Showing 150001 words to 153000 words out of 306755 words
Chapter 51 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt
masa car key dake hannuta tace "bnsn hauka wuce muje, magajin gari..." Tana fadar hkn ne tana tafia, da wasu files a hannunta dayawa, ta nufa motarta dan Ustaz ya tashi daga tsugunnen ya biyota a guje yana gudun yana faduwa yana tashi sbda tsantsin takalmin dake kafarsa Kafin ya karaso yayi faduwa tafi goma amma kuma yana tashi, ya karaso ya nufa dreva seat ya shiga hajiya maryam kam tini ta dade a cikin motar a gidan gaba, dan Ustaz yaja motar suka fice a gidan....
Koda salwah ta karasa dakin kwance ta samu hilwah a kasan carpet din tini ma bacci ya dauketa, se sauke ajiyar zucia takeyi dagani a wahalce take ajiyar zuciar. ajiye mata mgnin salwah tayi ta dauko duvet din dake kan bed din, ta lullubeta dashi, ajiyar zucia hilwah ta sauke ta kara kudindinewa a cikin duvet din tana me kara sauke ajiyar zucia, hadi da shashsheka. Salwah ta tsaya ta zuba ma fuskar hilwah ido, kasancewar bata lullube fuskar tata ba. Zucia cike da tausan hilwah salwah ta ta tsugunna ta dauki trea din data kawowa hilwah breakfast din ta juya ta fice a dakin, ta nufa side din Amihh, direct kiching ta nufa dan hada abincin rana sbda yau zataje scul tanada lecture 2:am, kiching din ta isa ita da Ma'aikatan gidan suka shiga hidimar abincin ranar....
A bangaren AB'ILAL Be samu bacci ba kwata kwata sede ya gaji da juyi ya tashi dan knsa wuraren 10:30am ya sauko daga kn bed din , yana me jin knsa na juya masa na rashin baccin da beyi ba, fadawa bathroom yayi, seda ya kwashe 1h a bathroom yana wanka, kana ya fito bayan ya dauro alwala, ya goge jikinsa sosai, kana ya shafa kyakyawan lotion dinsa ya shirya cikin danyar shadda mint color dinkin kaftani, dinkin ya matukar amarshi ainun, kasancewar yau juma'arh ce shirin zuwa masallacin yakeyi. ya feshe ko ina da ko ina na jikinsa da perfume , ya dauki hula ya kafa wadda ta dace da tsarin shaddar dake jikinsa, fuskarnan tasa ta fito das, sajensa ya kwanta luf se shining yakeyi yana walwali, ya hadu iya haduwa! Nan take ya fito a zallar asalinsa na me kyau, kallo daya zaka masa ka fahimci cewa shi din ruwa biyu ne Wato de ba zallar nigeria bane shi, sbda kyaun nasa ya shahara, ya fito sosai zanensa ya zanu tako ina cif cif das das, shu'umin kyau garesa hadi da makirin kyau tako ina ya cika taf, yanada cikar haiba, kyaunshi na bugawa ne a mujallah , ya hadu iya haduwa, ko a indian film ban taba ganin me kyaunshi ba. dauko makirin watch dinsa yayi ya daura a tsintsiyar hannunsa, ya kara fashe jikinsa da turarensa, ya zira takalminsa me mugun tsada, ya kara fashe jikinsa da perfume dinsa, again and again sbda shi din ma'abocin kamshi blne, baya gajia da kamshi. ya dauki counter dinsa dake kn mirorr da car key ya fito falon se zuba kamshi yakeyi, dai dai agogon bangon falon ya buga karfe shabiyun rana dai-dai. tsayawa yayi ya zubawa inda ya bar yarinyar dazu tana kuka da ido , kawai se yaji jikinsa ya masa wani iri se hasko yarinyar yakeyi a durkushe a gun, rintse kwayar idonsa yayi na wasu yan daqiqu kana ya budesu jiki a sanyaye ya juya ya fice a Falon, fitowa compound yayi, yana takunsa na isa tamkar dawisu ma'aikatan gidan nata miko masa gaisuwa amma sam be bi ta knsu ba, tafiyarsa kawai yaci gaba dayi, shaddar nan tasa se faman walwali takeyi tana daukar kwayar idon me kallo. Direct ya nufa packing space karasawa yayi cikin gareji ya fito da motar daya sewa hilwah daman key dinta ne a hannunsa, yasa me wankin mota ya wanke masa ita yana daga nan zaune a kn wata kyakyawar kujera ta hutawa dan Ustaz ne ya dauko masa kujerar ganin da yana tsaye. yana daga zaunen yana danna wayarsa har aka gama wanke motar aka gogeta dmn batayi wani datti ba sbda ko a garejin an lullubeta da rigar mota. shiga motar AB'ILAL yayi ya figeta ya fice a gidan ya nufa babban masallacin santan bello, daman a nan yake juma'arh inhar yana nan kaduna....bayan sun idar da sallarh ya fito suka hadu da Alhaji babba, kasancewar shima a nan masallacin yake sallarh juma'arh. Karasawa AB'ILAL yayi ya gaidashi dukda haushinshi yakeji sbda yasan hadda sa hannunshi a auren da Amihh ta masa, bayan sun gaisa Alhaji Murtala ke tambayar AB'ILAL ya iyalin tasa, AB'ILAL yayi kmr be gane me yake cewa ba, ya canza akalar hirar zuwa ga tambayarshi yaushe ze koma kasar USA sbda a can ake duba masa lafiar jikinsa..'' Alhaji babba yace yana tunanin se Nan da 2 month ab'ilal ya jinjina kai kawai dmn ya kawo mgnr ne dan ya canza akalar bnzar tambayar da alhaji babba ya masa. Daga bisani yama Alhajin sallamah ya nufa motarshi ya shiga yaja ya bar masallacin , shima Alhaji babba ya shiga tashi motar dreva yajashii subaka bar masallacin. Ab'ilal na isowa gidan direct side din Amihh ya nufa dan samawa knsa abinda zeci, yana shiga dai-dai salwah na riqe da trea tana shirin barin side din zuwa side din AB'ILAL din domin ta kaiwa hilwah abincin rana. AB'ILAL Yayi kmr ma be gnta ba. ta gaidashi yaki amsawa kawai ya nufa dinning ya zauna, salwah na nan tsaye tsakiyar falon kmr an dasata, ta daga kafa da kyar ta fara tafiya da niyar ta fice a falon, ta tsinkayi muryar AB'ILAL na cewa "Ke zo kiyi serving dina...'' Jiki na rawa Salwah tace to ta dawo ta ajiye trea din dake dauke da abincin hilwah a kn dinning table din, ta fara bubbudewa AB'ILAL kulolin dake kan table din, abinci Kala biyar ne amma AB'ILAL yace duk basu masa ba. Ya umurce salwah data shiga kiching ynzu ta dafa masa tuwan shinkafa miyar kubewa danya. Takaici kmr ze kashe salwah gashi tanaso ta kaiwa hilwah abincinta a hk ma tasan ta batta da yunwa, gashi tanaso taje scul tanada lecture 2:am gashi ynzu ma 2:am din ta kusa befi 15mnt ba 2:am din tayi. Zucia babu ddh kuma ba damar ta nuna ta juya da niyar ta shiga kiching yace ta fara hado masa coffee tace toh kawai ta juya ta nufa kiching din, a gaggauce salwah ta hado masa coffee din ta kawo masa yanata aikin shafar wayarsa kirar Samsung, ta ajiye masa ta shiga kiching din ta fara kokarin daura masa tuwan xucia babu dadih, tasan de yau tayi missn lecture dinta. Se faman jin haushi takeyi tana aikin tuwon ma'aikatan gidan suka temaka mata gun hada masa tuwon, ta samu ta gama takai masa taga ko coffee dinma besha ba, se faman shafar wayarsa yake har lokacin, ta zauna tana jiran sadda ze gama yace tayi serving dinsa tasan bata isa ba ta bar falon batayi serving dinsa ba. Seda ya mula ya mulmule kana yace tayi serving dinsa, tana gama serving din nasa AB'ILAL ya fara cin tuwon a yangance Salwah nata satar kallonsa se yatsina fuska yakeyi, ya dauki cup din coffee din ya Kai bakinsa yaji ba ddh sbda sanyin da yy, ya kalli salwah yace taje ta kara hado masa wani, Jiki na rawa Salwah ta juya ta koma kiching din ta kara hado masa wani coffee din, ya amsa ya fara sha, ya kalleta yace taje ta masa farfesun kayan ciki yanzunnan..a zucia salwah tace ta shiga uku, kana ta juya ta nufa kiching ta shiga aikin hada masa farfesun Hilwah ce kawai a ranta tasan yunwa nacan tana kwakularta, mkrntarta ta yau kam tini ta hkra da ita...
A bangaren hilwah Ba karamin jin dadin baccin tayi ba at the end, amma a fari baccin be mata ddh ba. se juyi kawai takeyi a tsakiyar carpet din, bata tashi ba se karfe daya saura. ta tashi tana miqar gajiya da ciwon jiki dake addabarta, ta sauke ajiyar zucia hadi da miqewa tsaye ta nufa toilet a daddafe mazaunanta se ciwo suke mata sbda kwanan zaunen datayi se yanzu abun ke tambayarta. Wanka ta karayi da ruwan dumi sosai ta sake gasa jikinta, ta fito daure da alwala azahar kirjinta daure da bathrobe peach , ta karaso bakin mirror ta shafa versiline shi take shafawa dukda ga wasu creams sunfi kala ashirin amma bata shafasu sbda babu wanda take using a ciki shiyasa take shafa normal verselin kawai. Shiryawa tayi cikin wata riga dark green me stone a saman wuyanta sosai rigar ta dameta daf tako ina ta cika taf taf, kasannan nata kmr ze fashe a cikn rigar dake jikinta, ta feshe jikinta da turarrukan dake gaban mirror din wanda sukafi Kala hamsin, duk abinda takeyi cikin dauria takeyi amma batajin ddhn jikinta, side din inda ya maretanma ya kumbura. karasa tayi ta nufa inda aka tanada danyin sallah, ta zumbula hijjabi ta tada sallarh azahar din, tanajin knta na mata nauyi. A daddafe ta samu ta gama sallarh ta cire hijjabin jikinta ta shiga aikin gyaran dakin, tana gyaran taga mgnin da Salwah ta ajiye mata Ta dauka ta ajiyeshi a bedside, Da kyar take iya gyaran tanayi tana hutawa harta gama ta fito falon ta shiga gyaransa sbda gudun karta kara masa lefin daze Kai hannunsa jikinta, tasan in batayi aikinba ta shiga uku kila ma ya mata rashin mutumcin Dayafi na jiya daya mata ya barta waje ta kwana kuma ya hada mata da mari, a gaggauce ta gyara falon, ta nufa dakunan ta musu mopping kawai sbda basuyi datti ba, duk gyaran datakeyi bata sauri sbda rashin kwarewa. ta nufa saman ta Upstairs din ta gyarashi, kana ta dawo kasan, ta tsaya bakin kofar dakinsa so takeyi ta shiga domin ta gyara masa kmr yadda ya umurceta, Amma tana tsoron kar azo yana ciki harga ALLAH mugun tsoronsa takeji, data gnsa se gabanta ya yanke ya fadi, kmr yadda takejin tsoron mutuwarta hk take tsoronshi, jingina bayanta tayi da kofar dakin, tanajin zuciarta na fat fat, tunani tunani zuciar tata ta shiga yi, a ynzu tsoronshi takeji sosai abnda ya mata jia ya kara firgitata, tashi tayi daga jikin kofar data jingina, ta Kai hannu ta bude handle din dakin kmr zata bude se kuma ta fasa, ta fara sallahma a kofar dakin, seda tayi sallahma biyu uku kana ta bude Handle din dakin a hnkli zucia fal fargaba ta bude kofar dakin knta na kasa da sallama a bakinta ta shigo dakin, duk a tsorace take knta ma kasa tayi dashi ss kmr a ce arr ta arta a guje hk takejin ranta, bayan ta shigo dakin ta kasa rufe kofar taja ta tsaya still hannunta na riqe da murfin kofar, Sanyin Ac hadi da kamshin turarensa suka shiga ratsata ba krmin ddh kamshin dakin ya mata ba, seda ta lumshe kwayar idonta ta budesu a kasan tiles din dakin, hatta da tiles din dakin special one ne, dago kwayar idonta tayi ta zubawa kan bed din dakin ido, ajiyar zucia ta sauke me tattare da natsuwa, dagani be dakin, ganin bathrobe din da ya cire da yayi wanka tayi a kasan dakin dagani wanka yayi ya fita, ko ina a dan hargitse ranar nan batawa dakin kallon tsaf ba se yanzu ne ta samu damar yima dakin kallon tsaf, komi na dakin perfect ne, kmr yadda me dakin yake perfect, tsarin dakin ya hadu iya haduwa, adon furnitures dinsa royal blue ne, komi de acan acan, hatta da AC dake dakin daban ce, zubawa AC dake dakin ido tayi, nan ta shiga wani tunanin da ban, lumshe kwayar idonta tayi ta budesu a kn Bedside dinsa na left, ta sauke ajiyar zucia ta zubawa dankareren agogonsa dake kn bedside din ido, ajiyar zucia ta sauke a gaggauce ta shiga aikin gyara dakin da sauri sauri gudun kada yazo ya taddata, a dakin, ta nufa bathroom dinsa ta wanke masa ko ina daman ko ina tsaf yake, dukda kuwa ba a gyarawa inba ita ta gyaranba, ya dakatar da duk ma'aikatan dake aikin side dinsa sbda ga me Aiki ya samu a cewarsa. Tayi shara tayi mopping da sinadarai masu kamshi, duk bata iya ayyukunnan ba a rayuwarta a sanadiar zamanta a side dinsa gashi ta iya dolen dole. Tana gamawa ta fice a dakin taja ta rufe se uban haki takeyi ga yunwa na cinta ga gajiya again ga rashin jin ddhn jikinta da batayi, kuma ga azababben zazzabi datakeji yana zuwar mata har cikin kwayar idonta duk sanadin saurayen dasuka cijeta ne. Fitowarta daga dakin tana shirin nufar kofar dakinta salwah ta turo kofar falon ta shigo hannunta rike da trea, se ynxu ne ta samu ta samu knta daga hannun muguncan wuraren 4:2pm ake nema ynzu. salwah ta bi hilwah da ido ganin kmr daga dakin yah AB'ILAL ta fito, taja ta tsaya ta dakata ma daga shigowa tsakiyar falon, ta zuba mata ido sosai kwayar idonta dauke da alamar tambaya, hilwah ma idon ta zuba mata. Salwah ta juya bayanta ta kalli bakin kofa, gudun kada AB'ILAL ya shigo sbda ta barshi falon Amihh ya gama ma cin abincin ya koma ma falo ya zauna yanata aikin iyayi. Cikin hanzari salwah ta karaso ta kamo hannun hilwah suka karasa bedroom din Salwah, a kasan carpet suka yada zango. Salwah ta ajiye trea din hannunta a tsakiyarsu ta zubawa hilwah ido fuskarta dauke da tambayiyi a kn ganinta datayi a jikin kofar dakin AB'ILAL dagani ko ba a gaya mata ba tasan daga dakinsa hilwah ta fito. hilwah tayi kasa da knta tana wasa da zoben gold din dake hannunta na hagu a yatsanta wanda dagashi se karamin yatsa, Amihh ce tasa Mata zoben. nan take salwah taga kurajen cizon sauran har a hannayen hilwah a hk ma duk sun rarrage dande ma abinka da farin mutum ne, mamaki ya cika zuciar salwah takai hannu kan hannun Salwah ta shiga shafar hannun hilwah mamaki ya kara rufeta tambayar dake ranta ta gushe. "me rabin suna wai wannan wani irin sauro ne ya cijeki haka?" Ta karashe mgnr kwayar idonta na isa ga wuyan hilwah, nanma ta kara ganin jajayen kurajen cizon sauron. "Wannan wani irin sauro ne ya cike ki plx? Sekace kn kwana a waje..." Ta girgiza mata kai Kawai. Salwah taja tsukin da batasanma tajashi ba halin hilwah yana mugun kular da ita yana bata mata rai sosai. "Kuma wai se kkje dakinsa yau, wai memaya kaiki dakin yah AB'ILAL din? Ya dakeki jia amma yau kin koma dakinsa, salan yazo ya sameki ya miki rashin mutumci,..har ynzu ma bakisan halin yah Ab'ilal bane, beda mutumci wlhy, ni Shiyasa tin a farko bnso hadinku dashi ba wlhy,da Amihh tayi shawara dani da ban yadda ta hadaki da yah AB'ILAL ba beda kirki, ga mugun hali, se mugunta fal ran,.." Ringing din wayarta ya hanata karasa abinda tayi niya. Zaro wayar tayi daga aljihun doguwar rigar dake jikinta, taga number Amihh ta bayyana a kn wayarta da sunanta baro baro wato Auwal Hubb, jiki na rawa ta daga wayar ta kara a kunne, ta masa sallahma cikin ladabi.
*ba editing....ayi hkri...*
*littafinnan na kudi ne...08136349646*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 35***
Daga cikin wayar Amihh tace "Wa'alaykumussalam,...ya kuke? ina hilwah? Hope kn kai mata abincin safe da rana kou?'' Salwah ta amsa da"Eh Amihh na kai mata gani ma a kusa da ita..." Daga cikin wayar Hajiya maryam tace "ok bata wayar...'' Salwah ta mikawa hilwah wayar ta miko hannu ta amsa ta kara a kunnenta cikin sanyin murya tawa Amihh sallama ta cikin wayar. Jin muryar tata ta isarwa da Amihh cewa wani abu na damunta, ko yayane, batare data amsa sallamar tata ba ta shiga aikin tambayarta "meke damunki sweetheart? Naji muryarki very cool? Kinci abinci Kou?'' Hilwah tace "um naci..." Amihh tace "to meke damunki? Kin karamin mgna da cooling voice dinki, meke damunki plx gayamin knji my baby?'' Hilwah ta girgizawa Amihh kai kmr tana gabanta, kana tace "ba komi Amihh..." Badan hajiya maryam ta yarda ba 100% tace "ok are you sure?'' Hilwah ta amsa mata da ''yeah Amihh....yau baki dawo aiki da wuri ba Amihh?'' Ta karashe mgnr hadi da tambayarta cike da kulawa. Amihh tace "Eh wlhy, bama zan samu dawowa ba, inajin har monday ma Ynzu hk ina hanyar zuwa abuja ne, insha Allah..." Hilwah tayi narai narai da fuska kmr zatayi kuka tace "amihh kin tafi banganki ba?'' Hajia maryam taji dadin kalamin hilwah gareta tayi murmushi kana tace "Nima tafiar dole ta kamani munada meeting a can ne gobe Saturday da rnr monday ma, da wuya ma na dawo rnr monday,..ku kula da knku plx, a ci abinci sosai, knji kou?'' Hilwah tace "toh Amihh take care 2 Allah ya tsareki...'' Hajiya maryam ta amsa da "Ameen cikin jin ddh...kana ta kara da cewa "ina me gidanki?" Hilwah tayi jim Abinda AB'ILAL ya mata ya fado mata rai, ajiyar zucia ta sauke kana tace "lafia lau Amihh,,," Hajiya maryam ta danji ddhn yadda yarinyar ta amsata seda tayi murmushi kana tace "be miki komi ba kou?'' Hilwah tayi jim kana tace ''bemin komi ba Amihh...'' Hajiya maryam tayi shiru tana nazarin yadda hilwah ta amsa mata kana tace "kin tabbatar?'' Hilwah ta daga mata Kai hadi da cewa "A Amihh narh..." Hajiya maryam tayi murmushi sbda jin ddhn sunan data kirayeta dashi, tace "baku bukatar komi kou?'' Hilwah tace "A..." Hajiya