Showing 210001 words to 213000 words out of 259215 words
Chapter 71 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
gabansa tace "kana nufin baka yarda da mgnta ba ? gsky ban yarda ba ta yaya mahaifinki zai yarda ki auri mutun Irina yasan koni waye a garin nan fa "? sau nawa zan fad'a maka ka daina fadar haka nice fa zan zauna da kai Kuma nasan zaka canza da izinin Allah Kuma wallahi sun amince da gaske nake fada maka bada wasa ba ."
jaguwa ya sake gyara zama da wayar hannunsa yana murmushin Jin dadi anas ya juyo a lokacin daya d'aura bakin bindiga akan alhj tahir yana masa gargadi girgiza Kai kawai yayi yana ciza lip's dinsa na kasa shi Kuwa jaguwa ko ajikinsa hankalinsa kacokan yana gurin tanweer shi kadai yasan sanyin da yake ji a sansar jikinsa adalilin jin sautinta sai ma yake ganin tamka tana gabansa yayi missing din komai nata yana jin kamar tana bisa qirjinsa ne a hankali ya fara shafa faffadan qirjinsa “adnan dina!“Yes tanwer ina tsananin qaunarka burina akoda yaushe mu kasance tare matsayin miji da mata murmushi kawai yayi batare da yace komai ba a ransa yace lokacin baki amsar tayi tanwer dan ni kaina ina ganin lokaci yayi da zan ajiye iyali kuma ba kowa bace face my tanwer.”
A hankalin ruwa ya soma sauka gbdy suka koma cikin wasu lema kamar yadda jaguwa yake ciki suka cigaba da sauraron anas.”
"Alhji tahir me ya hadaka da nazifi kake neman rayuwarsa ?"wata mummunar fad'uwar gaba ta ziyarcesa tsoro da fargaba suka mamayesa baya raba dayan biyu a hannunsu nazifi ya fad'a tunda kuwa ya fad'a hannunsu shikenan ya shiga uku tashi ta samesa yayinda Nazifi ya tsira daga mutuwa, duk da kasanceearsu yan fashi amman su din masu gaskiya ne da rashin son zalinci ko danne hakin wani uwa uba alkawari zakuyi aiki dasu lafiya batare da wata matsala ba .
kimanin minti uku anas na saurarensa yaji me zai ce amman shiru yayinda jaguwa ke sake nitso cikin hira da tanweer hannunsa ya kai ya daga wajen lemar da suke zaune ciki yana wasa da ruwa fuskarsa kwance da murmushin Jin dadi kana ganinsa zaka fahimci yayi nitso cikin tafkin soyayya
Anas ya cigaba da mgn "me yasa sai ka shiga abinda babu ruwanka ?" alhj Tahir yayi shiru yana sake shiga tashin hankali “ka dauka kai kad'ai kake da karfi acikin garin nan ?" yayi mgn idanunshi akansa yana jin babu dadi a ransa “ko da yake kai fa mugun mai laifi ne sannan ,da kake sawa abi yaron mutane dan daukar maka rayuwarsa idan komai ya kwabe kafin yashafemu ta kanka zai fara , kabi ka ta kurawa yaro,yaron nan ma a maganarsa matsayin mahaifi kake dashi agurinsa ,kai dai wallahi mugu ne gbdy halaiyanka marasa kyau ne , wai hatta dan cikinka baka bari ba ,gsky kai din azzalumi ne ,dan iskanci shine kake amfani da damar da kake dashi kake damun mutane Idan har baka cire hannunka akan niyyarka ta son ganin baya nazifi ba wallahi matsaloli zasu faru amman matsalar kai kadai zata shafa dan mu yanzu mun rigada muyi karfin da babu Wani wanda ya Isa “. ya karasa mgnr tare da bawa sky umarmin ya zo da nazifi adaidai lokacin da jaguwa ya watso ruwa bai sauka a fuska sai a fuskar Ana’s ya waiga ya kallesa yana girgiza Kai ko cikakken minti goma ba’a yi ba suka dawo tare nazifi kallon kallo suka shiga yiwa juna daga nazifi har alhj tahir .”
gbdy alhj tahir ya rasa inda zai saka Kansa dan kunya yayi bakinciki da wannan rana "ka kula da kyau ka dauki maganarmu da mahimmanci babu Kai babu shi kowa yayi harkar gabansa idan ka ...."shiru yayi batare daya k'arasa maganarsa ba sakamakon ruwan da jaguwa ya sake watso masa ya waigo ya sake kallonsa gbdy ya fahimci hankalinsa bai garesu ana ma kawai ya yarda yana son tanweer ,soyayyar ma bazata misaltatu ba gbdy daga anas har su Kamal da jubi da sauransu kallon jaguwa suke ..
Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️37
........"Ke aganinki har yanzu na dace dake ?me yasa bazaki fahimci illar abinda kike son yiwa rayuwarki ba ?yayi mata tambayar kamar bai ji dadin maganar data fada masa ba ,ya lumshe rikitattun idanunshi tamkar tana gabansa saboda sanyin dadin dake kai kawo a sansar jikinsa ,yayinda har lokacin hannunsa ke aikin shafa faffadan qirjinsa "eh kai kadai ne ka dace dani adnan shiyasa ,kai ne zabina , na baka yardata da amincewata da kai kawai zan iya rayuwa ,
Murmushin gefen baki yayi sannan ya d'an motsa lip's dinsa kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya kasa furta komai ,ya cigaba da lumlumshe idanunshi yadda yake murmshin farinciki haka yaransa dake tsaye a gefensa suna dabansa suke tayasa murmushi ."
wani irin yanayi ya shiga mai wuyar misaltuwa sosai tsigar jikinsa ke mikewa ,ta kwantar da murya sosai tana fada masa zantuttuka masu sanyi da ratsa sansar jiki ,sosai ta dinga zayyane masa muraran qaunar da take masa ,a hankali ya fara jin jikinsa yana samun sauyi tamkar ana masa wanka da ruwan sanyi ,cikin mintuna da basu wuce goma ba komai nasa ya sake sauyawa maganarta ba iya gangar jikinsa kawai ta tsaya ba har kunnuwansa sun daina fahimtar maganar kowa sai nata ,suna cikin haka ya jiyo sautin muryar mahaifiyarta tana kiran sunanta "habibi I will call you back " ta fada tana katse kiran ."
ya dan lashi lip's dinsa na kasa yana mai maimaita sabon sunan data kirasa dashi a saman lip's dinsa "habibi! ta yadda babu mai ji "Oh my god tanwer allah yasa karki zautar dani ,gbdy hakurina ya kusan karewa akanki ,ya ajiye wayar hannunsa akan table din gabansa ya had'e hannunwansa guri d'aya ya tsarkesu yana sake lumshe rikitattun idanunshi anas ya sauke numfashi tare da d'auke bakin bindiga akan alhaji tahir ya kai goshinsa batare daya ce komai ba ,a natse jaguwa ya d'auki kwalban wine da d'an yatsantsa ya mike tsaye a rikice cikin tsananin tashin hankali duk suka dukar da kansu kasa kar kwalbar ta subuce a yatsansa ya samesu ,ya soma tafiya a hankali dan kar kwalbar ta subuce ta fadi ,duk suka d'ago kansu suka juya suna dubansa yana yawo acikin lambum cike da matsanancin mamakinsa dan basu ta'ba ganinsa cikin wannan yanayin mai tattare da shaukin soyayya ba ."
sun sha jin ana's na fad'a masa cewar ya fad'a soyayyarta amman sai ya karyata hakan ,yau dai ga zahiri sun gani da idanuwansu bai kuma isa ya karyata hakan ba,ahankali ya juyo still da kwalbar a d'an yatsan hannunsa yana gama juyowa kwalbar ta fad'i akan table dake tsakiyarsu gabadayansu suka ja da baya da sauri sukayi ta kansu shi kuwa dafe goshinsa yayi yana runtse idanunshi ya koma mazauninsa ya zauna dafe da keyarsa da hannunwansa duka yana fesar da numfashi bai ma lura da halin da suke ciki ba ,anas ya cire bindiga a goshinsa dan tun daya dafe goshinsa da bindiga bai cire ya kalli jaguwa daga diramar soyayyarsa ba sai yanzu ,ya waigo inda yake zaune yana murmushi yayi masa kallon tsaf gbdy baya cikin haiyacinsa,
suka shiga kallon juna ,gano yanayin baya cikin haiyacinsa yasa suka sake tattara hankalinsu garesa suna kallonsa har nazifi ."
ganin yadda gbdy jaguwa ya susuce tare da lulawa duniyar tunanin soyayya yasa anas ya maida hankalinsa sosai a kan nazifi "za,a d'aukeka yanzu a fitar da kai yau daga gidan nan ,zaka koma gidanka ka cigaba rayuwarka da lamuran gabanka kamar yadda ka saba ,kasa aranka cewar babu wani baraza da za'a sake yi maka ko kawowa zuciyarka farmakin boye an gama da wannan matsalar "ya karasa maganar yana kiran sunan eku !.
"Yes boss ya amsa masa cike da girmamawa da yake da haka suke kiran gbdynsu ,"ka tasa keyar wannan mutumin ka mai dashi inda ka d,aukosa har zuwa lokacin da shi wannan zai dawo haiyacinsa asan yadda za'a yi dashi anas yayi maganar yana nuna alhj tahir dake rakube wanda ruwan sama dake sauka ahankali ya gama jika masa kayansa da jaguwa wanda bai san a duniyar da yake ciki ba ,
Batare da bata lokaci ba eku ya tasa keyar alhji tahir gaba suka nufi bangaren bq ya bude dakin daya kasance nashi né shi kadai ya turasa ya janyo kofar ya rufe sannan ya kulle kofar da mukulli ya juya . "
Nazifi ya dube anas fuskarsa cike da matsanancin farinciki yace "na gode sosai ranka ya dade allah yasa ku gama da duniya lafiya ,allah kuma ya jikan iyayenku idan sun riga mu gidan gsky idan kuma suna raye ,allah ya kara musu lafiya mai amfani "Ameen suka had'a baki gbdy ,amman ranka ya dade wayata dake dauke da sheidu akan dady fa ?"Karka damu a yanzu zamu kwashe komai dake ciki mu baka wayarka ,sheidu zai cigaba da kasancewa agurinmu ne kawai , gyada kai nazifi yayi dan ya yarda dasu dari bisa dari a dan zaman da yayi tare dasu ya amince bazasu yaudaresa ba tunda ga kamanin alhji tahir nan ya canza ba sai an fada masa ba a inda aka ajiyesa muguwar wahala yake sha ."wanda shi bai sani ba ba iya alhj tahir ne kawai ke cikin wannan halin baka'i zaune acikin gidan ba suna dayawa ."
a hankali ya dan juya yana satar kallon jaguwa da shaukin soyayya ke dibarsa yana son yayi masa sallama da karin godiya akan taimakon da yayi masa mman babu halin yin haka , ya juyo da hankalinsa ya fuskanci ana's yana cewa "ranka ya dade ina da wata yar tambaya da zanyi maka idan bazaka damu ba ?karka damu kayi tambayarka Ana's ya fada yana bawa sky umarnin ya kwashe komai daya danganci sheida akan alhj tahir acikin wayar nazifi ya kawowa nazifi wayar ,ya juya da sauri ya bar gurin domin aiwatar da abinda aka sakashi."
"Tambayata shine ku din su waye domin ya kamata nasanin kafin na bar gidan nan dan ina komawa gida dole yan'uwa da abokan arzikina zasu so suji komai daya faru dani ,sannan zasu so suji su wadan ni mutane ne suka taimaka min jami'an tsaro ne ko kuwa akasin haka?"kada kayi mafarkin fad'awa kowa komai daya faru da kai dan bama son asani shiyasa ma muka rabaka da sheidar hannunka, bama bukatar kowa yasan su wayemu dan duk aikin da zakayi dan allah bai dace wasu su sani ba .
nazifi yayi shiru yana sauraransa yana nazarin maganarsa só yake ya gano gaskiyar su din su waye ga bindigu kala dabam dabam agabansu kamar jami'an tsaro kamar kuma yan fashi da makami a shigowarsa gida yaga abubuwa dabam dabam duk da a killace yake amman ya kan leka ta window dakin daaka masa masauki idan yaji motsi, mutane dabam dabam suna shigowa gidan idan kuma dare yayi yana jin Ihun mutane suna kuka da neman dauki wanda ya rasa dalilin haka ,sannan yanzu haka gashi agabansu amman bashi da dalilin sake antaya masa wata tambayar yaja bakinsa ."
yayi shiru yana kallon cikin lambun yana saka da war wara acikin zuciyarsa gargadin da anas yayiwa alhj tahir ne dazu ya shiga dawo masa daya bayan daya yana samun kyakkyawan mazauni acikin kwakwaluwarsa "lallai su din sunfi kama da yan fashi da makami abinda ma zuciyarsa yafi yarda dashi kenan sune sukayiwa mahaifin tanwer fashi sannan suka wuce daita na tsawonlokaci , idan ba haka bane a ina suka san alhji tahir ? me ye kuma hujjarsu nayi masa gargadi akansa? tambayar da yayiwa kansa kenan wanda bashi da mai basu amsarta .shiru ya cigaba dayi agurin yana sake yiwa tunaninsa dalla dalla lallai so yake ya gano wani abu a tattare dasu da zai bayyana masa gaskiya sai dai duk dogon tunaninsa da nazarinsa bai hango abinda zuciyarsa ke zarginsu akai ba dan kuwa babu ta inda sukayi kama da yan fashi ,idan kuma sun tabbata yan fashi ne to kuwa nasu fashin mai kyau ne da adalci "to ma ina tanwer din take ?tambayar da zuciyarsa ta sake aikawa kwakwaluwarsa kenan har ya bude baki da niyyar yi magana sai kuma ya fasa yaji kamar an saka superglue ya manne masa baki ne ."
cikin kankanin lokaci sky ya dawo hannunsa rike da wayar nazifi ya mikowa anas shi kuma yace ya mikawa nazifi ,ya karba yana sake yin godiya sannan anas ya bawa scorpion umarnin ya kai shi gida atare suka mike suka soma tafiya ,yayinda gbdynsu suka tsura wa jaguwa idanunsu suka cigaba da kallonsa eku sky suka kallesu sannan suka kalli jaguwa tare da kwashewa da wata dariya garin subawa juna hannu dan su kashe suka bugi table din gabansa nan take glas cup's din dake ajiye akai suka tarwatse ,bugun table din ne ya dawo da hankalin jaguwa jikinsa ya kuma ankarar dashi halin da yake ciki "Am ranka ya dade daman haka idanunka suke ?" "Sosai ya sake dawo wa haiyacinsa yana dubansu fuskarsa tattare da alamun tambaya "lallai wannna soyayya hakika ta tabbata sosai jabir ya fad'a yana murmushin tsokana" da wa kenna?jaguwa ya tambayesa ya dan kallonsa idanushi still a lumshe tamkar wani mashayi "da kai mana idan ma ba kai ba wa za'a nunawa irin wannan soyayyar ? "uhm ka duba dan allah sai kace ita din ba diyar minister ba, idan tana yin wasu abubuwa sai ka dauka ita din ba diyar babban mutun bace ,amman kowa ya ganta yasan yar gidan manya ce jubi ya fad'a yana kwashewa da dariya."
"Nata kuke gani shi fa ?gbdy ya canza tamkar ba jaguwa ba ,yau dai kowannenmu ya gano wani sirri atattare dai kai ba kuma ka isa ka mutsa mana ba ,mu dai zamu maka fatan alkhairi dan gaskiya jaguwa ka dace kaji dadi wallahi karka tsaya sanya ka duba yarinya irin wannan haka amman ta makale sai kai congratulations kamil ya fada yana mika masa hannu yana sakar masa murmushi amman kememe jaguwa yaki bashi hannu dan wani mugun haushinsu da haushin kansa yaji ."
"yanzu dai ku me kuke tunanin abun zai kasance ? jaguwa ya mike tsaye cike da jin haushi "kai dan allah kuyi min shiru karku dame ni da wata magnr soyayya" ya soma tafiya anas yabi bayansa da ido cikin jimami kawai yana kallonsa ko har sai yaushe zai fahimci halin da yake ciki ?yana gudar masa randa soyayya zata wujijigashi tayi waccajali dashi ,
yaso yadda ya samu damar nan yayi amfani daita "kaji abinda yace Ana's wai kar mu damesa a zuwan ba gskiya bane ?"Haka zai ta nuna mana anas ya fada tare da kokarin mikewa tsaye "ina ma zanga wannan yarinyar dana fada mata ta rabu dashi da fita rayuwarsa wallahi zai fito da abinda ke ransa "bazata iya ba domin ba irinsu jaguwa mace
kewa irin wannan wasan ba , ko kun manta cewar shi din dokin tsare ne ya fada yana cigaba da tafiya ya nufi hanyar fita daga cikin lambum."
kai tsaye jaguwa hanyar dakinsa ya nufa yana gyara kwalar rigarsa yayinda hoton fuskar tanwer ya shiga masa gezo acikin kwayar idanunshi ,tun daga kwayar idanunta karamin bakinta hip's dinta har zuwa qirjinta dake cike bammm a nan ya tsaya yana kare musu kallo tamkar a zahiri , nan kuwa tunaninsa ne kawai ,a hankalin ya fara juyi acikin dakin tare da zaro tsarkar gold dake makale a wuyansa boye cikin rigarsa yana juyawa a hankali tamkar yadda yake zagaye dakin fuskarsa kunshe da murmushin farinciki yana sake zurfi acikin tunaninta."
a natse ya daga kansa saman dakin yana kallon celling dakin "ina sonka adnan dina ban samu damar yin soyayya da kowa ba sai da kai ,dan allah kace kana sona ,ka canza sana'a zanyi confused din iyayena su bari na aureka sannan zan nemo maka sana'a bazan barka haka ba kalamanta suka dinga dawo masa daki daki suna haskaka zuciyarsa ,
a hankali ya jingina bayansa da bangon dakin tare da tokare kafarsa daya "bayan kamar minti goma ya sauke kafarsa yasa dan yatsantsa jikin bangon takin yana tafiya yana bin bango da yatsansa har lokacin murmshi ne kwance a fuskarsa ,yau yana cikin farincki mara misaltuwa ,na kiran da tanwer tayi masa ne ko kuwa naji albishirin dinta ne shi dai bai sani ba amman dai yana cikin farinciki da bai san dame zai misaltashi ba ."
"nima ina sonki tanwer son da ban taba tsammanin yiwa wani mahaluki irinsa ba ,ina jinki ajinina acikin bargona da tsokar jikina bazan iya rayuwa babu ke ba but just give me