Showing 102001 words to 105000 words out of 306755 words

Chapter 35 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

harde yau ta fara tunanin akwaide abinda ke faruwa.... Da asubahi amihh tazo dan ta tashesu suyi sallarh asubahin ta taddasu suna kn dadduma ne ma suna nafilfili, juyawa tayi ta koma dakinta zucia fal farin ciki, ada kullum seta tashi Salwah danyin sallarh asubahin amma ynzu Alhamdulillahi zuwan hilwah yasa har sallarh dare sukeyi. Seda sukayi sallarh asubahi gari ya fara haske kana suka koma suka kwanta, bacci ya daukesu ba wani me ddh ba, se mafarke mafarke sukeyi a kan abinda ke zuciyoyinsu. A bangaren Amihh ma hkn ta kasance.


A bangaren Ab'ilal ma sam be rintsaba. Hk alhasan shima be rintsaba. 1:am alhasan ya bawa AB'ILAL shawarar su tashi suyi sallar nafilah, ba musu AB'ILAL ya tashi suka dauro alwala a nan falon suka tada sallarh nafilar, sunatayi hadi da adddu'ur'i har asubahi.. suka kara Alwala suka nufa masallaci dan samun sallarh asubahin a jam'i. Da aka idar basu baro masallacinba seda alfijir ya fara bayyana kana suka dawo gidan. AB'ILAL ya zube a falo, yana dan jin sassuci a zuciarsa ba kmr jiyannan ba. Alhasan ya dubeshi yace "mushiga bedroom mna.." AB'ILAL ya masa bnza. Alhasan be kara mgna ba sbda yasan ko ya kara ba tanka masa AB'ILAL din zeyi ba. Yabar falon ya nufa bedroom danya samu ya kwanta yayi bacci, yana kwancia kuwa bacci me nauyi ya kwasheshi....A bangaren AB'ILAL kam gaza baccin yayi ga damuwa na cinsa duk silar yarinyar ne, ga yunwa na kwakular cikinsa beci ba, be sha ba har ynzu. Jiyama da Alhasan ya masa tayin cin abinci saura kadan AB'ILAL din ya zagesa dole ya barshi. A zahirin gaskia sam shi yunwarma bata damesaba kmr yadda tunani da tsanar yarinyar suka hadu suka ma zuciarsa rubdugu har Amihh ma dan beda yadda zeyi ne Amma da haushin abinda ta masa yakeji. Se 8:am ya samu bacci barawo a wahalce ya daukesa, baccin yakeyi amma bayajin dadinsa kwata-kwata.


A bangaren su kankana kam, shida Amal sun shiga tsananin damuwar Rashin hilwah har wata rama sukayi a kwana daya, inka gansu kasha ko uwarsu da ubansu ne suka mace, saboda iyakar damuwa sun shiga. Kankana ya kira alhaji sunusi yana kuka ya sanar dashi abinda ke faruwa, seda ya fadi ya suma a rnr hawan jininsa ya tashi aka kwasheshi a can kasar da yake se asibiti, washe gari dayaji sauki ya baro kasar yabi jirgi ya dawo kasar nigerian direct gidan dandi ya nufa,..nan ya tadda sun kankana da Amal a tashin hnkli, kankana ya kara kwashe lbrin komi ya gayawa alhaji sunusi iyakar dmwa alhaji sunusi ya kara shiga. Kawai ya fashe da kuka yana tambayar su kankama da Amal suna kiranta kuma yana shiga? kankana ya tabbatar masa da kullum se sun kirata amma bata dagawa washe garin rnr da tazo gidan Amihh ta amshe wayar dake hannunta. Iyakar tashin hnkli alhaji sunusi ya kara shiga, a zahiri daxesan inda hilwah take da har can ze bita ga iyayenta ya Aureta , sbda ita ce farin cikinsa. A nan garinma seda Alhajin ya kara kwancia asibitin, sbda damuwar rashin hilwah dukda kuwa alhajin naji a ransa ze kara ganin Hilwah, kwananshi uku a asibitin aka sallamesa Kankana da Amal sukayi jinyarsa be sanarma da iyalinsa ma yana Nigerian ba. Ita knta magajiyar karuwai ta shiga dmwar rashin hilwah sbda zamanta a gidan ba karamin alheri take samu ba dukda kuwa hilwah ba bada gindinta takeyiba anaci, amma mnyan maxa naso kuma ko basu ciba suna bada kudi,..aiko jin uwar hilwah taxo ra tafi da hilwah seda hajiya magajiyar karuwai tayi zazzabi wannan qibar tata ta asara duk seda ta sab'eta ta zaizaye ta rame... Khamilah kanta data samu labari ta dan damu kadan, shima sbda ganin Amal ta damu ne. Amma a zahirin gaskia khamilah dadih taji, sede kuma ta gaza gano kan Amal... D&D su qamas su Anty kwalba, dasu hadin sigag duk sun shiga dmwa, sbda suna mugunyin hilwah sam basa son wanda ze bata mata rai, to a yau Gashi babu ita kilama ta bar gidan dandi ne na har abadan, Baraka da dan taure ma sun shiga dmwa da suka samu lbri, suma suna mugun missn hilwah, amma basu kai zallar D&D missn din hilwah ba...kankana kam har gobe yanaji a jikinsa Wata Rana uwar dakinsa zata dawo garesa, motarta da gidan data bari Alhaji sunusi ya mallakawa kankana, da niyar ko yau hilwah ta dawo ze sake mata wasu abubuwan duniar da sukafi Wannan, seda bata nan ne ya tabbatar da yana sonta tamkar yadda me rai ke son ran dake jikinsa. Kankana yama Alhaji sunusi godia da kyautarsa garesa, amma sam be wani farin ciki iskncinma duk sun rage shida Amal sede shaye shayensu ne ya karu, shike rage musu wata damuwar. Amal da kankana a yan kwanakin nan kullum cikin zagaye garin kaduna suke ko ALLAH zesa suga Hilwah Amma ko me kama da siffartama basa gani sede su karata da yawonsu su dawo gidan jiki bb laka, zucia babu dadih, kullum se kankana ya dauko kayan hilwah ya rungume seya fashe da kuka amal ce ke bashi hkri kafin daga bisani itama ta fashe da kukan. Satin Alhaji sunusi daya a garin kaduna yama Amal da kankana sha tara ta arziki kana ya juya ya koma kasar daya fito domin ci gaba da aikinsa, amma fa zuciarsa babu ddh, kuma ya ce kankana yaci gaba da neman hilwah in Allah yasa ya gano inda take, ko ya gnta ya gaya masa shi kuma a rnr zezo gidan su Hilwah ayi mgnr Aurensu Ko rnr ne a daura musu aure ya mallaki wannan kayan dadin ya killaceta a tamfatsetsen gida yayita more rayuwarsa da arzikin da Allah ya mallaka mata... Hilwah ta tafi tabar zuciyoyi da kewarta hadi da dumbin kaunarta na har abadan da'iman. Amal da kankana suka sa aka wanke musu hotunan hilwah dake wayoyinsu suka zo suka manna tako ina a dakin suna kalla kuma sunajin ddh, ALLAH sarki rayuwa kenan basu taba zaton zasu rabu da hilwah ba a rayuwarsa, a kullum suna tuna alherin hilwah ne da kyakyawan halinta, zuwa ynzu Amal da kankana har sallah suka farayi sunata adduarh Allah ya bayyana musu hilwah koda sau daya ne su kara ganinta a rayuwarsu, tin number dinta na shiga gashi zuwa ynzu ma bata shiga hajiya maryam ra kashe wayar gabaki daya ta jefata a drower. Se hnkulansu ya kara tashi jin suna kiranta basa samunta, amma dukda hkn basu bar sa ran kara ganintaba.....






*for more information 08136349646...*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: *YAR DANDI CEH...* 🅿️23
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽

Yau kimanin kwana biyu kenan da zuwan AB'ILAL gidan, tinda ya fita Amihh bata sake ganinshi ba dukda tana damuwa Amma hkn besa ta nemeshi ba ko da ta waya ne, a wannan karon so takeyi ta nuna masa tabbas ita ta haifeshi bashi ya haifeta ba. Bayan tayi sallar azahar tana zaune nan kan dadduma, ta tashi ta karasa bakin bed dinta ta zauna, ta dauki wayarta dake kan gadon, ta shiga dealing number din hajiya Juwairriyya bugu daya ta daga, daga bngarenta ta fara mgna cike da kewar hajiya maryam. "Hajiya wainshin kina kasar nan?'' Hajiya maryam tayi murmushi da iyakarshi yaqe ne, kana tace "Assallamu Alayki..." Hajiya Juwairriyya tayi yar dariya kana ta amsa "Wa'alaykissalam, na mnta ashe bamu nemawa juna aminci ba,,to ya kike aminiata? Kwana biyu kin boye nima kuma na boye..." Hajiya maryam tayi yar daria ita ma kana tace "yauwa ynzu kikayi mgna, amma da kince ina kasar ne, bayan nida ke duk bama kasar...." Dariya sosai hajiya Juwairriyya tayi Tana nazarin dariyar maryam da klmnta tasan basu kai kai ciki ba. "Bari hajiya Ai alhaji ne ke gida yana hutu wlhy bani da katafus, ..." Cewar Hajiya Juwairriyya. Hajiya maryam ta kara Murmushi tace "masha ALLAH, Allah de ya Kara dankon soyayya da nisan kwana..." Hajiya Juwairriyya ta amsa da Ameen..." Duk sukayi jim na wasu yan daqiqu, kana hajiya Juwairriyya taci gaba da mgna. "Ashe Alhaji karami na nan kd kou? " Hajiya maryam ta sauke ajiyar zucia tace "eh yana nan kd hajiya Juwairriyya, lamarin yaron nan yana damuna hajiya, abin nasa se adduarh , kwata kwata yaronnan beda mutumci,.." Hajiya Juwairriyya ta sauke ajiyar zucia dmn tasan a can damuwar hjya maryam take,
tace "Ai ni nasan dajin wannan murya taki da abinda ke damunki hajiya, meya faru?" Hajiya maryam ta sauke numfashi kana ta fara mgna "Hajiya yaronnan kwata-kwata beda ladabi beda biyayya, Gashi nan de a tsaye ko rankwafawa beyi! ALLAH wadaran halin wannan yaron,.." Ta karashe mgnr da muryar takaici. Hajiya Juwairriyya tayi shiru tana sauraren hajiya maryam dajin hkn se tayi tunanin AB'ILAL ya kara wata tsiyar ne. tayi gyaran murya kana ta dauka da cewa "me yayi na rashin Ladabi hajiya?" Hajiya Maryam ta kwashe lbrin komi na auren data ma AB'ILAL A,to,Z ta shaidawa hajiya Juwairriyya, amna bnda na inda taga hilwah, wato gidan karuwai, sam bata gaya mata wannanba, tadece mata hilwah marainiya ce daga gidan marayu. Hajiya juwairiyya dake a zaune Amma seda ta tashi tsaye byn hajiya maryam ta gama shaida mata komi. "What! Tashin hnkli!" Sune Kalmar dasuka fito daga bakin Hajiya Juwairriyya. "Kai hajiya abin naki yayi tsauri a wannan karon dole yaronnan ya tubure, haba hajiya ki rinka Sara kina duban bakin gatari mna..." Cewar hajiya Juwairriyya. Cikin sanyin murya hajiya maryam ta amshe da "me nayi na rashin duban bakin gatari a wannan karon hajiya Juwairriyya?'' Cikin fada hajiya Juwairriyya ta dauka da "gaskia kin tauyewa yaronnan hakkinshi, haba maryam, auren dole kenan fa kika masa,.." Hajiya maryam ta amshe da ''na musu de hajiya, ai bashi kadai nayi mawa ba ita ma yarinyar nayi mata Ai ita ma aka cuta, amma knga ita tamin biyayya, gashi dan ciki na ya gaza min, shiyasa bahaushe yace da d'a da dukiya ba a musu mugunta duk da rnr su, d'anda ka haifa seya gaza mka abu se na wani ya maka cikin mutumci..." Hajiyar Juwairriyya ta amshe da ''ba wannan mgnr hajiya, ko be miki biyayya ba a wannan datsin beda lefi sam beda lefi...ai abinda zakiyi la'akari shi namiji ne ita kuma macece mace tafi namiji hkri a wannan fannin , kiyayyar namiji tafi ta mace zafi, gaskia ni de hajiya bnso kikayi wannan hadin ba, sbda knsan halin mutuminki da zafin kai, mata masu ji da knsu ma bebi ta knsu ba, balle wadda ke gidan marayuba, wadda bata da nasabah...." Mgnr Hajiya Juwairriyya ta karshe ba karamin dukan Hajiya Maryam tayi ba, kmr ita aka jifa da kalmar, cikin rashin jin ddh hajiya maryam ta dauka dacewa "tanada nasaba mana hajiya...." Hajiya Juwairriyya ta amshe da ''nasaba a ina? Bayan bakisan uwartaba bakisan ubanta ba,,,wannan ma duk ba problem bane, nasan aikin alheri kkyi hajiya maryam, Amma gaskia da baki kaiga zuwa wannan stage dinba, yayi tsauri da yawa gaskia ...kina shawara dani a komi naki amma a wannan stage din baki sakoni bama a zancan naki, kawai knyi gamin kanki,..." Hajiya maryam tayi shiru tana nazarin kalaman hajiya juwairiyya ita sam basu shigetaba, infect ma bata fahimci inda zancenta ya dosaba, tadesan son kai ne ke dawainiya da juwairiyyar sbda tanason AB'ILAL batason abinda ze dameshi shi yasa take ta wadannan zantuttukan. "Hajiya rayuwarta da ta bayar saboda ni yarinyarnan? Shin ina da abinda zan biyata dashi?'' Cewar hajiya maryam Hajiya Juwairriyya ta dafe knta kana ta fara magana. "Kin iyawa wani adalci hajiya amma baki iyawa naki adalci ba, a nan fa naki kk cuta kuma baki kyauta ba, dakin saka mata ta wata hanyar bata wannan hanyar ba..." Hajiya maryam tayi murmushi kawai kana ta amshe da "a wannan fannin nawan nama adalci na shiga haqqin baiwar Allah.." Hajiya Juwairriyya tace "meyasa kkce haka?'' Hajiya maryam ta ci gaba da cewa "Ai hakan nema,...ynzu duk yadda zan miki bayani bazaki fahimta ba sbda son zucia na dawainiyya daku keda danki.. " hajiya Juwairriyya tayi yar Dariya kana tace "shikenan Hajiya munji son zuciar ne ke dawainiyya damu , ande cucemu kawai..." Hajiya maryam tayi murmushi tace "very soon se bakinku ya mutu hajiya, wlhy gata nama yaronnan amma a zahirin gaskia ai yarinyar nan aka cuta..." Hajiya Juwairriyya ta tabe baki kmr tana gaban hajiya maryam tace "saboda duk jikin yarinyar da danyar gold aka yita Kou?'' Hajiya naryam tayi murmushi tace "wannan ai tafi gold hajiya, kede ki bari ki gnta...kun tsinci dami a kalah... " Hajiya Juwairriyya tayi murmushi itama tace "anya damin da muka tsinta na gaske ne, ina tantama? bade tarin dusa bane a ciki kou?'' Hajiya maryam ta danyi shiru tana nazarin hausar hajiya Juwairriyya na wasu yan dakiku , seda ta fahimceta tas kana tace "Hmmm...Hajiya kenan, ALLAH ya rabaku da son kai.." Hajiya Juwairriyya tace "Ai kowa nason knshi hajiya,...ni wlhy tinda kk fara gayamin mgnr nan tunanin halin da yaronnan ze shiga kawai nakeyi..." Hajiyar maryam tayi shiru kana tace "Au bama tunani rashin mutumcin da yayi ba kikeyi ...Hajiya wannan yaron wani lokaci se in rinka ganin kmr an chanza min shine dana haifeshi a asibiti .." Ta karashe mgnr murta cike da takaicin AB'ILAL. Hajiya Juwairriyya tace "meyasa kikace haka hajiya maryan?'' Hajiya maryam ta sauke nannauyar ajitar zucia kana tace "yaronnan beda kunya kwata kwata, beda tsoro, knsan cewa yayi seya saketa a rnr da nace masa na masa Aure...kinga haukan da yayitamin ne wai hajiya?'' Hajiya Juwairriyya ta amshe da ''kin taboshi ne hajiya..." Hajiya Maryam ta girgiza kai kawai tace "ALLAH ya shirya...amma akwai Aiki babba..." Hajiya Juwairriyya ta amshe da "Ameen ..aike kk jawo mna Aikin,...in de bame yuwwa bace ya sawaqewa yarinyar kawai. " Hajiya maryam tayi wani shu'umin Murmushi kana tace "idan gaf mutanen garin kano da kaduna da katsina, dangin ubansa ne, ya saki yarinyarnan sena ci masa mutunci a nigerian ma gabaki daya ...ko a zucia ya saketa ni dashi har abadan, dan na gaya masa ma ya nemi wata uwar bade niba..." "Tashin hnkli!'' Ita ce kalmar data fito daga bakin hajiya Juwairriyya, tayi kasak'e tana nazarin klman Hajiya maryam kana tace "Hajiya ki rinka bi a hnkali plx..." Hajiya maryam tace "in ba hkn na masa ba baza mu dai-dai taba,..nake gaya miki ma da yanzu lbri yasha bam-bam..." Hajiya Juwairriyya tace "Hmmm,,to shikenan ALLAH yasa ace kwara da Akayi..." Hajiya maryam ta amshe da "Ameen.." Cikin farin ciki. Hajiya Juwairriyya tace "to ynzu ya akayi da Amarya da angon namu?'' Hajiya maryam tace "kamar yaya?'' Hajiya Juwairriyya tace "mgnr tarewar Amaryar ? A wani gidan zasu tare? Kd ko nan kano?'' Hajiyar Maryam ta zaro ido jin hajiya ta ambaci kano tace "ta ina zan bashi ita suzo kano? Wannan yaron daba imani a ransa .. Ai a nan gidan ma zata zauna har inga gudun ruwansa, wannan yaron beda hnkli, innaga me yuwwa ce, se ta koma side dinsa na nan gidan, amma ynzuma ba wannan mgnr tukunna..." Hajiya Juwairriyya tayi murmushi danta kula hajiyar najin wannan amarya a can kasan zuciarta tace "Ai shikenan kede burinki ya cika, ALLAH de Yasa Alheri dan Alfarmar Annabi..." A tare suka karasa da S.A.W... "Ina salwah nah? Kota koma ne?'' Hajiya juwairiyya ta tambaya. Hajiya Maryam tace "ina ai bata koma ba, tana ma scul, ai ynzu an samu abokiya ba amason rabuwa da juna, shigowar yarinyarnan rayuwata alheri ce .." Maryam Ta karashe mgnr zucia da farin ciki. Hajiya Juwairriyya tayi murmushi kana tace "Wai! Sunan wani film na hausa daga temako... Daga temako seki wanke yaronki tas tas ki hadasu Aure ..." Hajiya maryam tayi Murmushi sbda mgnr ta hajiya abar a murmusa ce tace "ko kuma na wanke yar mutane na hadasu ba, inda badan ni bama Ai yarinyarnan tafi karfin ajinsa..." Hajiya juwairiyya tayi wata iriyar guda, Da bata masan ta iyataba se yau, kawai ta bar hajiya Maryam da gudar bata ce mata komi ba,a ranta tana so taga wannan yarinya me sa'ar auren AB'ILAL a lokaci kankani....daga hk suka juya akalar hirarsu zuwa wata siffar ...Daga bisani sukayi sallahma, sunayin sallamar hajiya Juwairriyya tayi dealing number din AB'ILAL, be daga ba, daman taso ne ta masa natsiha kn abinda ya faru, dabe daga ba seta barshi, ta bisu da adduarh kawai..... Bayan sun gama wayar hajiya maryam ta mike ta fito falon gidan, a kan kujerar 3ct ta samu hilwah kwance kewar Salwah duk tabi ta addabeta, da a bedroom take shine ta dawo falon duk ta kagu salwah ta dawo, time to time seta kalli kofar shigowa falo. Karasowa Amihh tayi ta tsaya ta zuba mata ido sanye take da doguwar riga mara nauyi me launin layi layi red and golden hannun rigar hannun best ne ba karamin kyau rigar ta mata ba, dukda bata kwanta a jikintaba amma ta amsheta abu me kyau ya hade da me kyau. zuwanta gidan Amihh ta kula ita ba ma'abociyar son sa kaya masu nauyi bace, atamfofin da amihh ta dinka mata sunfi kala ashirin amma ko daya bata taba sawa ba, balle laces da amihh ta siya mata dinkakku duk bata ma kallesu ba, badan Amihh naso ba take barinta tanasa irin wadannan rigunan, sedan taga tafi sabawa dasu amma ita in a san samuntane hilwah tasa riga da zani na atamfa, amma sam taki sawa,,Amihh ta mata mgna kn ta saka tace toh kawai har ynzu bata saka ba, bata ma da niyar sawa. Tsura mata ido sosai Amihh tayi ganin batama san tana gurinba, gashinnan na kanta har gadon baya, akwai dan Mayafi karami a knta kalar red, dukda ta rufe knta ruf


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login