Showing 63001 words to 66000 words out of 306755 words

Chapter 22 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

takeyi da ido ita nan a make take ta bugu iya buguwa danma shegen kai gareta, amal kam se satar kallon nonuwanta takeyi wadanda keta miqo mata zagi, ji takeyi kmr ta danneta ta mammatsa su taji sanyi ga ranta. Kankana ya fara shigewa dakin, kana hilwah da Amal suka mara masa baya.

Alhasan ya kira Alhaji samah, shine shugaba a asibitin da Amihh ke Aiki, ya mika masa bukatunsa na son yama Hajiya maryam trnsper ta dawo kd da aiki, alhaji samah yaso ya tubure sbda basu son rasa maryam a asibitin nasu, Amma alhasan ya cika shi da magiya beda yadda zeyi yace ba damuwa domin kuwa yana ganin mutumcin alhasan sosai shima yana darajasa ainun. A ranar Alhaji sama ya rubutowa hajiya maryam trnsper daga asibitin kd zuwa asibitin nosing home dake kaduna. Hajiya maryamna zaune a office dinta da system dinta a gabanta tana wasu yan tabe tabe, shugaban asibitin ya aiko kiranta, mikewa tayi ta je dan amsa kira. Ta nufa office dinsa, ta nemi izinin shigowa akayi mata ta shigo ta gaidasa ya amsa zucia cike da jin ddh, ba karamin kaunarta yakeyi ba, suna jin dadin aikinta sosai tanada karatu me zurfi wanda babu algush, sam beso yi mata trnsper ba dande beda yadda zeyi ne. Kujerar dake facing dinsa ya nuna mata ta zauna ya miko mata wata yar takadda tasa hannu ta amsa cikin ladabi , ta bude ta karantata ba bata lokaci, bayan ta gama karantar takaddar ta dago kwayar idonta ta zubawa alhaji samah ido, tana me neman karin bayani. Cikin harshen turanci ta fara magana ''sir naga knr trnsper ne ko? Zuwa kd? Kmr hkn ne" Alhaji samah shima ya mayar mata da harshen nasarah "Yeah trnsper ne kika samu zuwa kd tare da babban matsayin dayafi wannan da kk a wannan asibitin..." Hajiya maryam tayi jim kwayar idonta na kan Alhaji samah taci gaba da mgna da harshen turanci ''Sir babu ta yadda za a hanya wannan trnsper din plx...sbda bana da bukata...kuma ma Ai na kusa ajiye Aiki...." Alhaji samah ya amshe da "dukda hk dr...Ai su sunada bukatarki dr, aikin ceton rai kkeyi, Allah kadai yasan irin ladar dake takaddarki a lahira, kiyi hkri plx..." Ya karashe mgnr yana dawo da hnklinsa kn system din dake gabansa hajiya maryam ta masa godia badan rai yasoba ta fice a office din da takaddar trnsper din ga hannunta, direct office dinta ta nufa zucia babu dadih ta suri bag dinta da car key dinta ta fice a office din, farfajiyar kayataccen asibitin ta fito, ta shiga motarta ta fice zucia babu dadih, ta fara tunanin anya ba Alhaji Murtala bane yasa aka mata trnsper dinnan zuwa kd sbda taki amincewa da hkn, shine ya biyo mata ta bayan gida. "Amma ko dabe kyautaminba..." Ta fadi a bayyane yayin da take komarin Karya kan motarta zuwa gidan juwairiyya. Da takaddar a hannunta ta shigo falon Hajiya Juwairriyya zucia babu dadih. Hajiya dake zaune kan kujerar 2ct ta dago kwayar idonta ta zubawa hajiya maryam kallo daya ta mata ta gane bata cikin walwala. Ba tare da hajiya maryam tace komi ba ta ajiyewa hajiya Juwairriyya takaddar dake hannunta a kn jikinta ta nemi kujerar dake facing Juwairriyya ta zauna. Hajiya Juwairriyya ta shiga aikin warwarar takaddar ta budeta tas kana ta karantata trnsper tagani daga kano to kaduna. Ita knta tayi mamaki duk yadda asibitin kno ke ji ita amma suka turata kd lallai akwai laushe cikin nadi. "Trnsper nagani Hajiya?" Cewar hajiya Juwairriyya tyi mgnr fuskarta dauke da neman karin bayani. Hajiya maryam ta d'aga mata kai kana tace "yadda kk ganta haka nima na gnta kwatsam, yadda kksan saukar araduh ..." Hajiya Juwairriyya ta sauke ajiyar zucia hadi da rafka uban tagumi hannu biyu biyu kana tace ''to ynzu yaza ayi ne?'' Maryam ta watsa hannu hadi da cewa ''bnsani ba hajiya...amma ni ina tunanin na hakura da Aikinnan kawai danni gaskia bnda ra'ayin komawa kd..." Hajiya Juwairriyya dake cike da mamaki har lokacin tace "ikon Allah kenan, Hajiya daza kibi ta tawa dakin koma kd kawai , bata yuwwa fa ki ajiye aikinki nan asibitinki ai akwai doctors kwararru, meze hana kawai ki koma kd plx maybe Alheri ne ke kira ...." Hajiya maryam tayi kasak'e tana sauraron hajiya Juwairriyya tace "Alheri ta ina hajia? Nifa na fara tunanin alhaji babba ne yasa akamin trnsper dinnan...." Hajiya Juwairriyya tace "in kuma bashi bane knga kin dauki alhakinsa ,,kawai ki barwa Allah lamarin Allah ya zaba mna abnda yafi alheri in alherine Allah ya tabbatar mana...."hajiya maryam ta amsa da Ameen kawai, sam batajin zuciarta ta aminta da tafiyarta kd. Nan hajiya Juwairriyya tayita bata shawarwari tace taje taci gaba da adduarh itama zata tayata in alherine komawarta kd ALLAH ya tabbatar, inde zatayi ta adduarh to insha ALLAH zataji hnklinta ya kwanta. Sosai hajiya maryam kejin ddn shawarwarin hajiya Juwairriyya sbda tanada zurfin ilmin addini sam bata bata gurbatacciyar shawara suna tare da junansu ne da zucia daya. Da addu'ur'i a ranta ta bar gidan ta nufa gidanta , rnr kwana tayi kiyamun laili tana rokon Allah zabi na gari. A washe garin rnr data tashi taji zuciarta ta kwanta mata da zuwanta kd haka kawaima taji kaf hnklinta ya koma garin kaduna, kai kace asiri aka mata. 2:pm byn ta idar da sallar azahar ta lalubo wayarta ta kira Alhaji murtala ta sanar dashi zuwa next week zata dawo kd sbda an mata trnsper daga gun Aiki, ba karamin ddh Alhaji babba yaji ba, yace za a nema mata gidan zama, ta masa godiya Sosai kana ta katse wayar, ta kira Juwairriyya ta sanar da kta zata fara shirye shiryen komawa kd, Hajiya Juwairriyya tayi mamakin saukowar tata a lokaci kankani, lallai babu abnda yafi karfin Allah fatan alheri Juwairriyya ta mata dukda kuwa zuciarta na cike da kewar aminiyarta abokiyar shawararta ta tabbatr wata kewarma se in ta bar garin.

Alhaji murtala ya kira AB'ILAL ya sanar dashi hajiya maryam tace zata dawo kd ta hanyar trnsper da akayi mata, nan sukayi mgnr gida AB'ILAL yace ai gida ba damuwa bane sunada gida,...daga hk sukayi sallahma AB'ILAL se murmushi yakeyi karkaso ka bincika kasan zuciarsa data ke fara sol. Ba bata lokaci ya shaidawa alhasan, shima nan ya hau murna da farin ciki, a ranar suka fita sukaje gidan da Amihh zata zauna wanda ke malali GRA gidane dankarere na gani na fa ko gidan shugaban kasa se haka...ranar aka nemo ma'aikatan dazasu karasa aiyukan gidan dmn ba wani aiki bane na azo a gani AB'ILAL da Alhasan suka sakarwa ma'aikatan kudi iya kudi, aiko jiki na rawa suka hau aiki ba kama hannun yaro.... A satin aka hada komi na buqatuwa a gidan aka kira ma'aikatan sanat Turkish suka tsara komi yadda ya dace kama daga side din hajiya maryam da side din AB'ILAL se bangarori guda uku na saukar baki duk aka tsarasu tsaf an zuba dukiya iya dukiya saboda arzikin akwaishi bawai karyarshi akeyiba kudinne akwaisu Alhamdulillahi. Komi da ake bukata an zuba a kicking na bukatuwa stores din gidan duk aka cikesu da abinci iri iri kama daga abincin larabawa dana Indians dana hausawa dana turawa dade sauransu. Gida fa ya hadu iya haduwa tsarin yayi iya tsaruwa domin kuwa yafi gidan hajiya maryam na kano nesa ba kusa ba. A kano kam hajiya maryam se shirye shirye takeyi na dawowarta kd, sosai salwah taji ddh data samu lmrin Amihh zata dawo kd. Yan uwa dake nan kd ma suna cike da murnar dawowarta kd musammanma hajiya karama wato autar su ALHAJI MURTALA wadda salwah ke zaune gunta.... Motoci suka kwashi abubuwan da hajiya maryam zasu bukata wasu na amfaninsu da ma'aikatansu na nan suka fara yin gaba byn sun isa Nan suma suka kara kimtsa komi kowa se santin gidan sukeyi, Hajiya maryam kam taga picture din gidan a waya Alhaji Murtala ne ya turo mata ta WhatsApp ita knta ta yaba da kyaun gidan, sannan ya mata masha Allahu. Washe gari ita da hajiya Juwairriyya da Salwah suka biyo jirgi zuwa garin kaduna sukayima kano bye bye, da sunan duk weekend hajiya maryam zata rinka zuwa kano, sam hajiya maryam bataji dmwa ba kmr yadda tayi tsammani jin zuciarta takeyi wasai sema dumbin farin ciki dake dawainiya da ranta.... Lafia lau suka sauka a jirgin Alhaji murtala da iyalinsa wato bebynsa zee sukazo tarbarsu da motoci na alfarma, AB'ILAL kam be yadda ma yazo ba sbda tsaro. Suka shiga motoci suka nufa malali GRA kowannensu zucia zallar farin ciki , dasuka isa gidan nan suka tadda su hajiya karama da gudu salwah taje ta rungumeta zucia cike da farin ciki hadi da kewarta... Nan fa aka hau farin ciki aka gaggaisa, kana daga bisani suka huta sukaci abincin da hajiya karama ta shirya musu sukaci suka koshi suka gabatar da sallarh azahar da la'asar kana suka shiga aikin zagaye gidan kowa seda yayi santin gidan hadda alhaji babba dske kara ganin gidan ynzu, domin tin kafin a zuba furnitures AB'ILAL ya kawosa ya gani, Hajiya Juwairriyya kam se fadi takeyi gida yayi masha Allah an narka dukiya! Murmushi kawai maryam keyi hk kawai takejin knta a nishadi, se godia takewa alhaji murtala a tunaninta Aikin nasa ne. Matan alhaji murtala duk sunzo da yayanshi nan duk suka wuni se dare suka koma gidajensu wasu kuma nan suka kwana ciki hadda zee da hajiya salamatu mace ta uku ga Alhaji babba, Hajiya karama ma nan Ta kwana. rnr kwana akayi ana hirar zumunci.... Washe gari aka watse gida ya rage daga hajiya Maryam se Juwairriyya se ma'aikatan gidan salwah kam tini tabi hajiya karama zuwa gidanta dmn dukta kagu jinta takeyi kamar a qaya take. Rnr ne aka tara malamai aka kara saukar alqur'ani a gidan, hajiya maryam tasaka aka nemosu , domin batasan cewa AB'ILAL yasa anyi saukr alqur'ani ba a gidan. Tare da hajiya maryam da hajiya Juwairriyya akayi saukar, bayan an gama ta musu sha tara ta arziki suka bar gidan zucia fal jin ddh..... Washe garin ranar Ab'ilal da alhasan sukazo gidan, a falo suka samesu zazzaune suna hutawa ac na ratsasu hajiya maryam kallo daya tama AB'ILAL taga tsantsar ramar da yayi dan haka bata bi ta knsaba Amma so tayi ta koresa. Sugunnawa sukayi a kasa suka gaidasu Hajiya Juwairriyya ce ta iya amsawa hadi da tambayarsu lafiarsu suka amsa da lafia lau..hajiya maryam kam shiru tayi, AB'ILAL ya matso daf da kafafuwanta yayin datake gishin gide a kn kujerar 2ct ita kuma Juwairriyya tana kn 3ct kowacccensu da kyn marmari a gabanta. Ido AB'ILAL ya zubawa mahaifiyar tasa wadda ta hade girar sama da kasa babu alamar annuri a kan fuskarta. "Hajiya Amiih , barka da hutawa?''cewar AB'ILAL hajiya maryam ta masa bnza, nan ya shiga aikin mammatsa mata kafafuwa hajiya Juwairriyya da Alhasan suka zubo musu ido ba karamin burge juwairiyya AB'ILAL keyi ba. Ganin ta masa bnza yasashi ci gaba da mgna. "Allah de yasa kin dawo kd a sa'arh Amiih ki rabu da yaran kawaye...." Karashen mgnr tasa se taso bawa Juwairriyya drya alhasan kam seda ya murmusa hajiya Juwairriyya kuma hadiye dariyarta tayi. Hajiya maryam kam kin tanka masa tayi amma ina be daddaraba yaci gaba da mgna yana mata tausa har zuwa hannayenta "Amihh To wai ya mgnr mgnin karfin mazan nan dazaki nemo min, kafin de kimin Auren daza kiyimin , kinsan kwanaki na gaya miki nifa ba Aurene bnsoba lafia ce bndashi..." Duk ilahirin halittar dake falon seda kunya ta rufesu musammanma hajiya maryam ji tayi kmr kasa ta bude ta shige don tsabar kunya, ta saki baki kawai. AB'ILAL be daddaraba ya bude baki da niyar ze kara mgna A hasale Amiih ta tashi zaune ta taso masa da tsiya "Inka kuma mgna a falon nan kaf shanayen dangin ubanka se na hadasu nashi k'asusuwan bura ubasu kaji na gaya maka....tinda kai baka data ido..mara tarbia kawai..." Shiru AB'ILAL yayi hadi da kame baki kamar karamin yaro. Hajiya Juwairriyya da Alhasan suka zubo musu ido ba karamin burge juwairiyya AB'ILAL keyi ba rashin jinsa na burgeta tin yana yaro taso da tanada diya mace ta hadasu da duk iskncin nan nasa zata jure. "Auwal hubb de an dawo kd to Allah yasa alheri nan de ba ruwanki da kwashe kwashen yaran kawaye ki mannamin..." Be daddaraba seda yaci gaba da magaba. Takaici ya kara rufe zuciar Hajiya maryam ji tayi kmr ta dokesa shi de ya rantse da ALLAH ko zagin ne seta kutuntuma masa ko zeji ddh. "Tashi ka fitarmin a falo dan sitirar dangin ubanka , tashi ka fice min a falona kaji na gaya maka.... In har bazaka natsu ba karka kara shigomin gidana kaji na gaya maka...wannan bakin naka mara tsarki ka saisaitasa kanajina kou?" Qur AB'ILAL ya kureta da ido yadda kikasan badashi take mgna ba a hasale Amihh ta zaburo zata kai masa hannu tana fadin "tashi nace ka fitarmin a falo..." Da hnzari ya tashi ya fice a falon still bakinsa be mutu ba. "To nifa yunwa nkeji Hubb, banci abnciba 2days..." Ya fadi hkn dai-dai yaka bakin kofar fita daga falon. Hajiya Maryam tace "ka mutu dan ubanka!" A hasale tayi mgnr murmushi AB'ILAL yayi yace ''bazan mutu ba sena cika miki burinki nason inyi Aure hadda jikoki zan haifa miki, masu kama da ke Amihh..." Takaici ya kara rufeta kawai tayi kasa da knta tana jinsa ya fice a falon , alhasan ya mike shima ya mara masa baya. Hajiya Juwairriyya ta kwashe da Dariyarta dataketa adanawa hadda riqe ciki tace "kai! Muhammad cases ne to ina mgnin da kika amso masan na lafiyar maza...." Juwairriyya tayi mgnr murya cike da zolaya. Fuska dauke da takaici hajiya maryam ta dago ta kalli Juwairriyya wadda keta faman daria tace "Wallahi Allah bamuyi hk da yaronnan ba, kawai tsabar sharri ne, ni Hajiya ke kin sani ta ina zance zan Amso masa mgnin maza..wlhy yaronnan ya rainani hajiya!'' Hajiya Juwairriyya ta kara tintsirewa da dariya tace "Ba raini bane hajiya maryam shi nature dinsa ne hk..." Takaici ya kara rufe hajiya maryam tace "wai se anyi mgna kice nature nature, kenan haka yake beda kunya...'' Juwairriyya dake dariya tace "ba haka nake nufi ba ni fa hajiya ..." Tabe baki hajiya maryam tayi tace "to ALLAH ya shirya...." Juwairriyya daketa dariya har zuwa lokacin ta amsa da Ameen.


AB'ILAL na fita direct side dinsa ya nufa , alhasan na biye dashi a baya har suka iso cikin kayataccen falon nasa Alhasan be bar Dariaba kasa kasa . falon ya hadu iya haduwa har ma ya gaji da haduwar komi a falon golden and milk ne . A falon suka yada zango a kan tamfatsa tamfatsa din kujerun dake falon Se sanyin AC dake a kunne koda yaushe ke ratsasu kai kace dakasa kafa a falon zaka taka kasan ruwah ne sbda tsabar sanyi. "Mamman na ta'alah Ya kamata muje a dauko motarka dake hotel dinnan fa...'' Cewar Alhasan dake zaune kn 1ct gogan kuma yana zaune kan 2ct yana sauraron me Alhasan ke cewa mikewa yayi tsaye hadi da cewa "tashi muje plx danni gobe zan bar garinnan ..." Alhasan ya tashi a tare suka fice a falon, suka hau motar Alhasan din, suka nufa gidan Alhasan din suka dauki car key din AB'ILAL dake hotel din kana suka hau hanyar zuwa hotel din. Nan fa suka tadda uban holdup ko motsi bayayi .... Duk suna cikinsa har akayi sallarh
magrib ma duk basu fita a holdup dinba wanda suka shigeshi tin 5:30pm takaici da bakim ciki ya cika zuciyoyonsu musammanma AB'ILAL se uban tsuki yakeja kai kace tsaka ya hadiya. Alhasan ya sauke motar tasu a kn titin ya shiga bi ta layi ta yadda zasu isa da wuri. "Da kasan da wannan layin shine ka barmu a wancan tsinannan holdup din..." Cewar AB'ILAL alhasan yayi bnza dashi yana me cigaba da duba area din sbda hnyar bata da kyau sosai wahalar tuki sbda ba kwalta, se kacau kacau yaketa cin karo dashi.


Dai-dai kankana ya fito da motar hilwah daga gidan DANDI zeje ya nemo mata fura da nono na shagon sadauz home me mugun dadih, shi tace tana sha'awa da snacks dinta shine zeje ya siyo mata fitowarshi daga gida kenan...Dai-dai Alhasan ya saki tasa motar ba tare daya ankare da fitowar wata mota ba kawai se ji yayi ya gogi gaban motar garaf! raf! Seda ya rintse ido sbda daji ba karamin barna yayima dayar motar ba, hayeta yasoma yayi,,, AB'ILAL kam seda ya taso zaune daga kwanciar da yake a firgice ya zaro ido ganin irin uban ta'adin da Alhasan yayima motar daya buga. Ba shiri Alhasan yayi packing kankana kam motar tasama tsayawa tayi taki tafiya ranshi yayi MUMMUNAR baci ga haske tako ina fau kai kace rana ce dukda kuwa duhu ya dan farayi tsabar hasken lantarki ne sbda suna da yalwar wuta a kd. "Tab! Wlhy kayi barna...wai! " Cewar AB'ILAL dake kara bude ido yana kallon yadda alhasan ya lalata gaban motar, Sbda ita ta danyi kasa su kuma wadda suke ciki babbar mota ce. Alhasan ya dafe goshi hadi da fadin "aiko ba makawa me motar nan se yaci kutmar ubana..." Alhasan ya karashe mgnr yana karewa motar kallo. Bude motar kankana yayi ya fito yana gyara zanin dake jikinsa se faman rarraba ido yakeyi kmr angon kare ya karaso gaban motar ya kalleta yaga uban daga dagan da tayi kawai ya samu wani uban ashar ya mulmula "Jar babbar bura uba kai! Durun uwa! Kan babbar bura uba kai! Gindin durun uwar nan!!!" Manya manyan zagin dasuka rinka fitowa daga bakin knkana kenan sbda ya firgice da ganin yadda gaban motar yayi daga daga,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login