Showing 177001 words to 180000 words out of 306755 words

Chapter 60 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

dataji ta shigeta amma bata damu ba duk rakinta batayi ko gezauba sede ta ribtse ido ta ta bude su a knsa ta zuba masa sexy eyes dinta dasuka koma red red shima idon ya zuba mata fuskar nan tasa babu ni'ima balle annuri kmr be taba daria ba. Faduwar plate din kmr a ransa yajita kuma yaga sadda ta dauke kafarta dagani plate din ya caketa a kafar sbda ganin ta rintse idonta gam na wasu yan dakiku ta bude, wani iri yaji a ransa amma ya basar ya wani kara shan mur matsifa na cin inside dinsa, daman shifa normally jarababbe ne yace "Ke! Na ajiye wasu takaddu ina kika kaimin su?'' Hilwah da har ynzu jikinta ke rawa, mgnrsa kuma ta karasa jikin nata daukar wani rawan tace "banganshi ba..." Cikin sanyin muryarta hadi da karyayyen harshenta tayi mgnr. AB'ILAL dake satar kare mata kallo doguwar rigar material ce a jikinta free amma kuma seda ta bayya ne kirar jikinta kan nononta ya fito radau dashi nan yafi kallo amma a sace ya kara hade rai kmr ba kn nononta yake kallo ba kana yace "inba keba uban wake shigar min room ko nida wani ne a side din...., ke look kinajina kou? banason isknci wuce muje ki nemomin takadduna, ko kina nufin bake kk kyara dakinnan ba yau?'' Ya karashe mgnr hadi da kara tsare gida, fuskarnan tasa kmr zata kama da wuta, sbda hadewa . Hilwah da kafarta ke mata zafi duk tabi ta kara gigicewa again kuma gashi yanata kara gigitata Da maganganunsa, ko kallonta yy seta firgita sbda babu ni'ima a kn fuskarsa kmr ba musulmi ba, ta gaza mgna sbda tsoronsa dake ranta. "Ke bada ke nake mgna ba!'' Ya daka mata tsawa ganin bata amsashi ba, firgigit tayi ta matsa ta kara taka kwalbar plate din da kafarta ta damar again duk ta gigice ne batasanma ta takan ba, ta matsa jiki na rawa hadi da rintse ido ta fasa ihu "Wayyo Momy!" Ta fadi hawaye na gangaro wa daga kwayar idonta, taji azaba sosai. Harga zuciarsa yaji ihun nata amma ya basar ya sauke kwayar idonsa a kasan kafarta yaga tana jini ya dauke kwayar idonsa cikin hanzari ganin tausanta na neman darsar masa. "Ke! Banfa da lokacin iskncinki nan ba gidan karuwai bane, ya ina miki mgna 2tyms kinyi bnza dani, na gaya miki bana mgna biyu kinajina kou? Mgnata ta biyo duka ce knji na gaya miki, Ni ba dan iska bane, ki wuce muje ki nemo min takadduna ki bani tin ban miki dukan dase na lahira yafiki jin dadih ba, kadan daga aykina in kakkaryaki a gidannan,..... kizo ki nemo min takadduna tin muna only me and you....." Yana gama fadar hkn ya juya ya fice a kiching din cikin hanzari. jikinta ya kara daukar rawa ta tsugunna ta cire kwalebanin dasuka makale mata kafa tana kuka, jini ya kara ballewa ya hau zubo mata daga inda ta cire kwale banin, gudun kada yazo ya sameta a kiching din yasata mikewa jinin na fita a kafar tata ta dama, ta fice a kiching din da kafarta ta hagu take takawa har ta iso bakin bedroom din nasa ta tura kofa ta shigo bakinta dauke da sallama se uban hawaye takeyi na axabar da kafarta keyi mata, a tsaye ta semesa matsifa naci masa zucia daman daukar takaddun ne ya dawo dashi gidan, ya duba yaga be gnsu ba inda ya ajiyesu dunia ya tsani ya ajiye ko tsinke ne a canza masa gun zama, hkn na d'ugurzuma mssa zucia. "Ki nemo min takadduna knji na gaya miki, kuma ki biyani plate dina da kk fasa tinda bana gidan karuwai bane!'kuma bana gidan ubanki bane!'' Ya fadi da muryarsa ta wulaknci da cin mutumci hadi da tijara, da zallar ruwan matsifa. Jiki a sanyaye ta shiga bincika wurare a dakin tana d'ingishin kafarta da har ynzu take zubda jini, tabbas ta gyara dakin dazu amma bata ga wasu takaddu ba, inma ta gani ta manta inda ta ajiyesu sbda tunani tunani dasuka mata yawa a zucia. Duk iya dibawarta bata gnsu ba yana tsaye yana jira anata kiransa a waya ji yakeyi kmr ya rufeta da duka, dande kawai yakai zuciarsa nesa ne,dase ya kusan kakkaryata, ya juya ya fice a dakin yana jarabar da batasan me yake cewa ba, ba jimawa ya dawo dakin ya kalleta yace "Ina takadduna?'' Zuxia cike da fargabar meze mata Tayi shiru, zuciarta kmr zata fito fili. ya daka mata tsawa. ""Ina takadduna nace!!'' Murya da jiki na rawa tace "Bangani ba...."tana durkushe a kn kafafuwanta jikin bed dinsa, tayi mgnr. Hade rai ya karayi kmr ze ciji saman dakin dan jaraba yace "Wallahi kafin in dawo ki nemo min abuna, knji na gaya miki in ba hk ba wlhy sena miki dukan mutuwa...." Yana gama fadar hkn ya juya ya fice a dakin da gidanma gabaki daya jaraba na cinsa, ransa se tafarfasa yakeyi be tabbatar da raini ya shiga tsakaninsa da yarinyarnan ba se yau, amma ze saita mata hankali inhar ya dawo gidan bata ganin masa takaddunsa ba, da jaraba yaja motarshi ya fice a gidan. Bayan fitarsa dakin Juyawa tayi taci gaba da diba takaddun jiki na rawa tanayi tana kuka duk iya dubawanta bata gani ba, duk sani lungu da sako ta duba bata gani ba, hatta karkashin gadonsa ta duba babu, seda ta hargitse dakin duka bataga komi ba, ta maida dakin ta gyara da kyar kaf jikinta ciwo yake mata ga kafarta na ciwo jininma har ya gaji ya bar zuba daga kafarta, ta zauna ta huta tana hawaye a dakin bayan ta gama gyaran ko ina data bata, bata taba tsammanin zata fada irin wannan rayuwarba ko a mafarki a rayuwarta ba, amma gashi a zahiri ta afka a wannan rayuwar mara dadih me wuyar kai, tafijin dadin zaman gidan dandi a kn zama a gidan a side din AB'ILAL , taci kukanta sosai ta koshi taba uku lada ta tashi tana mejin kafarta tayi tsami dai-dai ana kiran sallarh magrib , ta nufa toilet ta dauko moper da bucket din mopping din duk inda ta bata da jinin kafarta ta gogeshi sosai, ta fice da bucket dn moper din tana dingishi ta nufa kiching ta share plate din data fasa, ta shaye gun tsaf kana ta nufa dakinta ta fada toilet ta dauro alwalar sallah, taxo ta dauki hijjabinta na sallah ta saka duk abinda takeyi da kafa daya take tafia ta gaxa taka kafarta daya. ta nufa dadduma ta tayar da sallarh la'asar ga magrib ta shigo, tana sallarh tana kuka sbda kafarta data ajiye a kasa sbda sallarh da takeyi zafi takeyi mata inta takata sosai, tana adduarh amihh ta shigo dakin, saurin goge hawayenta tayi ta saita knta ta shafa adduarhta ta juyo taga amihh zaune gefen bed din da gani dawowarta daga Aiki kenan, ta zubo mata ido, hilwah tayi kasa da knta, sbda idon da Amihh ta zubo mata. "Sannu da dawowa Amihhnarh ina wuni?'' Ta gaidata da muryarta data cika da kuka. A muryar tata Amihh ta fahimci wani abu, domin taki yadda taga kwayar idonta. "Lafia lau Sweetheart,..ya naji muryarki yayi sanyi sosai uhum my love? Taso ki karaso inda nake inji ya akayi uhum waya tabawa Amihh babynta...." Ta karashe mgnr zucia cike da zallarh soyayyar Hilwah, har ga jininta takejin yarinyar, tamkar ita ta haifota da jikinta.


















*littafin na kudi ne....08136349646*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 41***
Mikewa tayi ta Yunkura ta tashi tana mejin jikinta ya mata tsami sbda aikin data ci a dakin nasa dazu, ta manta ta taka kafarta tana fara takata taji wani irin zafi, dole ta daga kafar tata tana mejin zafi na ratsata, har tsakiyar kai, Amihh ta zubo mata ido, a hnkli ta fara taka kafarta cikin dauria Gudun kada Amihh ta gane tana ding'ishi amma ta gaza daurewa dole sede da dinkishin take tahowa.... "Subhanallahi ! Meyasa samu kafar ne?'' Cewar Amihh da tayi mgnr hadi da mikewa tsaye ta nufo inda hilwah take ta rungumota jikinta suka karasa bakin bed din ta zaunar da ita, tana cije cijen lebe sbda zafin kafarta data taka, amihh ta kara kureta da ido, hadda kara kure kan nononta da ido taga kaciar kan nonon ta kara fitowa radau da ita ta kumburo masha Allah farin ciki ya cika zuciar Amihh ita ga zatonta ko Sun sadu da juna ne(tasha an buga ne an kwashe...) "Sannu hilwah, kin shiga ruwan zafi de kou?'' Ta karashe mgnr hadi da rabawa gefen hilwah ta zauna , da ido Hilwah ta bita ita bata fahimci me take nufi ba. "Ruwan zafin me Amihh?'' Hilwah ta tambaya fuska dauke da rashin fahimta. Hajiya maryam dake kallon Hilwah tayi murmushi irin murmushinnan na nasan komi tace "bayan kun tare da mijinki nake nufi, baki shiga ruwan zafi ba?'' Amihh ta kara sa hilwah a duhu kawai tayi kasa da knta, Se amihh tasha ko kunya ce da gaske sun tare din a zuciarta tashiga adduarh ALLAH yasa ya zuba mata ruwa a saiti after 9month a haifo mata yan biyu. "Yau karkije dakin nasa, ki kwana a nan har ki warke seki koma dakin nasa, knsan maza iri iri ne wani inde ya kusanceka se kayi ciwo....'' Hilwah tabi amihh da ido se ynzu ta fara fahimtar kn tushen mgnr Amihh, kasa tayi da knta tace "Amihh bn kwana ba a dakin nasa ai,..." Hajiya maryam murna ta koma ciki tace "Kmrya? Kina nufin baki kwana dakin nasa ba? Shima bezo dakin naki ba?" Hilwah ta dagawa amihh kai alamar eh,... Wani irin kulluto ya tokarewa Amihh zucia tace "to meya sameki kike d'ingishi?ni ai nasha kin kwana ne dakinsa koshi yazo naki dakin harkun tare da junanku ashe ba hk bane...." Hilwah ta daga mata kai alamar eh kana tace "Plate ne ya fadi kasa ya cakarmin kafa dazu da ina wanke wanke,...'' Nan hnklin amihh ya tashi ta shiga tambayarta garin yaya hkn ta faru, hilwah tace tsautsayi ne,... Nan Amihh ta sauka kasa ta dago kafar tata ta dubata, ta fice a dakin tana fadin dole a miki allura, ta nufa side dinta ba jimawa ta dawo dakin hannunta riqe da srinji da ruwan allura, hnklin hilwah ya tashi ganin ruwan allura da srinji a hannun Amihh. "Amihh na warke plx..." Tayi mgnr hadi da marairaicewa Amihh tace "aah zaki warke dinde....ki tsaya in miki allurar karia ce daga kamuwa da cututtuka, kinga mara zafi zan miki ki tsaya kawai in miki..." Zucia cike da rashin jin som Allura ta tashi tsaye tana fadin "Aah amihh karkimin na warke..." Ta karashe mgnr hadi daja da baya Amihh ta biyota tana mata magia kn ta tsaya ta mata allurar har suka isa ga bango taki tsayawa. hilwah ta juyo ta kalli Amihh tana girgiza mata kai byn sun kai karshen bangon alamar batason alkurar, kuka ta saka ma Amihh hadi da cewa"ah'a karki min Amihh plx na warke, kafan ma ya bar min zafi, inda kkmin allura last time be warke ba, karkimin wata amihh..." Daganin yadda take mgnr zakasan a firgice take, Amihh dake kallonta da fuskar tausai tace "Ai baki mulmulawa ne inna miki dole kiji zafi sweetheart, ki tsaya in mik...." Kafin ta karasa mgnr aka turo kofar dakin aka shigo da karfi kmr da tsiya bako sallahma, ab'ilal ne , amihh ta juyu ta zuba masa ido hilwah ma idon ta zubo masa tanayin arba dashi jikinta ya hau rawar firgicin tsoronsa,.. Ya bude baki zeyi mgnarsa ta rashin mutumci ganin Amihh ya dajatar dashi, ya zuba musu ido ita da hilwar da kuma allura da sirinjin dake hannunta, hkn ya basa tabbacin allura zata mata.. "Wani irin isknci ne wannan kake budewa mutane kofa da karfi kmr an tunkud'oka ba sallahma kmr goyon hauka...." Amihh ta fadi cike dajin haushin yadda ya bankad'o kofar ya shigo. Juyawa yayi ya rufe kofar dakin ba tare dayace komi ba ya koma, yaso ace be samu Amihh ba dase ya mata dukan tsiya in bata fito masa da takaddunsa ba, shi yama fara tunanin boye masa takaddun nasa tayi da gangan, tsuki yaja kawai ya koma bedroom dinsa. Amihh taja kwafa bayan yaja kofar, ta juya ta samu ta lallaba hilwah da kyar ta tsaya aka mata allurar, ana gamawa ta kwanta a kn bed din tana me jin rashin ddn allurar , harda kuka tayi, ba wai dan taji zafin allurar Amihhn ba kawai de batason allurar ne, amma sam allurar amihh ba zafi, hajiya maryam ta kara duba mata kafar taga base ta mata komi ba ta fice a dakin hilwah na kallonta, ba jimawa ta dawo hannunta riqe da mgni da bottle water, ta Bali maganin, ta dago hilwah tasa mata a baki ta kora mata da ruwa ta hadiye ta koma ta kwanta tana mejin Kafar tata na mata zafi har lokacin, sbda famatan da tayi gun guje gujen tsoron Allura.. Amihh ta mata sannu kana ta dauki bag dinta ta fice a dakin direct bedroom din AB'ILAL din ta nufa, tana murda handle din kofar tajita a bude tasako kai bakinta dauke da sallahma, zaune ta sameshi a gefen bed dinsa ya rafka tagumi da 2hands ta shiga karewa dakin kallo ko ina tsaf tsaf se kamshi da sanyin AC ke tashi, dmn tin a falon gidan Amihh taji kamshi tasan aikin hilwah ne sbda ita ta bata turaren wutar tace ta rinka sa musu a side dinsu da dakin mijinta. AB'ILAL ya dago kwayar idonsa jin an bude masa kofar daki an shifo ya saukewa me shigowar kwayar idon nasa, nan yaga amihh ce, mikewa tsaye yy ta karaso ta zauna inda ya tashi, ya zauna a kasan dakin kusa da kafafuwan Amihhn. Hajiya maryam ta zuba masa ido a natse ta fara magana, wannan karon bada fada fada ba danta kula kmr fadan be masa, dan hk ta bullo ta lalama. "Wai meyasa bakabin umarnina ne Muhammad, me na maka har haka da kake sabawa umarnina? Muhammad nifa na dauki nauyin cikinka har na tsawon wata tara, anma ace abinda raina keso sam baka min, kullum kafi ganewa ka rinka batamin kana baqantamin kana kuntatamin, har wadda ma bani na haifeta ba amma take bin umarnina kaida na haifa ka gaza min abinda yarinyarnan keyimin ba fannin ladabi da biyayya, sbda bakasan darajata ba shiyasa bahaushe yace dana kowa ne, se kaga wanda ka haifa be girmamakaba se wanda baka haifa ba yaga mutumcinka ya girmamaka,...ynzu sbda Allah kana neman albarka a rayuwarka,? Karfa kasha bana ankare da duk abubuwan da kakeyiwa yarinyarnan , amma bani kake cuta ba, kanka kake cuta sbda duk wanda ya cuci wani yana ganin wanin ya cuta to to wallahi knshi ya cuta sbda Allah baya yafe haqqin wani a kn wani..." AB'ILAL yayi shiru yana sauraren Amihh shi ga zatonsa ko Hilwah ce ta gayawa amihh wani abu shiyasa tazo tana masa wadannan maganganun se yaji ya karajin kiyayyar yarinyar a zuciarsa , gani yakeyi kmr so takeyi Amihh ta tsine masa, shi ynzu yama fara gann kmr aikota akayi cikin rayuwarsa makiyansa sbda ta damula masa lissafi. "Me kuma nayi dan ALLAH amihh?''' Ya fadi hadi da dago kwayar idonsa ya kalli amihh girgiza kai tayi tace "komi kayi Allah na gani sbda ni bn gani kuma bn sani ba, amma majibancin lamuranmu yanajinka kuma yana ganinka, duk wanda ya gyara ya sani kuma duk wanda ya bata ya sani yarnan de amana ce na baka, inkaci amana , amana zata cika a lokacin da bakayi tsammani ba, kowa yayi na gari dan kansa,.. sannan mgnr hada daki da nace kuyi da yarinyarnan ba shawara na nema ba a gareka hukunci ne na yanke kuma hkn yake a addinin musulunci, kai ka tattara yanaka ya naka ka koma dakinta ko ita ta tattaro nata tarkacen ta dawo dakinka,..." AB'ILAL da tinda amihh ta fara mgnr ya dago yake kallonta sam tsarin data kawo masa be masa ba, duk wa'azin data masa ko daya be shigeshi ba inde a kn yarinyarnan ne be gane wani wa'azi ko wa'anzartarwa. "Gaskia Amihh bana da sha'awar hkn a kn yarinyarnan fa, karuwa ce ba mutuniar kwarai bace, bin maza fa takeyi amihh tabi wancan tabi wannan, kwata kwata bata da kamun kai, nifa bnda sha'awar na kwana daki daya da ita to muyi me?"' Hajiya maryam ta miko masa dakuwa tace "kuyi wan babanka!'' AB'ILAL dake kallonta ya kauda knsa gefe ganin zata fara antayo masa na katsinawa. "Ka tattara kayanka kawai ka koma dakinta yau yau dinnan, banason abinda zan maka baki shiyasa kake ganin inata binka da lalama, ina fatan mu rabu lafia...." Shiru yy yana nazarin abinda tace, idonsa na knta, Ganin da gaske takeyi waishi ya koma dakinta yasa AB'ILAL cewa "gaskia Amihh am sorry amma ni bazan iya komawa dakinta ba to inyi me? Wai Amihh to in bukatar namiji takeyi kawai in sauwaqe mata tinda dmn ni bani nace inaso ba ke kika aurota fa Amihh, knga inna sauqaqe mata se taje taci gaba da iskncinta ba shikenan ba? Kng bata da matsalar bukatuwa da d'ana namiji..." Hajiya maryam taji kmr ta watsa masa mari jin mgnr bnzar dake fitowa daga bakinsa."Dan dangin babanka ni kake gayawa zaka sauqaqe mata? Ka sauqaqe matan inhar ka cika kai jinin bakatsinawa ne ka sauqaqe mata kaji!, a rnr sede ka nemi wata uwar bani ba! " A zarane AB'ILAL ya kureta da ido sosai duk jikinsa yayi sanyi Jin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login