Showing 93001 words to 96000 words out of 259215 words
Chapter 32 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
hannunsa yayi taku d'aya zuwa uku ya tsaya ya rike kugunsa da duka hannuwansa yana furzar da iska shi kad'ai yasan irin halin tashin hankali da yake ciki "shi zata mara?" wannan shine karonta na biyu data kai hannunta fuskarsa tsaki yaja yana kokarin juyowa hannunsa na hagu tayi saurin matsoshi zata taresa ya kauce yana ƙoƙarin bin dama nan ma ta taresa a karshe yayi wani irin juyi ya sha gabanta ya soma tafiya cike da zuciya .
ta biyosa da sauri tana Kuka ,yadda yake sauri haka itama take d'aga ka'fafunta tana sheshekan kuka, dan zuwa wannan lokacin ta fara hango irin halin balai da zata tsinci kanta agurinsa muddin bata sauko dashi ba ,ta Kai hannunta ta ta'bashi tana Kiran sunansa "ad....... " wani irin juyowa yayi tare da buga mata razananniyar tsawar data sata kamewa guri d'aya had'e da dafe qirjinta yayinda jikinta ke wani irin rawa, ta kasa kallonsa tsabar tsoran da firgicin data hango kwance acikin kwayar idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa tana sheshekar kuka cike da tsananin tashin hankali .
"tayi data sani wannan marin da tai masa Ina ma adawo da abinda ya faru baya a seconin daya wuce wallahi da bata aikata hakan ba .
ya kafeta da tsumammun idanunshi kusan minti biyu idanunshi na yawo ajikinta yana hukuntata da idanunshi ganin bashi da niyyar cewa komai Kuma ta fahimci ko zasu kwana a haka bazai ce mata qala ba yasa tayi karfin halin matso da ka'fafunta, tayi taku biyu ta rungumesa ajikinta very tight tana wani irin kuka "kayi hakuri Adnan! kayi hakuri dan Allah". k'okarin fixgeta ajikinsa yake ta kamkameshi gam tana wani irin kuka me ta'ba zuciya "dan Allah Adnan kayi hakuri, Ina me baka hakuri karkayi fushi dani ". ta k'arasa fad'ar haka tare da durkushewa a gabansa tana kallonsa hawaye na gangarowa akan quncinta "kayi hakuri karkayi fushi dani nasan nayi kuskure ta k'arasa maganar tana girgiza masa Kai alamun bazata sake ba ," bansan me yasa na aikata maka hakan ba amman kayi hakuri bana cikin haiyacina ne kaji Adnan . wani irin wahalalle numfashi ya fesar yana jin wani sanyi na ratsa sansar jikinsa ko babu komai tasan tayi masa ba daidai ba tunda gashi duk ta rud'e ta fita haiyacinta tana kuka tana bashi hakuri ,gashi daman shi abinda ke saurin karyar masa da zuciya kenan kukan mace ,bare km nata wanda ya rasa dalilin da yasa baya qaunar jin sautinsu yana mugun d'aga masa hankali .
ya ciza lip's dinsa na kasa da karfi yana dubanta, Ido cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun juna "dan Allah kayi magana kace ka yafe min bazan sake ba ." lumshe mata tsumammun idanunshi yayi yana sauke naunayen ajiyar zuciya Jiki a sanyaye ta mike ta kamo hannuwansa duka cikin nata suna fuskantar juna ".
a hankali ta kai hancinta daidai saitin nashi suna shakar numfashin juna a tare suka lumshe idanu zuciyoyinsu na sake amsar soyayyar junansu "am so sorry Adnan " bai ce mata uffan ba dan haka ta cigaba da kuka sosai kamar ranta zai fita amman still jaguwa yaki magana.
fuskashi ta kamo ta rike da duka hannuwanta ta had'e fuskokinsu guri d'aya tana hawaye cikin kuka tace ",nayi nadama na rantse maka bazan sake ba kayi hakuri bansan qaddarar data kaini marinka ba "qaddara tanweer ? ya furta hakan numfashinsa na shigar mata hanci tayi saurin runtse idanunta, numfashi ya sauke da karfi , "qaddara ce tasa kika sauke yatsunki biyar a fuskata ?"tayi saurin gyada masa Kai tana marairaicewa " "wannan shine Karo na biyu da hannunki ya sauka akan fuskata why tanweer?yayi maganar zuciyarsa na rawa . kife fuskarta tayi a tsakiyar qirjinsa ta saki wani sabon kuka me tsuma zuciya" an dokeni a makaranta sojaji a lokacin baya bisa gaskiyata adalilin na d'auki matakin abinda akayiwa kanwata bayan wannan ban sake shan duka a hannun kowa ba sai ke yarinya karama dake" ya k'arasa maganar yana fesar da numfashi had'e da kawar da fuskarsa gefe baya jin zai yafe mata wannan marin cikin sauki .
rungumesa tsam ta sake yi ajikinta tayi masa riko me karfi tare da lumshe idanunta .
wani irin yanayi me yuwar misaltuwa ya tsinci Kansa ciki ya dinga sauke ajiyar zuciya akai akai , lufewa tayi sosai ajikinsa tana sheshekar kuka ",kayi hakuri dan Allah " sosai ta rungumesa shima abinda yake son yi kenan ya rungumeta sai dai bazai iya ba dan bacin rai bazai barshi ya aikata hakan ba ,har sanda anas ya k'araso ya tsaya akansu rungume da hannuwansa duka a qirji basu sani ba ."
murmushi yayi tare da yin gyaran murya "jaguwa Ina matukar farinciki yau " anas ya fada , jaguwa ya bud'e idanunshi da sauri sakamakon jin sautin anas cikin sauri tanweer ta sake shi tare da sunkuyar da kanta kasa cikin tsananin Jin kunya .
had'e rai jaguwa yayi tamkar bai ta'ba dariya ba arayuwarsa "me ye ka wani had'e rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa? ai tun d'azu nake biye daku, ka barni cikin damuwa kai Kuma kana nan kana ta Shan shagalin ko?" gaskiya hakan yayi matukar burgeni da sauri tanweer ta juya cike da matsanacin kunya ta bar gurin."
jaguwa ya juya zai bar gurin anas ya riko hannunsa "haba kai kuwa abokina Ina zaka Kuma ?wani mugun kallo yayi masa sannan ya yatsina face dinsa yace "zanje nayi wani aiki ne ya fad'a yana kokarin fixge hanunsa ya sake rikosa "ni zaka rai....."
"enough anas banason abinda kake min maganarka na bata min rai wallahi, idan baka daina ba zamu samu matsala "to mu samu mana in dai akan wannan ne wallahi na yarda mu samu taya ga gaskiya Ina gani amman kake waskewa ,lokacin da aka rasa yarinyar nan dawowa kayi tamkar wani zautacce mahaukaci ,hankalinka ya tashi ,bama ni ba kowa a gidan nan yasan son yarinyar nan kake wata muguwar shaka ya yayiwa anas a fusace yace "don't ever say it again ko me ya tuna yayi saurin sakin wuyan anas yana duban hannunsa daya damki wuyansa dashi kamar zaiyi kuka .
wani irin kallo anas yake masa cikin rashin tsoro da fargaba ya cigaba da magana idan da sabo ya saba da halinsa "wallahi ka natsu da kyau ka saurari zuciyarka wani bakon alamari na shirin faruwa da kai Adnan idan ka kasa fahimta yanzu nan gaba zaka gane son yarinyar nan kake "wallahi bana son..."
"Wallahi kana son yarinyar nan anas ya katse shi ta hanyar fad'ar haka "ya Isa banson ji komai daga bakinka Kuma ka daina min maganar , sannan ka daina damun kanka akan Ina Sonta dan babu komai acikin nan ya fad'a yana nuna masa saitin zuciyarsa "adnan!"
"Allah ka yarda ka fad'a son tanweer ya sake fad'a tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake faman bugawa da karfi, bafa yau na sanka ba ka yarda ko karka yarda wannan zuciyar ta kamo da matsanacin qaunar tanweer jaguwa yaja dogon tsaki kana ya juya yana tafiya anas na biye dashi atare suka shiga falon ya fad'a cikin d'aya daga cikin kujerun falon yana sakin numfashi"ad...!
"Na had'aka da daraja Allah ka barni haka ni wannan yarinyar ma wallahi sai naci ubanta kafin ta bar gidan zata San ta mareni "ka ..."shiiiiii bafa na son Jin komai daga bakinka kaje kawai "tsaye anas yayi yana kallonsa ga gaskiya a zahiri amman yaki yarda, jaguwa ya runtse idanunshi yana jin wani irin abu na taso masa akan yarinyar yana tokare masa kahon zuciyarsa ..."
Ya dade zaune har kusan karfe biyu na dare kafin daga bisani bacci ya d'aukesa sai goshin asuba ya tashi ya koma d'akinsa Bai koma bacci ba ya shige bayi yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya Isa Inda daddumar sallarsa yake shimfide ya tadda sallah ,sai da yayi sallah asuba ya koma bacci ya dade yana bacci kasancewar weekend ce ."
Da misalin karfe biyar na yamma ya fito daga d'akinsa cikin shirin fita riga da wando red and ash ne sanye ajikinsa ,
kafafunsa sanye cikin takalmi canvers Ash me ratsin red ta gefe da gefensa , hannunsa d'aure da agogon fata mai kyau da tsada yayinda kwantaccen sumar Kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf Hakan ya karawa fuskarsa kyau da annuri sai dai fuskar a hade take babu alamun fara'a ko kad'an ,key din motarsa ferari ne rike a hannunsa Kai tsaye d'akin da tanweer take ya kutsa ya shiga bakinsa d'auke da sallama sai da aciki yayi ,kamshin turarensa daya saba amfanin dashi ne ya doki hancinta ta d'ago a natse ta tsura masa idanunta kamar Koda yaushe fuskar nan tashi babu wadataccen fara'a, muryarta a sanyaye ta motsa labbanta"Ina yini ?"bai amsa mata ba sai ma wani kallon banza daya bita dashi kafin ya d'auke kanshi daga kallonta ya nufi Inda bedside yake ya bude.
bata damu ba dan tasan dole zuciyarsa ta d'auki fushi daita sakamakon abinda tayi masa jiya wasu file ya ciro yana dubawa ya d'auki minti biyar yana tsaye yana dubawa sannan ya mayar ya ajiye ya juya ya fita ya nufi parlour yana taku a hankali kamar bai son taka kasa har sanda ya fito parlour'nsa .
Gbdy abokansa suna zaune kamil nacin abinci ,yayinda jubi ke k'okarin nada tabar wiwi , kunnen anas manne da waya yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana binsa da kallo .
Shima jaguwa Tsura masa Ido yayi yana karanta yanayin wayar da yake , anas ya karasa sosai kusa dashi ya rike masa hannu yana cewa "tanko gote ne wai yana da alqalla me kyau da yake son muyi masa ya kira layinka ba baka d'auka ba shine ya kirani kayi magana dashi ya mika masa wayar . "bazan yi magana dashi ba kaima karka sake d'aukar wayarsa sanin kanka ne anas bama Kulla alqalla da irinsu tanko gote mutumin da nake fatan a karshen rayuwarsa ya zamo mabaraci akan titi ya numfasa sannan ya cigaba da magana a sanyaye " ka kula da kyau anas banason wani abu ya sameka idan wani abu ya sameka bazan yafe maka ba ".duk maganar jaguwa d'aya byn d'aya suke shiga kunnen tanko gote ya runtse idanunshi tare da disconnecting din kira."
" Inshallahu zan kular maka da kaina Ina zuwa haka ga abinci anyi order da Kai ? numfashi ya fesar yana yamutsa fuska kafin yace "zanje ganin ahlina idan naje can zanci zan dan d'auki lokaci ban dawo ba dan zan fara da biyawa gidan marayu akwai sakon da zan Kai musu yana gama fad'ar haka ya zare hannunsa ya juya ya fice daga parlour'n dan yasan yanzu raunin anas zai bayyana .
ilai kuwa hakan ce ta kasance gbdy yanayin anas ya canza rauninsa ya bayyana kamar zai yi kuka ,ya danne hawayensa suka koma, a duk sanda yaga jaguwa za shi ga ahlinsa sai yaji zuciyarsa tayi rauni saboda rasa nashi ahlin da yayi bashi da kowa a halin yanzu sai jaguwa shine komai nashi zama yayi ya shiga duniyar tunani .Kai tsaye Inda motarsa ferari yake ya nufa ya danna keyn hannunsa ya bud'e ya shiga ya zauna yana me kunna motar tare da yin hon me gadi ya wangalemasa get din gidan ya fice.
tafiyar awa d'aya ce ta kawoshi gidan marayu babus'salam dake ikeja gra yayi hon aka bud'e masa get ya shiga, yasa guri ya
yi parking din motarsa ya fito ya bud'e bayan boot dinsa ya ciro bakar jaka dake shake da kudi ya kulle motar Kai tsaye office din shugaban makarantar ya nufa .malam yusif na ganinsa ya fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi dan yawon zuwan jaguwa yasa sabo me karfi ya shiga tsakaninsu ,ya nuna masa gurin zama byn jaguwa ya zauna ya mika masa hannunsa suka gaisa "yalla'bai barka da zuwa ya aiki da k'okari ? "alhamdulillah ya naku k'okarin da fama da yara ? malam yusif yayi murmushi kawai ,sun dan ta'ba hirar duniya sannan jaguwa ya mika masa jakar kudin daya zo dashi "ga wadan nan kudaden ayi wa marayu hidima dasu.
"Kai masha Allah ,Allah yasa Saka da alkhairi ,Allah yasa maka ladan a mizani ,yadda kake faranta zukatan marayu Allah ya faranta naka , Allah ya kawo farinciki a rayuwarka data iyalinka, Allah ya tsareka". "Ameen na gode sosai da addua ni zan wuce har ya juya malam yasif yace "yalla'bai har yau baka fad'a min sunanka ba gashi za'a Saka cikin sunayen masu tallafawa marayu "ya juyo a natse yana cewa"bana bukatar a Saka suna , sukayi sallama ya wuce ya d'auki hanya zuwa unguwarsu ko gama daidaita parking din motarsa bai yi ba Jamar'sa na unguwar suka zagaye motarsa tare da Kawo masa gaisuwa.
a natse ya fito yana ƙoƙarin kulle motar byn ya kulle ya mika musu hannunsa d'aya bayan suka gaisa ya Ciro kudi masu yawa ya shiga raba musu me dubu biyar me dubu goma cike da murna suka dinga masa addua shi km yana amsawa da Ameen sannan ya sa Kai zuwa cikin gidansu.
yana shiga gidan ya hargitse da murnar ganinsa ya samu guri ya zauna akan kujera me zaman mutun biyu idanunshi na kan fuskar amminsa dake zaune fuskarta d'auke da annurin ganinsa duk cikin ya'yanta tafi qaunarsa saboda tausayin dake garesa, yana qaunarta da qaunar kannensa ,yana tausaya musu, duk abinda suke so zai musu batare da bata lokaci ba shine komai nasu ita da yaranta.
kannensa suka durkusa har
suka gaishesa ,bayan sun gaishesa kowacce ta samu guri ta zauna akan hannun kujerar da yake zaune.
yayi murmushi kana ya dan zamo ya gaishe da mahaifiyarsa "ammi Ina yini ?Lafiya lau ya gida ya fama da aiki ?
"alhamdulillah ammina ya fad'a tare da juyowa ya Kalli hally "Ina sadiq ko ya fita aiki ne ?bai fita ba father yana gida yanzu nan ya fita raka ya marwan bata qarasa rufe bakinta ba sai gashi ya shigo fuskarsa da murmushi dan tun daya ga motarsa a kofar gida yasan yazo ya gaishesa yana tmbyr me jiki jaguwa ya waske tamkar ba dashi yake magana ba.
ammi taso ta tambayesa abinda ya faru dashi jiya amman ganin Babu damuwa atare dashi sai zallar farinciki yasa ta kame bakinta sadiq ya samu guri ya zauna a gefen ammi yana sake tmbyrsa tanweer , ammi ta gyara zamanta tana cewa wacece babu Lafiya ne ?"budurwarsa ce ammi "ya fad'a cikin tsigar zolaya Jin haka yasa jaguwa ya waigo ya watsa masa katuwar harara "Kai haba sadiq yanzu daman yayanka yana da budurwa baka ta'ba fad'a min ba ? lallai kayi min laifi me girma zaka fuskanci hukunci ? Tayi mgnr kmr Adnan ba dan farinta bane, ta rasa dalilin da soyayyar dan nata yake hana kunyarta tasiri idan tagansa neman kunyar take ta rasa "Allah ammi Nima ban dade da sani ba "oh nace dai ta Kalli jaguwa banda abunka ai sai kayi magana a tura gidansu ba sai a had'a dana shafiqa ba a wuce gurin" .
jaguwa ya sake watsawa sadiq harara yana cewa "Allah ammi karki amince da maganarsa ba budurwata bace taimako nayi "taimako! ?ta tmbyesa tana tsura masa idanunta domin gano gaskiyar dake zuciyarsa ,ya gyada mata Kai alamun "eh ".
to ai shikenan idan dai har ka bata lokaci Allah auren dole zan maka na huta da wannan shan kamshin da kakewa aure ta k'arasa maganar tana cewa shafiqa "jeki zubowa yayanki abinci da sauri ta mike ta fita ko cikakken minti biyu batayi ba ta shigo rike da plet ,hally ta mike ta janyo karamin stood gabansa shafiqa ta ajiye abinci tare da bude masa cike da farinciki suka dinga Ina na Saka Ina ajiye da yayansu kowannensu na kokarin faranta masa, cike da matsanacin farinciki da soyayya jaguwa ya kai loman shikafa da miya bakinsa ya ajiye spoon shima sadiq ya matso ya d'auki spoon din da jaguwa yayi amfani dashi ya Kai bakinsa ,ya ajiye spoon jaguwa ya sake d'auka Sadiq yace "gsky father ya dace yadda kayi kyau din nan na rakaka gurin yarinyar nan zance Allah Kun dace ban ta'ba ganin mutanen da suka dace da junansu ba kmar ku ba ......"jaguwa ya wani kallesa shekeke yana cewa menene Kuma zance ? yayi mgnr tare da ajiye spoon din hannunsa ya d'auki tissue yana goge bakinsa "haba father karka waske mana ni dai dan Allah ka auri yarinyar nan wallahi tayi min "na fika sanin tayi aurenta ne dai bazan yi ba kwarya tabi kwarya ya fad'a a zuciyarsa .
"kasan Allah Sadiq yayanka Adnan yafi karfin zuwa wani zance ko menene kace sunansa Allah dai ya tsareni da ..."wani kallo da ammi tayi masa yasa shi katse abinda zai ce ya yamutsa fuska yana lumshewa ammi Idanunshi "duk kagama cika bakinka Muna nan zaka zo kayi auren ai duk dan sunan dole zai so aure "Allah ammi ko zanyi aure bazan je wani zance ba wannan zuwa zance fa kauyanci ne " agurinka ba me ra'ayin rikau amman meye na kauyanci aciki ?"
Allah ammin bayan kauyanci har da lalata Yara yake shi yasa kikaga bana son yaran nan nayi zance "a'a ban yarda da mgnrka ba zance baya wani lalata yaro sai dai can yaron dan iska ne Amman irin zance da shafiq ke yi taya yaro zai lalace a parlour'n nan suke zama gashi mutane ma na Kai kawo Kai dai ka Maida hankali ka tsaida matar aure ,
ni jikina ma ya fara bani lokaci yayi ".sadiq yayi tsigil yace "sosai ma kuwa ammi sai ma Kinga yarinyar dana ganshi daita Allah cewa zakiyi ya aureta kawai "Nan fa hirar ta juye zuwa ta aure jaguwa ya wani shagwa'be fuska kamar karamin yaro yace "ni dan Allah ka rabani da zance aure nan ,nifa auren nan ban ta'ba Jin zanyisa nan kusa ba Kuma ma idan zanyi zanyi ne dan ya zama sunnah da faranta ran ammi Kuma ko zanyi sai na nemo wacce zatayi hakurin zama dani ba wacce zan dinga rage murya ba Ina kaskantar da kaina ba, kasan fa mata idan suka ga ka damu dasu sai salo da iskanci ya tashi babu ma abinda ke bani takaici kmr kaga katon nmj a gaban karamar yarinya yana rage murya da kaskantar da