Showing 135001 words to 138000 words out of 306755 words

Chapter 46 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

yana dansa bacci. Karasowa yayi cikin dakin ya maida kofar ya rufe yanajin zuciarsa na masa kuna da zafi sbda ganinta da yg kwance, karasowa yy bakin bed din datake kwance kmr gadon gidan ubanta, ko gadon gidan karuwai, ya fadi hkn a ranshi ganin yadda taketa bacci, takaici ya rufeshi wato bacci ma takeyi tsanarta ta kara yawaita a zuciarsa, ji yayi kmr ya rufeta da duka sbda kiyayya, gata de da fari da kyau amma shi ganin bakinta yakeyi, sam ko kyaun nata ma be gani ynzu, jiya zuwa yau ya kara tsanarta sbda kalaman Amihh garesa. Duvet din dake lullube a jikinta ya yayeshi ya jefoshi kasa, cikin kyama ya bita da ido, har lokacin bacci takeyi, batasanma anayi ba, sanye take da riga mara nauyi, red se hijjabin jikinta golden. Wata iriyar uwar wawiyar tsawa ya daka mata. "Keehhhh!!!!''' Ya fadi da karfin tsiya kmr ze fasa dakin, muryarsa cike sa karad'i. A matukar gigice ta farka, batasanma sadda ta diro kasan gadonba jikinta na rawa duk tabi ta firgice ta tsure jin tsawar tasa, har tsakiyar knta... Ido ya bita dashi zuciarsa babu alamar tausanta...dago kwayar idonta tayi ta zuba masa su, jikinta na rawa nan da nan ta fara hawaye ita daman akwai saurin kuka, zuciarta se up up takeyi kmr zata fashe, data diro daga bed din bata ankare dashi ba se ynzu . "Ubanwa ya baki danar yin bacci? Nan gidan ubanki ne, ko an gaya miki gidan karuwai ne, na ...." Ya fadi kwayar idonshi na knta cikin tsantsar tsagwaron tsanar yake mgnr, ko a kwayar ido ya isa ya tabbatar maka da AB'ILAL be kaunar hilwah.




*Akwai mutane masu min karamci ngde sosai, Hajiya Saadia na'aman (momyna) bazan iya miki godia ba ngde sosai Allah ya rabaki da bakin cikin dunia da lahira baki daya, Allah ya kara lafia. Ameen*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 31***
Kasa tayi da knta, yayinda hawaye masu zafi keta aikin zirya a kn kuncinta, zuciarta na kuna sbda kalmar karuwa daya jefeta dashi. ko karuwar asali bataso a kirata da wanannan kalmar balle ita da bata taba sanin hanyar karuwancinba. Wani irin kallo yake binta dashi me cike da tsana hadi da takaici, ji yakeyi kmr yayi ball da ita yadda take tsugunne a kn guiwowintannan, murya cike da tsanarta yaci gaba da mgna yana motsi da yatsunsa irin alamar warning dinnan. "Daga rana me kamar ta yau ya zamana na farko kuma karshe, karki kara koda zama ne a kn bed din dake gaf side dinnan! Bama bed ba, hatta da kushin din dake side dinnan karki kuskura ki zauna a kai, nan ba gidan karuwai bane, gida ne na masu tsarki, so banason marasa tsarki su rinka zamar min a kn abubuwana masu tsafta kin gane kou? Nan ba hotel bane!'' Ya karashe mgnr yana tunawa da farkon inda ya fara ganinta, hawayen dake zubowa daga kwayar idonta suka yawaita, bata taba tsammanin rashin mutumcinsa yakai har haka ba se yau, a kalamansa tasan babu alamar wasa. "Ina me kara tabbatar miki da cewa duk wani abu dake side dinnan ya haramta gareki har abadan! Kinjini kou?'' Ya karashe mgnr yana me jan kunnensa alamar gargadi. Kara kasa tayi da knta tana shashshekar kuka kmr zata hadiye zucia ta mutu. "Bakiga komi ba..." Ya fadi cikin muryarsa dake cike da tsanarta, sam ko alamar tausanta bejiba, dukda kukan datakeyi kmr ranta ze fita, sema haushinta daya karaji. "Daga yau ke zaki rinka kaf Aiyukan dake gidannan, zan dakatar da ma"aikatan side dinnan , kece zaki rinka komi kama daga kn gyaran sama zuwa gyaran nan kasan, da wankin kayayyakina, da gyara dakin baccina, ke komi ke zaki rinka yi, kuma bnson kazanta dannan ba gidan karuwai bane!" AB'ILAL ya fadi babu alamar jin kanta a muryarsa, sema dumbin haushinta da tsanarta. Ajiyar zucia ta sauke yayinda kalamansa ke shigarta tako ina, ta rintse idonta ta bude dan gani takeyi kmr mafarki takeyi ba gaske bane zata fada wannan mummunar rayuwar, wani irin zazzabi me zafi taji ya kara rufeta na tsantsar damuwa da tunani me zurfi. AB'ILAL ya daka mata tsawa "Ko bakiji bane!?" Tsawar tasa seda ra gigitata har hkn yajawo ta zabura, ita dako hayania bataso, Gashi yanzu har tsawa ake mata, me karfi wadda in yayita se hantar cikinta ta kad'a sbda gigita. "Badake nake mgna ba! Yar iska kawai karuwah!'' Ya karashe da murya cike da tsanarta da bazata misaltuba a fili. Saurin daga masa Kai tayi, zuciarta cike da daci da zafin karuwah da yake kiranta dashi, ko yar iska daya ce bata mata zafi ba kmr kalmar karuwa daya kirata dashi. Wata iriyar kwafa yaja kawai zucia babu dadih shi da knshi yasan tsanar da yayiwa yarinyar tayi yawa, ci gaba yy da mgna murya cike da matsifa "Ashe ba kurma bace! Nasha iskncin gidan karuwai ya kurmantan dake yar iska kawai!'' Ya karashe mgnr ko a jikinsa se binta yakeyi da kallon kyama, ya juya da niyar ze fice a dakin har ya kai bakin kofar fita ya juyo ya kalleta Cikin tsana ya nunota da yatsa. "Ammm..bari in kara jaddada miki karki sake ki kuskura kiyi amfani da koda cokali a side dinnan, in zaki kwanta ki kwanta a kasan tiles shima da sassafe in kikatashi ki gogemin tile's dina ni bnson kazanta, nan ba gidan yan iska da kazamai bane...bade knce kin Aminta da Aure naba wlhy kadan kk fara gani, se knyi nadamar rayuwarkima baki daya! Kuma daga yau zaki fara aiyukan dana lissafa miki! " Yana gama fadar hkn ya fice a dakin yana haki ya nufa bedroom dinsa.... nan kasan dakin ta zauna zaman dirshan kawai ta kara fashewa da matsanancin kuka me tsuma zuciar me sauraro, kalamansa kawai keta aikin yawo a brain dinta, tayi kuka tayi kuka, ta tuna uwarta mahaifiyya duk a yau, kuma tayi nadamar zuwanta ma gidan dan tasan zata tsinta abinda batayi tsammani ba, gashinanma ta fara tsinta tin yanzu, zamanta gidan dandi yafi mata nan gidan sau dubu. Har akayi sallarh La'asar aka idar tana nan kasan tiles din tanata aikin kukan babu kakkautawa,,da kyar ta bawa knta hkri da knta sbda bame bata ta mike da kyar yayin da takejin knta ya kara mata nauyi kawai ta fada toilet tana dafe bngo, tayi tsarki ta dauro alwala ta dawo dakin ta fara jero sallarh azahar da la'asar, tana sallarh tana tunani tunani, se ynzu takeji a ranta anya ba barin gidansu datayi bane ALLAH ke nuna mata ishara a yanzu , duk da bataga isharaba se ynzu ne take gani, kalaman mahaifinta keta dawowa kwakwalwar knta, tana wannan yanayin amihh ta turo kofar dakin ta shigo dawowarta kenan daga aiki ko side dinta bataje ba ta nufo side din AB'ILAL dan taga hilwah. "Oh my sweery i miss you..."_ itace kalmar data fito daga bakin Hajiya maryam ta karaso inda hilwah take zaune bisa dadduma ta zuba mata ido yayinda knta ke kasa, tin shigowar Amihh ta kalleta kallo daya ta dauke knta tayi hanzarin goge hawayen dake kn fuskarta. ganin Amihhn da hilwah tayi seya sama ma wani bangare na zuciarta kwanciar hnkli, hadi da sassaucin dmwarta. "Sannu da zuwa Amihh. " ita ce Kalmar data fito daga bakinta har lokacin knta na kasa, tayi controlling knta zuwa kmr bata cikin dmwa. Hajiya maryam ta zuba mata ido tana me naxarin muryarta, nan take ta fahimci tayi kuka sbda har muryarta ta dishe. "Yauwa sweery narh...plx dago min face dnki in gani kuka kikayi koh?'' Hilwah ta girgiza mata kai ba tare data dago kn nata ba, ta riga datama knta alqawarin insha ALLAH koda AB'ILAL ze kasheta ne bazata taba gayawa Amihh ba sbda karamcinta gareta kuma bataso tayi silar batawarta da danta. "Oya to dago min beauty face dnki in gani mana?'' Cewar Amihh. Hilwah ta dago knta a hnkli sbda batason jayayya da Amihh,. Hajiya maryam ta zubawa red face din tata ido. "Sweetheart kinyi kuka ne sosai ma kou?" Hilwah tayi saurin girgiza mata kai hadi dayin kasa da knta. Hajiya maryam tace "ban yadda ba, knyi kuka ne zaki girgiza min Kai, bansanki da karyaba ko wani abu wancan dan neman ya miki? Ki gayamin knji my love, karkimin hiding komi plx knsan ina sonki fiye da yadda nakeson yar ciki na kou?'' Hilwah ta daga mata kai domin kuwa ta aminta da amihh na sonta fiye da yadda takeson salwah, inma be fi ba to zexo diro diro, ballan tana ma tanada tabbacin yafi din kmr yadda ta fada din yau da bakinta. Amihh taci gaba da mgna fuska dauke da damuwa "To gayamin why are you Crying? Wayasa bbyn Amihh kuka?" Hilwah tayi shiru kawai tana me kara kasa da knta, hajiya maryam taci gaba da mgna " Ko de ba babyna bace ba?'' Hilwah tayi saurin grgiza mata kai, Amihh tace ''to yau ba bakin mgna ne?'' Hilwah tace "Akwai..." Cikin sanyin murya tayi mgnr amihh tayi murmushi harga wajen ubangiji tana kaunar yarinyarnan. "To tinda akwai baki gayamin meyasa bbyn Amihh kuka?'' Hilwah tace "ciwon Kaine..." Amihh tayi jim tana nazarin abinda hilwah tace da muryarta irin ta wadanda sukaci kuka suka koshi. "Ba ciwon Kai bane, kukan ne. kukan ne ma ya jawo ciwon kan...na cinka Kou?'' Amihh ta karashe mgnr tana zama nan kasa kasa kusa da hilwah ta jawota jikinta duk kunya ta rufeta na yadda Amihh ta gano cewa kukan datayi ne yasa mata ciwon kai. Rungumeta Amihh tayi jikinta, nan take taji jikinta yayi wani irin mugun zafi, daji zazzabi ne a jikinta, nan da nan Amihh ta gigice, "Kn gani kou zazzabi kkeyi kou? Kukannan da kkyi ne ya kawo miki zazzabi..kinci abinci?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Ehh, Amihh tace "tin yaushe?'' Hilwah tace "tin kafin salwah ta fita tazo ta hadamin tea and egg, ta bani mgnin zazzabin ai..." Amihh ta kara shafo jikinta tajishi zafi rau rau, murya cike da tausayawa tace "sorry my love, tashi ki hau bed in hado miki abinci kici in miki allura kou?'' Nan take jikin Hilwah ya hau kakkarwa jin Amihh ta ambaci allura, abinda tafi tsoro kenan ba a taba mata ba tin zuwanta dunia har rana me kmr ta yau. Amihh ta ankare da hkn tayi Murmushi tace "kina tsoron Allura ne?'' Hilwah tayi saurin daga mata kai, Amihh ta riqe baki tace "to wannan rnr haihuwa yazakiyi?'' Hilwah tayi shiru kawai tana me kara lafewa jikin Amihh, har lokacin zuciarta bata bar bugu ba dajin sunan allura. "Kwantar da hnklinki anma fasa allurar...tashi ki hau bed inje in hado miki abinda zakici kisha mgni kou?'' Jin amihh ta ambaci ta tashi ta hau bed yasata tunanowa da irin uban warning din da AB'ILAL ya mata, nan take taji a ranta ko zata mutu bazata kara hawa bed din ba, yau kawai ya dasa mata tsoronshi a ranta, amma fa har gobe bata bar tunaninsa ba.amihh ta tashi ta kamota da niyar tasata ta hau kn bed din hilwah taki tacema Amihh nan din yafi mata, tayi mgbr hadi da karasawa kn carpet ta kwanta. ba tare da Amihh tayi tunanin wani abu ba tace ok tana zuwa ta fice ta bar dakin, tana fita hilwah ta daure ta tashi ta dauro alwala a daddafe ta dawo ta hau dadduma ta fara jero sallar azahar da la'asar, tanajin knta na sarawa yayinda kalaman AB'ILAL keta mata yawo a kwakwalwar knta. Amihh Ta na fitowa falon sukayi kicibus dai-dai ya fito daga bedroom dinsa yana sanye da jallabiya peach color me mugun kyau, shima yana mugun son peach dande color din na mata ne. Ido ya zuba mata itama ta zuba masa nata kwayar idon. "Ina wuni Amihh.." Ya gaisheta cikin ladabi yana kokarin Karasowa inda take tsaye duk iskncinsa yana respecting dinta sbda yasan beda kowa a halin yanzu inba ita ba. Ba tare data amsa gaisuwar tasa ba ta kalleshi ta basar, se jikinsa ya basa ko de yarinyar ta sanar da Amihh irin abubuwan daya gaya mata ne, daya shiga bedroom dinta, dan hk seyasha jikin jikinsa, Ya karaso ya rissina mata, cikinb ladabi Ya kara gaisheta taki amsawa sema ta jefo masa tambaya"Meyasa yarinyar nan kuka?'' Ita ce kalmar data fito daga bakin Amihh, yayinda tadawo da kwayar idonta a knsa, kasa yy da knsa, dayake bashi da kunya yace "kmrya Amihh, ni meye nawa a kukanta, ko wani abun tace na mata?'' Amihh ta girgiza kai kana Tace "nasani abu a duhu..ai dayake nasan halinka, ba mutumci ne dakai ba, inma ka mata Ai ba fadi zatayi ba, tinda ita tanada tarbia alkunya , ba fadar mugun halinka zatayi ba gareta,.." AB'ILAL ya dago ya tabe baki jin Amihh ta ambaci tarbia wai hilwah ce me tarbia, gani yakeyi kmr Amihh batasanma me take fadaba. Ciki rashin kunya ya fara mgna "Gaskia ni Amihh, dande ba yadda zanyi ne, amma abinda kikeyimin ya isheni a kn yarinyarnan, wlhy bna kaunarta Amihh, daza kice in sawaqe mata daya fi min Alheri..." Amihh tayi murmushi irin Murmushin nan me taken yaro besan wuta ba seya taka, ta fara mgna cikin natsuwwa amma fa me mugun zafi. "You are free Muhammad, ka saketa in har kai ka haihu da ruwan katsinawa ka saketa, inajin kana ganin turirin wuta ne, Amma bakasan zafin ta ba, zanso ka gwada kai hannunka kaji yaya yanayin zafinta yake, a ranar zakayi nadamar zuwanka dunia, a lokacin nadamarka bnza take gareni, abinda zucia da ruhinka ke ingizaka ka aikatasu wlhy ni na maka alqawari ubangiji baya bacci se kayi nadamar abinda ka aikata a lokacin da nadamar ka bata da amfani... I wish ka kuskureni nima kuma zan kuskureka da mummunan abinda ke raina, garin kaduna zuwa katsina da kewayenta ta mna kadan ni da Kai Muhammad!'' Ta karashe mgnr tana nunasa da yatsa kawai ta juya ta fice a falon, isa yayi ga kujerar dake kusa dashi ya zauna, kalaman Amihh sun masa nauyi a kai gashi de cikin natsuwa tayisu amma sun shegeshi da gangar jikinsa, Wai a hk ma danya kula yarinyar bata gayawa Amihh irin abinda ya mata dazu ba, abin ya masa dadih, duk wannan abubuwan da Amihh ke masa a knta ze huce, ita ma se na lahira yafita jin dadin dunia, kadanma ta gani!" Ya fadi hkn a ransa yana me murmushin mugunta a bayyane se faman aikin girgiza kafa yakeyi... Yana nan zaune bisa kujerar yana dafe da knsa Amihh ta dawo falon hannunta riqe da trea tinda ya juyo ya kalleta ya dauke knsa, ita kam ko kallon inda yake batayi ba, yana gani ta nufa bedroom din hilwah da trea din a hannunsa wanda yakeda tabbacin abinci ne a ciki, zuciarsa ta cika da mamakin irin bautar da Amihh kewa yarinyar , ko su yayan cikinta bata musu hkn koda kuwa suma ciwo ne, nan AB'ILAL ya kara nitso cikin duniar tunani ko a nan kawai yanada tabbacin amihh na son yarinyar nan fiye da tunaninsa, kashh!!, se aka samu akasin shi be kaunarta fiye da tunanin me karatu.

A kn daddumar Amihh ta sameta data idar da sallarh seta koma ta kwanta, a hk Amihh tazo ta sameta. da knta ta tasota zuwa toilet ta kara mata brush suka dawo dakin ta jawota jikinta a hk tayi feeding dinta da superghetti Jlp wadda taji kayan lambu da kifi bushshe da namah, ta danci ba lefi, sbda Amihh ta matsa mata, a karshe ta bata magunguna na zazzabi dade wanda zesa taji dadih a jikinta. Hilwah ta mata godia yana daya daga cikin abubuwan dakesa Amihh karason hilwah komi aka mata seta nuna halin Katsina wa dukda ita ba bakatsiniar bace, wato karamci, bakatsinen mutum be manta alheri, kuma akwai raya alheri da alheri. Komawa hilwah tayi ta kwanta kan daddumar ta kudind'ine da hijjabin jikinta , Amihh tayi juyin dunia kn ta hau bed, hilwah taki hawa ta kara ce mata nan yafi mata ddh, nanko ta ciki na ciki bata da yadda zatayi ne kawai amma ita ason samunta ne ta koma kn bed din sam bata saba da kwancia a kasa ba, ballantana ma ynzu datakejin jikinta duk babu dadih kawai tana manage ne. Badan Amihh taso ba ta batta nan kasan sbda ta kula hkn takeso ta lullubeta da duvet din gadon data gnshi a kasa inda AB'ILAL ya wurgardashi, amihh ta mata sannu kana ta juya ta fice a dakin ta nufa side dinta da trea din a hannunta, dazata wuce falon ko kallon inda yake bata kara yiba tayi ficewarta. Amihh na ficewa ta cire duvet din data lulllube mata jikinta dashi ta jefashi can kasa kusa da bed din, zuciarta cike da tunanin warning din AB'ILAL gareta, sam bata mantaba, tasan har abadan bazata taba mantawa ba, domin ita akwaita da riqon Abubuwan Alheri dana sharri.

Amihh na ficewa a falon ya taso ya isa yayima falon key luck , ya koma ya zauba bisa kushin din daya tashi ya daura kafarsa daya kan daya yanata aikin karkadata kmr dan sarki, jefi jefi seya juya ya kalli kofar dakin yarinyar jira yakeyi yaga fitowarta dan Aiwatar da aiyukan daya bata, amma yaji shiru har kusan mintuna talatin suka shude, mikewa yayi rai a matukar bace, ya nufa bedroom din nata, ya turo kofa ya shigo yana haki, idanuwansa suka sauka a knta tana kwance kan daddumar duk tabi ta kara kudindine knta a cikin hijjabin dake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login