Showing 192001 words to 195000 words out of 259215 words
Chapter 65 - Kuskuren Baya Complete by Aisha Bagudu .txt
anas allah ba haka bane ba kuma bana damuwa da kai bane , ka fahimceni ina jin tsoro ne allah ka tmbyi ammi ni daman can abu kankani ke firgitani da kaina ma tsorata kaina nake ya muskuta ya sake motsawa ya shige mata har tana jin harbawar jijiyarsa hakan yasa ta kawar da kanta gefe tana cewa kayi hakuri “daman kullum cikin hakuri nake my princess amman ina son ki fahimci ina cikin tsananin bukatarki ina son naga alamun kina bukatata wannan tsoron da nake gani a fuskarki yana maseefar daga min hankali cike da wayo da dabara irin na maza ya dinga romamcing dinta wannan abu da yake mata yasa ta sake lula
duniyar tunaninsa .”
Yau kwanan hally shabiyar agidan wadan kwanakin tayi su cikin zullumi da tsananin tsoron da ta kasa fiddashi bare ta bari wani abu ya shiga tsakninsu da Ana’s , shima bai sake nuna mata damuwarsa ba ya cigaba da tsabgoginsa dan har ya soma fita duk da bai samu sex ba ya samu kwanciyar hankali tunda yana tare da matarsa yana sonta kuma dukkanin alamu sun nuna tana son shi dan tana bashi kulawa gurin ci da tsaftace masa muhalinsa da jikinta domin kuwa tun data zo gidan bai taba jin wani abu byn kamshi ajikinta ba haka ma gidan matsalar dai rashin samun sex ne shima zai cigaba da lallabata yana ma sa rai nan kusa zai amshi abu mai mahimanci agurinta.”
******
Haddden gidan rawa né mai hade da gurin shakatawa acikin Ikoyi hotel ,duk da dare ne amman gurin tamkar safiya ne agurin sakamakon hasken fitilun da suka haskaka gurin , guri ne na sai wane da wane da manya kadangarun bariki wadan da suka amsa sunansu,matan bariki ne kala dabam dabam kowacce da shiga ta tsiraci yayinda wasu ke rawa a tskiyar maza wasu kuma suna zaune akan kujeru na alfarma ciki kuwa har da babban aminin tanko gote wanda ya kasance dillalin koken da abokan alqallarsa mutun uku suna zaune daga baya gurin shakawatar suna tautaunawa akan business dinsu .”gabansu makeken table ne wanda ke dauke da ruwa da manya drinks masu tsada .”
alhj tajjudeen ya kalli abokin alqallarsa dake sanye da complete din bakajen Kaya “Kilo arbain fa kace idan kana bukata zan maka rangi kilo goma daga ciki , ya numfasa sannan yace ina kayan suke?suna border idiroko ya bashi amsa yana daukar kwalbar wine mai dauke da tattaccen ruwan inibi ya bude ya tsiyaya a glass cup yana kokarin kaiwa bakinsa alhji tajjudini yace “cinikin zai yuwu sai dai mai dauko min kayan ne matsala saboda sai mun samu wanda muka yarda dashi” karka damu da wanda zai fito maka dashi inji cikon na hudu ya cigaba da mgn “akwai wanda zai yi alqallar cikin sauki .
“waye shi ? ya tambayesa yana tsaresa da jajayen idanunshi “Jaguwa!
“Jaguwa ?
ya furta sunan ahankali yana tunani inda yasan sunan, idan kuma bai san sunan ba to lallai ya taba jinsa kuma abakin takon gate. “jaguwa ya kasance babban dan fashi da makami ne a kasar nan sannnan yana da basera da zai iya shigo maka da wannnan kayan cikin sauki batare da wata matsalar ba .“Kana ganin zai iya “?
“shine kawai zai iya kawo maka akoda yaushe cikin aiki yake kuma sam bashi da tsoro ko tunanin abinda gwanaty zatayi “well done haka nake son mutun mara tsoro ,yanzu ya zaa yi na samu ganawa dashi “? “ ina da wani abokina yana da number na hannun damansa wanda ya kasance babban amininsa “ tô shikenan ka nemishi ka fada masa sannan kayi masa biya mai kyau, ka dai san hatsarin aikin namu akwai hatsari karka biyasa kudi kadan “
“Haka ne sai dai zan kara tabbatar maka ka sa aranka babu wani matsala zan hadu da abokina gobe zamuyi mgn kuma a goben zaa kirasa ya karasa maganar tare da mikewa yayi masa sallama yana tafiya alhj tajjudini ya mike tsaye shina jami’an tsaron dake tare dashi ya mike shima mutun dayan daya saura ya mike suka jera suna magana wacce zaka dauka ta arziki ce nan kuwa ta kwaya ce.”
Anas na zaune a babban falo jaguwa wanda shigowarsa kenan aka kira layinsa yana amsa waya jaguwa da jubi da kamil har ma da jabir suka shigo suka fara neman gurin zama “lallai muna yi amman bama yin wannna alqallar yana gama fadar haka ya katse kiran “meye shi bama yi ?
“Alqallar safarar miyagun kwayoyo bai yi magana ba ya daura kafarsa kan daya yana girgizawa jubi ya kallesa yace “wannnna ai ba komai bane me zai hana muyi ana samu kudi sosai ? sai lokacin jaguwa yayi magana rai a bace kai kake ganin ba komai bane amman mu agurina komai ne har gara fashi da wannan sanar “ka daina cewa haka muna aiki dan mu samu kudi kaga bamu da choice akan kowani irin aiki da zaa kawo inji cewar kamil “nima shine abinda nagani tunda mun sadaukar da rayukanmu me kuma yayi saura? jaguwa ya cire kafarsa akan dayar ya fuskancesu gbdy “a yanzu zaku iya fadar komai amman me yasa da police suka farmaki rayuwarmu a wancan ranar abuja kuka shiga damuwa da tashin hankali tunda kusan kun sadsukar da rayukanku“?
Shiru sukayi babu wanda ya sake cewa uffan “kuna son zama dani ya zama dole kubi abinda nake só ban yarda ba sannan ban amince ba duk kuma wanda yayi kokarin yin wannan aikin abayana zai sha mamaki.”har gama Babu wanda ya sake cewa komai anas ya lumshe idanunshi dan dadin abinda ya fada wannan shine karo na biyu daya burgesa a rayuwarsa “
Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️35
………Alhaji tajjudeeni ya dauki sama da awa daya zaune kwakwaluwarsa na mamakin maganar da yaronsa ajuwon ya kawo masa akan tautaunarwasu da jaguwa bayan sunyi waya dana hannun damarsa babu nasara suka tunkaresa kai tsaye shima dai maganar daya ce ta shiga tsakaninsu dashi basa yin wannan alqallar ,sai daya sake yiwa yaronsa duban tsanake sannan ya numfasa yace “ka sheida masa aikina zai yi da har ya tsaya maka taurin kai ?
“Tabbas ya sani domin kuwa nayi masa bayaninka dalla dalla da irin matsayi da karfin ikon fada aji da kake dashi a garin nan ,amman isa da izzarsa suka rufe masa idanu har yana cewa babu ruwansa da wani matsayi da karfin ikonka ,“wannan ikon da isan sai dai kayi wa karnunka yaranka da kake iko akansu amman shi babu wanda ya isa yayi masa dole akan aikinsa “.
nan take zuciyar alhj tajudeeni ta dagule ta soma masa ciwo yaji kamar ta kama da wuta tsabar bakinciki ,ya tattara kan takardun dake gabansa da sauran kayayyakin da yake aiki akansu ya ajiyesu amaajiyarsu sannan ya mike tsaye ya zagayo ya bar kan kujerarsa ya fara zariya acikin office dinsa goye da hannuwansa duka a bayansa yana sake jin mamakin jaguwa .”
cak yaja ya tsaya yana fuskarta ajuwon tamkar shine jaguwa sannan yaja wani wawan tsaki tare da kai hannu ya daki kan makeken table din dake office din “lallai ya kamata naga wannan tantirin yaron yana gama fadar haka ya dauki manya wayoyinsa guda biyu ya nufi hanyar fita ajuwon ya biyo shi da sauri yana masa magana cikin tsananin tashin hankali “shi fa wannan ba kamar sauran mutanen da muka saba mu’amula dasu bane ,shi mutun ne da yasan abinda yake , mutun ne da idanunsa suke a bude tunda ya nuna bazai yi aikin nan ba kawai aganina gara a hakura dan…”
“Baza’a hakura ba duk abinda ka lissafa kai ka san shi ,ni bansan haka ba baya ga karfin ikona da ikon fada aji da nake dashi sautin furucin alhji tajudeeni kenan wanda yasa ajuwon ya katse maganarsa da sauri ya cigaba da binsa yana cewa “sorry sir !.
kai tsaye haraban companie dinsa TGI GROUP ya fito yana kiran number direbansa wanda shi tuni tun fitowarsa ya zabura ya mike ya soma kokarin karasowa inda kafin ya karaso escourt dinsa sun zagayesa rike da bindigu ,daya daga cikinsu ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna yana jin tuttukin bakin ciki acikin zuciyarsa a fusace ya bawa escort dinsa umarnin karsu biyosa .”
ajuwon ya zagaya ya bude gaban mota ya shiga ya zauna a lokacin da direba ya shiga har ya tada mota yana cewa ranka shi dade ina muka nufa?
“Ka fada masa inda zamu alhj tajuddeeni ya fada a fusace yana kallon wani gefe ,allah allah yake kwayar idanunshi ta sauka akan jaguwa da dan iskan na hannun damarsa zai nuna musu karfin ikonsa ,zai nuna masu yadda ake saka mutu yayi abinda bai yi niyya ba sai dan karfin iko ,zan nuna masu isar da nake dashi da karfin iko da fada ajin da nake dashi a garin nan .”yayi maganar aransa yana jijiga kafarsa daya.
a hankali ajuwon yake direct din direba har suka karaso igando tun daga nesa ya nuna masa gidan suna gama isa bakin tangamemen get din gidan ya tsaya tare da yin hon ,mai gadi ya mike da sauri ya leka ta karamin hujin get ganin bai san motar ba ya rufe ya fito gbdy alokacin har ajuwon ya fito daga cikin mota ya mika masa hannu shima mai gadi ya mika masa hannu suka gaisa “dan allah ko jaguwa yana around“.?
“Eh yana nan sai dai bai sheida min cewar wani zai zo nemansa ba amman zaku iya kiransa idan yasan da zuwanku zai kirani,“no ka bari mu shiga da motar ciki sai kayi mana iso gurinsa “A’a bari dai na fara sheida masa idan ya amince babu matsala sai ku shigo din wa zance ?.
ajuwon da maganar mai gadi ta bata masa rai ya dai daure ya motsa bakinsa da kyar“kace masa ajuwon ne mu zo ne tare da alhji tajudeeni“to shikenan ka bani minti biyar zan dawo yanzu mai gadi ya juya da sauri ya koma ciki shi kuma ajuwon ya koma jikin mota ya tsaya rungume da hannunwansa alhji tajudeeni yayi wani glass din bangaren da yake zaune “tsayuwar me mukeyi anan ?.
“Wai sai ya nemi izininsa sannan zai bari mu shiga “ ya kalli get din gidan yanawa gidan wani irin kallon tsana sannan yace “wa dan fashin yake da wannan matsayin ?ai fa ya wuce duk wani tunanin mutane gagara badau ne dan dai bakasan shi bane shiyasa amman idan kana jin oba loud ,Ijile , jagu…..“.
tsakin da alhji tajudeeni yaja yasa yayi shiru yana kallon wani gefe yana dariyar mugunta a ransa yace “kadan ka gani yau dai matsayinku yazo inda bashi da amfani.”
mai gadi bai dauki lokaci ba ya dawo yana cewa “wai yace ku shigo amman banda motar ku “.
ajuwon ya sheidawa alhji tajudeeni abinda jaguwa ya fada nan ya sake shiga tashin hankali matuka har ya shigo cikin hadadden falon da’akayi musu masauki mamaki yake .parlour yayi shiru kamar yadda alhj tajudeeni da ajuwon sukayi sai dai idanunsu na aikin karewa falon kallo ne komai tsaf sannan kuma a tsaftacce a tsare ,ahankali suka fara jiyo kamshin dadaddan turare na kamfanin flower mai dadin kamshi a natse alhji tajudeeni ya waigo idanunshi zuwa dogon koridor dake gefensa da jaguwa idanunsa suka fara yin tozali cikin wando da rigar shan iska mai hannun singlet mai azabar kyau .”
anatse ya cigaba da taku cikin isar nan nashi yayinda abokansa ke biye dashi kowannensu cikin kanana kaya kallonsa yake har sanda ya karaso ya samu guri ya zauna ya daura kafarsa daya akan daya yana girgiza wa haka ma abokansa banda anas suka yiwa kansu gurin zama eku ya karaso gabansa cike da girmamawa ya ajiye wayoyinsa akan hannun kujerar da yake zaune sannna ya koma cikin yan’uwansa suka tsaya rungume da hannunwansu akirji .”
Shiru babu wanda yayi magana acikinsu hakan ya tabbatarwa alhji tajudeeni lallai yana da izar da aka fada masa yana daita ,kiran daya shigo wayoyinsa ne ya katse masa zance zucin da yake anas ne dan haka yayi hanzari ya daga dan tun safe bai ji sautin muryarsa ba kuma ya kirasa bai shiga ba “anas ina ka shiga ne nayita kiran wayarka bata shiga ?.”
“subhallah ya fada wanda hakan ya janyo hankular sauran abokansa gbd suka tattara hankalinsu da natsuwarsu garesa “okay allah ya baka lafiya hope kasha magani? Okay shikenan sai ka shigo yana gama wayar ya katse ya kai hannu ya zaro bindiga akarkashin kujerar da yake zaune ya rike yana kallonta yana shafawa still bai ce komai ba .”
da idanu yayiwa sky alamar ya kunna masa tv ya karasa da hanzari ya kunna ya dauko masa fear less mai sanyi ya ajiye akan karamin table ya janyo gabansa ya koma matsayarsa ya kame .
Jaguwa ya gyara zama ya fuskanci tv yayi kamar bai san da zaman wasu halittun mutane agurin ba har lokacin da anas ya karaso cikin shiga ta kamala ya mika musu hannu d’aya bayan d’aya sannan ya samu guri kusa da jaguwa ya zauna suka kalli juna ya kai hannu ya shafa wuyansa yaji zafi sosai alamun baya jin dadi “kaji abinda naji kuwa ajikinka anas ?jikinka kamar garwashin wuta sky kawo masa magani ya sha dan da alamun bai sha ba”.
Sky ya juya da sauri ya bar gurin “nan su jubi suka fahimci shine bashi da lafiya gbdynsu suka masa sannu ya amsa yana dafe kansa dake masa mugun sara sannan suka sake maida hankalinsu akan wayoyinsu yayinda alhji tajudeeni ya maida hankalinsa kacokan akansu duk ya qagu jaguwa bai masa mgn ba gbdy sai yaji ya munzanta agurin har yayi daya sanin zuwa ajuwon ya kai bakinsa daidai kunnensa yayi masa magana cikin rada “wannan daya shigo yanzu shine anas na hannun damarsa kai kawai ya gyada alamun ya fahimta .”sky ya dawo hannunsa rike da magani da ruwan roba ya mikawa anas cike da girmamawa anas ya mika hannunsa ya amsa yana masa godiya sannan ya sha, jaguwa ya sauke numfashi yana sake masa sannu idan bakaji sauki ba sai muje gurin sadiq ya duba min kai “inshaallahu ma zanji sauki daman rashin ban sha magani ba .”
Gyaran murya alhj tajudeeni yayi yace “jaguwa kake ko wa kana kallon mutane amman kayi kamar baka san da zama na ba sai faman uzurin gabanka kake ?jaguwa bai dago ya kallesa ba yace “kar nayi uzurin gabana acikin gidana abun ikona? “ ka kuwa san ko waye zaune a gabanka ? sai lokacin jaguwa ya dan dago ya kallesa a wulakance kana yayi murmushin irin nasu na goggun yan duniya yace “waye kai !?
“Ni kakewa wannan tambayar?idan baka sani ba shi wannan dake zaune shima bakasanshi ba ?
“Eh! “ya fada kai tsaye yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa tare da kafesa da idanunshi.
ganin yadda jaguwa ya hassala ya canza cikin kankanin lokaci ya dawo tamkar zaki yasa alhj tajudeeni ya sausauta muraya “ok shikenan daman ba wani abu bane ya kawoni sai akan maganar shigo min da magani “amman ai na fada ma wannan banzanyi ba …”
“ni kuma kai nake son kayi ya karasa maganar yana dubansa tare da kwabe fuska alamun bai isa yakiyi ba “ to bazan yi ba ya fada atakaice sannan ya gyara zama ya jingina jikinsa da kujerar dayake zaune yayi crossing leg’s dinsa ya rungume hannunwansa duka akirji yana dubansu a kaskance.
Alhj tajudeeni yayi shiru yana kallonsa yana nazarinsa kafin a hankali ya cigaba da magana “
hakika zillarka ta matukar burgeni sai dai ko bakayi wannan alqallar ba zamu samu wadan da zasuyi .”
“bazai yiwu ba wannan aikin ni kadai ne zan iya duk kuma wanda zaka sa ka tabbatar da sai ya shiga hannun hukuma idan kuma bai shiga ba ni nan zan maka fashinsu na kaiwa hukuma “tô meye bako aciki yansanda? yansanda karnunka farautarmu né su din tamkar dabbobi ne agurin mu ,kowa yasan bukatarsu da burinsu kudi ne kuma akwai su ,idan bakasani ba bari kaji dukkanin wata alqalla da mukeyi acikin garin nan yansanda suna da kaso mai tsoka aciki dan haka ko da kai ko babu kai zamuyi abinda mukayi niyya kuma babu wanda ya isa ya hana wannan kayan shigowa su iso gareni”. ya karasa maganar yana kallon jaguwa a dage domin sake tabbatar masa da bai isa ya hana aiwatar da nufinsu ba “.
“Lallai kun fargab da d’an zakin da bai shirya karawa da ku ba, babu shakka wannan niyyar taka bazai taba yiwuwa ba domin kuwa ina da yakinin allah bazai baku saa ba a duk lokacin da ubangiji ya baka wata kyakkyawa dama kayi amfani dashi gurin kyautatawa gobenka idan ba haka ba zaka riski gobenka a gurgunce ya karasa maganar a matukar fusace cikin yanayi na tashin hankali yana dukan hannun kujerar da yake zaune wani irin numfashi ya fesar mai zafi kana ya maida kansa jikin kujera ya kwantar tare da lumshe idanun shi “anas ya matso daf da jaguwa ya riko hannunsa cikin nashi yana cewa“Wannan shine tajudeeni din ?
“Tajudeeni!?”
Alhj tajudeeni ya maimaita sunansa da anas ya furta without respect yana dubansa ahankali Jaguwa ya gyada masa