansu "kamar kuwa kun sani ,"ina zamu samowa jaguwa mai zafi data iya chilling fiyye da zahra ?
"ai babu wata mai zafi sosai data wuce zahra ita zan kira yanzu "zaro ido jaguwa yayi "lallai ku yanzu wannan shirmen ne a gabanku ni yadda zanga ammina nake tunani ba wannan shirmen ba "
"Ogbeni ejalo shaye jare Oti sele oppprr kpk Eyonla chuwale sir🙌🏽 se kinwa gbenusi no be atenu " zaka gun ammi amman amman dole zahra zata yi aiki "


A hankali Anas ya kira su eku remo cikin minti goma suka karasao suka shiga fito da buhuhun kudadde da jaguwa yazo dasu suna shigowa dashi daya bayan daya , yayinda su Anas ke zaune suna mamaki yadda har ya iya rabo tanko gote da wadan nan makudan kudaden shi kadai , cikin minti da bai wuce goma ba sukaji mai gadi yana kwankwasa kofa jubi ne ya tashi ya tsaya daga bakin kofa ya bude , cikin yaren turanci mai gadi yace "akwai wani bako da yake ta zuwa gidan nan yau shine zuwansa na biyar baya samun nasarar ganin oga yana fama da matsalolin rayuwa ne gashi yana da yarinya mara lafiya mai kimanin shekara goma tana igondo general hospital ,likitoci sunki bata kulawa sakamakon rashin kuɗi , kafin jubi yace wani abu jaguwa yayi gyaran murya , juyowa jubi yayi a hankali ya dawo inda suke ya tsaya yana duban jaguwa nuna masa wata yar kamara jaka mai zip yayi da hannunsa "zuba masa adadin da zai cika jakar nan ka bashi "yesssss boss an gama Allah yaja da nisan kwana ,jakar ya cika da kudi yayi ziping dinsa ya mikawa mai gadi da hanzari mai gadi ya amsa jakar ya rungume ya juya ya nufi kofar waje ya mikawa mutumin , mutumin na ganin kudin gabad'aya ya rude ya gigice ya soma wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya,lallai baa rasa na allah koina kuma yadda aka bashi labari wannan matashin mai tsatsanin kirki da tausayi haka ne, take ya nemi mai gadi da yayi masa iso gurin mai gidan domin yi masa godiya , amman mai gadi yaki saboda sanin da yayi wa jaguwa baya son godiya ko kyauta yayi maka kace ka gode sai yace ka godewa Allah ,duk da ban samu ganinsa ba tabbas zan dangwama ina yiwa rayuwarsa addua domin allah ya buda masa kofofin farinciki kamar yadda yayi min , iri mutanen da ake so kenan masu taimako dan allah"
" karka damu ba kai ba duk wanda kaga yana bukatar taimako kana iya masa hanya wannna gidan gidan masu tallafawa rayuwa marasa shi ne da marasa galihu a haka nasan shi da zaka zo kofar gidan a duk safiyar allah zakayi mamakin yadda mutane suke shawagi kayi masa adduar kamar yadda ka kudurta domin shine zai zama tsani na rayuwarsa "mutumin ya sauke numfashi ya kama gabansa yana masa addua.


Duk yadda yake kallon buhubuhun kudaden dake gabansa hakan bai sanya shi jin farinciki ba, waɗan nan makudan kudadde daya amsa daga Tanko gote ba zai taɓa goge abinda yayi masa a shafukan rayuwarsa ,sannan bazasu taɓa maida masa jin dadin daya rasa a shekarun da suka gabata ba, fuskar ƙaramar kanwarsa ne ya shiga yi masa gezo a lokacin da numfashinta na karshe ke shirin barin gangar jikinta tana kallonsa hawaye na turereniyar zubowa daga kwarnin idanunta bakinta na amai jini ,yayinda mahaifinsa da mahaifinyarsa ke manne da jikin bangon daki sun dawo tamkar matattu a tsaye tsabar firgici da tashin hankalin halin da diyarsu ke ciki kukan zuci dana zahiri suke a wannan lokacin har rai yayi halinsa wanda sanadiyyar haka zuciyar mahaifinsa ya buga take shima yace ga garinku ......."


"Anas ya dafa kafad'ansa saboda yasan abinda yake tunani "ka manta da abinda ya faru, jiya ta wuce mu fuskanci yau samun waɗan kudadden kadai ya isa ya goge abinda ya faru a zuciyarka sannan waɗan nan kudade zasuyi maka abinda basu yi maka a da can baya ba "


"bazasu yi ba Anas rayuwar mahaifina data kanwata sun fi min waɗan nan kudadden mahimman ... hatta mahaifiyata da zata san abinda ke gudana a rayuwata zata iya saka hannu cikin raba Tanko gote da duk wasu masu hali irin nasa daga duniya "me yasa bazaka ɗauke shi daga duniyar gaba-daya ba kowa ya huta ?inji cewar kamil , girgiza kai jaguwa yayi sannan ya fashe da wani kuka mai cin rai da ban tausayi yana tuna rayuwar da suka yi a baya shi da yan'uwansa rayuwar kunci da talauci da rashin galihu , a hankali komai ke dawo masa gabad'aya sukayi kanshi suna bashi baki da hakuri "


ya mike tsaye yana layi ya rataye yar saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login