Showing 42001 words to 45000 words out of 259215 words

Chapter 15 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16581

tayi tana zance zuci" shi take mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace , tunda suka had'u yake kyautata mata ta hanyar bata kulawa sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce ya 'bata mata rai ta hanyar fada mata baqaqen maganganu . tasan ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata kyau sama sama ta dinga fidda numfashi tana danne damuwarta "dan Allah direba ka taka motar nan da sauri Ina son d'aura kwayar idanuna akan iyayena wad'anda suka zamo min bango abun ma jingina kuma farincikina nasan suma nice farincikinsu rashina baqaramin babban tashin hankali bane garesu suna can suna mararina"


"shiiiii......." munafurcin banza kawai kina dai son kije kiga wad'an can rubabbun samarin naki barin wancan me murya gangarin da bata dadin saurara "ya Allah ta furta dan sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace "kafa san irin maganar da zaka dinga fad'a min dan ni din ba motar haya bace bare kayi tunanin Ina tara kwashe kwashen samari Ko da yake yau ne final kasancewata da kai zaka mayardani gidanmu na gode da taimako ta k'arasa maganar tana murgad'a masa 'karamin bakinta "karki gode min ki godewa Allah sannan na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace " aikin banza kawai Nima daga yau ai bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan dogon tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke fuskarsa yace "wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa'anki ne da zaki dinga ja min tsaki yayi tmbyr yana murd'e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa "a'a kayi hakuri hannuna zafi bai mata magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun tare da bud'e tafin hannun ya tsurawa tsakiyar hannunta kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d'aura dayan hannunsa ciki ya fara mata tafiyar tsutsa wani irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin da take saukewa da kyar tare da jin wani sauyi na dabam a sansar jikinta. Shima wani irin abu yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu ,wayarsa ya d'auka ya soma danne danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake tukasu ."eku ka duba wayarka na tura maka sako eku yace "noted boss ya tura wa su anas dake bayansa Sako kamar yadda ya turawa eku sannan ya koma ya jingina bayansa ya runtse idanunshi .."


motar bata tsaya a koina ba sai gaban katon get din Rita Lori hotel dake onipan , get din already a bud'e yake kamar Koda yaushe security's ne tam ciki da wajen hotel din saboda manya masu kudi da kusoshin gwanati dake zuwa da manya manyan yan fashi da makami , gurin fitowa daga ciki hotel din dabam haka zalika gurin shiga dabam , eku ya sanya hancin motarsa cikin Rita Lori, d'aya daga cikin security's din gurin ya mike da sauri ya zare karfen da sakale Wanda ke bawa mutun damar shiga, eku ya samu guri ya soma k'okarin parking adaidai lokacin da motar alqali danasu anas ya shigo
haraban hotel ne dake da bangare dabam dabam dan shakatawa sam tanweer bata fahimci Inda suke ba saboda ranta dake 'bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune ya bud' mata kofa "fito ko ".ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa
ta yunkura a hankali ta fito tana jiran ta ganta a haraban gidansu kawai ta ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar hannunta ya fara tafiya daita zuwa cikin had'ad'd'en club din dake ciki, banda sautin kidi da waka baka Jin sautin komai "Ina ne nan ka kawoni ? tayi masa tambayar muryarta a tsarke "gurin shakatawa yayi maganar a dake yana cigaba da tafiya daita yayinda har lokacin hannunta na cikin nashi jikinta na rawa taja ta tsaya qirjinta na wani irin bugu fiyye da kaida juyowa yayi ya tsaida idanunshi a kanta take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke "gida mukayi da Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau sotsan lips dinta ." ni gaskiya gida nake son zuwa ba nan ba ka Kai gidanmu tayi maganar kamar zatayi kuka dan tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace "Kinga dan Allah ki kwantar da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d'aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin maganrsa " kennan idan ta fahimci maganarsa shine d'an fashin daya d'aukota daga gaban iyayenta ? wani irin bugu gabanta ya sake yi da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k'okarin tsayawa hankalinta yayi matukar tashi ta dinga maimaita kalmarsa ta karshe daya furta ."


a hankali ta shiga girgiza Kai "no no impossible bashi bane sam bai yi kama da irin wad'an nan mutane ba dukkanin alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne zuciyarta ta tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba da tafiya cikin Isa da izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa wani yawu ta hadeye tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta shiga d'aga ka'fafunta kmr walkiya ya nemeta ya rasa Yana nan tsaye su anas suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa kowanne ya kama gabansa kasancewar kowannensu akwai bangaren da yafi so ."


*******
Tsaye tanweer tayi aguri d'aya kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda ta tsinci kanta a yau din nan , ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya samu guri ya zauna akan d'aya daga cikin fararen kujerarun dake gurin ta waiga bangarenta na dama tsaye taga wasu matasan mata su biyu akan stage daya sanye da kaya wando da riga yellow dinki gbamu gbamu ka'fafunta sanye da sander shima baki hannunta rike da speaker tana rera waka yayinda yaranata ke mata amshi dayar mata itama sanye da wando da riga sai dai nata kalar ja ne gbdy haraban gurin shirye yake da fararen kujeru da table a tsakiya ."
tun daga nesa mawakiyar ta fara bud'e hakoranta dan ganin anas na shigowa nan take salon wakar ya canza salo ta soma masa waka tana sake fad'ada fuskarta da murmushin irin nasu na gogaggun yan duniya Shima murmushi ya sakar mata sannan ya soma qarasowa Inda take itama ta nufo shi suka rungume juna har da kiss ta manna masa a goshi kana ya nufi gurin empty chairs ya samu guri ya zauna zamansa ke da wuya ma'aikatan gurin suka qaraso garesa tare da kwalaben giya da soyayyen nama da yaji yaji domin sun san irin abinda yake bukata kenan sa'banin jaguwa da malt kawai yake sha idan yazo.


"subhanallah tanweer ta furta a ranta tana mamakin "wai yau itace a irin wannan gurin wasu hawaye ne masu zafi sukayi nasarar biyo gefen fuskarta tana k'okarin sharesu jaguwa ya qaraso gabanta yana girgiza mata Kai alamar kartayi kuka sannan ya rungumota jikinsa ta kwantar da kanta a faffadan qirjinsa dake fitar da sihirtaccen kamshi , cikin tsananin tashin hankali yasa hannunsa ya share mata hawaye ya sake rungumeta tsam yana zagaye weist dinta da hannunwansa duka wani irin tsalle hade buguwar zuciya tanweer tayi Wanda har hakan ya haifar mata da tsayawan numfashi na wasu yan mintuna haka duk wani tunani dake tafiyar da bugun zuciyarta sai daya motsa ta dinga Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta.
yau ce rana ta farko da jaguwa ya rungume mace acikin mutane batare daya ji komai ba ajikinsa hasalima wani sanyi yaji yana bin jijiyon jikinsa ,bakinsa ya Kai cikin kunnenta yana mata rad'a wanda hkn yasa tsigar jikinta tashi "kukan ya Isa haka please kar zazzabi ya kamaki " cike da muryar kuka tace "me yasa ka kawo ni nan ? shiru yay mata tausayinta na kamashi ya d'ago fuskarta suna kallon kwayar idanun juna can ya motsa lip's dinsa "baki so mu wuce na mai dake gida yanzu ?shiru tayi ta cigaba da kallonsa yayinda zuwa lokacin idanun mutane sunyi caa akansu ciki kuwa har da abokansa da alqali daya samu nasarar shigowa "kiyi min magana idan baki bukatar kasancewa damu anan na mayar dake " nan ma shiru tayi hawaye na sake zubo mata masu zafi da radadi "wai kasancewa dasu ko su dawa oho masa ?tafiya ya soma yi daita tana makale ajikinsa har ya Kaita kan table din daya fara zama ya zaunar daita a hankali .
kuka tayi sosai taki yin shiru yayi mata magana yafi sau goma dan gbdy ya manta Kansa a gabanta sai wani narke mata yake zuciyarsa na sanyi akanta sannan baya son rabuwa daita shiru tayi kawai tana makale ajikinsa tayi yawo kasashen duniya sosai amman bata ta'ba Kai kanta irin wad'an guraren ba sai gashi a kasarta ta tsinci kanta da kyar ya rarrasheta tayi shiru ya bude mata kwalban malt ya Kai bakinta idanunshi na kanta . suna nan zaune mawakiyar ta fara bin Site by site tana waka yayinda mazauna kan table suka dinga mata liki har ta k'araso table din da jaguwa ke zaune bai daga idanunshi ya kalleta ba sai anas ne ya taso daga mazauninsa ya shiga lika mata 'yan dubu day day ta dan durkusa tare da furta "thank you sir shiyasa nake son ganinka sannan ta tsaida wakar tare da cewa ayi mata tafi nan take gurin ya d'auki tafi raf raf banda jaguwa da tanweer , sautinta ne ya cigaba da karad'e gurin anas ya tashi yana layi ya shiga rawa bayan ya gama rawa ya nufi gurin zamansa Yana rawa aikuwa makiyar ta biyosa nan gurin ya hargitse da dariya har shi anas din dariya yake sakamakon ya fahimci abinda take bukata daga garesa kudi take so ya fito da bandir din kudi ya shiga lika mata yana rawa irin tasu ta mashaya ."


Yammata ne su uku zaune acikin runfa me zagaye da wutar lantarki sai tsirarun bishiyoyi kowacce daga cikinsu hannunta rike da karan sigari da glass cup dake cike da ruwan giya "Kalli d'an iskan mutumin nan , ai na sha fad'awa sweet zahra ta fita hanyarsa ta tsaya taci lokacinta taki kamar jijiyarsa ce kadai ke da dadi , "ai Ina ganin sai ta tsinci kanta a lahira zata gane matakin daya dace daita , sam taki yarda tayi muamula da masu bukatarta inji cewar helen "kyale banza yanzu dey kirata tazo ta ganewa idanunta wata Killa tasan Inda ke mata ciwo wallahi tunda ta had'u da mutumin nan komai nata yayi qasa Ina dalili inji cewar hafcy no-no suna cewa mata haka kasancewarsa tana da dukiyar Fulani over "haka za'a yi hafcy bari na kira shegiya ta bud'e jakarta ta ciro wayarta kira d'aya zahra ta d'aga wayar cikin fara'a" sweety nah dake haka suke Kiran junansu dashi "yes sweet Helen meye labari ne ? ta amsa mata ciki fara'a.


"sweety kina ina ?" Ina gida kwance wallahi Ina hutawata " bazaki fito bane ma yau ? cikin Marairaicewa murya Zahra tace "da wahala na fito Ina son na cigaba da kame kaina a gida dan ta haka ne kawai burina zai cika akan Adnan idan ya daina ganina a guraren shakawata ko hotel hotel may be zai yi kewata har ya nemini ,ni Kuma ta haka zan bijiro masa da lallai sai dai muyi aure "wani dogon tsaki helen taja "Kinga ki raba mutane da zance wani Adnan mutumin nan ba aurenki zai yi ba sau nawa yana fad'a miki bazai aureki ba amman da yake ke karamin brain gareki kin kasa ganewa? "me Kuma ya kawo wannan maganar sweety ? kin kirani ne dan ki ta'ba zuciyata ko me ? Ko d'aya na kiraki ne dan na fahimtar dake wani abu me mahimmam na tura miki Sako ta what's app dinki ki shiga ki duba idan km zaki iya zuwa Rita Lori hotel yanzu kina iya zuwa ki ganewa idanunki komai tana gama fad'ar haka ta katse Kiran .
zahra tayi shiru sororo da waya a hannunta tana tunanin maganar Helen what's app dinta ta shiga nan idanunta suka ci karo da mugun Abu domin kuwa adana dinta ne rungume da wata yarinya da bata san kowacece ba , ta sake bude wani hoto su din ne yarinyar na tsaye a gabansa shi km yana rike da kugunta wani irin abu taji yayi mata diran makiya a qirjinta nan take ta fara jin zafi a zuciyarta tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta adalilin bugawar da take .


take gumi ya shiga karyo mata ciwon daya dade yana damun zuciyarta ya sake taso mata ya mamaye kahon zuciyarta , wannan alamarin akwai ciwo, ciwon da mikinsa ke azabtar da zuciya da gangar jikinta ,ciwon da kullum yake qara girma acikin zuciyarta, tunda ta fara son Adnan ta tsani ganinsa da kowace mace sannan Kuma zuciyarta ke cikin tashin hankali , ta zabura ta mike ta sauya kaya riga fara sol iya gwiwarta ta sakala jaka fara , haka ma takalimi fari ta fito cikin sauri tana Uber ,cikin kankanin lokaci mai Uber ya k'araso dan yana kusa daita, ta shiga gidan baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login