Showing 147001 words to 150000 words out of 306755 words

Chapter 50 - YAR DANDI CEH COMPLET BY SAADATU BINTU ABDULLAHI.txt

mata ba tasan shadin hannu ne. "Meya sameki dea? Meye wannan? Waya mareki?'' Salwah ta jero mata tambayoyin duk a gigice take, ta zubawa shadin yatsun dake kwance kn fuskar hilwah ido, Salwah tayi saurin maida hijjabinta a gurin ta lullube, tayi kasa da knta hadi da cema Salwah "ba komi..." Salwah ta kara zubawa fuskar tata ido, ko ba a gaya mata ba tasan be wuce yah AB'ILAL ne ya daketa ba sbda mugune azzalumi ne ba imani bane a ransa, nan da nan zuciarta ta hasala, tausan hilwah ya kara lullubeta,taji kmr ta mata kuka, duk tabi ta gigice, dagani ba karamin wuya taci ba daga jiya zuwa yau. "Yazakice ba komi plx,,bayan ga shaidar hannu nan a kn kuncinki again ga wasu kuraje, plx ki gayamin gaskia bnaso kice min ba komi Dan Allah... Ki bar zurfin ciki kawai ni ki gayamin gaskia, yah AB'ILAL ne ya dakeki kou?'' Salwah ta karashe mgnr a hasale, bata tabajin haushin yayan nata kuma jinintaba se yau, sbda tasan wannan Aikin nasa ne. Hilwah tayi kasa da knta hadi da fashewa da kukan da batasan dalilin sa ba, daman kmr tana jira. Salwah ta matsa jikinta ta jawota t rungumota jikinta itama ta fashe da kukan tana fadin "Amma bross be kyautaba, Wlhy ni shiyasa banso kk dawo side dinnan ba sbda nasan cutarki zetayi Allah kadai yasanma me yake miki, wlhy sena gayawa Amihh inta dawo Daga Aiki (kasancewar yau 7:am ma bata cika ba ta fice a gidan, sbda aikin gaggawa daya sameta, shiyasa batazo taga hilwah ba sbda yayi sassafe dayawa ita ga zatonta ma basu tashi ba)" salwah ta kara rungumo hilwah jikinta, salwah taji jikin hilwah nata kakkarwa Ga uban zafi daya dauka , se faman kuka sukeyi kmr wadanda iyayensu suka mutu, zuciar salwah cike da tausan hilwah...seda suka kwashi 15mnt a hk suna kukan kana salwah ta dago fuskarta daga jikinta ta tallabota da dukkanin hannayenta biyu ta zuba mata ido har lokacin se kuka takeyi tausanta suka kara cika Salwah, cikin muryar kuka Salwah tace "dea AB'ILAL ne ya dakeki kou? Ki gayamin Nasanma shine ko baki fad'iba..." Hilwah ta girgiza mata kai alamar ah'a salwah tace "plx ki gayamin, wlhy sena gayawa Amihh koda hkm zesa ya kasheni, ai ba kawoki akayi ba yayita cutarki ba, ni nasan yana cutarki kawai kinki fad'i ne...." Cikin muryar me cike da gajiyawa da kuka Hilwah tace "ni...be...min...ko...mi...ba..." Ta fadi muryarta na sarqewa sbda kukan dake cinta har lokacin, kmr numfashinta ze dauke. Salwah ta hade rai takaici ya rufeta ga abu tana gani ganin idonta amma kuma hilwah na karyatata. "Why zaki cemin ah'a, bayan ga shadin yatsu nan a kn fuskarki, Wlhy dukanki yayi, su wad'annan kurajen ina kk samosu Plx?'' Salwah ta karashe mgnr hadi da kara dago face din hilwah ta zubawa kurajen ido ss, nan take ta fahimci na cizon sauro ne abunka da farar fata irin ta jarirai. fuska dauke da mamaki salwah tace "kmr cizon sauro? Ta yaya sauro ya shigo ya cijeki?' Ina aka samu sauro har haka?' Salwah ta karashe mgnr tana karewa dakin kallo, sam babu wata kafa da sauro ze shigo to ta ina ya shigo ya mata wannan cizon, Hilwah tayi shiru hadi da kara kasa da knta, hilwah ta bita da ido ganin bata da niyar bata amsa yasata ci gaba da mgna itana hawaye . "Ki gayamin meye ya hadaki da AB'ILAL ya miki duka, kuma ya akayi sauro ya cijeki plx ki gayin plx? " hilwah ta goge hawayen dake zubo mata itana, ta sassauta kukanta ganin Salwah duk tabi ta damu har lokacin se kuka takeyi tace "ni be min komi ba,..." Ta fadi da muryarta ta kuka, hadi da karyayyen harshenta. Salwah taji takaicinta ya rufeta zurfin cikinta haushi yake bata "to wannan kurajen sauron ina kk samesu? Tinda kinki gayamin meya hadaki da yah AB'ILAL ya dakeki dan wlhy nasan dukanki yayi ga mari nanma a kn fuskarki, inna gayawa amihh ita tazo ta tambayeki zaki gaya mata gaskia Tinda ni baxaki gayamimba..." Hilwah ta tsagaita da kukanta jin Salwah tace zata gayawa Amihh kuma dagani da gaske take bada wasa take ba, ta kara goge hawayenta dake kn fuskarta kwayar idonta na kn salwah ta fara mgna ''plx karki gayawa Amihh, ni be min komi ba.." Salwah ta hade rai tace "in kina cewa be miki komi ba bnjin ddh, infect ma haushi kk bani sbda ga abu ina gani a zahiri... Kawai ki gayamin gaskia tinda bakiso in gayawa Amihh dan Allah ki gayamin?'' Salwah ta karashe mgnr da sigar roko, hilwah ta tsaya a kn bakarta kan be mata komi ba, salwah tayi juyin dunia Amma hilwah tace mata ba komi, aiko tace seta gayawa Amihh nan hilwah ta shiga rokonta tana mata magiya, kan karta gayawa Amihh, salwah tace seta gaya tinda bata gaya mata me yah ab'ilal ta mata ba, hilwah ta fashe da kuka tana rokon Salwah kn karta gayawa Amihh, Salwah tace to kawai sbda hilwah ta tsagaita daga kukan nata, da kyar kuwa ta samu ta tsagaita daga kukan nata, zuwa lokacin ta fara jin axababben ciwon kai na gefe da gefe biyu na knta, dan hk ta amshi hakurin da Salwah ta bata tayi shiru ta dau na annabawa, Salwah ta zuba ma hilwah kunun gyada da kosai ta tura mata gabanta, zuba musu ido hilwah tayi bata taba cin kosai ba gaskia kwara ma kunun gyad'a ta taba sha da tana gidan dandi wata rana kankana ya taba siyo musu. Mikewa tayi da niyar taje toilet tayi brushi salwah tace ina zata je ta bata amsa da brushi zatayi, salwah tace okay, ta bita da ido harta shige bathroom din jiki babu kwab'i, se tausanta ya kara ratsata salwah, ta rafka uban tagumi a zucia tana me adduarh Allah ya sakawa hilwah ga AB'ILAL tama mnta cewar shidin wai dan uwanta ne. Hilwah ta fito tazo ta zauna ta fara shan kunun gyad'an Amma sam bata kai hannu ga kosan ba sbda bata iya cinsa, ko tace ma bata taba ganinsa ba se yau, ita inbama datazo gidanba bata cin Abincin ire ire hkn, nata fa ban kankana ke dafa mata amma a gidan Amihh ta koyi cin Abincin iri irin wad'annan..Salwah ta tambayeta meyasa bazataci kosanba, hilwah tace bata taba ma ganinsa ba balle taci. Salwah ta bita da ido da mamaki a ranta tace "baki taba ganin kosai ba? kosai ne fa? ko de baki taba ciba?'' Salwah ta tambaya hilwah. "Ban taba ganinshi ba se yau..." Mamaki ya kara cika salwah jin hilwah tace bata taba ganinsa ba, ita de bata taba ganin dan nigerian dayace be taba ganin kosaiba se hilwah. "Kici kinji dea akwai ddh...'' Hilwah ta girgizawa Salwah kai kawai alamar ah'a, salwah ta bita da ido har lokacin se mamaki takeyi a ranta. Hilwah ta dansha kunun gyad'an da salwah ta zuba mata Rabi ta ajiye cup din tace ta koshi salwah tace ta dan kara mna ta girgiza mata kai, Salwah ta mike hadi da cewa bari inje in kawo miki magani naga alamar kinada zazzabi na maleria ne da ciwon kai, duk fuskarki tayi wani kubul kubul, bnsan ina kk samu sauro ba ya cijeki ba..., bari in kawo miki magunguna, har na ciwon jiki ma..." Hilwah ta daga mata kai alamar to, salwah ta fice a dakin hilwah na kallonta harta fice ta koma ta kwanta, nan kn carpet din jiki a sanyaye, ko ina nata ciwo yake mata,...abubuwan da AB'ILAL ya mata tin zuwanta gidan har zuwa ynzu suka shiga tariyowa a cikin kwakwalwar kanta, hk kawai takeji a zuciarta ta tsaneshi kmr yadda ta tsani mutuwarta, tasan itama ya tsaneta dan hk ta kara tsanarsa bisa kn tsana, bata taba tsanar wata halittaba a rayuwarta kmr yadda ta tsani AB'ILAL.

A bangaren gogan tinda ya shiga bedroom dinsa ya kwanta akan bed dinsa me laushi, ya riqe knsa kawai ya tsinci zuciarsa da kunci ya rasa dalilin hkn, yasan dan marin daya mata ne, to meyasa ya tsinci kn nasa da kunci? Bayan shi ba tausanta yaji ba shide kawai yaji zuciarsa cike da kunci...juyi ya shigayi a kn bed din, daya rintse ido kawai tunano yadda ya daga hannu ya sharara mata marin yakeyi. Dago hannunsa na hagun yayi ya zuba masa ido, har ynzu laushin fuskarta be bar jinsa ba a tafin hannun nasa Ba, rintse idanuwansa yayi yana me aikin tunano lauahi da tsantsin fuskarta a zuciarshi, qoqarin kauda hkm yy a ransa amma abu fa yaci tura kuma ya gagarah, bacci yakeso yayi amma baccin yaki zuwa har kusan ya shafi 1h se aikin juyi kawai yakeyi a kn tamfatsetse lallausar bed din nasa Zuciarsa se aikin jeka dawo takeyi a kn tunani abinda besan dalilinsaba, tsabar takaici, ji ya farayi kmr ya cire zuciar tasa daga jikinsa, sbda ta mugun bata masa rai, shi da knshi haushin kansa yaso ya fara ji, duk yadda fa yaso yayi bacci gazawa yayi sede yy shiru kawai hadi dayin likimu, Amma idanuwansa a bude...

Tana shiga side din Amihh Ta nufa bedroom din Amihhn ta dauko magunguna masu inganci na maleria dana ciwon kai da zazzabi, dana ciwok jiki, dukda de tasan mgnin maleriar zeyi aiki ga zazzabi da Ciwon kan amma ta dauko de na ciwon kn da zazzabin dana ciwon jikin, in case, ta nufo hanyar ficewa a falon ta kai hannu zata bude handle din kofar fita falon, Amihh ta rigata shigowa cikin falon, salwah ta bita da ido, itama Amihh ido ta zuba mata, duk a gaggauce take, dan hk bata ankare da magungunan dake hannun salwah ba . "Sannu da zuwa!'' Itace kalmar data fito daga baki salwah zuwa ga Amihh amsawa tayi dagani tana dan sauri ne, ta rabe salwah zata wuce tana me fadin "kin kaiwa hilwah breakfast?'' Salwah ta amsa da Eh..amihh tace okay kawai ta nufa hanyar shiga bedroom dinta Salwah ta juyo ta zubo mata ido ta gaza tafia so takeyi ta gayawa Amihh halin data samu hilwah a ciki kuma tana tsoro a ranta. "Am...ihh!'' Salwah ta cire tsoro a ranta ta kira sunan Amihh, hajiya maryam data kai Hannunta kn kofar dakinta tana shirin budewa ta dakata jin salwah ta kira sunan nata, ta juyo ta zubawa salwah ido tace "meya faru?'' Fuska babu alamar wasa tayi tambayar.


*bazan dena baku hkri ba a kan rashin editing.....*




*Ku bar AB'ILAL yayi iskncinsa plx time dinsa ne....hmmmm😂*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 34***
Salwah tayi kasa da knta ta rasa ma ta ina zata farawa Amihh mgnr dukan da AB'ILAL yama hilwah ita da bata tabbatarba hasashe takeyi, sbda hilwah bata gaya mata da bakinta ba... Ganin tayi shirun yasa Amihh jan guntun tsuki ta fara fad'a "banason isknci kinajina kou? Ni sa'arh dangin ubanki ce? Ko ni sa'arki ce daxaki kira sunana ki barni tsaye!'' Ta karashe mgnr cikin muryarta me cike da tsiwah da tsawa seda Salwah ta Dan firgita taja baya, dukda basa kusa da Amihh sunada nisa Amma gani takeyi kmr zata karaso ne ta tsinketa da mari... "Yi hkri Amihh..." Itace kalmar data fito daga bakin Salwah ba tare data ankare ba, sbda kallon da Amihh ta kuma jifanta dashi. Kwafa Amihh tayi ta nufa bedroom dinta kawai, salwah ta karasa ta dauki wayarta dake kn kujerar 3ct cikin hanzari ta fice a falon hannunta riqe da wayarta da magungunan. Dan ustaz dake zaune a kusa dame gadi a dan bencinsa dake kusa da bakin get din fita, ganin salwah ta fito daga falon Amihh yasashi tasowa a guje ya nufo inda salwah take tahowa tsantsin takalminsa se kwasarshi yakeyi. Salwah ta zubawa dan ustaz ido dan ganin yanata sauri ya karaso inda take, rana na haskashi yanata shining din man da yake shafawa, sanye yake da wata tsohuwar kod'addiyyar jallabia maroon amma ta koma kalar ash ash pink pink sbda tsabar kodewa. . "Dan Ustaz lafia kaketa gudu kmr agwagwar larabawa?'' Cewar Salwah dataja ta tsaya ita yanayin gudun dan ustaz dinma daria yaso ya bata. Gyara tsayuwa dan ustaz yayi bayan ya matso daf da salwah sbda tsabar gajartarsa salwah na ganin kwanyar knsa shi kuma se ya daga kwayar idonsa sama yake kallonta, ya kai hannu ya shafi gemunsa wanda keta maiqo, se faman washe green teeth dinda yakeyi yace "wato ainifin hajiya yar karama, ni nan da kk gani na a kasa me tsarki aka haife, ainifin shiyasa kika ganni na biyo wata halitta a kasar saudia , Amma se akayi rashin sa'arh na biyo agwagwarsu..." Salwah ta kwashe da daria hadi da girgiza kai kawai, tace "Amma ko bakaji ddhba Dan Ustaz a memakon ka biyo larabawa kayi kyau, Amma seka biyo agwagwa!'' Dan Ustaz ya kara fad'ad'a fara'arsa still hannunsa na kn gemunsa yace "Ainifin ni nan, ai matan aljanu sun mace a kaina yafi a kirga! Aiko knga ni din kyakyawa ne, knsan agwagwar larabawa Akwai kyau. '' Salwah ta zaro ido jin dan Ustaz ya ambato aljanu tace "wai! Aljanu fa kace dan ustaz?'' Daga mata kai yy alamar tabbatarwa ya hada da cewa "kwarai ma kuwwa hajiya karama..." Salwah ta jinjina kai tana me daria kasa kasa tace "kai dan Ustaz a rage na gobe...'' Dan ustaz ya hade rai ya wani sha murr, ya fara jawowa salwah ayoyi kn shi wai a dole malami ne baya karya, salwah se uban daria takeyi Dan Ustaz na mugun burgeta shi din akwai sani ne kuma akwai shagala. "Uhm dan ustaz inna biye maka semu kwana a nan bari in wuce kafin amihh ta fito...'' Cewar Salwah data karashe mgnr tana waiwayon kofar fitowa daga falon Amihh dan ganin ko zata fito, nan taga kofar ko motsi batayi, juyawa tayi cikin hanzari ta fara tafia da niyar tabar gurin, dan ustaz ya dakatar da ita ta hanyar cewa ''Dan dakata hajita keremarh wato ainifin inada mgna ne me muhimmanci dake...." Salwah ta dakata jin dan Ustaz yace mgna me muhimmanci tace "maza ka gayamin, bnso Amihh tazo ta ganni a nan..." Dan Ustaz yayi murmushi kana ya ci gaba da mgna "Ainifin nace dama, ina ita wannan yarinya me dankaran kyau?'' Salwah ta zubawa dan ustaz ido ta gano hilwah yake nufi amma tayi kmr bata gane ba tace ''wa kake mgna?'' Dan ustaz ya kara murmusawa yace ''Ainifin ina nufin wannan bakuwa taku me mugun kyaunnan, Wato anifin Wannan me kama da larabawar.." Salwah tace "ok Hilwah?'' Dan ustaz yayi jim yana me jinjina sunan hilwah a ranshi shi bema taba jin sunanta ba se yau, maimaita sunan ya shigayi a fili yana me kara jan gemun nasa, ysna murmushin jin ddh yaci gaba dacewa ''Hilwah! Hilwah ! Hilwah! Tebbas wannan suna nata ya dace da addinin musulinci kuma Ainifin ya dace da ita, Hilwah! Me kyau kenan a kalmar larabci aka masa kwaskwarima! Wayyo Allah na kaga zuciata, na kamu da kaunar wannan yarinya me Tsananin kyau irin na jinnul mahya..." Dan ustaz ys karashe mgnr yana daga knsa sama, ya hada hannayensa biyu alamar yana rokon ALLAH. Salwah data zubawa dan ustaz ido yanata hauka dan ita a ganinta hauka yakeyi. "Allah rabamu da jinnu, wannan fa mutum ce dan ustaz ba jinnu bace...." Dan Ustaz yayi murmushi harda farfar da kwayar ido yaci gaba dacewa ''Wato ainifin nasani, nasan ita mutum ce, kyauntane ya gigitani Masha Allah! ni de ina sonta Ainifin so na tsakani da ALLAH, wato ainifin nan Aurenta ma zanyi in kaita can kauyenmu mu raya sunnarh ma'aiki salallahu alayhi wasallam..." Salwah ta kara zaro ido waje tana kallon dan ustaz bata tabbatar beda hnkli ba se yau gaskia tama fara tunanin yanada takadda a gidan mahaukata. "Kai dan Ustaz ka kiyayi knka wlhy, hilwah kakeso,..'' Dan ustaz ya daga mata gira hadi da kama kugu kmr mace, damanshi d'abi'arsa kenan yace. " kwarai ma kuwwa, wato ainifin ni nan ba sonta nake ba kaunarta nakeyi....'' Salwah ta Kara zaro ido tace ''kai anya kuwa dan Ustaz kanka daya? Matar yah AB'ILAL dince kakeso?'' Dan Ustaz ya yatsina fuska jin ta kira sunan wani namiji wai AB'ILAL yace "Ainifin wa'izubillahi! Salamun salamun! Astagfurillahi! Wato nace waye kuma wannan gajan, ainifin da kk fad'a, to ko ya aureta seya saketa ya barmin ita ni in aureta, ainifin nake gaya miki sonta a raina ya hayayyafa yayi jikoki ya koma kaunah..." Salwah ta riqe baki, tana kallon Dan Ustaz yanata raftago zance na bnza da hofi, girgiza kai tayi, ta bude baki zatayi mgna taji an bude kofar falon Amihh, tasan Amihh ce ba tare data waiwayaba ta ruga a guje ta bar gun ta nufa side din AB'ILAL. Dan ustaz ya bita da ido yana yatsina baki, shifa harga Allah da gaske yake son yarinyarnan yakeyi. Hajiya maryam data turo kofar falon ta fito cikin sauri sauri take tafia, dan Ustaz ya rugo a guje inda take, ya tsugunna ya fara jero mata gaisuwa "Ainifin nace ina wuni hajajju mutanen mekkah ya aiyukan naki ainifin ya asibitin naku ya fama da marasa lafia na gida dana waje, ya dangi kuma ya yan uwa, ya qawayenki ya zirga zirga , ya hkri da hidima damu ma'aikata, ya kuma ita wannan yarinya me kyau, Wato ainifin hilwah, Ainifin nace hajiya ya danginku na can kasar saudi arebia..." Hajiya maryam ta saki baki tana saurarom gaishe gaishen dan ustaz ke mata na hauka, girgiza kai kawai tayi ta wulla


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login