Showing 246001 words to 249000 words out of 306755 words
Chapter 83 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt
taga shigowar motarsa cikin gidan, da mamaki tabi motar tasa da ido, tin tini takeji a jinin jikinta ba lafia ba, shiyasa ta gaza rintsawa,. "Daga ina yake a wannan tsohon daren?'' Take tambayar knta da knta, hadi da dumbin mamaki a tattare da zuciarta da fuskarta. Tana nan tsaye jikin window din tana tunani har taga fitowarsa daga motar ya nufa side dinsa duk tana tsaye bakin window din, ba jimawa taga fitowarsa daga side din nasa daure da Alwala sbda yalwar hasken dake compound din gidan kmr rana, dan hk ta hango ruwan Alwala a kn fuskarsa, Tana kallonsa ya fice a gidan zuwa masallaci, dai-dai ana kokarin tayar da sallarh asubahin, jiki ba laka Amihh ta juya ta nufa toilet ta dauro alwala itama, ta fito ba jimawa, ta saka hijjabi ta nufa kn dadduma ta tayar da sallar asubahain, sam ko natsuwa bata dashi, sbda tunanin daga ina AB'ILAL yake a wannan lokacin, dan sam bata da full kwanciar hnkli hk ta idar da sallar, ko adduarh batayi ba ta tashi ta fice a dakin, ta fito falo, ta fice a side din gabaki daya, sanye da hijjabin data idar da sallar asubahin dashi, ta nufa side dinsa, ta isa har bedroom dinsa bata gnshi ba, hkn ya bata tabbacin be dawo daga masallacin ba, ta dawo falon ta shiga zirya a tsakar falon idanuwanta se lumshewa sukeyi jikinta duk tako ina a mace yake, burinta ya dawo daga masallacin taji daga ina yake, abnda yasa abin ya dameta, sam be taba fita ba ya shigo gida a wannan lokacin, ita kawai a yanayin jikinta takeji wani abu na damunsa,,duba da la'akari datayi da irin gagarumar ramar da yayi, itama ta kara firgitata, hnklinta sam be kwanta ba tako ina, zuciarta na rawa. "Allah ka jarabcemu da abnda zamu iya...." Abinda ya fito daga bakinta kenan, se kara zirya takeyi a falon, zuciarta sam ba natsuwa, da tayi wannan tunanin ta dawo tayi wancan tunanin, gabaki daya knta ya kwance, babbar adduarhta Allah yasa ba mummunar harka ab'ilal ya jefa knsa a ciki ba... Ta sauke ajiyar zucia me cike da zallar tashin hnklin da take ciki, ita de kawai hnklinta be kwanta ba, taji a jikinta yana cikin wani hali ne, sam ma bataga alamar natsuwa ba a tattare dashi... Tana nan tana zirya a falon ya shigo wuraren 7:am kasancewar ya tsaya yayi askar din safe hadi da zikiri da salatuttuka ga ma'aiki S.A.W. yana shigowa idanuwansa suka sauka a kn Amihh se zirya takeyi a falon tana ganinshi ta kureshi da ido nan take ta hango Ainihin matukar ramar da yayi se taji zuciarta ta amsa da tausayin d'anta, Ainihi Amihh tana jarabar son AB'ILAL kmr k'ashi da tsoka daya a miya. "Hubbul ruhh!" Amihh ta kirashi da sunan datake kiranshi dashi da yana karamin yaro, karasowa yayi ya fada jikinta daman kmr yana jira ya sakar mata nauyinsa ya fashe da kuka, amihh ta rungumeshi a jikinta sosai nan ta kara tabbatar da ramar da yayi ta shahara, duk jikinsa yabi ya canza. "Hubbul ruhh, meye na kuka? Waya tabamin kai? Ciwo kayi ne kayi wannan ramar?'' Amihh ta jero masa wadannan tambayoyin duk ta shiga d'imauta da dmwa, AB'ILAL be tankataba yaci gaba da kukansa yayin da hawayensa keta sauka a kafadarta inda yasa knsa, sam ko nauyinsa Amihh bataji hnklinta kaf ya riga ya gama tashi kawai de tana danne zuciarta ne, amma ji takeyi kmr ta fashe da matsanancin kuka. "Tell me plz, meya sameka Abii na? Daga ina ka dawo da Asubah?'' Amihh ta kara tambayarsa muryarta na kokarin bayyana tashin hnklinta amma tanata daurewa hadi da kokarin control. Cikin kuka ya fara mgna "Amihh san yarinyarnan wlhy kasheni zeyi!, na rasa sukuni a rayuwata, amihh pls kimin adduarh , Amma ba adduarh dazan rabu da santa ba,,amihh ina santa wlhy, ko a ina take ina santa, koda bata da kowa a dunia Amihh ina santa, Allah ne ya jarabceni, a knta ban iya bacci ban iya sukuni rayuwata ba dadih, pls amihh me nayi ALLAH ya jarabceni da Tsananin santa har haka!? Pls ki tayani neman gafara ga ubangijina, ya yafemin abnda nayi ya jarabceni da soyayyar yarinyarnan me kashe zucia da gangar jiki!'' Ya karashe yana me kara fashewa da kuka daman ya jima yana neman inda ze samu ya kwanta yayi kuka, ko ze samu sassauci a zuciarsa. Tabbas kukansa na tabata, bata taba ganin kukansa ba se a yn kwanakinnan kuma duk a kn yarinyar, Abin ya daurewa Amihh kai, bata taba ganin so irin wannan ba Ace mutum marabarshi d mahaukaci shine sitirar dake jikinsa,. "Pls kayi shiru ny boy..Kana cin abnci ma kuwa babana?" Amihh ta tambaya tana kara rungumosa jikinta, duk taji ma nauyin nasa babu wani na kirki ynzu. Kwace jikinsa yayi daga jikinta, fuskarsa shabe shabe da ruwan hawaye, ya tsugunna a kasan guiwowinsa idaniarsa na zubda kwallah, , ya dago ya zuba mata sexy yum-yums idaniarsa, wadanda suka koma kalar jajjawur sbda kuka a yn mintunan kukan da yayi yafi karfin a kirgashi a mintoci ko awanni, sbda da zuciarsa yake kukan, zucia kuwa tafi Second ko mintoci da awanni gudu, ko bature be isa ya kiyasta gudun zucia ba. Cikin hawayen ya fara mgna idaniarsa na kn Amihh itama idanuwanta na kn dannata da duk take ma masa kallon full mahaukaci. "Amihh bana ta Abinci a halin da nake ciki ynzu,, pls ki gayamin ina yarinyarnan take, dan Allah Amihh ki gayamin! Ki dawomin da ita tinda akwai Aure na a knta, Auren sunnah kikasa aka mana da ita, Amihh Wlhy yarinyar ba irin sauran mata bace Allah subhanahu shiya jarabceni da soyayyarta hadi da tsananin sha'awarta dan Allah Amihh ki temakeni!'' Ya karashe zuciarsa na beating da karfi ji yakeyi kmr zata fito daga kirjinsa ta fito fili, ya fashe da kuka me tsananta zuciarta me sauraro a zurfin tausansa. Lumshe ido Amihh tayi klmnsa na dukanta, ji takeyi kmr ta maidashi ciki, a lokaci knkani kamanninta suka sauya zuwa zallar damuwarta data fi ta da. "Tashi muje kayi wanka heart beat, kaci abnci, se in gaya maka inda take..." Amihh ta fadi da karyayyiyar zuciarta, dukda batajin zata iya gaya masa inda take, sbda zalincin da yayima yarinyar kmr sabo take jinsa a cikin zuciarta, amma tana tsananin tausansa, a jini da tsokarta tasan ya azabtu. Farin ciki ya rufe AB'ILAL jin tace zata gaya masa inda hilwah take, nan take farin ciki me bayyanar da annuri hadi da annashuwa me tsananin haske ya bayyana a kn kyakyawar fuskarsa, kmr bashi ke kuka ba, duk yabi ya shige halarar farin ciki. Amihh ta zuba masa ido, hadi da lumsar kyawawan idaniarta a knsa, ta kara budesu a kn nasa. AB'ILAL ya kamo hannayenta ya rike cikin nasa, still yana tsugunne bisa guiwowinsa ya fara mgna cikin zallar farin ciki "Auwal hubb da gaske xaki gayamin inda take?'' Amihh ta daga masa kai alamar Eh, kana ta fara mgna "Amma seka gayamin daga ina kake tin safe, ka dawo gidannan da asubahi?'' AB'ILAL ya lumshe idanunsa, komi Amihh tace masa ze iya yi sbda kawai tace zata gaya masa inda hilwah dinsa take. "Naje neman hilwah ne..." Ya bata amsa nan take. Amihh ta tsiresa da ido tace "Ina kaje nemanta?'' Ab'ilal ya bata amsa "Duk inda nasan akwai jama'arh a garin nan Amihh, inna ci gaba da zama ba tare da ita ba zan iya mutuwa Amihh...taba kiji zuciata kullum cewa takeyi zata fashe wlhy Amihh ni inaji a jikina inada ciwon zucia, mutuwa zanyi Amihh..." Ya karashe yana me dafe kirjinsa dake masa barazanar tarwatsewa. Amihh ta zuba masa ido tana sauraron kalamansa, wad'anda take jinsu har a kasan zuciarta. "Babana ka sassautawa knka pl..." AB'ILAL yayi hanzari katseta ta hanyar cewa "Amihh ai bani na daura wa kaina ba, balle in sassautawa kaina,,ki temakeni ki roki ALLAH subhanahu ya sassautamin plz!" Amihh ta sauke ajiar zucia sam zuciar tata bata cikin ddh tace "ALLAH ya sassauta maka hubbul ruhh..." AB'ILAL ya amsa da Ameen, still hannayensa na cikin nata. "Hubb ki gayamin inda take plz?'' Amihh tace "Seka tashi munje kayi wanka, kaci abnci sosai, ka saki sannan zan gaya maka..."" Jiki a sanyaye ya mike tsaye yana tangal tangal kmr ze fadi kasa,.. matsowa Amihh tayi ta rungumo abinta jikinta, a hk suka karasa har bakin toilet din bedroom dinsa, ya shige toilet din jiki babu vitamin A, Amihh ta juya ta fice Zuwa side dinta, ta nufa kiching domin ta hada masa abinci mara nauyi me sauki,,ba bata lokaci ta gama hada masa dafadukan superghetti me Irish wanda ta cikashi da kayayyakin ganye na gina jiki, ta gama ta juye a kulah, ta hada masa farfesun cow leg, ta juyeshi a cikin kular shima,, ta hada masa drink me sauki hadi da gina jiki, ta hada duk kulolin a kn tray, hadi da jug din drink din, ta hada plate da bowl da cup din jug din, data zuba drink din a ciki, ta dauko bottle water me sanyi ta ajiye a tray din, jikinta har yana rawa ta gama ta dauko tray din zuwa side dinsa, a falo sukayi kicibus hanyar fitowa, ta tsaya ta zuba masa ido, sanye yake da jallabia me layi layin kalar dark mint color, and light mint, ta saman jallabiar duk aikine me kyau da tsaruwa, dukda ramat da yayi amma jallabiyar ta amsheshi.. ''fita zakayi?'' Amihh ta jefo masa tambayar. Daga mata kai yayi Alamar Eh, Amihh tace "Ina zakaje?'' Ab'ilal yace "Zanje gunki ne Amihh tin daxu na gama wankan, zanzo ne ki gayamin ina yarinyar take..." Hjya maryam tayi shiru ta zuba masa ido, yaro duk ya susuce. "Muje dining kaci abnci, tukunna...." Ta fadi hkn hadi dayin gaba, ya biyota a baya, ta ajiye tray din a kn dinning table din, AB'ILAL yaja kujerar daya daga kujerun dinning din ya zauna, hadi da zubo mata ido, ya rafka uban tagumi. "Babana cire tagumi ..." Amihh ta fadi hadi da jnye masa hannunsa daga tagumin da yayi, tana tsaye, ya langwabar da knsa gefe, se kara langwobewa yakeyi ko ze samu Amihh ta kara jin knsa, sosai ta gaya masa inda yarinyar take,,amma jikinsa na basa da wuya ta gaya masan. Da knta ta zuba mata superghetti din daketa kamshi a ciki plate, ta tura masa gabansa, hadi da caka masa face a cikin superghettin. ya zubawa superghattin ido , amihh ta zauna kujerar kusa dashi, sam ko yunwa bataji dukda ana nemn 10:am ne lokacin, ka ta saba karyawar wuri amma sam batajin yunwa. "Bismillah kaci mna, se in gaya maka inda take....." Cewar Amihh, ba bata lokaci AB'ILAL ya dauki fake ya faracin superghatti yanaci yana lumsar idanuwa, ji yayi abncin na Amihhn ma ba ddh har wani daci daci yake masa a baki, kawai yana daurewa ne, yanaci tunawa da yayi da tace zata fada masa inda hilwah take, Amma har zuciarsa tashi ma takeyi., yanacin superghatti yanawa Amihh sambatu a kn yarinyar, duk lbrinsa a kn yarinyar ne, "Amihh de nata ido, duk ta daskare a zaune, uban yan taurin kai da rashinji duk yabi yayi Sanyi kmr ma bashi ba. Kadan yadanci superghattn ya barshi hk, shi a ganinsa yaci da yawa sbda ya mance yaushe rabonsa da abnci me amsa sunansa abinci ya shiga cikinsa yama mnce, inba jiya ba dayaci kadan a gidan hjya karama, yau km yaci dayawa. "Ka k'oshi kenan?'' Amihh ta tambaya ganin ya ture plate din gabanshi. Daga mata kai yayi alamar A. "Ka kara plz..." AB'ILAL ya girgiza mata kai alamar Aa'h, ba tare dayayi mgna ba. "Ki gayamin ina take to Amihh tinda naci abncin..." Ya fadi a marairaice, duk yabi ya kagu. Ba tare da amihh tace masa komi ba, ta tashi ta dauki bowl ta zuba masa farfesun, ta tura masa gabansa ya kalli farfesun ya dago ya kalleta, hadi da girgiza mata kai, ta daga masa kai, ba musu ya fara cin farfesun kadan ya danci yasha drink ya tashi a kn dining din ya koma kn kujerar 3ct ya zauna, yanajin zuciarsa na tsananta tashi, Amihh ta biyoshi tana fadin 'Baka ci komi ba sosai..." AB'ILAL daya rike knsa dake tsananin masa ciwo, abncin daya gamaci se taso masa yakeyi sosai, cikin dakiya da dauriya yace "Am ok Amihh, in ba na gnta ba bazan iya cin abnci bama kwata kwata..." Karasowa Amihh tayi ta zauna kusa dashi, takawo hannunta ta taba knsa taji ya dau zafi rau-rau, "'kanka na ciwo ne?'' Ba tare daya bata amsa ba, ya mike cikin hnzari ya nufa toilet din falon, amihh ta biyoshi a baya, ta taddashi a durkushe a kasa Se kwarara aman abubuwan dayaci ma cikinsa yakeyi, Amihh ta zuba masa ido, har ya gama amayar da kaf abubuwan dake cikinsa, nan take jikinsa yayi laushi lubus, Amihh ta bashi ruwa ya kuskure bakinsa, ta zuba masa ruwa a knsa, se yaji sanyi, ta wanke masa face dinsa,, ta rikoshi suka dawo falon ya kwanta a kn kujerar 3ct se sauke numfarfashi yakeyi, cikinsa nata murd'a masa. Sannu kusan uku amihh ta jero masa a lokaci daya. daga mata kai kawai yy, ta juya ta nufa toilet din ta gyara inda ya bata da aman, kana ta dawo ta fice a dakin ta dauko kayayyakin aykinta ta dubashi sosai, a nan ta gane bugun zuciarsa ta yawaita ya wuce yadda akeso, hnklin Amihh ya tashi, tasa masa drib domin ya samu sassauci da karfin jikinsa, tasa masa alluran baccia drib din, ruwan na fara ratsa jijiyoyinsa, ba jimawa kuwa bacci ya kwasheshi, Amhh ta zauna kujerar dake fuskantarsa ta zuba masa ido, duk jikinta yy sanyi... Rnr nan side din nasa Amihh ta wuni, tanata bashi kulawa, har dare, se tambayarta yakeyi ina matarsa take, Amihh se kwantar masa da hnkli takeyi, tin 2:pm, drib din data sa masa ya kare. da daddare byn yayi sallar isha'i yau duk, a gida yayi sallolin sa, amihh ta bashi abnci ta matsa masa yaci, ta masa allurori, ya kwanta a kn bed dinsa, Amihh ta zauna a bedside se kara tambayarta yakeyi a kn ina matarsa, amihh ta masa shiru dan gani takeyi beda lafiar hnkli,, ta zura masa ido, har bacci ya kwasheshi yana sambatun cewa, ina matata! amihh tayi ta masa addu'ur'i tana tofesa dashi harta samu ya tsagaita da sambatun nasa, ta lullubeshi sosai da duvet ta fice a falon, zuwa side dinta, tana tafe tana zancan zuci, tana shiga bedroom dinta, ta jawo wayarta ta kiran lmbr wani dr babbar dr ne me duba lafiar kwakwalwa,, ta kirashi kn yazo ya duba AB'ILAL sbda ita ganinta ma beda lafiya kwakwalwar ne..
Washe gari 4:37am ya samu ya tashi daga nannauyan baccin daya suresa sbda allurorin da Amihh ta masa, ya tashi ya nufa toilet yayi wnka yana mejin saukin jikinsa, sbda drib da Amihh tasa masa, da kuma bacci daya samu sosai. fitowa yayi daure da alwala ya saka irin jallabiyar daya cire jiya, amma sede color ya bambamta, wannan ligt ash ce and light ya zira ya nufa masallaci, yayi sallar asubahi ana idarwa ya dawo gidan, ya ziri car key dinsa, ya hau motarsa ya fice a gidan, kawai yaji zuciarsa ta koma gidan hjya karama, dan hk direct gidan nata ya nufa, nesa da bakin get dinta yy packing yana duba agogon motar yaga 7:am ne, se yaga kmr yy sassafe inya shiga gidan ynzu, dan hk ya tsaya har zuwa 7;30am kana ya isa da motarsa ga get din gidan yy hon, me gadin ya wankale masa get din gidan bayan ya leko yaga motar tasa, ya danna da motar tasa cikin gidan, yayi packing a packing space ya fito, ya nufa side din hjya karama, ya taba kofar dazata sadashi da side din nata, yajita a akulle, ya tsaya kusan na 30mnt, kana ya shiga knocking kofar a hnkli, hadi da sakarwa kofar nauyinsa, yana sinsinar kofar ji yy tana kamshin yarinyar.. Dai-dai tana zaune a kn dinning tana shan ruwan tea, ta kasa baccine jiya da yau kwata kwata, shine ta fito tasha tea tasha mgnin dazata samu tayi bacci, kaf gidan yy sit salwah na bacci, Hjya karama kuma tana side din mijinta, ma'aikatan gidan kam tin kafin asubahi suke tashi , suyi aykin gidan su koma su kwanta, a bangarensu na ma'aikata, se wuraren 12:am suke tashi, breakfast kam kowa da knsa yake hada abnda yakeso yaci, zuwan hilwah da salwah gidan ma suke yawan yin girke girken gidan, hjya karama km ita ke zama tawa me gidanta girki da knta. Ta kai cup bakinta taji ana knocking kofar farko sbda kofa ta biyu ce kofar dazata sadaka da babban falon gidan, ajiye cup din tayi ta taso a hnkli, sanye take da rigar bacci Light golden me mugun laushi ta samanta duk lace ne dark golden, se tamfarin wasu flowers suma dark golden ne, rigar ta amsheta ainun knta babu dankwali sumar nan taya ta kwanto ta barbazu a gadon bayanta, yayinda nakn goshinta suka kwanta lufluf, ta kara kyau kmr a tabata jini ya fito, kafafuwanta sanye suke da slifas light golden color irin na yan hutawar nan, ta iso ga bakin kofar datakeji anata knocking, kadan kadan, tsayawa tayi cik, jin kamshin turarensa dake tinkaro ta yayinda bugun zuciarta ke yawaita,,,a hnkli takai hannunta ta bude kofar hadi, da murd'a handle din ta budeshi sam be ankare ba, itama bata ankare ba, kasancewar yana kwance ne a jikin kofar dan hk tana bude kofar ya fado jikinta