Showing 90001 words to 93000 words out of 306755 words

Chapter 31 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

ido,,salwah kam ta zuba musu ido farin ciki kmr zuciarta zata fito fili ko yunwah ma bataji sbda jin ddhn ganin hilwah yau a gidansu, duk ta kagu su kebance ta tambayi hilwah din ko ta dawo gidansu ne kou! Dan bataso ta tafi. Seda amihh ta tabbatr ta koshi kana ta batta haka, salwah ta kwashi kayayyakin ta nufa kiching dasu ta dawo ta kwashi sauran.... Rnr hk Amihh ta wuni tana tarairayar hilwah har dare ya tsala, after sunci abincin dare, sun dan taba hirah, yau salwah ce ke hira da Amihh cikin mutumci da mutumtawa, ba krmin ddh hkn ya ma salwah ba tasan duk dan sbda hilwah ne, dan hk ta kara kaunar hilwah a ranta. 11:pm bayan hilwah tayi wanka ta canza kaya zuwa na bacci sabbi dal dasu riga da wando masu laushn tsiya amihh tama hilwah adduarh ta lullubeta da duvet a dakin salwah dan ta kula tafi so ta kwana nan din, ta mata seda safe ta fice a dakin ta nufa nata dakin , domin samun dmr yin tunanin abinda ke ranta... Salwah dake toilet tayi wanka ta futo taga Hilwah kwance a kn bed amihh ta fita, hkn ya bata tabbacin ta tafi nata dakin ne seda safe kuma. Kure hilwah tayi da ido taga har zuwa lokacin idonta biyu ta kurewa gefe guda ido dagani tunanin wani abu takeyi, kuma hkn ne tana tunanin kayan mayen data saba sha ne, yau kuma babu, musammanma cocaine tafi sabawa da shanta. Shiryawa salwah tayi cikin kayan bacci ta feshe jikinta da Indians perfume nan ta hau aikin zuba kamshi. hilwah uwar yan son kamshi hadda lumshe ido ta rinkayi tana shaqar kamshin. Salwah ta hauro kn bed din ta zauna ta lankwashe kafa, hilwah ta waigo ta zubawa mata idanuwa suka sakarwa juna murmushi. "Kin dawo gidan mu kenan har abadan kou me rabin suna?'' Salwah ta jefowa hilwah tambayar. Murmushi kawai hilwah ta sakarwa salwah...salwah taci gaba da jan Hilwah da surutu har zuwa 12:30am , mikewa hilwah tayi ta fada bathroom idanuwanta a soye babu alamar bacci ta dauro alwala ta fito, Salwah nata binta da ido, ta nufa inda aka tanada dan gabatar da sallah, ta tayar da sallarh nafilah, salwah de nata binta da ido, duk raka'ah biyu inta kai seta dakata tayi karatun alqur'ani me girma. daga izifi goma ta fara zuwa kasa, cikin zazzakar muryarta me fidda fitinannan sauti. Salwah ta mike itama tayo alwala tazo tabi sahunta suka cigaba da nafilfilin.... Har zuwa wannan lokacin idanuwanta biyu bata samu ta rintsa ba se aikin zagaye takeyi tana safa da marwa a dakin nata, wasu irin tunani daban daban sunata bijiro mata a kn hilwah tabbas tanaso ta mata abnda bazata taba barin gidannan ba, ballan tana tayi tunanin komawa gidan ruwah. "Wani abu ne wannan?'' Wani bangare na zuciar hajiya maryam ta jefo mata wannan tambayar...dayan bngren zuciar na qoqarin bata amsa ta fara jiyo karatun alqur'ani me girma kasa kasa, fitowa tayi falo, tana me lumsar ido saboda dadin karatun al'qur'anin data rasa a ina take jiyosa....Tazo zata gifta dakin Salwah ta kara jiyo karatun na kusantarta, manna kunnanta tayi a jikin kofar dakin, tana jiyo daddadar muryar hilwah na karatu alqurani amma ta gaza gano ko wacece, tadesan ba muryar Salwah bace, bata tsammaci hilwah ta iya kira'arh sudais har haka ba,,sak kira'arta sak ta malam sudais. Turo handle din dakin tayi ta shigo idanuwanta suka sauka kn hilwah daketa karatun al'qur'anin se salwah daketa faman jero nafilfili. Hilwah ta dago kwayar idonta sanadiyar turo kofar dakin da akayi aka shifo tasata dago kwayar idon nata, Nan taga Amihh tayi shiru hadi da sauke kwayar idonta kasa sbda amihh daketa kallonta,,,juyawa hajiya maryam tayi ta fice a dakin ta nufa dakinta zuciarta ta kara yin full da soyayya da kaunar hilwah, tare da fatan kasancewa da ita har abadan da'iman. "To ta yaya?" Zuciarta ta tambayeta, bata tsaya bata lokacin bata amsa ba ta fada toilet ta dauro alwala ta fito ta zumbula hijjabi ta hau jero nafilfili tana me rokon Allah yasa tasamu mafita me salama a zuciarta a kn yadda hilwah zata kasance dasu har abadan...seda tayi sallarh asubahi gari yadan fara wayewa kana ta kwanta zuciarta wasai kmr ta sabon jariri yayin da tin tana nafilfili ta yankewa knta abinda ya dace da ita a kn hilwah. A bangaren su hilwah ma seda sukayi sallarh asubahi kana suka koma suka kwanta bacci, hilwah baccinta me cike da tsantsar mafarkan wannan guy din tayi, wai gata gashi suna kallon juna amma babu wanda ya tanka juna, se kallon tsana kawai guy din ke Aiko mata.... Yau ta kasance friday ce. 9:am Amihh ta tashi ta fada bathroom tayi wanka a daddafe ta fito ta shirya cikin abaya Cotton color ta yane knta da mayafin abayar ta karasa ta dauki kudi kimanin dubu dari hudu a drower din da take ajiye kudade. Ta saka
400k din a cikin bag dinta dmn already akwai 150k a ciki, ta xira plat shoe dinta na manyan mata ta dauki mukullin motarta ta fice a dakin, ta fito falo bataga kowa ba, sede ko ina tsaf tsaf yake, ta isa kofar dakin Salwah ta gnshi a rufe dagani basu tashi a bacci ba, sbda basu kwanta da wuri ba. Da fara'arh a kn fuskarta ta fice a falon, compound ta fito dai-dai watch din zallar gold dake hannunya ya nuna 10:13am. kukan tsintsaye iri daban daban se tashi yakeyi a compound din yayinda bishoyoyin dake gidan da flowers masu koren ganye se kadasu iska keyi a hnkli a hnkli. Dan ustaz dake zaune bakin get shida me gadi yaga fitowar hajiya maryam a guje ya taso se uban sheki yakeyi yayi wankan safe ya lafta uban mai kannan nashi tal-tal ya karaso inda hajiya maryam ke kokarin karasawa packing space yace "khaifak asbahtah yah hajjaju?'' Hajiya Maryam ta dago kwayar idonta ta zubawa dan ustaz tin daga kasan kafafuwanshi ta fara kallonshi inda yake sanye da green din slifas dan madina kafarnan tashi se sheki takeyi ya shafa mai sosai hatta da slifas dinma kullum in yy wanka seya shafa masa mai, kafarnan baki kirin, gashi an lafta mata mai seta kara bakikirin da ita. Hajiya maryam ta dawo ta kalli rigar jallabiyar dake jikinsa wadda da kadan ta wuce guiwa ta dawo da idonta kan fuskarshi se uban shinning takeyi, kusan mai kwalba daya yake shafewa a kwana biyu kuma me gurguwa yake shafawa, be murzawa sosai dukse fuskar tasa tayi yellow yellow gemunsa kuwa ya mayar dashi brown color, se murmushi yakewa hajiya Maryam, ita ko tasha kuka zeyi. "Meya faru zakayi kuka kuma? Mutuwa aka maka?'' Hajiya maryam ta tambayi dan Ustaz yynda dariya ke shirin subuce mata, Sbda shigar ta dan ustaz da ynyin siffarsa. Kara washe baki dan ustaz yayi yace "lah! Lah! Ana latagadab! Wato ainifin ni bana fushi hajiya, wato ainifin ma'aiki s.a.w ya mana natsiha da mu yawaita murmushi, to Murmushi nakeyi hajiya..." Ya karashe mgnr yana jawo gemun shi nan da nan kuwa hannunshi ya dauke da maikon dake gemun nasa. Hajiya maryam ta girgiza kai ashe Murmushi yakeyi ita wlhy tasha kuka ma yakeyi ko yake shirin yi. "ALLAH ya KYAUTAR..." Hajiyar maryam ta fadi hadi da juyawa ta nufa packing space dan ustaz ya biyota yana fadin "Wato ainifin Hajiya nace anguwa zakije ne? Ainifin ni zan jaki ko zaki tafi da kanki ne?" "Da kaina zanja kaina..." A takaice Hajiya maryam ta bawa dan ustaz amsa. Watsa hannu dan ustaz yayi ya dawo baya yana fadin "latagadab! Wato ainifin nace kada kiyi fishi hajjaju mutanen makka, ALLAH ya tsare hnya,...wato ainifin nace ko shagon saida kayan metahh yauma zaki je?" ya karashe mgnr
Da tambayar Hajiya maryam kai kace shi ya ajiyeta, bata bi ta knsa ta karasa ta shiga tamfatsetsiyar motarta wadda keya kyalli tana walwali, sbda wanki da tasha, tin 6;am me wanke mota ke wanke motocin gidan. Motar data shiga tanada kyau ainun kirar jeep ce amma tafi jeep kyau da tsaruwa, ta shiga taja motar ta iso bakin get me gadi ya bude mata get din gidan, ta fice da motar daga gidan dan ustaz se dago mata hannu yakeyi yana washe baki hadi da waqar larabci, ya dawo ya zauna kusa da baba me gadi suka cigaba da hirar da duk rabinta wa'azi ce dan ustaz ke masa.

Hajiya maryam bata tsaya da motarta a ko ina ba se a packing space din gidan Alhaji murtala wato alhaji babba. Fitowa tayi daga motar dai-dai 10:47am ma'aikatan gidan suka hau jero mata gaisuwa wasu sun santa wasu kuma basu santaba tsoffin ma'aimatan gidan duk sun santa wato wadanda ke musu aiki tin suna katsina,. Amsawa tayi ba yabo ba fallasa ta fara takawa a cikin gidan da jagoran daya daga ma'aikatan da suka santa zuwa bangaren hajiya babbah, wato matar Alhaji ta farko. Tini ta tashi a falo ta sameta suka gaisa a mutumce, sauran matan ma dasukaji zuwanta duk sukaxo suka miko gaisuwa aka cika mata gabanta da kayan motsa baki sam Hajiya maryam ta gaza sa komi a bakinta, abinda ke zuciarta shi kawai takeso ta aiwatar ko zata samu salama. "Alhaji ya tashi kuwa?'' Hajiya maryam tayi tambayar da hajiya babba. Dattijuwar matar tace "Bansani ba de..bari a tambayi zainab muji.." Ta karashe mgnr kwayar idonta na kn Hajiya zee wadda keta faman taunar ciwgum, kmr zata taune haqoranta Sbda hajiya Maryam ta iya amsawa da mutumci. " ya tashi, yanata shirin zuwa masallaci ne..." Hajiya maryam ta zubawa zee ido wadda ke mgna tana yatsinar baki, a hkma wai a mutumce ta amsa. Hajiya babba ta kalli hajiya maryam tace "To knji ummu AB'ILAL ya tashi, na manta ma yau Friday knsan 12:30pm yake zuwa masallacin jumna'arh..." Hajiya maryam tace "okay toh bari in ganshi..." Tayi mgnr hadi da mikewa. "Toh a fito lafia..." Cewar hajiya babbah. hajiya zee ta tashi itama tabi bayan hajiya Maryam ita ta mata iso zuwa falon Alhaji babbah dayake bata taba zuwa gidanba se yau. Da sallahma ta shigo falon...Alhaji babbah na zaune kan kujerar zallar royal din dake falon 3ct sanye yake da danyar gezner me mugu mugun kyau, kalarta kalar blue ce light me kyau, hadda babbar riga, hannunshi riqe da counter yanata lazimi yayinda zallar hular zanna bukar take gefensa, karatun alqur'ani ne ke tashi a falon kasa kasa cikin natsuwa. "Wa'alaykumussalam..." Ya amsa sallahmar hajiya Maryam domin zee batayi ma sallamar ba. Ya dago ya zubawa maryam ido, zuciarsa ta cika da mamakin wai yau maryam ce a gidansa, ko gizau take masa, " tabbas yau take jumma'ah ga maryama a gidana..." Cewar Alhaji babba da mamakinsa ya gaza boyuwa. Karasowa hajiya maryam tayi ta zauna a kan kujerar dake kusa da alhaji 1ct zee ta karasa ta zauna gefen Alhajin. "Barkanku da safiya alhaji babba..." Cewar Hajiya maryam data dan rissina. Fara'arh dake kan fuskar Alhaji ta kara bayyana, farin ciki fal ranshi ya amsa da "Barka ka de maryamu matar muhammadu kuma uwar muhammad..." Murmushi kawai Hajiya maryam tayi. Alhaji babba shima yy murmushi yana me gyara siririn glashin dake kwayar idonsa ya zubawa Hajiya maryam , wadda ke sanye da siririn glashinta itama, shi dij take kallo. "Kai yau ba banzaba hajiya kikaxo gidana ... Da walakin wai goro cikin miya..." Wani irin shimfidadden kayataccen Murmushi hajiya maryam ta sakarwa alhaji babba wanda be taba ganin irinsa ba se yau, dan hk ya kara tabbatar da cewa da walakin din goro cikin miya. A natse ta fara mgna "Haka ne kam Alhaji...akwai muhimmiyar mgna da nake tafe da ita, insha ALLAH...kuma alheri ce..." Alhaji babba ya washe baki yana me gyara babbar rigar dake jikinsa yace "Alhamdulillahi ! To bismillah ina jinki..." Hajiya maryam ta kalli zee da tayi kasak'e tanaso taji gulma. Hajiya maryam ta hade rai tace ''ke dan bamu guri..." Mikewa hajiya zee tayi ta fice a falon alhaji babba ya kalli hajiya maryam yace "Ai dakin batta karamar yarinya ce batasan komi ba..." A zucia hajiya maryam tace "amma tasan namiji kou..." Amma a fili tace "A gaskia Alhaji abinda kakeyi baka kyautawa wlhy baxan fasa gaya maka ba, yaza ayi ka auro yarinya karama sa'arh kananan yaranka, ai dole ma ta raina sauran matanka..." A hasale Amihh tayi mgnr. Alhaji babbah ya washe baki yace "maryama, maryama kenan, Ai addinina be hanani auren taba..." Hajiya maryam ta amshe da ''dukda hk amma ai ana barin halak dan kunya ...." Alhaji yayi yar daria yace "Well, bazaki ganeba...ynzu de meke tafe dake..." Fara'arh Hajiya maryam data gushe ta dawo sabuwa a kn fuskarta, ta zuge bag dinta ta ciro kudade kimanin 500k yan dubu dubu ta ajiye a gaban table din Alhaji murtala, yabi kudin da kallo yan 1k 1k ne bandir bandir biyar wato dubu dari biyar, ya kalli kudin ya kalli maryam fuakatshi dauke da neman karin bayani yace " Wannan kudin na menene maryamu?"kara gyara glashin dake idanuwanta tayi ta gyara zamanta sosai fara'arh dake kn fuskarta ta yawaita tamkar gonar audiga ta kalli kudin kana ta dawo ta kalli Alhaji babbah tace "So nakeyi yau bayan an sallami sallarh jumma'arh a daura Auren Muhammad AB'ILAL da hilwah Muhammad AB'ILAL......"


*for more information...08136349646*


Gumbar madara 😋
Gumbar kankana
Gumbar Alkama
Gumbar gero
Gumbar ridi
Gumbar hatsi
Gumbar gyada
Gumbar Ayah
Gumbar me rubutun mallaka.


Tsumin tabaje
Tsumin baure
Tsumin kankana
Tsumin kwakwa
Tsumin zam-zam
Tsumin rubutu
Tsumin al'ajabu

Ingantaccen maganin infection sadidan insha ALLAH.

Ingantaccen matsi, mesa dadin gaba ga me gida, da maganin gyaran nono, maganin sa kiba, da maganin rage tumbi, maganin kara hips available.

Turaren mallala E.T.C humrar mallaka...

Masu bukatar hadin *yar gatah* komi da komi za asa a ciki na NA MALLAKA dana mgnin infection 20K 30K 40k 50k 70k 80k 90k 100k iya kudinki iya yadda zakiyi shagalinki . MATA KU TASHI KUYI GYARA SABODA MASU GIDA MAGUNGUNANMU masu inganci ne Da kyau sayen na gari maida kudi gida . 08136349646.pls karki dauki lmbata ki dameni in baki shiryaba plx.
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: *YAR DANDI CEH...* 🅿️20
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽

Alhaji babba kanshi ya kara kullewa, jin tace hilwah Muhammad AB'ILAL, to ina kuma suka samu hilwah a danginsu? Gaf Hajiya maryam ta kara kwance masa tunani, ya kureta da ido, yayinda take kara tabbatar masa da abnda ta fada a kan fuskarta. "Me kike nufi? Waye kuma hilwah ko gilwah AB'ILAL Muhammad?" "Ita ce wadda nkeso a daura Auren nata da AB'ILAL a yau..." Hajiya maryam ta fadi fuska babu alamar wasa. Alhaji murtala ya bita da ido, yasan halin maryam kaifi daya ce, sannan bata taba zuwa masa da mgna me girma ba kmr ta yau. "Da amincewar shi na ta'alah za ayi auren ko yayane?'' Alhaji murtala ya jefowa hajiya maryam tambayar. "Dukkaninsu ban nemi amincewarsu ba, ni naga hakan ya dace, kuma na bukata dan ALLAH Alhaji karka zurfafa bincike, ni nasan me na hango kawai a daura auren..." A wannan karon da sanyin murya tayi mgnar. Alhaji babba ya sauke ajiyar zucia shi be taba ganin inda akayi haka ba. "Kina nufin ita ma macen bata amince ba? Ta yaya hkn ze yu, aure babu amincewar mace balle amincewar namiji?'' Cewar alhaji murtala. Hajiya maryam tace "Wannan duk ba dmwa bane, zasu amincewa junansu daga baya, dan Allah alhaji karka kara cewa komi plx! Ni nasan insha ALLAH akwai alheri..." Alhaji murtala ya sauke ajiyar zucia beda yadda zeyi da maryam in taso abu kawai ayi shine kwanciar hnkli. "Shikenan Allah yasa hkn ne Alheri..." Cewar Alhaji murtala, hajiya Maryam taji wani irin mugun dadih ya ratsata seda tayi yar Dariya tace "Ameen...alhaji kai nakeso ka zama waliyinta in yaso se a nad'a wani a matsayin waliyin Shi yaron naku..." Alhaji murtala ya jinjina kai yana me nazarin maganganun hajiya maryam. Knshi ya kara kullewa a karo na biyu yace "ita yarinyar bata da iyaye ne?" hajiya maryam tace "tana dasu .." Alhaji murtala yace ''suna ina ?'' Hajiya Maryam ta amshe da "gani nan ni ce uwarta ni ce ubanta..." Alhaji murtala ya zaro ido zucia fal mamaki, gani yakeyi kmr de hajiya maryam bata hayyacinta a yau. Ya bude baki zeyi mgna,ta katseshi "Dan ALLAH alhaji kar kace komi plx, kasan bazan kawo abinda ze cuci danku ba, a wannan fannin zamu hada sunnah ne kuma zamu samu lada insha Allah...plx kar kayi musu dan ALLAH..." Alhaji murtala yayi shiru kawai dukda bakinshi na cike da maganganu, Amma ya danne. "ALLAH ya sa muce kwara da Akayi..." Cewar alhaji murtala. "Ameen..." Amihh ta amsa da farin ciki a ranta. "Wannan kudi naki ki kwashe su, hajiya maryam, ai mune mukeda alhakin biyawa yaronnam sadaki bake ba ..." Cewar Alhaji murtala. Sosai hajiya maryam taji ddh, ta masa godia ta kwashe kudinta tasa a bag, alhaji Murtala ya mike ganin lokaci ya tafi yama hajiya maryam sallahma ya fice a gidan ya nufa masallaci, hajiya maryam ta dawo side din hajiya babba dan tace baxata tafi ba harse alhaji ya dawo taji meke tafita, nan ta zauna sunata hira da hajiya babba...


A babban masallacin santan brllow dake anguwar sarki. bayan an kammala sallar jumma'arh aka daura auren AB'ILAL da hilwah a kan sadaki nera dubu dari uku. 1m alhaji babba yaso bayarwa a matsayin sadakin auren, abokinsa yace masa ai ba sadaki me yawa ba, albarkar auren ake nema. Zucial fal farin cikin da alhaji babba besan dalilinsa ba ya dawo gidan, yasa zee ta kirawo masa hajiya maryam, taje ta sameta ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login