Showing 21001 words to 24000 words out of 142497 words

Chapter 8 - NI DA YAYA SADAM Complete Document by Binta Umar Abbale.txt

09 Dec 2024

50457

yace."Auran ne bana so kawai shiyasa sam! bana d'okinsa har so nake lokacin tafiyar yazo in matsa in basu guri."


Captain Habu yace."Amma ka bani mamaki wallahi!!! Sadam! murmishi kawai yayi baice komai ba, Habu yace."In tambaye ka mana."
Yace."Ina sauraronka." Yace."Yanzu ya zakayi da Halima idan taji maganar auranka baka tunanin abinda zai faru da ita."?


Sadam! ya 'bata fuskarsa yace."Wai shin Habu ni nake son Halima ko kuma ita ke sona."!? Captain Habu yace."Itace take sonka." Sai ya d'aga kafad'a yana ya mutsa fuska yace."To kagani ni banda matsala tunda dai ni da bakina ba'a ta'baji nace ina sonta ba ballanta kuce na yaudareta itake yaudarar kanta tunda tasan ni ba mahaukaci bane da zan aureta bayan kowa ya mayar da ita rigar sanyawarsa Kawai ina biye mata ne saboda darajar son da take min wannan shine dalili."


Captain Habu ya girgiza kai yace."Tabbas to amma ni ina tunanin al'amarin da zai faru taji labarin auranka wallahi zata iya kashe kanta saboda bakin ciki."


Sadam! yasa dariya yana kallon abokin nasa yace."Na lura kana tausayawa Halima da yawa kaje kawai ka aureta na bar maka kai nifa har yanzu banga wata 'ya macen da zata ya mutsa min tunani ba wallahi idan ba Uwata ba bana daukar wata mace wani abu saboda dukaninsu basu da kirki.''


Sulaiman yace."Me yayi zafi kake wannan maganar mace ni'ima ce ga d'a namiji sa'ida ce kuma salama ce ba zaka san da haka ba sai ranar da kayi aure sannan zaka gane abinda nake so ka gane."


Murmushi kawai yayi Habu yace."Don Allah abokina ka dinga 'kimanta mata kuma idan na baka shawara ka dinga dauka kamar yanda idan ka bani shawara nake dauka."


Yace."To na dauka." Habu yace."To yanzu yaushe zaka kaini inga amaryar tamu."?


'Bata fuska yayi yace."Kaji ka da wani zance kuma ka bari kawai ai in an daura auran nan zan kawo ta kaduna."


Yace."A'a dole fa kafin daurin aure muje in ganta gaskiyar magana kenan.'' Okey Zamu je insha Allah sati me zuwa."! Habu yace."Allah ya kaimu lafiya." To da wannan magana sukayi sallama Captain Habu yayi masa sallama ya koma ofis din sa.


*****


Sulaiman kuwa bayan komawarsa Kaduna sai da yayi jinyar zuciyarsa na sati guda sannan ya shirya tsaf ya nufi kasar india domin cigaba da gudanar da harkokinsa na kasuwanci Sulaiman komai da ruwanka ne shi ko wace sana'a tashi ce ya fita 'kasashen waje da dama domin gudanar da harkokinsa shiyasa kullum Allah yake kara yalwata masa arzkinsa gashi yana d'an ta'ba siyasa in lokacinta yazo.
Da tunanin Sayyada ya nufi 'kasar hindu.


****


Sayyada fa ananan ana rawar kai da giringid'ishi kullum ana gidan Mariya ana maganar aure ita kuma mariyar in ta kad'a magani da madara na 'karin ni'ima sai ta tsiyayawa Sayyadar tace ta shanye duk sanda mijinta ya soma kwanciyar aure da ita zaji dad'inta aikuwa Sayyada ta bada himma har ta zo gida tana fad'awa Baba Ladi tace"Ta had'a mata maganin Ni'ima wanda Sadam! zai dinga gamsuwa da ita yayin kwanciyar aure.


Baba Ladi da Baba Marka suka dinga salati da sallalami! Baba Ladi tace"Don Ubanki a ina kikaji waannan maganar." ? babu kunya tace"Mariya ce ta fad'a mata. Tundaga ranar Baba Ladi ta hanata fita tace tana zuwa gidan Mariya tana koya mata rashin kunya.....Sayyada kam! tace"Lallai Baba kar! kar! nake kallon kowa idan Baba Ladi ta idar da sallahar walha bacci ya kwashe ta sai ta lalla'ba ta fice daga gidan bata dawowa sai yamma Baba Ladidi ta dinga fad'a kamar ta ari baki.


Suna zaune a tsakiyar dakin Mariya Ummi ta shigo sai suka hau shewa harda tafawa Ummi tace"Wace wainar kuke toyawa ne? Sayyada akayi wani fari da ido akace "Ke ma kin san wainar."! Ummi ta bata hannu suka tafa suna dariya.


Mariya tace" Wai Ummi kinji so ta take ta samu maganin da zai 'kara mata girman nono saboda tana so ya dinga cikawa angon nata hannu." Sai suka kwashe da dariya Sayyada tace"Wallahi da gaske nakeyi ni kunya nakeji duba fa ki gani nono kananu ne ko rigar nono bana sawa fa."


Ummi tace"Ke Dallah! banza kawai Wallahi ki kwantar da hankalinki nononki zai fito yayinda aka kai ki gidan miji shikkenan kullum idan yana ta'bawa shikkenan sai dai kiga suna girma sun cika riga." Sayyada ta bata hannu suka tafa tace"Da gaske kike don Allah."?
Ummi tace"Wallahi da gaske nake." Mariya tace"Hakane nima fa lokacin da aka kawo ni gidanan ba nonon arziki gareni ba amma ko wata uku banyi ba naga nonowana sunyi manya manya." Dariya sukayi suka tafa Sayyada tace"Wayyo Allah na ni wallahi har na 'kagara lokacin nan yazo wai don Allah Mariya yaya mutum yake ji idan yana sha'awar d'a namiji wayyo."!!!!!!!
Ta kare maganar tana kwanciya tare da lumshe ido.


Ummi tace"Kai! Sayyada gaskiya ke fitananniya ce anya kuwa."!?? Sayyada ta kai mata duka tana dariya tace"Ke sonsa ne kawai yayi min yawa shiyasa sai kunyi min uziri." Mariya tace"Wai yaushe zamu ganshi ne nifa ban san shi ba nafi sanin Yaya Sulaiman."! Ummi tace"Wallahi nima ban sanshi ba jikina na bani kyakkyawa ne dan gayu."


Sayyada aka lumshe ido ana murmushi mi'kewa tayi zaune tace"Sojana kenan." Suka kalleta gabadaya sukace "Au! Soja ne dama."!? Daga kai tayi tace " Eh mana ai ba zaku gane shi ba tunda ba sosai yake zuwa ba sannan kuma idan yazo baya dad'ewa yake tafiya watarana ma yini guda yake ya tafi sannan shi bashi da fara'a kamar Yaya Sulaiman kullum fuskarsa a murtuke take nima fa baya wani sakar min fuska."


Mariya tace"Ai dole mana Amina tace shi take so shegiya ni wallahi haushinta ma nakeji." Sayyada taja tsaki tare da fad'in"Rabu da tsinanniya kawai ai tuntuni na daina kulata."


Mariya tace"Kinyi min dai-dai 'kawata." Tafawa sukayi suna dariya *To ni dai fitowa nayi na barsu na lura hirar tasu ba zata 'kare ba*


*****


Sayyada sam! bata sanya Amina cikin sabgarta da kawayenta kawai take harka ko Aminar ce ta shigo kofar su Sayyada ba tayi mata kallon arziki Ballanta ta kulata Baba Ladi tayi mata fad'a har ta gaji......Wannan lamari na masifar 'batawa Amina rai! shin wai meye duniyar ne akan Namiji Sayyada duk ta tayar da hankalinta tana gaba da ita itafa bata zafafa ba duk da tana son Sadam! to idan shi baya sonta ya zatayi dole ta hakura kuma idan yace ba zai aureta ba nan ma dole ta hakura ta fito da mijin aure ita a ganinta wannan ba abun tayar da hankali bane.
To ammafa a cikin ranta tanan da wannan kudiri na duk sanda Sadam! d'in ya shigo garin zata sanar masa halin da take ciki a kansa tasan idan ya hadasu duka ya aura ai ba haramun ya aikata ba.


****


Saura Sati guda daurin aure Baba Ladi da baba Marka tsaye gaban wani katon turmi me zurfi ko wanne da ta'barya mai tsayi a hannunsa dagab tukud'i suke da gumbar mata.


Tsaf! suka daka suka kwashe sannan suka zauna zaman had'awa! lokacin Sayyada nacan gidan Mariya wai nan dilka ake da kurkur Mariya ta dage! tana wa Sayyada dilka wai lallai sai tayi kyau kafin Ranar daurin aure.


Amina ce ta shiga kofar taga abinda sukeyi tace"Baba Wannan meye?"? Baba Marka tace"Zaki san ko meye idan lokacinki yazo maza kije gidan Mariya ki kirawo Sayyada." Amina tace"To." Ta nufi gidan Mariya dake bayan layi.


Tsakar gida ta tarar dasu sunyi d'an malele da yaji da manja harda tumatiri da albasa suna sha suna dariya da hirar aure kamar yanda suka saba.


Babu wacce ta amsa gaisuwarta sai kallon banza da suka watsa mata Amina tace"Sayyada kije Baba Ladidi na kiranki." Ta juya zata fita Sai taji Sayyada na kwaikwaiyar maganar ta da hanci "Wai Sayyada kije Baba Ladidi na kiranki yan! yan! yan!!!!! Ta juyo tana kallonsu sai suka kwashe da dariya Amina ta bar gidan da sauri takaici kamar ya kasheta wai Sayyada ce take biyewa wasu bare suna wulakantata......Sayyada ta wanke hannunta tare da zura hijab dinta tace" Bari naje na dawo yanzu." takalmanta tasa ta fice daga gidan.


Amina ta hango tana tafiya so take ta isketa har inda take ta ci mata Uwa! tana karya kwana taga motar da ya saba zuwa da ita garin tayi parking irin motocin nan ne na gurin aiki.Kafin ta an kara Taga ya fito daga motar tare da Abokinsa sai gabanta ya hau dukan uku uku! ta hau kallon jikinta wani ko d'ad'd'an zanin atamfa ne a jikinta da wata t_shirt mai karamin hannu kanta ko d'ankwali babu sai hijab data zurma "Wallahi ba zai ganni a haka ba." a fili tayi wannan maganar la'bewa tayi tana le'kensu inda taga Amina ta iskesu ta tsuguna har 'kasa ta gaishesu, girgiza kai tayi haushi ya turnuketa tana kallon sanda Yake amsawa yana mata dariyarsa mai tsada Sayyada kamar ta kurma ihu! sai cije baki take tana gyada kai tana kallonsu suka nufi cikin gidan tare........Sai bayan taga shigewarsu ne sannan ta fito daga inda ta 'buya. Gidan ta nufa duk ranta babu dadi.


6/6/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
*NI DA YAYA SADAM!!*
👫👫


*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*


*🌍MANAZARTA*
*WRITES ASSOCIATION🖊📚*
*M.W.A*

_'Kungiya d'aya tamkar da dubu, masu nazari da aiki da Iliminsu burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishad'antar da masoyanta._
__________________________________


*Free Pege 13*
Cike da farin ciki Baba Marka take fad'in"Sannuku da zuwa sannu kunsha hanya ashe dai angon nawa yana tafe da har ina cewa zanzo biko ashe dai ana sane dani." Tabarma ta shimfida musu suka zauna Captain Habu sai murmushi yakeyi karamcin matar ke bashi sha'awa gaisawa sukayi a mutunce tana tambayar mutanan gida Sadam! ya kalli 'kofar dakin Baba Ladidi yace."Ina sauran mutanan gidan suke."!? Baba Marka tace"Baba Ladidi dai bata dad'e da fita kasuwa ba ita kuma Sayyada yanzu yanzu na aika kiranta tana gidan Kawarta Mariya." Ta kalli Amina dake tsaye tace"Ina Sayyadar."? Amina tace"Tana kan hanya." Kafin Baba Marka tace wani abu Sayyada ta shigo bakinta dauke da sallama.
Baba Marka tace"Yawwa gatanan ma." Sayyada ta karaso inda suke fuska babu yabo babu fallasa take gaishe su, Sadam! ya kalleta yana wani ya mutsa fuska sam! bai amsa gaisuwar ta ba Captain Habu ne ya amsa da fara'a a fuskarsa Sadam yaji takaicin yanda Habu yaga sayyada kaca-kaca duk da cewar bai tabbatar da cewar itace ba.


Dakin Baba Ladidi ta shiga ta cire kayan jikinta dogon hijab ta sanya har kasa ta fito kai tsaye bakin rijiya ta nufa ta jawo ruwa cikin rijiya bandaki ta nufa tayi wanka tana fitowa idanunsu suka game da juna yayi saurin kauda kansa yana kur'bar damammiyar furar da Baba Marka ta damo musu


Baba Ladidi ce tayi sallama ta shigo hannunta rike da wani buhu mayafi a saman ka tace"Ai tunda na doso bakin layi na hango motar sojoji a kafe nace to Soja yazo ganin amaryar tasa." Ta karashe maganar tana dariya hade da kokarin aje buhun a gefe ta cire mayafin dake saman kanta tana fad'in"Ai fa wannan ranar dama nasan dole ne ta tambaye ni." Baba Marka tace"Ai sai da na fad'a miki cewar ki bari ranar tayi sanyi in yaso sai ki tafi."


Ya d'ago kansa a nutse yana kallonta yace."Wai shin ma ina taje da wannan ranar."!? Baba Marka tace"Haba kaiko sai kace wani kurma kana ji fa nace kasuwa ta tafi."


Ya kalli Baba Ladidi dake firfita da mafici yace."Baba ashe dai baki fasa yawon kasuwar nan ba ko."!?


"Oo! ni ba abinda kake tunani ne ya kaini kasuwa ba ato tawa ce ta kaini ta wani gefan kuma sai in ce ta dalilin ka na shiga kasuwar."


Ta'be bakinsa yayi ya mayar da kansa 'kasa Baba Ladidi ta washe baki tana kallon captain Habu tace"Ashe tare kake da ba'ko sannu da zuwa samari ya mutan gida da fatan duk sunannan lafiya ko."?


Captain Habu yace."Kowa lafiya lau ai sunce ma a gaisheku da kyau."!


Baba Ladidi tace" Alhamdullhi ." Sai ta fara zazzage abinda ke cikin buhun tana dubawa tace"Kinga na samo saiwowin maganin nan da duk abinda ake bukata saboda haka yanzu yanzu zan sanya 'Dantani ya yanka min kazar."


Baba Marka tace"Hakan yayi sai ya had'a da Zabi gudu uku ya yankawa ba'ki ayi musu miya ko."!?


Tace"Kwarai kuwa kinga kuwa naga kayan miya masu kyau a kasuwa wallahi wannan ranar da ake kwalawa itace ta hanani na tsaya na siyo."


"Aifa! gwara da kika nufo gida a aika Dantani ya siyo yanzu." Baba Marka tafada tana kokarin mikewa mayafi ta dauko jikin kyauran dakinta ta yafa ta fito tana fad'in"Bari in kira Dantani d'in nasan dai yanzu ya dawo cin abinci daga gurin sana'arshi."


Har ta kai kofar fita Baba Ladidi tace"Wai Ina Sayyada ne? ko bata dawo daga gidan kawar tata ba."


Marka tace"Shigowarki ta shiga daki tana ciki tana jinki." Labule ta d'aga ta fito


Tana sanye da riga da siket na atamfa soso tayi wata irin kwalliya ta d'ige-d'ige a da kwalli kumatunta da saman goshinta sai le'banta data mulke shi da jan janbaki fuskar nan jazur da jar hoda abinka da farar fata. kanta babu dankwali sai ubangashi data daure shi a tsakiyar kai yana reto ga wani uban kyalli da yake saboda man data lafta masa


Sadam! na ganinta ta fito a haka ransa ya 'baci indai ba idonsa ne ke masa gizo ba har cibiyar ta sai da ya hango lokacin da take kokarin zama kusa da Baba dake rigar karama ce sannan hannunta me fad'i ne wanda tana d'agawa za'a iya ganin hamtarta Gashi kanta babu dankwali duk ta fito da surar jikinta, Rai a 'bace ya daka tsawa tare da fad'in"Maza ki tashi ki sanjo kaya wannan ai sun matse ki sannan dake ke mara hankali ce kin fito babu dankwali wai ke kinyi ado."


Cikin jin haushi ta watsa masa harara! ta dauke kanta tana zumbura baki.


Baba Ladidi tace"Dad'ina da kai kenan kai ba'ayi maka gwaninta a maimakon ka yaba da kwalliyar da tayi maka sai ka kushe hakan bai dace ba." Ta kalli Captain Habu tace"Don Allah ka dinga bawa abokinka shawara ya rage fad'a! da jarabar masifa yarinyar nan dai marainiya ce."


Captain Habu yayi dariya yana d'an kallon Sayyada ta 'kasan Ido gaskiya abokinsa yayi dace da mace nan gaba kad'an yasan yarinyar zata zama cikakkiyar mace.


Yace."Muma can gurin aikin haka muke fama dashi Baba Sadam! din ne ai ya cika zafi shiyasa ko a filin daga! ba'a cin galaba a kanmu."!


Baba Ladidi tayi dariya tana fad'in"Ai filin ya'ki daban damu da iyalinsa bana so a daura aure yazo ya tsawalawa yarinyar mutane."


Captain Habu yace."Karkiji komai Baba insha Allahu zamu rike Sayyada da kyau da kulawa." Baba tace"To nagode Mai gidana na kaina."!


Mikewa tayi ta shige d'aki Sayyada ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da 'yan ya tsunta na hannu Sadam! sai dalla! mata harara yake yana ya mutsa fuska. Shi ko Captain Habu sai janta yake da wasa tana murmushi.


Tsaki yayi yace"Wai don Allah Captain me ka hango naso a jikin wannan yarinyar ne? dube ta da kyau ka gani in banda iyaye iyayene Allah da ba zan takurawa kaina ba Duk tsiya nasan Halima ta fita komai da komai."!!!


Sayyada ta d'ago kai ta kalleshi ranta ya 'baci idanunta suka kawo ruwa wacece kuma Halima? Captain Habu ya 'bata fuska yana fad'in"Aboki meye haka wannan ai cin fuska ne." Sadam! ya kauda kansa gefe waya ya ciro yana dubawa


"Kiyi hakuri kinji amarya." Captain Habu ya fada da kokarin ganin ta saki fuskarta, Kallonsa tayi tace"Abokinka yace bai ga abinso a tare dani ba Allah yasa bashi kad'ai gareni ba ko yanzu yace baya so akwai dubanninsa masu so saboda haka nima ba wai sonsa nake ba Umarnin magabatana kawai nake bi." Tana gama maganarta ta mike ta shige daki hijab ta zura ta fito Baba Na daki tana fad'in"Sayyada kar ki fita ina zakije dawo ki shanye maganin nan na dama miki kar ki fita fa."


"Baba nifa na tafi gidan su Ummi domin ba zan zauna a cikin gidan nan ba mutukar yana cikinsa sai ya tafi na dawo." Tana gama maganarta ta fuce daga gidan cikin bakin ciki da takaici, tana daf da fita babban soro suka ci karo da Amina hannunta rike da wata leda da alama daga shagon Magaji take lemon kwalba ne fenta da mirinda ta siyi da sanyi 'kara-'kara!! Sayyada ta tare mata hanya rai a 'bace tace"Dama neman ki nake.


Amina tace"Menene kuma."!? Sayyada ta rike 'kugu tana fad'in"Tambaya ta ma kike menene lallai ma Amina! dan kutumar ubanki wannan lemon ubanwa kika siyowa? Amina tace"Kar dai ki sake ki zageni Sayyada lemo kuma babu ruwanki da wanda na siyowa! Wallahi sai naji Uban da kika siyowa lemo sannan me zakiyi idan na zage ki." ? Amina tayi murmushi tana kokarin ratse ta ta wuce tace"Ni dai ba karya bace da zan zauna ina haus........Ai kafin ta 'karisa Sayyada ta buga tsalle ta kaud'a mata mari! "Nice karya dan babanki." Sai ta wafce ledar hannunta a take kwalbar lemukan suka fashe lemon ya zube a kasan gurin......Kwalbar lemon da ta fashe ta d'auka tayi kan Amina tana huci! wallahi sai nayi miki zane a fuskarki ni zaki kira karya ki shiga gonata ki kirani karya lallai Amina kin ta'bowa kanki bala'i! Amina da taga Sayyada na nema ta lahanta ta sai ta fara neman hanyar tserewa Sayyada ta jawo hijab dinta wanda gari jawo hijab din ta taka karamar kwalba a take ta huda mata kafa amma ko a jikinta kokari kawai take tayiwa Amina zane a fuska.....Ihu! Amina take tana fad'in "Wai Sayyada ke mahaukaciyar ina ce ne? me nayi miki.? A fusace tace" Mahaukaciyar gidaj Ubank....Kafin ta karasa taji saukar mari a fuskarta Yana tsaye ransa a 'bace yace"Sakar mata hijab." Sai ta rushe da kuka tana fad'in"Ai kamata yayi kafin ka yanke hukunci ka tambayi ba'asi kawai sai ka mareni alhalin itace da rashin gaskiya." Hararta yayi yace"Ban tambaye ki komai ba saketa ki wuce cikin gida." Sayyada ta sakar mata hijab Ya kalli Amina dake motsa baki yace."Ke Amina meye ya had'aku."? "Wallahi Yaya Sadam! ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login