Showing 54001 words to 57000 words out of 259215 words

Chapter 19 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16538

na sauka ajikinsa sannan ya fito kugunsa d'aure da farin towel wanda bai wuce cinyoyarsa ba byn ya goge jikinsa
ya shafa body lotion yayi cumb din sumar kanshi ya soma shirya kansa cikin Kanana kaya riga blue wanda a gabansa aka rubuta polo 1967 yayinda wondon da canvers din kafafunsa suka kasance ja ,kansa sanye da facing cap ja kmr yadda rigar jikinsa yake , tsintsiyar hannunsa d'aure da agogon rolex ya rufe idanunshi da glass baki ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi, sosai kyawunsa ya bayyana ya soke hannunsa daya cikin aljihun wandonsa kamar Koda yaushe ya nufi kofar fita, falon ya dawo Inda ya iske scopio ya dawo bai tsaya bata lokaci ba ya karbi farar ledar hannunsa ya juya zuwa d'akin da tanweer take ."


tana Jin shigowarsa amman taki d'agowa daga kwance da take dan wani irin haushinsa take ji ,ya ajiye ledar akan bedside yana cewa "ga abinci nan ki tashi kici sannan zanje wani aiki me mahimmanci zan dan dade kafin na dawo batare data d'ago ba tace "a dawo Lafiya amman dan Allah ka bani waya ". "ki daina damun kanki ba waya ba gidan ma zaki bari gbdy idan lokaci yayi ya juya ya fara tafiya cikin hanzarin wannan karon d'akin dake gefen d'akinsa ya shiga ya jima sosai dan kusan awa d'aya yayi sautin muryar scopio ya fito dashi "boss komai ya kammala "okay kana iya tafiya ya fad'a d'akin tanweer yana cewa " nasa a kawo komai na kayan abinci muje kiga kitchen din ". banza tayi masa taki cewa komai hakazalika taki tashi hatta abincin da ya kawo bata ci ba ya zuba mata Ido har kusan minti biyar kome ta tuna tayi zumbur ta mike tsaye tana dubansa yayi gaba ta biyosa a baya har cikin had'ad'd'en kitchen din ."


a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen din very Niet kamar mace ce ke amfani dashi babu abinda babu na kayan abinci komai gashin nan ajiye yasa an kawo," ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so ". idanunta da suka canza kala sukayi jazir tsabar kishi ta d'ago ta sauke su akan fuskar jaguwa dake tsaye a gabanta yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin matan nan ne masu shep din cocakola "dan tani da baka tanadin wad'an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na .." ".shiiiii ya d'aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma rungumeta ajikinsa yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .


wani irin haushi ne da bata ta'ba jin irinsa ba ya diran mata a kahon zuciya ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar iskar karfi da yaji ta soma mutsu mutsun kwatar jikinta domin zuwa wannan lokacin zuciyarta ban da zafin kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin karfinta amman yaki sakinta ya kamkameta tsam yana son yaga karshen karfinta "Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya quntatawa kannenka ". cak ya saketa yana furzar da numfashin mai zafi daga bakinsa idan akwai abinda ya tsana bai wuce a ta'ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa a tsarke yace"tan ...."bata d'ago ta kallesa ba "karki sake sako kannena cikin shirmenki idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake ."
"Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu muddin baka maidani ga iyayena ba wallahi na dinga ma kannenka mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni ne sai dai a yanzu taunina ya Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa "waye Kai Adnan ? Ka fad'a min waye Kai Ina son sani kai din waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din zuciyarsa na rawa bai ta'ba Jin tsoron wani yasan sana'arsa ba ko sanin ko shi waye sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta bazai ta'ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa haraban gidan , tuni su kamil ,anas, jubi, da jabir da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya bud'e masa gidan baya ya shiga yana cewa "hope kowannenku yayi shiri me kyau? " sosai suka bashi amsa motarsu na kokarin fita daga gidan Idanunsa ya sauka akan wani dattijo zaune a gindin bishiyar dake gefen gidansa nan take yace wa eku "stop ! ".eku ya tsaya nan take mutumin ya mike tsaye yana kallon motocin jaguwa masu shegen kyau da daukar hankali da hannu ya yafito me gadi ya k'araso da d'an saurinsa ya tsaya yana rusunwa "wacan mutumin fa me yake yi anan ? "wallahi oga gurinka yazo wai yana son ganinka tun jiya byn fitarka yazo nace baka nan shine dazu byn dawowarka sai gashi ya dawo na shiga domin nasar maka sky yace Kuna meeting shine na dawo na sheida masa ya dawo Koda karshen sati ne amman yace lallai sai ya ganka ."


shiru jaguwa yayi yana nazari sannan ya dan Kalli Inda dattijon mutumin yake tsaye cikin kod'ad'un kaya marasa fasali yana cigaba da nazarinsa ,a hankali ya fito ya soma tafiya har ya k'araso garesa , dattijon na ganinsa ya shiga rawar jikin "barka da fitowa ranka ya dade "barkanmu baba ya kwanan iyalin ?" Alhamdulillah duk muna Lafiya ,
jaguwa ya kad'a Kai sannan yace " baba fatan dai lfy kake son ganina ?"dattijon ya marairaice murya kmr zai yi kuka sannan ya fara mgn muryarsa na rawa gwanin tausayi "daman matsalace ke tafe dani gareka a wajen mutane na samu labarin irin taimakon da kake yiwa mutane ". jaguwa na jin haka ya sauke numfashi yana dubansa a tsanake " Ina Jinka baba wacce irin matsalar ce ?"daman akan yarona ne shekararsa biyar kenan da kammala karatunsa na degree sai dai yadda kasar nan tamu ta dawo yasa har yanzu yake gida zaune, duk Inda yaje apply din aiki sai ace sai ya biya kamin dubu dari biyar kudin office kafin a daukeshi gashi bashi da hanyar da zai samu kudin, ni ya kamata na biya masa ya samun aikin to ni din ma babu dan na abinci ma da kyar muke samu, dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka ka samo masa aiki ko Kuma ka yarda ya kasance a karkashinka ya karasa maganar yana zubar da hawaye ."


jaguwa yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya "karkayi kuka baba inshallahu zan yi iyakar kokarina yanzu dai Ina kan hanya ne zani wani aiki amman ka dawo zuwa karshen sati da yaron inshallahu matsalarka tazo karshe dattijon ya soma k'okarin durkusawa jaguwa domin yi masa godiya, jaguwa yay saurin sa duka hannuwansa ya taresa "haba baba karka min haka mana " na gode d'ana Allah ya albarkaci rayuwarka , Allah yasa ka gama da duniya lafiya ,Allah ya jikan iyayenka idan sun rigamu gidan gsky, idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu Lafiya mai amfani na gode na gode daman da gaske ana samun mutane irinka ?karka damu baba ya k'arasa maganar yana tsaida dattijon bisa kafafunsa ya Ciro dubu goma a aljihun wandonsa ya mika masa "ga wannan kayi kudin mota yana gama mikasa ya juya ya shiga mota suka bawa motacinsu wuta suka bar unguwar ,da sauri dattijon ya Ciro wata rubabbiyar wayarsa ya shiga neman number d'ansa domin yi masa albishiri ."


******


Bangaren minister of health kuwa gbdy hankalinsa yaki kwanciya kullum yana manne da hjy zainab yana rarrashi wacce kuka ya zame mata abincin ruhinta , yanzu ma zaune yake kusa daita yana aikin daya saba tare da babban amininsa alhj Tahir dake k'okarin shawo kanta "kada kiyi fushi da hukuncin Allah zainab wannan abu daya faru gbdy bai mana dadi ba sai dai bawa baya wuce qaddararsa Allah ya rigada ya qaddaro surayya zata fad'a cikin wannan tashin hankali bamu Isa mu canza mata qaddararta ba, fatan mu dai Allah yasa bata cikin tsanani cikin muryar kuka tace "na kasa jurewa dady dake hk take kiransa kmr yadda Ib ke kiransa " yau da mutuwa tanweer tayi na binneta da zan fi samun natsuwar zuciya amman Ina raye tanweer tana hannun 'yan fashin da ko labarinsu ba'a samu ba , taya kuke tunanin hankalina zai kwanta ?". Suma kiramu muji me suke bukata daga garemu sunki ta k'arasa maganar tana kallon saman falon hawaye masu zafin gaske na gangaro mata wanda zafinsu da rad'ad'insu ya wuce tunanin mai karatu .
"wannan haka ne amman duk da haka addua zamu taru muyi allah ya bayyanata cikin koshin lfy "amen ta furta a kasan makoshi tana cewa ya jikin Ib kuwa? kullum Ina sa ranar zanzo na dubasa mutanen dake shige da fice agidan nan zuwa jaje ke hanani fita ammn inshallahu zan samu lokaci na leko na dubashi .
"to jikinsa dai da sauki zamu ce Allah dai ya iya mana da iyawarsa dan rayuwar Ibrahim na daf da fuskantar matsala da Kuma qalubalin rayuwa ya kasa jurewa rashin tanweer "Allah sarki ib yana qaunar tanweer kmr yadda yake qaunar rayuwarsa inshallahu zata dawo har ma suyi aure ta k'arasa maganar tana sake matso ruwan hawaye sun dade suna tautauna wa akarshe minister ya kira cp yaji halin da'a ake ciki ,byn cp ya d'auki Kiran suka gaisa "wai ya ake ciki ne da batun yarinyata shirun fa yayi yawa zuciyata ta fara tsinkewa Ina Jin kamar Allah ya d'auki raina na huta ? na kasa jurewa rashin diyata da rashin kwanciyar hankalin matata ".naunayen ajiyar zuciya cp ya sauke sannan ya fara magana a natse"mun baza mutanen mu cikin gari yanzu haka mun fara samun improvement akan lamarin "to alhamdulillah Allah ya taimaka yasa aga yarinyata cikin koshin lfy "karka damu inshallahu komai yazo karshe ka kara mana lokaci kad'an "na gode na gode " sukayi sallama minister ya fuskanci hjy zainab tare da yi mata albashiri da abinda cp ya fad'a masa nan take farinciki ya mamaye zuciyarta shi kuwa alhj Tahir cikinsa ne ya duri ruwa gabansa ya shiga fad'uwa hankalinsa yayi kololuwar tashi .
babu shiri yayi musu sallama ya shiga motarsa direbansa ya ja suka kama hanyar zuwa gida ,yasan ya taro wa kanshi match tunda yayi sanadin da'aka d'auke tanweer wayarsa ya Ciro yanata Kiran number jaguwa ana ce masa akashe take har ya k'araso gida bai samesa ba , ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa yasan muddin su jaguwa sukazo hannu kashinsa ya bushe domin asirinsa ya tono ."


fitowa yayi da sauri daga cikin motar bai tsaya jiran direbansa ya fito ya bude masa ba kmr zai tuntsura ya shiga cikin gidansa gumi na karyo masa ta koina a sansar jikinsa kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya rage kayan jikinsa ya shiga zariya yana neman mafuta , yana tsaye hjy baseera ta shigo tana binsa da kallon mamaki dan ta kwana biyu bata gansa cikin yanayi irin haka ba "wai Lafiya ka shigo kamar wani kububuwa me km ya faru ? tsaki yaja yace "babu komai . "To daga Ina kake yanzu "?. daga gidan minister nake ya bata amsa yana fifita da hannunsa dan wani irin azababben zafi yake ji ta koina tana Jin haka na gane komai ta kama gabanta zata fita ya d'auki remut din ac yana kokarin qara karfinta tare da cewa "ya kuma zaki wuce ki barni ga dan iska kin samu kin tmbyeni na baki amsa kawai zaki juya ki kama gabanki "oh to ni me zanyi maka ?" zata sake magana ya d'aga mata hannu"jeki kawai bananason jin komai tunda babu abinda zakiyi shasha kawai ya fad'a a matukar fusace yana juya mata baya.
tabe baki tayi a ranta tace "ai Kai ne Sha Sha ,mutumin banza kawai da bai san ciwon kanshi ba aurenka ko hasara duk a tunaninka ban San halin da kake ciki bane byn na san komai a juri zuwa rafi dai wata rana tulun zai fashe juya tayi ta barshi tsaye yaji da damuwarsa .ta nufi gurin d'anta ta bashi maganin karfin jiki dan ta sha alwashin bazata sake yarda da tsarin mijinta ba hk kawai ta rasa tilon d'anta a banza, gbdy magungunan da yasa nazifi ya rubuta masa an siyo sai dai bata bashi ya sha ba wasu dabam ta bashi jikin ne dai nashi yaki daidai saboda an rigada an karya masa garkuwar jiki " .


*******


Sannu a hankali motarsu jaguwa ta d'auki titin airport suna gama Isa kowace mota ta samu guri ta tsaya a Inda jaguwa yayi umarni tare da saka fuskokin roba , motar da jaguwa yake ciki ne kawai ta Kai cikin mutane sosai. shiru yayi yana nazari da karewa gurin kallon da tarin mutane dake bin mutane ko suna bukatar canza kudi .facing cap dinsa ya cire ya juya ta baya ya cire glass din dake manne da idanunshi ya makala a goshinsa bayan kamar minti talatin ya ciza lip's dinsa na kasa da karfi ya fito rike da bindigarsa ak 47 yana gama fitowa ya fara sakin harbi kamar ruwa domin Kore mutane dake safa da marwa agurin , kafin kace me mutane sun rud'e tare da neman gurin 'buya bayan kmr minti biyar sai ga anas shima ya fito had'e da harbi nan ma sauran mutanen da suka rage suka tarwatse ya tsaya yana huci "iam bally the deadly one, mutun ya kama kanshi idan baya son ya bukunci lahira ."ya fad'a yana sauke numfashi .


jubi ya fito ya saita bindigarsa wani lungu Inda ya hango wasu mutane suna likensu sai dai bai yi harbi ba bisa umarni jaguwa dake duk suna Jin maganarsa sakamakon connecting din da yayi da wayoyinsu ya sauke numfashi yana cewa "as you can see am gentle man to the core , I don't take what's beyond my capacity disprit that iam not the one to be taking for granted , go and ask those how have done such before ya k'arasa maganar yana numfasawa tare da gyara tsayuwarsa eku remo ya k'araso ya tsaya gefen jaguwa rike da bindigarsa yana cewa ""Jaguwa ne da kanshi d'an mutuwa Kuma mutuwa ta dade da kar'basa amatsayin d'anta so everyone should run for his life "yana gama fad'ar haka ya koma gurin tsayuwarsa ya had'e da sauran yan'uwansa suka tsaita bakin bindiga ."


Shiru jaguwa yayi ya fuskanci office din da aka kwatanta masa jubi ya matso kusa dashi yana cewa " jaguwa let's move to his office jaguwa yace "da alamun bai nan jikina ya bani amman Kuma wannan lokacin anamdi ya bamu "to mu juya mana mu koma girgiza masa Kai yayi yana ciza lips dinsa na kasa "to ko zamu shiga office office ne muyi operation ?"no ya bashi amsa atakaice "okay ya fad'a yana gyara bindigarsa .gbdy gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login