Showing 105001 words to 108000 words out of 306755 words
Chapter 36 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt
amma sumarta ta gaza zama a mayafin sbda tsananin yawanta, ya mata kadan, seda ta ballo ta fito waje. ta kurewa gu dya ido daga dukkann alamu tunani takeyi. "Hilwah!'' Amihh ta kira sunanta da muryarta me cike da narkakkiyar kaunar hilwah din. Firgigit hilwah ta dawo daga duniar tunanin data afka ta dawo da kwayar idonta kan Amihh wadda keta kallonta, a yanayin kallon da take mata ya bata tabbacin ta Dan jima a gurin tana kallonta. Tashi zaune tayi hadi da sakarwa Amihh murmushi "Amihh.." Ita ma ta kirata da muryarta me ddh, cikin karyayyen harshenta. Zaunawa Amihh tayi gefenta inda ta tashi, ta zuba mata ido ."tunanin me kikeyi sweetheart, matar AB'ILAL?'' Amihh ta jefo ma hilwah tambayar, hadi da mata kirari a karshe. Shiru hilwah tayi, hadi dayin kasa da knta jin kirarin da Amihh ta nata, se yau ma tasan sunan guy din AB'ILAL se maimaitawa takeyi a zuciar! "Tunanin me kkyi?'' Amihh ta kara tambayarta a karo na biyu. Ajiyar zucia hilwah ta sauke, tanaso tayi mgna amma tana shakkar Amih ko kunya zata ce oho. "Tunanin me kkyi sweetheart?'' Amihh ta kara jefo mata tambayarnan a karo na uku.. Hilwah tayi jim hadi da karayin kasa da knta murya cike da fargaba tace ''Amihh inaso inje gidannan in dauko wasu abubuwana..." Amihh taji jim tana kallon hilwah harta gama mgnar dimple dinta na kasan gemu se lotsawa yakeyi. "Zuwa gidan kk tunani kou?" Amihh ta tambayeta. girgiza mata kai hilwah tayi kawai... Amihh taci gaba da mgna ''banaso kije gidannan plx har abadan, knga ynzu kinada Aure bata yuwwa ma ki fita koda izinina ne sede inda izinin mijinki,... Me kkeso ki dauka a gidan?'' Amihh ta karashe mgnr da tambaya. Hilwah tace "abubuwana...." Amihh tace ''motar?'' Hilwah tayi shiru ita bama ta kawo motar ba a ranta, picture din mahaifiyarta shine abinda takeso ta dauka a farko se tab dinta, koda made bata dauka ba, ta siyo wani, sannan ta siya pad da take using ko ta samu wani sassaucin, dadin da dawa kuma tanaso ta dan shaqa koda cocaine dinta ne taji ddh, ko da ma bata sha codeine ba ko wiwi cocaine tafi tsaya mata a rai, jiya ma seda ta shiga toilet tayi kuka ma ishi sbda kewar kayan mayenta da tayi ba karamin shiga wani hali tayi ba, dukda tana cin abinci amma se faman rama takeyi. Kmr Amihh tasan me take tunani tace "Ko de kinaso ne kije kisha wadannan abubuwan danazo na samesu a dakinki ...wato kayan maye?" Shiru hilwah tayi ta kara kasa da knta kunya kmr zata nitse kasa, ita batamasan Amihh taga kyn maye ba a dakinta, se ynzu data fadi ta tuna da tama gama shansu ne ta kwanta a ranar. "Su kike tunani kou?'' Amihh ta kara tambayarta kur idanuwanta na knta. Hilwah ta girgiza mata kai kawai alamar ah'a Amihh taci gaba da mgna. "To shikenan inde ba shi kkeso kisha ba to ki hkra da tunanin xuwa gidannan plx?" Hilwah ta karayin shiru a rnta ba hk tasoba, ita de tanaso ta fita ko ba komi tade dauki tab dinta da pad dinta. "Kin hkra Knji ko?'' Cewar Amihh. Hilwah ta daga mata kai bata da yadda zatayi. Sosai Amihh taji dadin hkn tasan yarinyar na azabtuwa sbda sabo, Ka saba da abu a rabaka dashi na lokaci kankani babu dadih, dole ze tsaya maka a rai, ita tamaga hkrin hilwah koda yake ita din me hkri ce. "Kinci abinci?" Amihh ta kara tambayarta. Hilwah ta daga mata kai alamar Eh, dukda bata ci ba tasan in tace aah amihh zata matsa mata ne dole se taci ita kuma dmwar cikin rnta ta isheta, ko yunwa bataji...suna nan zaune amihh nata jan hilwah da hirah har salwah ta dawo ta samesu cikin farin ciki ta rungume hilwah nan suka hau murnan ganin juna, Amihh ta bisu da ido, zucia fal farin ciki. ga zuciarta salwah da hilwah bata bam-bam tasuba, kmr yadda takejin Salwah ga ranta haka takejin hilwah ga ranta, can can ma kuwa.
Yau kimanin Kwananshi uku a gidan Alhasan tinda yazo a kan kujerar nan yake kwana ya tashi, sallah da wanka ke tadashi daga kan kujerar. Abinci kuwa se alhasan ya matsa masa, sema sunyi kaca kaca kana yakeci, daya fara ci kuma se yace ya koshi, sbda tunaninta kawai yakeyi, duk abinda yakeyi inde ya tunata se yaji zuciarsa dukta dagule masa. Yau gabaki daya jarabar tasa ma karuwa tayi, tashinshi zuwa ynzu after azahar sunyi fada da alhasan yafi a kirga, xallar tijara kawai, Wai danma Alhasan be biye masa, mgnr arziki ma inya masa se ya maidata fada, shi kuma sbda shi be zuwa ko Aiki, sbda beso ya barshi a gida shi daya ganin halin da yake ciki. ko sallama AB'ILAL be ma alhasan ba, ya suri car key dinsa ya fice a falon Alhasan ya biyoshi yana tambayarsa ina zeje ya masa bnza, ya shiga motarshi ya fice a gidan, Alhasan ya koma cikin gidan yana girgiza Kai hadi dama AB'ILAL din fatan isa lafia, da kuma adduarh Allah ya sanyaya masa wannan guyababbiyar zuciartasa ta bala'i.
Yana driving motar yanata huci kamar kumurcin bakin maciji, jaraba na cinsa da matsifa kmr zeci knsa yakeji saboda tsabar tsiya, har ya isa gidan Amihh, yayi hon, hon dinma da matsifa yayisa a guje get man ya bude masa, ya shigo da motar cikin gidan, ko packing na kirki beyiba ya fito ya nufa side dinsa da niyar ya dauki wata karamar wayarsa daya bari a gidan, ya bar garin kawai shine a ransa. sbda kawai yaji a rnsa baze kara kwana ma a garin ba Kano ze tafi kwara yaje can bakin ciki ya kasheshi a can, dade ya mutu a kd, shifa duk yabi ya tsani kd, be fatanma ya mutuh a cikinta sbda makiyiyarsa na kadunar. A gurguje ya Shiga falonshi nan yaga wayar ya dauka, ya ajiye car key din motar dayaxo da ita, ya dauko mukullin wata motar, ya fito se sauri yakeyi ya isa ga wata mota dark ash me mugun kyau , tafi wadda ya ajiye kyau, ya shigeta ya mata key, yana kokarin ficewa a gidan Amihh ta danno da hancin tata motar, dole AB'ILAL ya koma baya ya jira ta shogo kafin shi ya fice. Tana ganinshi dan hk da hnzari tayi packing motar ta fito yana kokarin ficewa da motarshi da hnzari tace da get man ya rufe get, rufe get din yayi dai-dai yana qoqarin ficewa, duk yabi ya kagu ya fice a gidan kawai me gadin ya kulle masa get. sam be ankare da cewa Amihh bace ta bada umarnin hkn ya fito a zafafe da niyar ya karasa ya zazzabgawa me gadin rashin mutumci dmn ya tsaneshi. Ya karasa ze fara zabga masa Rashin Mutumcin Amihh ta karaso sbda har zuwa lokacin be ankare da ita ba, jaraba na cinsa idanuwansa sun kulle sbda tsabar tsananin baqar tijara. Ya bude baki ze zabgowa me gadi rashin mutumci Amihh ta dakatar dashi ta hnyar mgna. "Inka sake kayi mgna sena maka wulaknci kaji na gaya maka!'' Tayi mgnr hadi da tsare gida murya cike da tsiwah da tsananin tijara. Dole AB'ILAL ya dakata da rashin mutumcin dayaso zabgawa me gadin sbda Muryar Amihh daya jiyo a bayanshi, cikin hanzari ya juyo bayanshi inda Amihh ke tsaye, ya zuba mata ido babu alamar wasa a tattare da ita, hade rai ya karayi zucia fal takaici yace "why zaki ce a rufemin get Amihh? Tafiya fa zanyi zuwa kano fa,..." Ya karashe mgnr kmr me shirin fashewa da kuka ba karamin bakin ciki abinda Amihh ta masa ya masa ba. Hajiya maryam kara hade girar masa da kasa tayi, tana kare masa kallo cikin matsifa, se yau ne dazata fita zuwa asibiti da safe ta kula da baya gidan, ta tambayi me gadi, cewar ya fita ne? Me gadi yace mata Ai tin rnr dayazo be kwana a gidan ba ya fice. Tsa tsar takaici ya kulle mata kai, Ita ga zatonta ma ya koma kano ne. Ta kira wayarshi tayi ringin be dauka ba, har kira hudu, duk yana gani yaki dagawa aiko hkn ba karamin haushi ya tarawa hajiya maryam ba a zucia. A hasale tace "Baza kaje kanon ba, dan ubanka, wuce mu tafi?"ta karashe mgnr tana nuna masa hanyar zuwa side dinsa. Ya bude baki da niyar yy mgna ta daga masa hannu dole ya dakata, rai a matukar harzuqe ya juya ya nufa haryar data nuna masa na zuwa side din nasa, Amihh ta biyoshi a baya ma'aikatan gidan na kallon abinda ke faruwa su dan ustaz da silele abin nema ya samu, na gulma nan silele ya hau ma dan ustaz gulma, shiko yana saurare, daga bisani yace masa gulma ba kyau, bayan sun gama karaswa kenan ba.... Yana gaba amihh tana binsa a baya kuma yanajin alamar tana binsa a bayan har suka iso falon nashi ya zauna a kn 2ct Amihh ta karaso ta zauna a kn 3ct, seya zame ya zauna a kasan carpet din tsakiyar falon zuciarshi kmr zata fashe Amihh ta zuba masa ido, duk ya rame amma hkn besa taji tausansa ba a wannan karan sbda inma ya ramen shi yasawa knsa ya ramen. Dago kwayar idonsa yayi dasuka fara canxa launi ya zuba mata su murya cikin fushi da rashin jin ddhn abinda ta masa ynzu yace "Amihh meyasa kkeyimin hk plx? Kano fa nakeso naje ynzu, inada abinda zanyi nefa..." A hasale Amihh ta amshe da "bazakaje kanon ba nace dan ubanka, tinda baka da tarbia kwata kwata to dole seka zauna a nan na sake maka wata sabuwar tarbiar! Kanajina kiu? kai karamin mara kunya ne kaji na gayamah!'' Ta karashe mgnr da dan daga murya cikin hasala. Kasa da knshi kawai yayi ynajin abinda take masa yana kona masa rai, dande mahaifiyarsa ce kawai beda yadda zeyi ne. "Waishi za a sakewa sbwar tarbia?'' Ya maimaita hkn a ransa kawai zuciarsa na tafarfasa. "Dan knwar ubanka ina kaje na tsawon kwanaki hudu?'' AB'ILAL naji amma yayi kmr beji ba kawai yayi kasa da knsa se numfarfashi yakeyi kmr me asmah, nan ko tsabar tijara ce da matsifa. "Bada kai nake mgna ba!'' Amihh ta kara zaburo masa a hasale, dagowa yayi ya zuba mata ido, daganin kwayar idonta yasan tafishi tijara da matsifa. "Nace gidan dangin ubanwa ka kwana?'' Ta kara tambayarsa da matsifa hadi da tsananin tsiwah. Kmr bayason mgna ya bude baki yace "Gidan Alhasan naje fa Amihh..." Amihh tayi kwafa kawai taso ace kano ya koma wlhy dase taci masa mutumcinsa fiye da yadda yake tsammani. "Hmmm, bade kai dan kan bura uba ba, na fika bura uba, kaji na gaya ma! Mu zuba ni da kai, inde baxa kabi zabi naba zakasha whla, wato fushi ma kayi ka tafi gidan Alhasan din kou?" Ta karashe mgnr hadi da yin kwafa. AB'ILAL yayi shiru kawai zuciarsa na kara tafarfasa yayinda kwayar idonsa ke kara kadawa. Karayin kwafar Amihh tayi kwayar idonta na kan AB'ILAL taci gaba da mgna. "yau dinnan inaso kasa a kawo sabuwar mota irin ta mata ta wannan shekarar nkeso me kyau da me tsada sosai, a kawota cikin gidannan yau nke bukata..."dajin yada take mgnr kasan umarni take badawa ba neman shawara takeyi ba. Dagowa AB'ILAL yayi fuskarshi dauke da neman karin bayani, yasan de in kudi ne Amihh nadashi daxata se moto ci ma ba mota daya ba, sannan gidan ga motoci dayawa wasu ma ba a hawansu, ynzu kuma taxo tana mgnr a kawo sabuwar motar gidan "me za ayi da ita?" AB'ILAL yayi tambaya kwatar idonshi na kn Amihh. Hajiya maryam ta gallara masa harara kana tace "Me kakeyi da taka motar?" AB'ILAL yayi jim kana yace "ai naga ga motoci a gidannan dayaaa ba a hawa...kuma ma Amihh ai naga kema zaki iya sawa a kawo motoci gidannan, meyasa dole seda aka gaya min plz?" Amihh dake saurarensa Takaicinsa ya Kara rufe ta, wato tukumarta ma yakeyi cikin rainin hnkli. "Saboda kai keda haqqin siyan wannan motar tinda matarka ce zata hau..." Amihh ta bashi amsa da tsiwah. Bakin ciki da takaici da tsantsar haushi suka wa zuciarsa dirar mikiya sbda kalmar da Amihh ta ambata ta matarsa. "Wacece matata kuma?'' Ya tambayeta babu kunya A idonsa, Amihh ta kara watsa masa hara tace "Bnsani ba mara kunya. In baka san wacece ba, a ynzu ne zakasan wacece ai, me kakeci na bakinka na zuba...'' Da matsifa tayi mgnr hadi da zare masa kwayar idonta me cike da tsiya. Dauke knsa yayi, kawai duk se kara tsanar yarinyar yakeyi sbda yasan sbda ita ne Amihh ke masa cin mutumcin nan, duk tabi ta takura masa. "Za a kawo motar ko baza a kawo ba'?"" Amihh ta tambaya da muryarta me cike da tsantsar jaraba. Murya a sanyaye AB'ILAL yace "za a kawo ko zuwa gobe ne..." Amihh ta hayayyako tace ''yau dinnan za a kawota kana jina kou?" AB'ILAL ya daga mata kai kawai, yayin da bakin ciki ke cinsa inside. Kwafa Amihh tayi kwayar idonta na knsa ta ci gaba da mgna cikin isarta data dame tasa ta shanye. "Sannan kaje dubai ka hado akwati ma Amaryarka, tinda Auren sunnah kukayi kuma na gata ne,bawai bulus zaka ci ba, se kayi akwatuna na alfarma, kananan kaya sufi yawa kanajina kou?'' Tinda ta fara mgnr ya dago ya zuba mata ido a ranshi yana cewa wannan ne kuma baze yuba, shi ba dan iska bane daze hado mata wani kayan akwati, hadda wani kananan kaya, se kace an gayawa Amihh shi kawalin namiji ne. Data dire ya dauka da cewa "Gaskia ni bn shirya zuwa dubai ba, wani hado akwati,..." Hajiya maryam ta kara hade rai bama me kama da wargi a tattare da ita ta kalli AB'ILAL ta kara sakar masa harara tace "ai daman ni bnso ma ka shirya zuwa dubai din, dan hado lefen ai zakaje, kuma dolenka kaje kaji na gaya maka!" AB'ILAL ya hasala yaxo wuya shifa babu wanda ze sashi zuwa wata bnzar dubai. " Gaskia Amihh sede kiyi hkri ni bazan je ba gaskia.. Naga ma bafa ni nace ki min Auren nan bafa, balle har inyi wani akwati..kiyi akwatin mana kawai Amihh tinda ni ba sonta nakeyi ba..." Babu tsoro a idonsa ya fadi. Hajiya maryam ta saki baki tana kallonsa yana mgnr ba alamar kunya balle alkunya a tattare dashi. "Dan ubanka kuma seka siyosu, nan da 2days na baka wlhy, tin muna mu biyu kaji na gaya ma!'' Ta karashe mgnr hadi da mikewa tanata matsifa. "Danma na nema maka sauki nace dubai, inkasa tsiya se in lulaka da nisa kana karyar iskanci ne, mara kunyar bnza kawai!" Ta karashe mgnr hadi da fara takawa a falon tana shirin ficewa, AB'ILAL ya bita da ido, Shi da knshi yasan tinda ta fadi dole yayi, takaice ya kara rufesa, harta kai bakin kofar fita falon ta juyo ga AB'ILAL fuska bb alamar wasa tace "dan ubanka inka cika ka haifu da ruwan katsinawa kar kayi abubuwan dana lissafa maka a kuma lokacin dana baka,,dan ALLAH kada kayi kaga inda me rabani da kai a Nigeria, inkana karyar isknci ne ka kuskureni kaga yadda zamu kark'e nida kai..." AB'ILAL ya bita da ido kawai shi knshi ma ke masa ciwoh ga kuma takaici na cinsa, zuciarsa se uban tiriri takeyi. Takai hannu zata bude handle din kofar falon ta jara juyowa ta jallesa ta watsa masa harara , yayi hanzarin yin kasa da kansa. Murya babu alamar wasa taci gaba dacewa "Da Allah inka haifu da ruwa da jinin katsinawa, ka bar gidannan zuwa kano kaga yadda zanyi maka kaca kaca...kai! bazama ka koma kanonba, inko ka bar gidannan da niyar ka tafi kano, in ranka yayi dubu wlhy sena bata maka shi. ." tana gama fadar hkn ta fice a falon AB'ILAL da knsa ke kasa yaji fitarta ya koma ya kwanta nan kasan carpet din dakin zuciarsa na masa suya, yayinda yaketa tiriri shi kadai kmr tafasashshen ruwan zafi. "Dole in rabu da yarinyarnan!" Ya fadi haka a bayyane, zucia fal takaici da dumbin tarkacan kayan tsanar yarinyar yasan duk a knta ne Amihh ke masa hakan, daya rabu da ita Ai shikena ya huta...ritse idanuwansa yayi wadanda ke masa yaji kmr an zuba masa barkono duk tsabar bakin ciki ne da bacin rai da takaici yasa idanuwan nasa ke masa zafih.
Tana fitowa daga falon, inda motarta take ta nufa ta bude gidan gaba mazaunin me zamannbanza, ta dauki hand bag dinta, da wata madaidaiciyar leda me dauke da magunguna ta rufe murgin motar kana tama motar luck ta nufa hanyar shiga falonta, da sallahma dauke a bakinta haushin AB'ILAL be bar kan fuskartaba ta shigo falon. Hilwah na kwance a kn 3ct Salwah na kwance a kasan carpet din tsakiyr falon batafi 1h da dawowa gidanba, daga mataranta. Dukkaninsu tamfatsetsen tv dake falon suka zubawa ido, inda suke kallon wani Indian series film me mugun ddh, duk ya tafi da hnklinsu, AMIHH ta shigo falon sallarmar datayi ne yasasu dagowa suka zubo mata ido tare da amsa sallamar tata. Murmushi Amihh ta Sakarwa hilwah. Tashi hilwah tayi Ta tasa ga amihh jiki a sanyaye yayinda duk sassan jikinta ke rawa ta karaso ta amshi hand bah da ledar dake hannun Amihh, suka karasa a tare kan kujerar da hilwah ta Tashi suka zauna. Salwah se sannu da zuwa takewa Amihh amma bata amsaba sbda gaf ilahirin hnklinta na kn hilwah, da ace amihh