Showing 126001 words to 129000 words out of 259215 words

Chapter 43 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16543

ya hadusu da anas amman yana jinsa Kamar sadiq dinsa, yadda zai Iya bawa Sadiq rayuwarsa haka zai iya bawa Anas ."


washegari a kasalance yayi komai daga karshe ma a kwance ya yini Ko ya Samu zuciya da gangar jikinsa su samu natsuwa da suka rasa, yana kwance yaji shigowar sako wayarsa ya mirgina ya lalubo wayar yana dubawa ga abinda ya gani wanda sai da gabansa yayi wani irin mugun tsalle sannan ya fadi .


_mai yasa kaki d'aukar kirana ?" kasan zaka barni kayita wasa da nonuwana ?"mai yasa ka amshi budurcina alokacin da bana cikin haiyacina kayi yadda kaga dama dani ? ka kirani dan allah zuciyata tana rawa sannan cike take da tsoron abinda zai biyo baya Sai dai ban yi tunanin zaka min hk ba bazan iya rayuwa babu kai ba kamar yadda nasan kai ma bazaka iya rayuwa babu ni ba_


"Oh my goodness god tanwer kina da damuwa, kina damun rayuwata nifa zan iya rayuwa babu Ke Kuma babu abinda zai dameni ya fad'a a fusace yana jan tsaki ,a hankali ya kwanta ya janyo pillow ya Kankame ajikinsa yana sake karanta sakonta yana jin zafi aranshi bayan kamar minti goma sha'awarta ta dinga taso masa tsaki yayita ja yana k'okarin kawar da tunaninta .




da yamma lis ya fito ya wuce su anas zaune suna kallo da sauri anas ya tashi ya biyo bayansa har ya kai bakin gate zai fita ya tsaida shi da dan gudunsa "lafiyarka kuwa Adnan "?anas ya fada yana fuskantan sa sosai ,sai ma yaga Kamar idanunsa sunyi ja "babu komai anas amman kaina , zuciyata , kai komai na jikina Kamar ba nawa ba ,ya k'arasa maganar Kamar zaiyi kuka "Kwantar da hankalinka duk fa ba komai bane Allah idan ma akwai abinda ke damunka har da rashin yarinyar nan atare da kai, ka d'aure ko sau daya ne kabawa zuciyarka abinda take so. "girgiza masa kai yayi alamun bazai iya ba " ka barni da maganarta anas ina da Kanne mata yaya kake tunanin zanji idan daya daga cikinsu ta kamu da soyayyar dan fashi "?
Sannan kana tunanin iyayenta zasu yarda su dauketa su bani"?
"Karka damu wannan ai al'amari ne na soyayya idan ta tsaya tsayin daka sai kai dole zasu baka aurenta .
"Shikenan tunda ka nace akan lallai ina son yarinyar nan zan bawa zuciyata dama mugani Ko zan fahimci hakan ,zanje gurin ammina bazan Jima ba zan dawo ka tsaya Ku kasa komai yadda ya kamata sai na dawo ."shikenan ka gaisheta dan Allah "zataji ya fada tare da juyawa ya cigaba da tafiya Kamar bai son taka Kasa har ya karaso wajen gidan .


a hankali yake taku zuciyarsa na hasko masa fuskar tanwer da tunanin sakonta yana jin Wani iri abu wanda bai san ko menene ba sai dai yasan ba normal yake jin jikinsa ba .
ya karasa bakin titi ya tari mai mashin zuwa unguwarsu adaidai kofar gidansu aka saukesa ya sauka ya Ciro duba daya ya mikawa mai machine ya juya ya soma tafiya,mai mashin ya Karba yana cewa "yallabai ga canjinka da hannu yayi masa alamar ya barshi batare daya juyo ba . "
Kamar koda yaushe jama'ar unguwar na ganinsa suka hau rigerigen Kawo gaisuwa , sai dai sunyi mamakin ganinsa babu mota yau, a hankali yake binsu daya byn daya yana mika musu hannu tare da mika musu kudi a karshe ya Shiga gidansu a falo ya Tarar da ammin tare da hasera da kannesa shafiq ta gaishesa tare da d'aukar dadduma ta shimfid'a masa ya amsa mata had'e da zama yana gaishe da ammin ta amsa cikin sakin fuska tana cewa "Sannu da zuwa, yayinda hasera ta gaishesa "Ina yini ya Adnan ?yajita sarai amman yayi Kamar badashi take ba, Sai da ammi tace "ana gaisheka fa sannan yace "lfy! atakaice shafiq ta shiga kitchen ta d'auko masa abinci wanda Kaida ne kullum sai an zuba an ajiye Idan yaxo yaci idan bai zo ba abayar, ammi tace wa maza ki Tashi ki amsa abincin Shafiq ta mikawa hasera abinci hasera ta amsa ta ajiye a gabansa tana sake masa sannu da zuwa sannan ta mike cikin rawar jiki ta d'auko masa ruwa ta Kawo masa bayan ta zuba masa abinci ta tashi ta kama gabanta ."


ruwa kawai ya sha dan bai Jin cin komai ammi tace "lafiya dai Ko ya aiki da abokan aikin naka suke ?"duk Suna lafiya sunce agisheki tace sannuku Ai kuna k'okari wannan aikin naku bakwa samu lokacin kanku gashi duk ka rame Ina fatan dai lafiya kake ?" ya gyada alamun "eh .
Tunda ya shigo gida hasera ta d'aura idanunta akanshi taji hankalinta ya sake tashi akanshi , taji komai ya sake tsaya mata, duk yadda take hasashen girmansa da haibansa da kyawunsa abun ya zarta tunaninta ita kuwa wacce irin dace tayi arayuwarta samun kyakkyawan miji ,suruka mai kyau da nagarta, dangin miji masu qaunarta wannan ma kawai sun isheta , zata zama matarsa acikin yan watani masu zuwa , am very lucky burina zai cika na samu cikar burinna tayi mgnr a kasan ranta.
irin mijin da take so shine agabanta idan Allah ya taimaketa haihuwar fari ta haifo masa da nmj mai kama dashi sak ita kuwa me zatacewa ubangiji ta ?"
Sai faman safa da marwa take tana satar kallonsa shi kuwa duk yana lura da duk zariyarta amman Ko ajikinsa duk yadda ya kai ga qaunar ubanta baya jin zai Iya rungumar qaddarar aurenta yana qaunar mahaifinta domin ya taka rawar gani arayuwarsa ta baya amman ya rasa dalilin da yaji bai qaunar yarinyar da babu abinda ta bari na mahaifinta .
shiru yayi sannan yaki cin abincin daaka kawo masa sai da ammi takurasa sannan ya gauguta cin abincin domin gaf ake da Kiran sallah magriba yana kammalawa lokaci yay ya mike " bari naje nayi sallah na dawo ". to a dawo lfy Allah tsare inji cewar ammi .




Bayan ya idar da Sallah kai tsaye gidan ya dawo a inda ya fita ya bar ammi anan ya dawo ya sameta akan daddumar sallah babu Kowa ya sake durkuahewa agabanta dan ya fahimci akwai magana abakinta zama ammi ta gyara sannan ta maida dubanta ga jaguwa ta Kira sunansa har sau uku "Adnan !!!!
ya d'ago a hankali ya tsura mata Ido yana dubanta kamar wata sabuwar halitta a gabansa sannan ya amsa da "na'am ammi nah ".
"Adnan ta Kara kiran sunansa a hankali ya tsura mata rikitattun idanunshi yana sauraronta "ga hasera nan yaruwarka diyar kanin mahaifinka uwa daya uba daya ,hasera yarinyar kirice mai tarbiya Kamar yadda kasani nima kuma na yaba daita dari bisa dari da kaje ka auro min wacce ban san halinta ba gara ka aureta .


"nasan kai yaro ne mai biyayya ba zakaki abinda nake so ba hasera nake so ka aura bisa umarnina takarsa maganar tana numfasawa .
numfashi ya sauke sannan ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa gbdy sai yaji bazai iya kin bin umarninta ba kawai ya tsinci kanshi da cewa "ammina na amince zan aureta tunda kin amince daita nima amince ya karasa magana a raunace cike da tashin hankali "alhamdulillahi Allah yayiwa rayuwarka albarka daman nasan bazaka bani kunya ba yadda kake min biyayya Allah yasa yaranka suyi maka .
"Ameen ya furta a can kasan makoshi zuciyarsa na masa zafi da tuttukin bakinciki .


hasera dake safa da marwa ta kwasa da gudu ta shige daki tayi wani irin tsalle ta fada saman katifa tana fidda numfashi da kyar , wani irin haushi yaji alokacin daya ga ta kwasa da gudu kamr wata mahaukaciya "wacce irin mace ce ita sam babu alkunya bare Kamun kai ?" yayita jan tsaki a ransa sun dauki lokaci yana tare da mahaifiyarsa a karshe ta Kira masa hasera su fahimci juna ita kuma ta tashi ta barmusu falon.
tunda ta zauna ta kasa kwakwaran motsi tamkar babu ita agurin a fusace ya kalleta zaune a gabansa ta kafeshi da Ido kmr zata cinyesa abinda yafi tsana daga mace Kenan kallo yace "ki dauke idanunki akaina sannan ki bar ruhinki ya Samu salama duk kin Wani hana kanki sukuni akaina sai Wani Jin dadi kike zaki auri mutumin da baki san kowayeshi ba ".murmshin jin dadi ta saki tana cewa "ni kuwa nasani kowaye Shi ,kai fa mutumin kirkine waje da gida Kowa yana alfahari da kai ,ni dai tunda ka amince zaka aureni na gode maka ta k'arasa maganar tana murmushin jin dadi .


"ya subhallah"!.
Ya furta a kasan ransa " yanzu irin matar da amminsa ta zaba masa Kenan babu Kan gado, babu alkunya ina tarbiyar da tace tana dashi ?"numfashi ya fesar yana dubanta kasa Kasa , shi kallon tababbiya ma yake mata sannan wawiya wawiya shasha Kamar wacce aka kwantota daga gidan mahaukata ba wai mai tarbiya ba .
tunda ya shigo gidan take bud'e hakora har zuwa yanzu da take gabansa ta kasa control din Kanta.
ta sake bude baki da zumar sake yin mgn yace"yi min shiru anan banza shasha kawai sai wani bare baki kike ".tsit tayi kmr ruwa ya cinyeta .Falon ya dauki shiru har kusan minti talatin sannan ya sake bude bakinsa da kyar ya cigaba da mgn amman a tsawace "kin yarda zaki aureni ?"ta gyada masa Kamar zatayi kuka tare da shagwabe fuska ".
"Ina da wata mummunar dabi'a da babu wanda ya sani daita daga Allah sai abokan alqalta, Adnan da kike burin aure mashayi ne, sannan ma nemin mata ne kuma yana da mummunar sanar da nan gaba Ko a yanzu zai iya shiga hannun hukuma kuma su rikeshi riko na har abada kin yarda zaki auresa da dabiyarsa ?"
jikinta yayi sanyi jin da bakinsa ya furta abinda yake aikatawa amman ita tana sonshi Ko a Yaya yake ,shi take so ba dabiarsa ba ,ita dai tunda zai aureta ai shikenan , muryarta a hankali ta fito "na amince zan aureka saboda ina sonka, zan zauna da kai a duk yadda kake ,Allah kuma baxaisa kashiga Hannun hukuma ba inshaallahu zaka daina duk abunda ka lisafa kana......"
dogon tsakin da yaja yasa ta katse maganarta ya mike a fusace ya fice daga gidan batare da yayiwa ammin sallama ba ."
Ransa abace ya shigo gidan ya cire rigarsa yayi filinging dashi ya zauna akan kujera gbdy friend's dinsa suka zagayesa suna tambayarsa "bai ce musu komai ba illa tsakin da yake ja akai akai gbdy gankalinsu yayi marukar tashin a karshe ya Tashi ya shige daki ya kulle kansa ya wiwi ya kunna ya fara zuga yana fitar da hayaki ta hancinsa zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take . "


*******


alhj Tahir bai farka daga naunayyen baccinsa ba sai washegari da yamma , gbdy ilahirin jikinsa ya mutu da kyar yay mika haka zalika da kyar ya daddage ya mike zaune yana duban d'akin da yake jin yana jujjuya masa ,tunani ya shiga yi akan naunayyen baccinsa . yayi tunanin duniya akan baccinsa bai gano dalilin baccin ba shida baccin dare ma ba kasafai yake yinsa ba bare na safe har ya kai yamma da kyar ya Tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya rama salolinsa sannan ya nufi bangaren hajiya baseera yana tafiya qirjinsa na bugawa da karfin gaske wanda ya rasa faruwar haka.
cikin Wani irin Taku na sanyi jiki ya karasa shiga part din da masu aikinta ya fara Cin Karo suna kai Kawo bazakace matar gidan bata nan ba kodayake suma a tunaninsu fita tayi kuma zata dawo .
A hankali ya Samu guri ya zauna yana cigaba jin faduwar gaba ,ya kusan minti talatin bai ji motsinta ba dan haka ya mike ya shiga part dinta cike da tashin hankali yake bin d'akin da kallo Kamar ranar ya fara shigowa koina a hargitse nan take gabansa ya cigaba da bugawar da yake , zuciyar ta kaiwa kwaluwarsa sakon daya firgitashi cikin tsananin tashin hankali ya karasa bakin kofar bayi ya kwankwasa Ko tanayi wa Ibrahim wanka ne, sai dai still shiru ya Kira sunanta da karfi sannan a firgice ya tura kofar bayi wayam babu Kowa da mugun gudu ta fito Kamar Wani zautacce ya isa bakin get yana kwallawa mai gadi Kira "sabitu ! sabitu!!! Zuciyarsa na sake shiga garari "tun yaushe matar gidan nan ta fita ?"shiru yayi yana kallonsa yana tunanin amsar da zai bashi Kar ya fadi abinda zai jawo masa matsala da aikinsa bai ankara ba yaji sauka mari daga yatsun alhji Tahir "dan ubanka tunani na tambayeka Ko inda matata da dana sukaje ?
"a gigice mai gadi ya rike kuncinsa inda alhj Tahir ya zabga masa mari yana cewa "nidai tun jiya hjy ta fita amman ita kad'ai "ita kad'ai fa kace?
"da idanuna naganta ita kadai ta fita gama direban can ka tambayesa ita kad'ai ta fita acikin jar mota .
babu wanda ya shigo gidan nan cikin kawayenta Ko yanuwanta ?"ya sake masa tambayr a rude "gsky babu wanda yashigo bayan naxifi shine Kawai ya shigo bayan wani lokaci ya fita sannan itama ta fita sake tambayarsa yayi ka tabbatar da naxifi ne kawai yashigo gidan nan sannan ta fita?"
mai gadi yayi saurin gyada masa kai nan take ya juya Kamar zai Kifa ya nufi part dinsa ya soma bincike hatta camerorin gidan an tsadasu sun daina aiki bare yaga wainar daaka toya .
wani gumi ya shiga tsatsafo masa hankalinsa yayi mugun mugun tashi wayarsa ya d'auka ya shiga neman layin naxifi kira daya ya dauka cike da ladabi da biyayya " barka da yamma dady?" Ina ka kai min matata da dana ?Tambayar da ya soma yi masa Kenan cikin tsananin tashin hankali naxifi yace "dady bangane nufinka ba ?"Ni rabona dasu tun jiya danazo duba jikin Ibrahim "Kaci nalafar ubanka da tun jiya rabonka dasu, kun kashe min camerorin gida dan kusamu damar aiwatar da nufinku ba to wallahi Kaji na rantse kwana biyu kawai na baka ka dawo min dasu ingansu agidana suna shawagi idan ba haka ba wallahi ka kuka da kanka dan sai na aikaka lahira byn nasa an daddatsa kai yana gama fadar haka ya kashe Kiran yana huci .
take gumi yashiga karyowa naxifi ta koina ajikinsa tsoro da matsanancin fargaba suka mamayesa , yasan ya tarowa kansa March dan alhji Tahir zai Iya aikata abinda ya fada mutumin da bai bar dan ckinsa ba to wazai Bari?"da sauri ya Shiga tattara kayan aikinsa ya fito cikin sauri kunnensa manne da waya ...."




*********


Bangare tanweer kuwa yau tashi tayi da kurmususun ciwon ciki , ita kad'ai a d'akinta dan mumy da dad basu shigo d'akin ba a tunaninsu bacci take karsu takura mata, sai wajen azahar bacci mai nauyi ya d'auketa, rabonta da cin abinci kirki kuwa tun tana gidan jaguwa, shiru har kusan karfe bakwai na dare bata fito ba yasa mumy ta shigo d'akin kallo d'aya tayi mata gabanta ya fadi ta taba jikinta taji zafi rau a hankali ta dinga shafa mata jiki har ta farka wani irin nauyi taji jikinta yayi mata ta Kasa motsa jikinta ,da kyar da taimakon mumy ta mike ta rakata har bayi ta hada mata ruwa wanka sannan ta fito ta tsaya jiran fitowarta cikin kankani lokaci ta fito ta shirya
Yayinda mumy ta jawota zuwa falo ta shiga kitchen da kanta ta daura mata ruwa zafi ta kawo mata ta zauna a gefenta tana mata sannu bayan ta sha ruwan lip ton ta numfasa tace "mumy wallahi bani da karfi juya juya nake gani "to ai kece ki tsaya a duba lafiyarki a hospital kinki kika matsa lallai sai kin fito ai ga irinta Nan "wallahi mumy naji jiki jiya da daddare banyi bacci ba kwana nayi ciwon ciki "shine dan wauta baki bari mun sani ba yanzu da wani abu ya faru dake fa ?" karki Kara min irin wannan ganganci gashin nan har wata katuwar rama kika yi Ina fatan dai yanzu bakya Jin komai "?
Ta gyada mata Kai alamun "eh .
Mumy ta sake tashi ta kawo mata abinci da kyar ta tura tana kammalawa lokacin mumy ta mike tana fad'in "ki tashi kije kiyi sallah ta amsa da "to" ta wuce d'akinta mumy ta kwashe kayan ta maida kitchen bata tsaya jiran masu aiki ba sannan ta nufi d'akinta dan tayi sallah itama ."


Bayan tanwer ta Idar da Sallah wayarta ta janyo daga inda tayi sallahr ta shiga turawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login