Showing 54001 words to 57000 words out of 306755 words

Chapter 19 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

beda ra'ayin amsa masa ne kuma beda ra'ayin shan coffee din, se faman lumsar idanuwa yake tayi a cikin bargon ya juya ya koma ya kwanta rubda ciki, yana kara lumshe kwayar idonshi yana budewa a hnkli a hnkli duk sun kara masa nauyi sbda be rintsaba tin jia har zuwa yau, rabonshi da bacci tin shekaran jiya da daddare shima ba wani baccin kirki yayiba sbda ibadar dare da yakeyi. A haka dr kabeer yazo ya sameshi da kayan aikinsa, shi knshi dr kabeer din ya girgiza da ganin yadda zazzabin yy ma AB'ILAL mugun kamu, seda ya tambaya wai kwananshi nawa a wannan yanayin, Alhasan ya shaida masa daga jiya ne zuwa yau kawai. Dr kabeer da idanuwansa ke manne da glass yace "what! Jiya zuwa yau shine yayi laga laga haka?" Ya karashe mgnr da mamaki a ransa, Alhasan ya daga masa kai alamar tabbatarwa. Dr kabeer ya jinjina kai kawai shi da kanshi ya tausayawa AB'ILAL sbda yana jin jiki, "yaci abinci?" Dr kabeer ya tambayi Alhasan, jinjina masa kai Alhasan yy alamar ah'a ya nuna masa inda ya ajiye plt din dake dauke da cup me Coffee din daya hada masa yace "Ga coffee ma na hada masa be sha ba...'' dr kabeer yace "Okay ba damuwa..." Daga hk ya fara kokarin duba ab'ilal ba wani bata lokaci ya duba BP dinsa yaga yy kasa kuma damuwa ce tasa hkn, cikin hnzari ya bashi taimakon gaggawa yasa masa drib byn ya debi jininsa domin yaje ya masa gwaje gwaje, domin kuwa already yazo da komi nasa na bukatuwa, cikin drib din ya narka masa allurorin bacci domin alhasan ya sanar dashi beyi bacci ba jiya. Wasu magunnguna dr kabeer ya rubutawa Alhasan ya bashi yace ya nemo ynxu a ciki a bawa AB'ILAL guda daya in yayi bacci ya tashi. Alhasan yace to jiki na rawa suka fice daga dakin shida dr kabeer din , suka fito compound tare kowa ya hau motarsa suka fice a gidan bayan dr yace ze dawo bada jimawa ba. Direct Alhasan pharmacy ya nufa domin siyan magungunan, driving yakeyi amma tunanin AB'ILAL da halin daya barshi yana ranshi.A gaggauce ya isa dialogue pharmacy a nan ya siya magungunan ya juya ya koma gidansa. Yana yin packing ya fito cikin sassarfa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo, ya karasa cikin Gidan nasa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo. Koda ya shigo dakin yana tunanin zega AB'ILAL na bacci, nan fa ya ganshi idonshi tar a bude ya zubowa kofar dakin ido, ba karamin mamaki abin ya bashi ba, sbda an masa alluran bacci, shi ga tunaninsa tini ma yayi nisa a baccin, karasowa yayi bakin bed din ya tsaya tsaye ya zubo masa ido, yana fadin "kayi bacci ne ka tashi frnd? Ko bakayi baccin bane?'' Yayi masa tambayar fuskarshi dauke da mamaki, shuru AB'ILAL yayi ba tare daya ce masa komi ba, alhasan ya zuba masa ido yanada tabbacin be rintsaba sbda ga idanuwansa nan jajur kmr garwashin wuta, a bangaren AB'ILAL kuwa gaza baccin yayi, kwata kwata dukda ga baccin yanaji a idanuwansa amma ya gaza yinsa saboda tunaninta, ya gaza ficewa a kahon zuciyarsa. Rabawa Alhasan yayi ya zauna gefen bed din ta wurin kanshi, har ynzu cike yake da mamaki, ya ajiye ledar hannunsa a side drower ya cire wayarsa a aljihu ya danna wa dr kabeer kira, bugu daya ya daga, nan alhasan ya Roqeshi kan ya dawo da wuri, dr kabeer yace insha Allah nan da 30mnt ze dawo, alhasan yace okay daga hkn sukayi sallahma. Alhasan ya dawo da kwayar idonsa kan AB'ILAL byn ya gama wayar. Ya fara tunanin wani abu ne ke damun AB'ILAL abun ma gagarumi domin kuwa ruwa baya tsami banza, nan da nan Alhasan shima ya kara shiga dmwa. "Frnd Dan Allah meke damunka plx?'' Alhasan yy tambyar muryarsa cike da zaquwar yaji meke damun abokinsa. AB'ILAL ya lumshe idanuwansa kawai ya budesu ba tare daya ce komiba, kwata kwata ko mgna baya so a masa, saboda knshi kamar ze fashe yake jinsa, juyar da fuskarshi yy gefe guda, ji ykeyi kmr ana buga masa kacau kacau a tsakiyar Kansa, har wani dil-dil gefen da kwakwalwarsa take yakeyi masa, dafe kn nashi yayi zucia cike da damuwa, ya rintse idanuwansa. Sannu Alhasan ya bishi dashi domin kuwa ko ba a gaya masa ba yasan yana mugun jin jiki. Maganin da dr yace a bashi Alhasan ya dauko ya shiga kokarin bashi, amma fir Ab'ilal yaki amsa, karshe ma yace baze shaba, alhasan yy juyin duniya amma yakisha, gashi yaki cin komi, se abin ya kara damun Alhasan ya shiga dmwa Ainun, yace "Bari kawai in kira Alhaji babba in gaya masa bka da lafiya, ni ciwon nan naka tsoro yake bani, an baka mgni kaki sha again kaki cin abnci, an maka allurar bacci kakiyin baccin, ko tantama babu wani abu ke damunka a ranka, kwara in kira Auwal hubb, ko Alhaji babba in gaya musu kawai..." Yy mgnr cikin dmwa, idanuwansa na kan AB'ILAL , wanda yy shiru yana sauraronsa, harya dauka ya dire, cikin muryarsa ta marasa lafiar dake jin jiki ya fara mgna "Plx karka kirasu frnd.. , na fara jin sauki..." A hasale Alhasan ya amshe da "Sauki? a ina ? Kaki cin abinci, kakishan ruwa, kaki shan mgni, ta ina zaka samu sauki? Zakace kar in gaya musu? Ah'a kwara in gaya musu gaskia karkazo ka mutum min a gida, ka barni da gwaramar katsinawa da larabawa..." Ya karashe mgnr yana latsa karamar wayarsa dake hannunsa. AB'ILAL ya juyo da fuskarshi garesa ya zuba masa ido, cikin dakiya yace "plx wazaka kira?" Alhasan ya bashi amsa a takaice. "Alhaji babba..." Ab'ilal ya girgiza masa kai cikin karfin hali, yace " karka kirashi pls,..." Alhasan yace "why?" AB'ILAL ya cije lefe kansa na kara masa nauyi, kasa kasa ya fara mgna. "Karka kirashi plx ynzu inka kirashi, hnklinshi ze dawo nan ne, Kaga kuma gobe zeje kano, a kn maganar dawowar Auwal hubb nan garin..." Ya karashe mgnr da kyar, seda alhasan ya matso da Kunnenshi kusa dashi kana ya iya jin me yake ce masa. Jim alhasan yy kana yace "to shikenan, ynzu me kkeso kaci kasha mgni plx, kasan de banason ganinka a wannan yanayin wlhy? Ciwonka kafiya ba wanda ya isa ya saka kayi, a haka zaka samu sauki plx?" AB'ILAL yayi shiru hadi da maida fuskarshi gefe guda kawai, se ganin surar hilwah yakeyi a jikin bangon. "Na tsaneki..'' AB'ILAL ya fadi a bayyane cikin fitar hayyaci,sam be ankare da cewar mgnr da yayi ta fito fili ba, Alhasan dake saurarensa ya zubo masa ido Fuskarshi ta cika da mamaki, hadi da dumbin tambayoyi a zuciarsa , tunani yakeyi shin menene AB'ILAL ya tsana?" Wato kmr de yadda tunaninsa ya basa akwai wata a kasa. "Wacece ka tsana frnd?'' Alhasan Ya jefowa AB'ILAL tambaya. Ajiyar zucia AB'ILAL ya sauke me mugun ddh, yaja gwauron numfashi, yayi jim jim, ya sauke ajiyar zucia ya lumshe idanuwansa. Alhasan ya kara jefo masa tambayar daya masa a baya,cewa wacece ya tsana, shiru AB'ILAL ya masa danshi a zahirin gaskia besanma mgnr tasa ta fito ba. Alhasan yaja bakinshi yayi shiru kawai, yana nazarin rayuwar AB'ILAL daga jiya zuwa yau, kunna krtun alqur'ani yayi, shi har ynzu tunani yakeyi iskokaine. Da kyar ya samu ya lallaba AB'ILAL ya dansha tea kadan shima seda yace ze gayawa Alhaji babba, sannan ya samu yasha dan kadan, wanda ko yaron goye baze isheshi ba, alhasan ya bashi mgnin da dr yace a bashi ya koma ya kwanta ynajin jikinsa kmr ba nasa ba. Alhasan ya jona burner din turaren wuta domin yasan mutumin da mugun son kamshi kmr jinnu, lumshe ido AB'ILAL yayi ba karamin jin ddn kamshin yayi ba, hadda hkn yasa yake Nacewa gidan auwal hubb, a ko da yaushe kamshi yakeyi kmr gidan shuwa arab, koda yake shuwa su biyu bayan indians da larabawa a son kamshi da bakatsinen mutum. Kimtsa dakin Alhasan ya shigayi saboda mutumin uban yan son tsafta ne, karya ne kaga ko tsinke a bedroom dinsa ko bathroom dinsa, shi din yafi mace tsafta da kwaskwas...yana gama kimtsa dakin ya karaso inda gwaskan yaje, yayi masa tayin wanka ko ze karajin dadin jikinsa, banza AB'ILAL ya masa a zucia alhasan yace "uban yan izzah..." Yana gama fadar hkn ya fada bathroom yayi wanka, ya fito ya shirya cikin kananan kaya irin na yan hutu, sun amshi jikinsa Ainun. A hk dr kabeer ya shigo dakin hannunshi riqe da wata kyakyawar jaka me dauke da kyn aiyukansa, tinda ya shigo dakin idonshi ke kan AB'ILAL wanda idonsa ke bude, shima ya zuba masa ido kallo daya biyu ya dauke kwayar idonsa a kn dr kabeer din , karasowa yy cikin dakin bakinsa dauke da sallahma a karo na biyu, Alhasan ya amsa. "abokina har yayi baccin ya tashi ne?" Dr kabeer ya tambaya dai-dai yana karasowa bakin bed din da AB'ILAL ke kwance. Alhasan dake tsaye gaban dressing mirror ya gama fesa perfume kenan, ya karaso bakin bed din yana fadin "wlhy dr ko rintsawa beyi ba, yadda ka barshi hkn yake, shiyasa ma na kiraka Ai..." Dr kabeer ya zaro ido fuska dauke da mamaki yace "kana nufin beyi bacci ba? Dukda alluran dana masa?" Dr kabeer ya jefowa Alhasan tambayar, alhasan ya daga masa kai alamar tabbatarwa yace "Gashi nan wlhy ko rintsawa beyi ba..." Dr kabeer ya kara cika da mamaki ya ajiye jakar dake hannunsa a kasan dakin kana ya kara tambaya "ko kadan beyi bacci ba?" Ya karashe mgnr yana me kure AB'ILAL da kallo. Alhasan yace "Wallahi dr be rintsaba, ni kaina nayi mamaki ..." Dr kabeer yace "nima nayi mamaki, duk allurorin dana masa...."alhasan yace "Wallahi kuwa dr..." Dr kabeer yace "Yaci wani abu?" Alhasan yace "yasha tea kadan na bashi maganin dakace a bashi ..."dr yace "okay, bani maganin in gani..." Alhasan ya dauko magungunan ya nuna masa, ya dudduba kana ya karasa ya ajiye ledar mgnin a side drower din, ya karaso ya taba jikin AB'ILAL yana me tambayarsa ya jiki, uban yan izzar shiru ya masa, sam be tanka masa ba. Alhasan yace "Dr anyi masa gwaje gwajen jinin ne?'' Dr kabeer ya dago ya kalli Alhasan yace "Yeah anyi masa, result dinsa be numa komi ba,, BP dinsa dayayi low dinnan ne yasashi a wannan halin, kuma damuwa ce,..." Alhasan yayi shiru kawai yana kallon bakin dr, dr kabeer ya kara dudduba jikin AB'ILAL. zuwa lokacin drib din ya kare, dan hk ya cire masa. Ana cirewa ya miqe zumbur cikin dauria kmr ze fadi yakeji amma baka isa ka fahimci hkn ba sbda yanada matukar dauriya, alhasan ya karaso da niyar ya taimaka masa ya dakatar dashi, kawai ya fada bathroom. dr kabeer ya bishi da ido, kai dagani kasan izzar tasa bata banza bace domin kuwa nera ta zauna, gefe yaja ya zauna a gefen bed din, alhasan ya dawo ya zauna shima kawai yana murmushi, dr kabeer ya fara bashi shawara kan yadda zeyi ya temaki AB'ILAL wato yasan yadda zeyi dashi ya rage dmwar da yake ciki tin kafin azo level din da baze haifar masa da d'a me ido ba. Alhasan yace insha Allah kawai, amma a ranshi cewa yakeyi ai AB'ILAL halinshi se shi, ba wanda ya isa yasashi balle ya hanashi. Suna nan zaune suna tattaunawa a kan rashin lafiar AB'ILAL. Daga toilet AB'ILAL yayi kiran Alhasan, tashi yayi yaje bakin kofar toilet din, daga ciki AB'ILAL yace Alhasan ya bashi jallabiyarshi da boxes guda biyu a cikin kynsa. Alhasan yace okay ya juya ya dauki car key dinsa ya fice a dakin , compound din gidan ya fito, ya nufa motarshi daya fita da ita jiya, ya bude ya dauko kayayyakin AB'ILAL din dake motar, kana ya maida motar ya rufe ya dawo cikin gidan, koda ya dawo a falo ya samu dr kabeer ya zubawa tamfatsetsen tv ido, yasan dalilin barinsa dakin maybe danyaga AB'ILAL na wanka ne shiyasa ya bashi guri ya kimtsa, hakan ba karamin dadih ya masa ba. Alhasan ya idasa shiga bedroom din ya ajiye kayan hannunshi a Waldrop dinsa, ya dawo ya kakkabe Bed din, ya chanza bedsheet yasa wani me kyau, ya nufa toilet ya jefa bedsheet din daya cire a basket din ajiye masu datti. Alhasan yanada ma'aikata guda biyu dame girki dame masa share share duk maza ne, sunyi tafia ne, daman duk after 1year sukanje kauyukansu suyi kwanaki biyu uku hudu se su dawo to a wannan karonma sunyi tafiyar ne yana sa ran dawowarsu gobe. Jallabiya kalar ashe Alhasan ya fitowa da ab'ilal dashi, se boxes guda biyu kmr yadda ya umurceshi, se Dariar zuci alhasan yakeyi tinda AB'ILAL yace ya kawo masa boxes biyu yake dryr a zuciarsa, se a ynzu yake kara tabbatr da abnda ya fada gaskia ne, a cikin mgnrsa daya ne babu. "Abubuwa na cikin wanduna ana adanawa..." Alhasan ya fadi a ransa yau dabadan AB'ILAL beda lafia ba dayasha mgna a gun alhasan.. Karasawa bakin toilet din alhasan yayi ya sanar da AB'ILAL ya ajiye masa kyn a gefen bed, a karshe yace inka gama shiryawa muna falo.." Yana gama fadar hkn y juya ya bar dakin, duk AB'ILAL dake Bathroom din yana wanka, yana jiyosa amma be ce komi ba, a dazuma sbda dolene tasashi mgna a toilet...seda ya kwashe awa daya yana wankan kana ya fito kugunsa daure da bathrobe ya goggege jikinsa sam be bari ba ko alama na hango jarumar burarsa ba, se aikin kakkareta yakeyi, koda zesa boxes dinsa juya baya yayi ya saka abunsa, duka biyun ya dauki zumbuleliyar jallabiyarsa ya zumbula ba tare daya shafa cream ba, ya maida bathrobe din daya cire bathroom din. Ya dawo dakin yanajin wani irin ddh a jikinsa sbda wankan da yy, kashi ashirin na ciwon dake jikinsa ya ragu. Daman already yy alwalar sallarh azahar domin kuwa zuwa lokacin har an fara kiraye kirayen sallarh azahar din ne. A daddafe ya karasa ya dauki perfume din alhasan ya feshe jikinsa dashi seda ya sauke ajiyar zucia ya dauki counter din alhasan dake kan dressing, ya saka slifas duk abinda yakeyi jikinsa babu kwari ya fito falon. A falon AB'ILAL ya samu su Alhasan Da dr kabeer Zaune se hira sukeyi, suna ganinshi suka hau jero masa sannu, a wannan karon sunci saarh ya amsa cikin izza kai kace ma beso ne ya amsa, Ya juya ya fice a falon kawai ya nufa masallaci. Dr kabeer ya kalli alhasan yace "Ina zeje?'" Alhasan daya ankare da counter din dake hannun AB'ILAL yace "nasan be wuce masallaci zeje..." Dr kabeer ya jinjina kai yace "inbanda abnsa ai da a gida yayi sallarh sa, tinda beda lafia..." Alhasan yayi nurmushi yace "tab ai bana tunanin akwai ciwon daze hana AB'ILAL zuwa masallaci yabi sallah a jam'i.." Dr kabeer yayi murmushi hadi da mikewa yana fadin "Allah , cemin zakayi malam ne..." Alhasan yayi yar daria shima hadi da mikewa yace "Aah ustaz ne,," dr yayi murmushi, yace "muyi alwala muma muje masallacin..." Alhasan yace "gashima an kusa tada sallarh..." Yayi mgnr yana nufar badroom dinsa domin yin alwala. Dr kabeer ya shige toilet din falon. Ba jimawa duk suka fito suka nufa masallacin dai-dai ana qoqarin tayar da sallah azahar din...bayan sun idar da sallar a tare suka shigo gidan, AB'ILAL se laziminsa yakeyi, yanaji kansa na masa nauyi har zuwa wannan lokacin. Dr kabeer yace ze saka masa wani drib din, nanfa ya daka tsalle yace shi baza a saka masa ba, ya gaji a barshi ya samu sauki Ma kawai. dr kabeer yace "ina wani sauki, bakayi bacci ba.." A hasale Alhasan yace "bari in kira Alhaji babba, ni bazan iya ba gaskia, inyazo seya daukeka ya kaika asibiti ma kurum.." AB'ILAL dake kwance Kan bed din ya zubawa Alhasan ido, wadanda ke tsaye shida dr kabeer. ab'il ya gallarawa alhasan wata iriyar harara. alhasan ya masa gwalo, kana ya duba dr yace "dr sa masa drib Din plx..." Dr kabeer yace okay, da fargaba ya kai hannu, yana me tunanin ko AB'ILAL ze kara gaddana se kuma yaga ya tsayar da hannunshi, seda aka sake neman sabuwar jijiya sbda na dazu dayaje wanka ya tumbuke shegiya ya wurgar. Nan take dr ya mayar masa da drib din yasa msa wasu allurorin dayazo dasu nasa bacci masu karfi, da wata allura dazata zamar masa mazaunin abincin dabe ciba. Komawa yy ya kwanta byn drib din ya fara shigarsa, har ynzu tunaninta be bar ranshi ba..dr kabeer ya bawa alhasan wasu magungunan dayazo dasu, yace masa in drib din ya kusa karewa ya kirashi, yade zamana yana kusa dashi Alhasan yace okay. Dr kabeer ya masa sallahma ya fice gidan Alhasan se jero masa godia yakeyi. Shima ya fice a dakin ya nufa kiching ya hadowa knsa indomie sa dafaffen kwai, ya dawo dakin yayima ab'ilal tayi, ko kallo ma be isheshi ba, Murmushi yayi ya zauna yaci ya koshi ya kora da drink me sanyi, Ya kwashi plt din daya gama cin indomie din ya nufa kiching AB'ILAL ya bi bayansa da ido, da tunani tunani a ransa, duk na wannan kyajyawar yarinyar ne. Ba jimawa alhasan ya dawo dakin, zuwa lokacin AB'ILAL ya fara lumshe ido sbda allurorin da aka masa a wannan karon manya manyan ne, alhasan ya dawo ya zauna gefen bed din, ya zuba masa ido, a hnkli bacci me nauyi yayi surar iska dashi. Alhasan ya zubawa kyakyawar fuskarsa ido a zuciarsa yace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login