Showing 39001 words to 42000 words out of 306755 words
Chapter 14 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt
a ina? YAR DANDI CEH...kana ganinta kasan ta saba da maza kmr yayan dakin kakarsu, suke ita da maza..." Alhasan ya kara tintsirewa da dariya har kwallah na fitowa daga kwayar idonshi AB'ILAL yayi kwafa cikin tsiwa da matsifa yace ''kai! Tashi ka barmin daki tinda ba hauka nake ba..." Alhasan ya tsagaida da dariyarshi yana fadin "wayyo Allah nah! In tashi inje ina? Ka kirani kuma ka koreni, kana karyar bura uba ne... Ni ynzu to wai ta yaya ka gane Hameedah yar DANDI CEH plx? AB'ILAL ya kwashe lbrin tabashi da duk iskncin da hameedah ta masa ya labartawa Alhasan , Alhasan ya kwashe da dariya yana fadin "oh ikon Allah....daga tabawa se isknci...lalle kanada Aiki frnd sede ko in baza kayi Aure ba, ko ka koma kauye ka auro yar 11yrs itace bazata tabaka ba se randa ka gama iskncinka seka tabata..." Ya karashe mgnr yana daria, AB'ILAL daya gama zuwa wuya kawai yayi shiru dan beson mgna in rnshi ya bashi. Seda Alhasan yayi dariya me isarsa kana yace "Frnd gaskia da gyara a lamarinka... Kabi dunia a sannu kada ALLAH ya jarabceka da Abinda kafi tsana..." AB'ILAL yayi saurin amshewa da "Aniyarka kai zatabi insha ALLAH..." Alhasan yace "se me inta bini , se in amshi kaddarata hannu biyu biyu,..." AB'ILAL yaja guntun tsuki a hasale ya gimtse dan bakinshi Alhasan ya bishi da ido, yace ''to yanzu yaza kayi da Auwal hubb nasan de kwanan nan zata kara samo wata ta hadaka da ita? To yaza kayi?" AB'ILAL yayi shiru yna nazarin klmn Alhasan shiyasa yake mugun son Alhasan kwakwalwarshi naja a fannin nisan tunani shi sam ma beyi wannan tunaninba. "To yanzu frnd meye shawararka?" AB'ILAL yayi mgnr cike da neman shawara a gun Alhasan.jim yayi kana yace "inhar fa Amihh na kano to dole ne seta kara samo wata ta hadaka da ita, kuma tabbas baka da makawa dole seka Aureta A wannan karen, kasanma Amihh tana iya daura maka Aure kawai sede ka samu lbri, musammanma in kayi la'akari da yadda ta hasala Ainun A wannan datsin..." AB'ILAL yayi jim idonshi na kan bakin Alhasan se nazarin kalamanshi kawai yakeyi, shiru AB'ILAL yayi na tsawon 5mnt yna nazarin kalaman Alhasan ajiyar zucia ya sauke hadi da numfashi nannauye yace "Wato inna nazarci kalamanka, kana nufin in Amihh na kano dole seta kara jajibomin wata annobar.." Alhasan yayi murmushi kawai wai macece Annoba a gun AB'ILAL...daga masa kai kawai yayi alamar tabbatrwa.. AB'ILAL ya gyara zamanshi daram kasan carpet din dayake zaune kana yace "to ynzu meye abin yi? Domin gaskia bnso Amihh ta kara jajibomin wata annabor gaskia na gaji... '' ya karashe mgnr cikin kunar rai. Alhasan yayi jim kana yace "Aiko inde Amihh na kano, sede kaji ta daura mka Aure, amma in zata koma katsina hk kaga bata da qawaye ko daya dazata hadaka da yayansu, a kano ne Amihh keda frnds sosai, sbda tafi sabawa da nan din tasassan jama'arh kusan fin 30yrs take a kano fa,.." Ab'ilal yayi shiru kmr shaho yaci shirwa, yayi jim yna nazarin dukkanin maganganun Alhasan kama daga na baya zuwa na yanzu. " Auwal hubb kaduna zata dawo..." Yy mgnr hadi da nazari, se kuma yayi jim shi da knshi yasan abinda ya fada bame yuwwa bane. Alhasan yace "yauwa frnd kode ta koma katsina ko kaduna, ko wani gari de ba kano ba, in tana kanon nan ko frnds sata hure mata kunne suna bata yayansu tana hadaka dasu ..kai kuma baka so , kaga da kayita bata mata rai kwara kawai a nemi mafita.. " AB'ILAL yayi shiru yana cizon lips dinsa na kasa kana yace "shawararka tayi frnd, kawai ta dawo kd,... Amma ta yaya?" Alhasan ya buga hannunshi da dayan hannunshi kana yace "Shine babbar matsalar...Amihh wiyar kaine da ita sede mu bi a hnkli..." AB'ILAL ya amshe da "Ta yaya zamu bi a hankalin? Nifa shawarar nan taka tayi min, kawai ynzu ta yadda za ayi Amihh ta dawo kd shine matsalar?" Ab'ilal yayi mgnr cike da zaquwa duk yabi ya kosa Amihh ta dawo kd ma kowa ya huta. Jim Alhasan yayi kana yace "Last 1 month bakace Alhaji murtala wato Alhaji babba ba ya dawo kd da zama daga katsina harma munje mun gaidashi kou?" AB'ILAL yayi jim kana yace "Yeah daddy Babba ba , yana kd ai...kuma Addarmu ma tana nan kd itama, wadda salwah take gunta..." Alhasan yayi wani irin murmushin farin ciki yace "Yauwa....shikenan hanya zata zo mna da sauki insha ALLAH..." AB'ILAL yayi jim kana yace "me yasa kace haka?" Alhasan yayi shiru yana wasu nazari na wasu yan sakanni se faman kirga yatsunshi yakeshi kmr me kirga nanko tsabar nazari ne yace "Meze hana mu samu shi da kanshi Alhaji babba tinda naga yana sonka mu shawo knshi mu sashi yasa Amihh ta dawo kd da zama, yace mata tinda duk suna zaune kd shima ai naga da iyalenshi?" AB'ILAL ya yamutsa baki yace "matansa hudu ma...'' Alhasan yace ''yauwa....Kaga se ya gayawa Amihh duk suna zaune da iyalinsu itama ta dawo kd da zama sbda zumunci ze zamana duk suna kurkusa kowa zeji ihun kowa sbda halin rayuwa..." Jinjina kai AB'ILAL yy cike dajin dadin shawarar Alhasan yace ''Ka kawo shawara abokina... Ynzu de yadda za ayi mu fara zuwa gidan Alhaji babba mu sanar dashi, shi seya sanar da Amihh, Amma nasan be zama lallai Amihh ta amince ba kaga asibitin ta na kano fa, gashi tana Aiki a babban asibitin kano yaza ayi.?" Alhasan yayi jim yna nazari kana yace "zuwa zamuyi asibitin musa a mata trnsper zuwa kd...nasan me shugabancin asibitin a guna yake siyan motocinsa na hawa da iyalensa, kaga da an mata trnsper zuwa kd dole ta dawo nan, se a gina mata asibiti a nan dinma, nagama Ai ko asibitin na can kwararrun ma'aikata ne a ciki ba ita bace,.." AB'ILAL ya amshe da "yeah, bata ma zuwa sosai..." Alhasan yace "yauwa Alhamdulillahi,... ynzu se mu fara zuwa de gun Alhaji babba mu tsarashi, seya tsaro mna ita..." Wani irin shu'umin murmushi AB'ILAL ya saki hadi da yar dariya yace "Shawararka tayi frnd...yaushe zamuje gidan Alhajin?" Alhasan yace "gobe..." AB'ILAL yace "muje yau mna...'' Alhasan ya kallashi agogon dake tsinysiyar hannunshi yaga 6:2pm yace "ynzu fa 6:02pm ne time ya tafi, kwara mu bari goben de..." AB'ILAL ya dafe kai cike da mantuwa yace "sorry duk na shafa'ah ne, but na kagu inga Amihh a kaduna garin Malam..." Alhasan ya jefi ab'ilal da murmushi shima murmushin ya jefeshi dashi yace "Ai gobennan in mukaje uzurxurawa zamuyi , ta yadda shima ze uzura mata ta dawo kd da wuri...ynzu de gida tamfatsetse za a samu a siyama Amihh kou?'' Ab'ilal ya Kai hannunshi ya dafe goshinshi cike da gajiyawa da magana inba mgna me muhimmanci ba be tsayawa ya juma yana yinta. "Ka manta da gidanmu dake malali?" Alhasan yace "Yeah na tuna...Amma ai nasha ba a karasashi ba..." AB'ILAL ya kara dafe goshinshi zuwa ynzu knshi ya fara masa ciwo ma yace "Zansa a karasashi ai 1week yayi yawa za a karasa ba wani abu me yawa bane, se kayan Furniture kawai..." Alhasan yace "Wannan ba damuwa bane se muse furniture din sanat Turkish ne..." Ab'ilal ya rausayar da kai cike da gajiyawa yace "mu bar mgnr ni nagaji ma kaina ya fara ciwoh... Zuwa gobe ma karasa plx..." Alhasan ya jinjina kai kawai hadi da Murmushi shi yasan halin kayanshi ba a hirar 30mnt dashi zece ya gaji knshi na ciwo, a haka ai anci sa'arh ma yau da aka jima dashi ana hira. "Ba dole ka rinka iskan cinnan ba, 30yrs babu mace..." AB'ILAL ya dago kwayar idonshi ya dasawa alhasan wani irin mugun kallo kana yace "30yrs banyi ba mace, se aka gaya maka mace nake da bukata?" Alhasan yayi dariar shakiyanci dmn yasan haliin AB'ILAL da iya dasa muguwar mgna yace "ka rantse da ALLAH jelarka bata bukatar ramin mace? " mikewa AB'ILAL yayi cike da kosawa da mgnr iskncin da Alhasan ke janshi dashi, cikin izza yace "kai kasan wani ramin mace, ni nan bnsanshi ba,.." Alhasan ya kare masa kallo kawai yace "Karya kakeyi frnd Duk munsan irinku gida da jallabiya waje da manyan kaya dagani boxes uku kake hadawa a jikinka..." Girgiza kai AB'ILAL yayi a zuciarshi yana gasgata mgnr Alhasan domin kuwa kusan hkn ne wanduna biyu yake sawa saboda tsaro. Juyawa Ab'ilal yayi ba tare dayace komi ba ya nufa hanyar toilet yakai hannu ze bude handle din toilet din ya juyo ya kalli Alhasan yace "Inka gama mgnr batsar akwai ruwan me zafi a toilet dinnan, se kayi wankan tsarki kayi Alwala mu tafi masallaci ...." Yana gama fadar hkn be jira amsarshiba ya fada toilet. Alhasan ya kwashe da dariya yace "aka gaya maka na jige ne, kaide daka jik'e kaine zakayi wanka...." Ya karashe mgnr yana girgiza kai a zuciarsa kuma jinjina halin AB'ILAL yakeyi. Bayan AB'ILAL ya fito toilet din daure Da alwala alhasan ya nufa toilet din shima yayi alwalar ya fito ya samu ab'ilal a tsaye yna jiranshi sbda an kusan tada sallarh magrib dmn tini akayi kiran sallarh. "Kana abu kamar mace..." Ab'ilal ya fadi a hasale danshi a ganinshin alhasan ya jima a toilet din be fito ba. Jinjina kai alhasan yayi ba tare da yayi mgna ba , danya san in yy mgnr alwalarshi na iya karyewa shiko AB'ILAL ko a jikinshi danshi ba a gane ma a wani hali yake ciki. Ficewa sukayi daga dakin suka masa key kana suka nufa masallacin dake wajen hotel din...basu dawo ba seda sukayi sallarh isha'i da shafa'i Alhasan yayi wutiri shikam ab'ilal beyi ba sbda sallarh dare da yakeyi. dawowa dakin sukayi a falon suka yada zango wannan karonma AB'ILAL a kasan carpet ya yada zango har falonma kyamarshi yakeyi, alhasan ya girgiza kai kawai danyasan halin kayanshi ..ci gaba sukayi da hirar da Alhasan ne kawai ke yinta AB'ILAL de iyakarshi dashi ido... Order din white rise and stew da farfesun kayan ciki AB'ILAL yayi musu, ba jimawa aka kawo musu, sukaci suka koshi suka kora da drinks dinn dake frij din falon, Alhasan sema Ab'ilal tsiya yakeyi wai be iya amsar baki ba, tinda yazo ko ruwa be bashi ba, ab'ilal ya jishi Kawai amma bece masa komi ba,... 10:pm alhasan yace ze tafi gidanshi shima beda mata. AB'ILAL yace ''ka kwana a nan mna?" Alhasan yace "gidana zan tafi..." AB'ILAL yace "sekace me mata, se wani cewa gidanka, gidanka kakeyi, kai ba rami ka ajiye a gidanba, nidakai duk daya ne. amma ni akafi sawa ido
.." Alhasan ya kwashe da dariya hadi da miqewa yana fadin ''ai ka girmeni Frnd in baka mntaba 3yrs ka bani, kaga ya kamata ka rigani Aure...." AB'ILAL ya hade rai yace "Amma a zahiri ai kaine ke Bukatar auren..." Alhasan yayi dariya yace "waya sani abu a duhu a cikin wanduna uku... Zaka samu dmr rakani kuwa?'' Ya karashe mgnr idonshi na kn AB'ILAL wanda ke zaune kasan carpet ko gezau beyi ba ya tabe baki yace "gaskia bazan raka kaba, ynzu tsinannun yammatan nan yan DANDI duk zasu zubo min ido, shegu mayun maza..." Alhasan ya kwashe da dariya kawai ya juya ya fice a dakin ba tare daya kara cewa AB'ILAL ya rakashi ba danyasan ba samu zeyiba, ficewa yayi yna masa se goben, a gajiya AB'ILAL ya amsa da "ALLAH ya kaimu..." Kana ya mike yama dakin key byn alhasan ya fice ya nufa bedroom din , bathroom kawai ya fada ba bata lokaci, domin ynada bukatar wanka kuma yau so yakeyi ya dan kwanta zuwa 2:am seya tashi ya fara ibadah.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi πππ.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni ππ.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jikuππππππ
08/01/2022 Γ 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*YAR DANDI CEH*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
(SHE'S A WORLDLY PERSON)
SAADATU BINTU ABDULLAHIβπ½
*Writer of KYAUTAR ALLAH*
π
ΏοΈ10
Washe gari Ta kama ranar Sunday weekend ne. AB'ILAL yanada tabbacin zasu samu Alhaji Murtala a gida, kasancewar dan kasuwa ne shima, ba kullum yake fita ba sbda shekaru sun ja, amma wasu lokutan yakan fita,, yaranshi maxa biyu suke kan harkokinshi. yaranshi bakwai ne, biyu maza sauran duk mata ne. dan hk AB'ILAL be whlr da knshi ba wajen kiran Alhaji murtala a waya ba , da niyar ya sanar dashi xuwansu, shi fa a rayuwarshi kiran waya yafi masa komi zama aiki. 5:pm Alhasan yazo hotel din da niyar zasu je gidan Alhaji murtala kawai AB'ILAL ya rufeshi da matsifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba wai meyasa zezo a kurarren lokaci bayan tin tini yaketa kiranshi, dayake Alhasan yasan halin kayanshi Dan haka be bi ta kanshi ba se ya gaya masa uzurinsa na wasu aiyuka ne suka riqeshi...ab'ilal ya kara volume din maysifarshi "Aikin banza aikin hofi, aikin me?" Cewar AB'ILAL. Alhasan ya rausayar da kai gefe ya bashi hkri kawai. Suka fito harabar hotel din dukkaninsu sanye da manyan kaya na alfarma, suka hau motar Alhasan still ab'ilal Nata mita har alhasan yaja motar suka fice a hotel din AB'ILAL nata jarabarsa shi a dole an bata masa rai. Da alhasan ya gaji ya hade rai ya fara mgna a hasale "Kai zan zunduma maka ashar Wallahi ka dameni, ance kayi hkri...kai karma ka hkra, Dan iska kai!" Wani irin dogon kwafa AB'ILAL yaja kawai a cewarshi beda lokacin Alhasan, Amma still be bar mitarba har suka isa bakin get din Gidan Alhaji murtala dake kinkinau . Alhasan yayi hon ba bata lokaci me gadi ya leqo dan ganin waye sbda shi ba a sanar dashi zuwan kowa ba kuma a ka'idar gidan se an sanar dashi in wani zezo wato seda izinin masu gida su kuma su gaya masa danya sani. Karasowa dattijon yayi bakin motar yayi knocking kofar glass din side din Alhasan yana fadin " waye ?" Alhasan yayi kasa da glass din side dinsa suka hada ido da dan ladi me gadi Cikin girmamawa Alhasan ya gaida Dan ladi ya amsa cikin girmamawa shima kana yace "dannan Lafia de kou?" Sbda shi be gane su Alhasan ba dan last time da daddare suka zo. Alhasan yace "lafia lau baba...ka bude mana get plx..." Dan ladi yace "To ai ba' a shiga gidannan seda izinin masu gida , ni ba a Sanar dani zuwanku ba, sede naji hon kawai...ka kira wanda kuka zo gunshi ko gunta seta kirani..." AB'ILAL dake kwance kan kujerar gefen Alhasan yanajin duk me ke faruwa, dagowa yayi danya hango waye me mgnr nan nan yaga wani gajere baki kirin dashi , wato dan ladi me gadi, Zuciya tazo ma AB'ILAL wuya jin ma Abunda me gadin ke cewa wai se an sanar da masu gida sekace gidan governor me cin mulki. Alhasan ya juyo ga ab'ilal yace "Wai baka sanar da Alhaji babba zuwan namu bane?" AB'ILAL da ranshi ke a hade kmr be taba Dariya ba yace "A kan me zan sanar dashi governor ne shi....mtws!" Yaja guntun tsuki kawai ya fito daga motar, ya mayar da murfin ya rufe, ko kallon inda me gadin yake beyi ba ya karasa ya shige cikin gidan me gadin ya biyoshi a baya yana fadin "Dannan lafia kuwa? Ina zakaje? Ka rufamin asiri kar in rasa Aikina..." AB'ILAL ko bi ta knshi beyi ba ya shige gidan ya bude get din farko Alhasan dake mota se dariya kawai yakeyi yna kallon isknci irin na AB'ILAL kawai ya danna motarshi cikin gidan, AB'ILAL ya kara bude masa get na biyu, duk me gadin nata binshi yana rokonshi kan karya bude amma sam be bi ta kanshi ba, beda ma lokacin mgna dashi, Alhasan de se dariya yakeyi ya shige da motar cikin gidan dmn get biyu ne a gidan, yayi packing a packing space. Dan ladi me gadi dayaga AB'ILAL yafi karfinshi kawai yaja gefe ya zubawa sarautar Allah ido, shi tsoroma ya bashi tinda yayi tozali da wannan halittar tasa
Ta karfafan maza, dan hk a tsorace yake da AB'ILAL kmr yadda yake tsorace da duniya. AB'ILAL ya karaso bakin motar inda Alhasan ya fito suka hada ido da AB'ILAL , kawai Alhasan ya kwashe da dariya, ab'ilal ya hade rai kmr be taba dariya ba kai kace an aiko masa da mala'ikan mutuwa ne rannan nashi baki kirin, yabi ya hade girar sama da kasa. Alhasan ya rausayar da kanshi gefe still yana yar dariyar iskanci, nan ya shiga karewa gidan kallo dayake last time dasukazo da daddare ne, besanma ya gidan yake ba, se yau ya tabbatr da gidan kerarrene kuma hadadde ne, irin na bugawa a mujallah, wannan gidan yafi irin na hausa novel kyau da tsaruwa. packing space din gidan kanshi abin kallo ne, kusan motoci goma ke pake a packing space din motoci na Alfarma , kasancewar gidn babban gida ne me dauke da bangare bangare har bangares shida, hudu na matanshi se daya nashi se dayan na yaranshi maza Muhammad da Jibril. Alhasan yayi wani shu'umin murmushi idonshi na kan AB'ILAL yace "Kai Abokina Alhaji babba na kwasar dadih..." AB'ILAL ya yatsina fuska yna kallon Alhasan kana yace "Dadin me?" AB'ILAL yayi mgnr hadi da fara takawa zuwa side din Alhaji babba Alhasan ma takawar ya farayi ma'aikata se jero musu gaisuwa sukeyi, Alhasan