Showing 156001 words to 159000 words out of 259215 words

Chapter 53 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt

25 Nov 2024

16552

ta karaso gabansa ta buga table dake d'akin wanda takardunsa da system dinsa ne Akai tace "haka nan zaka hakura da abinda take so , zan fada mata da kaina cewar kace ya turo iyayensa idan Kuma kaki bakaki gani ba domin masu irin halinka suna nan cike a agarin nan."
zuwa yanzu gbdy jikin dady tsuma yake kanshi yaji yana jujjuyawa dashi saboda tashin hankali "wallahi ka cuceni ban taba hanaka aure ba amman kake neman mata tana gama fadar haka ta fice daga d'akin ya biyota da sauri yana kiran sunanta "zainab karki soma wannan dayen aiki "zan yi domin wannan shine hukuncin dayafi dace wa da kai ,data dinga binsa yaje ya sake yi mata wani cikin gara ta auresa tunda taji ta gani tana sonshi "karki min haka zainab arayuwa kinsan Ina matukar sonki fiyye da kowa da komai a duniya ban taba tunanin idan kinji abinda na aikata zaki yanke wannan hukuncin akaina ba.
na duara burin duniya akan diyta zata auri mijin da zatai alfahari koda bata auri Ibrahim ba dan haka kar muyi haka dake...."
" zamuyi koma nace muyi data zubar mana da mutunci kmr yadda kake yi a waje Allah gara ta aureshi ai shiriya ta Allah ce sai kaga ya shiryu a sanadiyyarta "bafa zan yarda ba, tanweer diyata ce "please ka fitar min a daki kana damuna da surutun banza,kai bana ma son ganinka kuma kasan allah babu wanda ya isa ya hana aure nan ".


da misalin karfe shida na yammacin rana
Suka fito cikin shiga iri daya sai dai kalar kowannensu dabam sannan kowannensu goye da school bag kawai jaguwa ne kawai mai akwati wanda yake dauke da kayan aiki da school bag idan ka gansu zaka dauka yan wasan kwalo ne saboda irin shigarsu sukayi suka shiga mota daya scopio yajasu suka bar gidan .
kai tsaye airport suka nufa koda suka isa jirgi ya kusan tasshi daman kuma suna sane suka fito late dan su samu damar wucewa da makamansu
da dan sauri suka isa reciption suka Mika body fast dinsu nan maiakatan wajen sukace sunyi lattin jirgi ya kusan tashi .
daya daga cikin maakatan gurin ya tashi kasancewar yasan jaguwa adalilin tafiye tafiyen da yake ,ya karbi akwatin jaguwa suka nufin filin jirgi cikin sauri ya karbi lebet a hannu wani ya manna a akwatin aka sakashi acikin kagon jirgi sannan suka shiga kowannensu ya nemi set dinsa .


Yayinda eku daya rigasu isa abuja tun safe
ya kama musu daki a humble star hotel a second floor ,yayi musu shopping kayan bukatarsu sannan ya zauna zaman jiran karasowarsu karfe bakwai daidai ya nufi airport ya jima kadan kafin ya karasa saboda nisan dake tsaknin inda yayi musu louge yana gama karasowa ya tsaya ariver domin jiran karasowarsu .
Karfe takwas daidai suka sauka,suna sauka eku ya dukesu kai tsaye unguwar Funsho Williams avenue suka nufa bai tsaya akoina ba sai abaki tafkeken get din humble star hotel ,get din abude yake kmar koda yaushe ya sanya hancin motar cikin haraban hotel din maakata hotel din suka taso suna nuna masa inda zai yi parking yana gama parking suka fito daya bayan daya cike da jin kai suke taku har suka karaso cikin reciption "gsky eku ka kama guri mai kyau da sirri allah yasa yadda wajen hotel yayi kyau cikinsa ma haka yake?"inji cewar kamil "ai kana gani ba magana jabir ya fada yana sosa keya suna gama karasowa second floor ya mikewa kowanensu key'n dakinsa sannan ya karasa da sauri bakin kofar dakin jaguwa room 120 ya bude ya tsaya har sai da jaguwa ya shiga sannan ya biyo bayansa babban daki ne dayaji komai da kayan more rayuwa zama yayi akan kujerar kwaya daya dake ajiye adakin eku ya dauki remut ya qara masa karfin ac dake aiki a dakin yayida jaguwa yayi shiru yana kallon tsarin dakin murya cike da ladabi eku yace "boss me zaa kawo maka?shiru kamar bazai yi magana ba sai kuma ya motsa lips dinsa "wani abu mara nauyi "okay sir ya juya ya fita jaguwa ya zuge zip din yar saman rigarsa ya ajiye akan gado ya kwanta flat yayi pillow da hannuwansa duka sannan ya runtse idanunshi babu wacce yake gani acikin kwayar idanunshi sai tanwer dinsa laulausar gashinta,surar jikinta uwa uba dukiyar fulaninta a yanzu ko baa fada masa ba yasan yana quanrta kamar shine ya haifeta musaman a irin qaunar da take masa mai tsanani sai dai duk wannan qaunar da yake mata zai rusheta ya zamanto kamar baa yi ba , zai bar wannan sirri acikin zuciyarsa bama zai bari wani mahaluki ya fahimci halin da yake ciki ba .
a hankali ya fara jin ana knocking a kofar dakin da kyar ya bude bakinsa ya bada Umarnin shigowa kuma har lokacin bai bude idanunshi ba maaikaciyar hotel din ce sanye cikin riga da siket iya gwiwarta ta gaishesa bai amsa ba ta ajiye faranti silver ta juya ta fita ta rufo masa kofa .
Byn fitarta da kamar minti gomasha biyar ya mike zaune yana jin sauyin yanayi ajikinsa ,iska ya furzar mai zafi sannan ya kira number anas da sauran abokansa kana ya janyo akwatinsa ya bude bindiga pistol ya soma fitowa dasu daya byn daya yana kallo kusan guda shida yana kokarin fito da cikon ta bakwai suka fara shigowa one by one anas ne ya shigo akarshe yayi wa kofar key.
Zama sukayi gbdy a gbansa suna kallonsa ya dago ya kallesu "bana bukatar kowanne aciinku ya kwana da kowace mace daga yanzu har zuwa sanda zamu Kammla abinda ya kawomu,bamu samu isashen lokacin tautaunawa ba kafin mu taho amman nasan kowa yasan abinda ya fito damu abu ne mai mahimanci.
Gyada masa kai sukayi "yanzu dame zamu fara?"jabir ya tambaya ya mike tsaye ya jingina da bangon dakin tare rugunme hannuwansa"zamu jira sky muji bayyanan daya samo mana akansu tukun idan ta kama ma a daren nan ma zamu iya fita .
zamuyi wannan aikin bisa kasada da rayuwarmu idan mun fadi ku yafemin idan kuma munyi nasara muyi farinciki tare.
" inshaallahu zamuyi nasara inji cewar Ana's "idan kaji ajiknka zamu fadi mu hakura mana?jubi ya fada yana dubansa "sam banji ajikina cewar zamu fadi ba amman wannan rayuwar tattare take da abubuwa ya fada yana lumshe ido sun jima suna tautaunawa har karfe dayan dare basu samu wani bayani daga sky ba dan haka ya sallamesu byn ya mikawa kowannensu bindiga sannan ya shiga yayi wanka ya fito ya kwanta ruf da ciki gbdynsu sun yi bacci amman Banda jaguwa bini bini zai dauki wayarsa ya duba ko zai ga wani bayani daga sky à hankali Sakonni sky ke Shigowa wayarsa ya zabura ya mike daga kwance da yake ,kwana yayi yana tsara yadda fitarsu zata kasance yayinda minister suka kwana suna tashin hankali da hjy zainab .
Washegari yana tashi ya bude school bag ya dauki brush da toothpaste ya shiga bayi bai jima ba ya fito yana kallon murdadden jikinsa zuwa kan nipple dinsa abinda yafi daukar hankali mata kenan akanshi inda zai sakewa mata da ya ci mata bilaadadin ya goge jikinsa ya fito da turare mai dadin kamshi ya feshe ilahirin jiinsa ya dauki riga da wondo bakake ya saka ya janyo wayarsa nan ya sake cin karo da sakon sky cikin sauri ya shiga neman layukan abokansa ,a haraban hotel din suka hadu suka shiga mota suka fita ."


tun da sanyi safiya shima dady ya shigo d'akin mumy ya isketa zaune ya tsaya a gabanta yana dubanta idanunta duk sun kubura saboda kuka "ni zanyi tafiya zuwa kaduna wata killa na dawo yau ko gobe "bata kallesa ba ta cigaba da jan casbaha ",kiyi hakuri zainab a halin yanzu zuciyata cike take da gariri da tashin hankali bama haka ba har cikin zuciyata nake Jin nadamar abinda nayi .
Wallahi Zainab nayi nadama tun kafin kisan komai na dade wani abu bai sake shiga tsakanina da diyar kowa ba adduata Allah ya yafe min ya Kuma min sausauci bata ce masa um ba bare um'um har ya Karaci maganarsa ya juya ya
tsallake ya bar garin zuwa kaduna yana fita
mumy ta tashi ta shiga d'akin tanweer ta sameta kwnace lamo tana tunani jaguwa yayinda hannunta ke rike da casbaha tana ja tana masa adduar
Allah ya karesa mumy ta samu guri ta zauna kusa daita tana shafa kanta hawaye suka shiga gangaro mata tanweer ta yunkura ta mike zaune taga mumy na Kuka cikin muryar kuka tace "kiyi hakuri mumy nasan saboda ni kike kuka ko ?" inshallahu zan canza, ta girgiza mata Kai tare da riko tafin hannunta cikin nata cike da tausaya mata
Sun dade a haka Mumy na shafa kanta so take ta furta mata abinda ke ranta amman ta rasa dalilin dayasa ta kasa .
cike da jajircewa irin ta sky jaguwa da abokansa sukayi nasara domin kuwa sun amshi makudan kadade kimanin million hamshin a hannun alhj usman koko betse farmer farm sectry , mutun biyu suka rage dan hk suka dawo masaukinsu cike da farincki sun so suyi ashararanci jaguwa ya hanna dan baya wasa da aikinsa sannan kuma baya son aka masa wasa".
Washgari suka fita neman Alhaji sani fefa shima cikin saa suka shiga gidansa suka amshi kudi mai yawa a hannunsa mutun daya yayi saura wato ajirebi .”


Su jaguwa na fita daga gidan alhj sani fefa suka kama gabansu ,shi kuwa zama yayi jagwab akan kujera mai zaman mutun daya zuciyarsa cike da matsanancin mamaki “shi da yake wa mutane fashi shine yau aka wayi gari har gidansa aka biyosa? dadinsa ma basu taba masa lafiyar iyali ba koda yake sun fada masa abinda ya kawo su “kudin da yayi ruwa yayi tsaki aka dannewa marayuwa suka zo amsa “.
Cike da rawar jiki da tashin hankali ya kira number alhj usman farmer farm sectry yana dauka ya fara cewa”anyaka tata shi fa domin kuwa anbiyo kudin da mukaci satin daya gabata “.
Naunayen ajiyar zuciya alhji Usman ya sauke yana mikewa tsaye daga zaunen da yake “sosai kuwa nima cikin tashin hankali nike domin kuwa jiya iwar haka ina cikin tashin hankali har gida barayi suka zo suka yasheni tasss “ kace kai ma anzo maka kenan nan?
“Kwarai kuwa?
“amman me yasa baka kira ka sanar dani ba har kabari suka riskeni har da takamar kudin marayu suka zo amsa ? kasa kunne nayi naga ta inda zanji wanda zaa wa acikin mu tunda yanzu anzo har gida anyasheka nasan ba daga gurinka bane nafi tunani daga sama ne tunda nima sun fada min wannan kalmar kudin marayu suka zo amsa “ ya karasa maganar yana cewa bari na hadamu conference cikin minti biyu kacal muryar ajirebi data galadima da garunmallam ta bayyana a bayanin da Alhaji sani fefa ya cigaba da yi yasa suka fahimci komai “ to wa yasan da wannan maganar “.?
“Byn mu biyar din nan babu wanda yasani “lallai akwai wanda yasani munyi shuka ne a idon wasu , lallai ya kamata mu san ko su waye suka fara bibiyarmu domin bana tunanin wanda zai iya karawa damu bare har ya bibiyemu, “ wannan gsky ne“.
“Gani nan zuwa kafin nazo ka kira jami’an tsoro lallai dole akama wadan nan yan fashi tun kafin su riski sauran dan haka lallai su maida hankali a kamo wadan nan barayin farmer farm sectry na gama fadar haka yayi disconnecting din kira yadda yayi haka sauran sukayi cikin tsananin tashin hankali ajirebi ya hada kudaden daaka raba aka bashi ya zuba cikin akwati ya bar gidansa dan daman cash suka amsa domin gudun idan asiri ya tono ko anbi diddigi bazaa gano daga inda kudn suka shigo ba.”


Shi kuwa Alhaji sani fefa ya soma neman layin jami’an yansanda ya zayyane musu duk abinda ake ciki,cikin kankanin lokaci suka karaso har zuwa babban falonsa ya mike yana sake musu bayani suna dube dube tare da tambayarsa ko akwai wata sheida da zaa iya kama yan fashin “shiru yayi yana tunani mai zufi,“ina iyalin naka suke “?
“Suna wancan dakin ya basu amsa yana sake zurfafa tunaninsa “fatan dai basu taba lafiyarsu ba “?babu wanda suka taba dan lokacin da suka bude kofar suka shigo basa wannan falon suna wancan bangaren ya karasa maganar yana sauke numfashi yana mamakin taaddacin yan fashi “abinda zai baku mamaki kamar walkiya nagansu agabana ni har yanzu mamakin nake yayi shiru goye da hannunwansa duka abayansa can yace “yauwa akwai ajiyar kamarar camerar dana yi a falon ya karasa da sauri inda karamar camerar daya makala a bangon falonsa take mai kallon duk wanda zai shigo.
ya ciro memory “sun yi son ransu amman da wannan bazasu tsira ba domin duk fuskokinsu a bude yake yana magana yana kokarin jona momery din acikin flash sannan ya jona da tv bangon dake manne a falon ana gama hada komai sai ga fuskokin su jaguwa daya byn daya ta bayyana kowannensu rike da bindiga .
daya daga cikin jami’in tsoro yace “gsky kayi dabarar saka wannan karamar camera dan sam babu wanda zai fahimci akwaita dan haka gbdynsu bazasu tsira ba duk inda suka shiga acikin garin nan sai an fito dasu .
“gsky a fito dasu shine kawai kwanciyar hankalina “an gama ranka shi dade “.
Sosai suka maida hankali ga tv duk inda aka hasko fuskar jaguwa da abokansa sai yansada sun dauki hoto , fuskokinsu tas ta fito bazaayi wahalar kamosu ba, cikin kankanin lokaci suka tura hotunansu zuwa headquarters sannan aka tuwa kowaneni maaikaci dake aiki cikin garin sannan suka masa sallama suka wuce …..”
Jaguwa na zaune a mota sakon sky ya shigo “boss byn fitarku a gidan jami’an tsaro sun zo gidan alh sani ku hanzarta komawa masaukinku “.uhm “!
Kawai ya furta a hankali sannan ya katse kiran.
a rana ta uku basu samu bayanin komai ba akan mutun na uku da suke hari daga bakin sky haka ma rana ta hudu wasa wasa suka share kwanaki suna nemansa batare da sun gano inda yake ba dan haka gbdy suka raba kansu suka bazama nemansa yayinda hotunnsu ya baza acikin garin abuja tare da baza jami’ai a kowani titi.
******


Cikin wata shiga ta kamala wacce idan ka kallesu bazaka taba cewa su din masu sata da azalumai da gwanati bane suka shigo cikin club kowannensu ya samu guri dabam ya zauna yana kare wa yanayi gurin kallo har sanda babban yaron ajirebi ya shigo ya isa inda aka ajiye empty chairs ya zauna tare da ciro wayarsa yana daddanawa atare suka kalli juna sannan sukayiwa junansu sigina da ido.
Zaman sa bai fi da minti biyar ba maikatan club din suka karaso inda yake yana tambayarsa abinda yake da bukata , "yallabai me zaa kawo maka ?" ya dago a hankali ya kalli matashin maaikacin dake sanye da uniform fari sannan yace " kwalba giya daya ma ya isa yaron ya juya da hanzari ko minti biyar bai yi ba ya dawo hannunsa rike da tire na silver da kwalbar giya da cup ya ajiye masa akan table duk su jaguwa na zaune suna kallonsa sai dai a shirye suke dashi a hankali ya dinga tsiyaya giya a cup yana sha har ya shanye tass cikin haka aka kira wayarsa ya dauka yay magana sannan ya mike tsaye yana kiran yaron daya kawo masa giya.
Yaron ya karaso cike da ladabi ya tsaya agabansa ya ciro kudi ya mika masa batare daya tsaya amsar canji ba ya juya yana isa haraban club din yaga an sha gabansa a matukar tsoarace yake kallonsu duk da bai san fuskarsu ba ya fahimci su din kamar zasu cutar dashi ne,ya juya da sauri zai gudu yaga mutun biyu a bayansa ,gbdy suka zagayeahi "ina bukatar ajirebi?".
"Wani ajirebi kenan ?"
"kenan amsa kake bukata daga garemu ?" Anas ya fada yana harbin gwiwarsa ya saki kara mai sauti tare da zubewa kasa rike da kafarsa yana cewa "yana wani hotel amaitama no 21 ameka anyaku number dakin 104 suka karbe wayarsa sannan suka turasa cikin motarsa suka rufe shi batare da sun zare key ba suka juya daya byn daya suka shiga motorsu .
jaguwa ya maida hankalinsa ga kallon titi zuciyarsa na hasko masa fuskar tanwer yana kwadayin ganinta da jin muryarta amman wannan aikin ya sha gabansa bazai samu damar kiranta ba sai ya kammala numfashi ya fesar tare da sauke numfashi alokacin da motarsu ta shiga emeka hotel .
sun jima basu fito ba suna jiran umarni daga jaguwa a hankali ya bude murfin motar ya fito yana gyra wuyan rigarsa batare da yace musu komai ba.
suma basu damu ba domin sun san shirunsa yana nufi su biyosa ko kuma su kama kansu ya soma tafiya sam bazakace dan fashi bane .
kai tsaye ya nufi kofar glass wacce zata kai mutun cikin hotel din yana shiga ya tsinci kanshi a reciption yana kokarin tamvayar wata maaikaciya number dakin ya hango ajirebi ta gurin swimming pool yana zukar taba kai tsaye ya zarce zuwa gurin yana hamdala .
Ajirebi na zaune yana cigba da zukar sigari yayinda jaguwa ke nufo gurinsa anas ,da kamil da jabir suna biye dashi sky da jubi da eku , suna waje cikin mota suna jiran umarni .
Ajirebi ya zuki sigari ya busar yana lumshe ido ko da zai bude idanunshi kawai yaga mutane sun zagayeshi cike da tsananin tsoro ya saki sigarin hannunsa kasa yana dubansu gabansa na faduwa anas yayi sama da rigarsa nan idanunshi suka ga bindiga "tashi muje masaukinka cikin lumana kafin ranka ya zama fansa ,ka dauka zaka gudar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login