Showing 183001 words to 186000 words out of 306755 words

Chapter 62 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

Ci gaba tayi dayin mopping din tana me shaqar kamshin turarensa me kwantar mata da hnkli, a hk har ta gama ta nufa dakinsa domin ta gyara, nan ta tadda kamshin sosai ga sanyin AC tayi ta shaqa tana gyaran dakin tana taka tsantsan da abubuwansa sbda kar yazo yace mata bega abu ba irin na jiya.....

Koda ya isa ga motarsa ya shiga ya zauna ya gaza kunnata sbda kawai sha'awarta data gaza shud'ewa a zuciarsa, Gashi wani aiki zejeyi da safen nan a ma'aikatarsa ta nan kd Signing zeyiwa wata paper daza a dauki kayansa zuwa england, 9:am jirgin jayan ze tadhi, tin 8:22am yake motar amma ya gaza kunnata har 9:am din, sbda jikinsa da yayi weak ga kiraye kiraye nata shigo masa waya na masu kayan ne amma yaki dagawa, seda yayi yaki da zuciarsa kana ya tayar da notar ya fice a gidan jiki a sanyaye, dayaga yarinyar abubuwa dayawa ke zuwar masa cikin brain wadanda baze iya misaltasu ba, abu daya yake iya misaltasa shine daya ganta se wannan gizon nata daya gnta taja hannun namiji suka koma cikin gidan karuwai, yazo masa, sannan seya tuna cewa ya taba ganinta a gidan karuwai, se kuma hotel inda nan ne ya fara ganinta a rayuwarsa se yaji haushinta da kiyayyarta sun karawa zuciarsa dirar mikia shifa gani yakeyi kmr ya kamata read hand ne da wani a saman mararta yana mata gwatso. shide kawai ya riga daya batta a mazinaciyya, a dunia inda abinda yafi tsana zina ce, ya tsaneta kuma ya tsani me aikatata shiyasa kiyayyar da yayiwa yarinyarnan tayi yawa, ga bin maza ga shigar bnza ga rashin sa dankwali, kaf alamomin rashin tarbia da rashin kunya sun taru sun tattare a tattare da yarinyar. Da wadannan tunani tunani a ransa ya isa office dinsa inda zesa hannun zuwa lokacin 9:30am ne, dole sede ya zamana tashin jirgin nasa gobe, sam ba hk Yaso ba yayi signing takaddar da sauran cike ciken da akeda bukata yayi kana ya bar ma'aikatar, yaje kamfaninsa na saida motoci, a can ya bata lokaci har yy azahar kana ya nufo gidan, direct side dn Amihh ya nufa be sameta ba dmn yasan baze same taba, tana gun Aiki tin 7:am ta fita, a kwanakinnan da wuri take fita sbda ayyuka dasuka kara mata yawa. Salwah ya samu a falo ta gaidasa ba Tare daya amsaba ya nufa kan 3ct ya zauna yana ne aikin sauke ajiar numfashi kmr wanda yayi dan gudu ko tafia me nisa ya fara tunanin rashin motsa jiki ne da bayayi yake sashi yawan numfarfashinnan. Ya umurci Salwah dake niar barin falon data hado masa abinda zecu mara nauyi, jiki na rawa tace to ta nufa kiching ta shiga hada masa abinda ya umurceta ba jimawa ta gama ta kawo masa ya dan tsatstsakura ya barshi ya kora da coffe kawai ya tashi ya bar falon ya nufa side dinsa, ya tura kofar falon ya shigo bega kowa ba, se zallar kamshi dake tashi ya tabe baki sbda shi duk abubuwannan da takeyi bawai yaji ko kadan ya fara sonta bane, ko ya fara tausanta hasalima haushi take basa, ya nufa bedroom dinsa yaga ko ina tsaf tsaf ta shigo ta gyara se kamshin jikinta ke tashi a dakin, ya nufa wata drower da niyar ya dauki wata yar karamar takadda da akayi laminating dinta yar karama ce sosai,, nanma be gnta ba Gashi ynzu yakeso ya fita da ita zuwa dayan gun aikin nasa, takaici ya rufe masa zucia yaji kmr yaci knsa da matsifa nan da nan yaji jaraba da matsifa da guyaba tayi ma tsakiyar zuciarsa dirar mikia, ya fito daga dakin a fusace yana cewa "Kee!! Kee!!" Dai-dai ta fito daga kofar kiching hannunta riqe da kulah ta gama Abincin rana ko abincin safe ma bata ci ba sbda Ayyukan datake tayi, shine taji yana cewa kee! Tasan da ita yake hnklinta yayi mummunan tashi jikinta ya hau rawa tasan kiransa ba alheri bane, ji tayi kular hannunta tana niar subucewa ta fadi kasa seda ta riqeta gam gam, ta duka ta ajiyeta a nan kasa zuciarta na dum dum, ya karaso inda take kmr ze daketa, ya fara zazzago matsifa hadda cewa wai ita ke masa satar takaddunsa tana kai masa wasu gurare yace ma aikota akayi, fada matsifa cin mutumci duk seda ya matasu ta hau hawaye daga nan tsaye, ya tasata gaba yace seta nemo masa takaddunsa da file dinsa da wannan yar takaddar, jaraba de iri iri seda ya mata, da zallar madarar tijara kai kace ma dukanta zeyi, ga fuskarnan tasa babu alamar rahama, ya tasata gaba sukaje bedroom dinsa ta shiga duba masa takaddar, bata ganta ba sede taga files din jia a kasan gadon kuma jia harnan ta diba dayake de hnkli ke gani ba ido ba. Ya fisge file din a hannunta yace ta nemo masa yar takaddarnan, nan ta shiga nemanta tako ina bata ganta ba, aiko ya zaburo mata da fada, yanata jifarta da muggan kalami karuwa, yar iska, kmr ze mareta ALLAH ya rufa asiri be maretan ba, yace ta nemo masa yar takaddarsa kafin ya dawo gidan ko ya kusan kasheta inya dawo dan ya riga daya rantse ma in har ya dawo bata nemo masa yar takaddarsa ba seya daketa ..da hk Ya fice a dakin ya batta da zullumi ga kirji na ciwo ga ciwon kai Gashi batayi karin kumallo ba amma yazo ya sata dan karan aikinnan, har gadonsa me shegen nauyi seda ta dagashi, taci gaba da dube duben dakin tako ina ko zataga takaddar amma bata gani ba, ta hargitse ko ina a dakin, sannan taci kuka sosai daman ita ga arbar hawaye, har kusan 1:53pm kana ta mike ta nufa dakinta ta kara wanka ta shirya shirin zuwa mkrnta kasancewar sunada lecture 2:am tayi sallarh ko abinci bataci ba ta sargafi jakarta, ta fice a falon sukayi kicibus da salwah a compound itama cikin shirin zuwa mkrntar zatazo ma side din su ne ta mata mgna su tafi shine sukayi kicibus. Suka juya suka hau mota dan Ustaz yaja suka fice a gidan, da gudu sbda sunyi latti. Salwah data kula da idanuwan hilwah a kumbure suke tinda suka hadu a compound din ta dankare da hkn. ta shiga tambayarta meya faru bayan sun shiga motar dan Ustaz ya dau titi. Hilwah tacewa Salwah bkm, salwah ta matsa mata da tambaya ganin hkn yasata ce mata batayi bacci bane tayi karatu ne sbda tanada test yau. Salwah tace ok ta yadda da hkn har zuciarta ta mata mgna kn dan ALLAH ta rinka bacci sosai rashin bacci ciwo ne, hilwah tace toh, hadi da mata godia da kulawa a hk har suka isa zuwa mkrntar, dan Ustaz dakejin me suke cewa se washe baki yakeyi Shida badashi ake mgna ba, harga ALLAH shifa yana ciki ne.

4:39pm ya dawo gidan zucia fal tira da matsifa abinka da tijararre, ya iso dakinsa ya taddasa a hargitse data birkiceshi bata gyarashi ba, nan ma ya kara cika da wata matsifar sbda shi be kaunar tarkace shiyasa dakinsa simple ne ba tarkace beson kace kace kwata kwata, samfarin dakinsa irin na turawa ne ba haya haya kwata kwata, amma shine ta yamutsa masa dakin, ya zamama tako ina tarkace ne, gaza ma kwancia yayi a dakin dukda kuwa a gajiye yake dole sede ya dawo falon yana me kwalo mata kira a fusace sunan ta de a bakinsa shine kee! Kee!! Har bedroom dinta ya nufa yana kiran kee! Ya bude bega kowa ba se kamshinta daya cika masa hancinsa yaja kwafa ya nufa kiching, be gnta ba a kicking din, hkn ya bashi tabbacin batama nan ma a side din yasan baya wuce tana Side din Amihh se yasawa ransa wato ma rainin hnkli ne yasata tama dakinsa filla filla kuma ta bar masashi hk nan ba fasali, isa yy ga kujerar 3st ya kwanta, se faman huci yakeyi shi kadai hadi da jan tsuki time to time, kiyayyar yarinyar na yawaita a zuciarsa da ransa yace wata rana inhar tana gyara masa daki seta masa sata, dan hk kwara ya dauki mataki a knta tin ynzu, sbda kwata kwata bata da natsuwa a hkn yake gani ... Da wanan tunanin a ransa ya shiga girgiza yana jan tsuki kmr dan sarki kawai ita yake jira ta shigo dakin ya rufeta da zallar tijara da matsifa. 5;am suka dawo daga scul a harabar gidan sukaga motar alhasan da motar Amihh. da side din Ab'ilal din zata nufa amma ta dawo suka nufa side din amihhn ganin motarta da motar alhasan sbda ynzu ta fara jinsa a ranta yana burgeta sosai rannan ma hadda ICE cream ya siyo musu ita da salwah yana mata kirki sosai shiyasa ta fara jinsa a ranta again kuma yanada fara'arh gareta ba kmr AB'ILAL ba, da yake kmr mala'ikan mutuwa game rai. A falo suka taddasu shida amihh, suna yar hira, suka tsugunna suka gaidasu suka amsa ba yabo ba fallasa, dukkaninsu kwayar idonsu na kallon hilwah tin shigowarta itan suka kure ds ido, hilwsh uwar kunya se faman kasa takeyo da knta, sbda tanata kasa da knta ya hana Amihh fahimtar wani abu a tattare da fuskar tata, ba gami da kumburin da tayyi, dukda zuwa yanzu ma ta sace. "Andawo lafia sweetien amihh...." Cewar Amihh datayi mgnr da hilwah. Ta amsa da lafia lau, cike da jin dadih.... Alhasan se kallon hilwah yakeyi yana daria kmr wani wawa, duk a cikin soyayya ne, shifa in yazo gidan ko hira sukeyi shida Amihh kawai sunayi ne amma be fahimtar komi, a halin ynzu se ayi cinikinsa a gabansa ma besan abyi ba. Hnklinsa fully sam baya wani zama a jikinsa krtun yaga hilwah kawai yake iya ganewa,ki hira akeyi shi be fahimta. Amihh tace musu su shiga ciki du huta.." Tana fadar hkn ta rigasu mike ta nufa kiching dmn abinci take hadawa tade dawo ta zauna ne suna hira da Alhasan amma tanayi tana tashi ta duba girkinta. Hilwah ta fice a falon alhasan ya bita da ido a ranshi yasha ko mota zataje tayi mantuwa ne. Salwah kuma ta mike ta nufa dakinta. Suka bar Alhasan a falon da tunanin hilwah a ransa.


Da sallahma ta turo kofar side din nasa ta shigo zuxia fal fargaba ko side din zata shigo to tabbas da faduwar gaba take shigowa. idanuwanta suka sauka a kansa yana kwance a kn kujerar 3st taji gabanta ya yanke ya fadi, a hnkli taci gaba da tafia zuwa bedroom dinta cikin dakia ne tattare da tsoro, har ta kusa bedroom dinta taji yace "kee!!!'' 2tms Cikin tsawa, jiki na rawa ta amsa da ''na'am!'' Ta dawo da baya jiki na rawa duk tabi ta firgice, ita ga zatonta ko yana bacci ne data wuceshi, ja tayi ta tsaya data kusa inda yake, ya dago ya tashi zaune zucia na kuna, ya daura kafa daya kan daya irin na rashin mutumcinnan, ya zubo mata ido daga inda take tsayen, rataye da jaka, ta saman hijjabin jikinta, Ya kureta da ido irin kallon wulakncinnan, ganin hijjabi a jikinta ya sashi tsayawa kallonta sosai, be taba ganinta da hijjabi ba se yau, guntun tsuki yaja, tinawa da yayi da inda ya fara ganinta ko hijjabin ma gani yayi be mata kyau ba. "Daga gidan uban wa kike?'' Ya fadi murya cike da matsifa, ta dago ta zuba masa ido jikinta ya kara daukar rawa Ta gaza bude bakinta tayi magana ta mayar da knta kasa,. haushi yazo masa wuya ganin yana mata mgna tanaji harma ta kalleshi amma ta gaza bashi amsa. "Kinje gidan naku na karuwai ne kou? " seda ta dago ta kalleshi Wannan karon cike da jin zafin abinda yace mata ta zuba nasa ido, kana ta dauke kwayar idonta dake masa zafi sbda bacin rai, sam zuciarta bata mata dadih ba dajin wannan kalamin nasa. Yaci gaba da jaraba. "Look ni ba dan iska bane kinaji na kou? Nan ba gidan iskanci bane, wlhy daga yau kk kara fita a gidannan se ranki ya baci, se wanda ke cikin oven ya fiki jin sanyi!.....wuce kije ki gyaramin dakina da kika batamin nan da 5mnt wlhy ko inzo in kakkaryaki, kuma ki fiddomin da takaddata,.... " yana gama fadar hkn ya koma ya kwanta kan kujerar harda mayar da kwayar ido ya rufe. Jiki a sanyaye ta nufa bedroom din nasa, se ynzu ta tuna da bata gyara masa dakin nasa ba ta fita. Cikin hanzari ta shiga gyaran dakin sha tana isa cikin dakin ta ganshi kace kace yadda ta barshi jiki na rawa ta shiga aikin gyare dakin, tana cikin gyaran taga Takaddar tasa da take nema ta ajiye masa a kn bedside ta gama gyaran cikin hnzari ta fice a dakin , bata gnshi a falon ba dan hk ta nufa dakinta cikin hnzari zuwa lokacin anata kiraye kirayen sallarh magrib. Bayan tayi wanka shap shap ta dauro alwala tayi sallarh magrib, ta nufa kiching ta hada abincin dare me sauki, ta ajiye a kn dining duk da yadda ta bar na dazu hk tazo ta sameshi amma ta sakeyin wani sabo, sbda amihh ta jadda ja mata ko bayaci kada ta gajiya da dafa masa. Be dawo gidan ba se after isha'i da jimawa, duk yna masallaci yana karatun alqur'ani, seda akayi magrib akayi isha'i kana ya shigo gidan direct side din Amihh ya nufa ya tadda alhasan na niar ficewa byn ya gaji da zaman jira bega hilwah ba, ko lallo be ishi AB'ILAL ba , ganin hkn yasa alhasan be tankasa ba yy murmushi kawai Dan yasan mulkin mutumin nasa, ya wuce ciki , kana Alhasan ya fice a falon. ya nufa dining zeci abinci amihh tace be isa ba, sede ya koma can side dinsa yaci abincin da matarsa ta dafa masa, , nan ya shiga mata magia sbda shi sam bayajin ze iya cin abincin karuwah, ai yana ankare da tana dafa wa ci ne kawai beyi ba, kuma bejinma ze iya ci.. Ynzu hk yunwa yakeji amma sam amihh taki saurarensa ta basa abncinta, tace yaje side dinsa yaci abinci inma matarsa bata dafa masa ba ya umurceta ta dafa masa, ta buga masa warning kan karma ya kara zuwar mata side yaci mata abinci. .." Jiki ba laka ya fice a side din zucia ba ddh, ya nufa bedroom dinsa ya ganshi tsaf ya haye kn bed kawai ga yunwa naci masa cikinsa ga sha'awah na kwakule masa mara, bayajin ko ze mutu ze iyacin abincin yarinyarnan, tashi yayi ya dauko fresh milk kawai yasha ya koma ya kwanta, wuraren 10:am ta shigo dakin jiki a sanyaye, tana sanye da hijjabi, se riga da wando na bacci a jikinta wando har kasa yake,. sam bataso zuwa ba Amihh ce tazo ta korota dakin sannan ta jadda ja mata kn kullum taje kar ta taba fashi, ko kallon inda yake batayi ba knta na kasa ta karasa kasan tiles inda ta kwana jia ta kwanta ta kudindine a hijjabin jikinta kasancewar yanada dan tsayi, zubo mata ido yy kawai ya juya ya kwanta ta yadda be ganinta, duk yadda yaso yy bacci gaza wa yayi, kamshin turarenta duk yabi ya cika masa hanci,...itama gaza baccin tayi ganin hkn yasata mikewa ta leqasa taga kmr yayi bacci batasan duk yna kallonta ba kawai de yayi likimo ne, ta fada toilet dinsa wanda yake tsaf tsaf ta dauro alwala ta fito ta nufa kan dadduma ta fara jero nafilfili lokacin ana neman 1:am ne, AB'ILAL ya juyo ya zuba mata ido ganin tana sallah kuma dai-dai wa daidah se ynzu ya yadda cewa musulmace ashe, amma fa yayi mamakin ganin tana sallah har wani kara bude kwayar idonsa yakeyi yana murzasu yana rufesu yana budesu a knta,...har asubahi tana sallarh seda aka fara kiraye kirayen sallarh asubahin farko kana ta tashi ta bar dakin zuwa dakinta. AB'ILAL daya kwana yana kallon ikon Allah yana al'ajabin yarinyar, jiki a sanyaye ya mike ya fada bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito still se mamakin yarinyar yakeyi a ransa, shifa be yadda tin rnr daya fara ganinta musulma bace sbda yanayin shigarta da dab'i'unta, yafi tunanin kila a nan gidan Amihh ta musuluntar da ita. Da wannan tunanin a ransa ya shirya zuwa masallacin asubahi....


Hk rayuwa taci gaba da gudana sam be shiga hargarta amma sha'awarta nata yawaita a zuciarsa, se uban azabtar da ita kawai yakeyi ynzu abin nasa harda duka abu kadan zatayi se duka ko mari, duk yabi ya bar tabon bulalarsa a jikinta, dai dai da rana daya hilwah bata taba barin wata kafa da Amihh zata fahimci hkn ba, sede duk yabi ya dasa mata kiyayyarsa a ranta, a ynzu ta dan fara rage tsoronsa a zuciarta.... A bangaren AB'ILAL kam a hk ma yana raga mata ne sbda ibadar da yake ganin tana kwana tanayi, sam bata bacci,....lokuta da dama ma tare sukeyin nafilfilin, , tana dadduma daban shima yana tasa daddumar daban, kowa sallarhshi yakeyi daban dsban..... Wata rana ya dawo daga masallacin sallarh asubahi ya taba jinta tana kira'arh alqur'ani ya tsaya ya saurara sosai harda leqata ta gefen kofar yaga tabbas ita ce, ya tsaya ya saurari karatun nata sosai, tabbas a karatunta ya fahimci tanada ilmin baqaqe da harrufa, sbda ta iya kira'arh sosai, rnr fa kwana yayi yana mamakin yadda ta iya karatun alqur'ani me girma, zuwa ynzu fa ya fara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login